Free chapter · Read without an account

Alhaji Muntari

by Azizat Hamza · ZAYTOONAH


*Chronicles of*

*...... ...... .......ZAYTOONAH*


Rubutawa.....Azizat

Wattpad@Azi_zat

*Free page*

*12-Muntari*

Bismillahir Rahmanir Rahim

Murmushi na jin daɗi yai lokacin da ya kalli plan ɗin gidan da ake gina ma sa.

Aljannar duniya zai gina ma ta, shekaru shabiyar da yai yana shan wahala yana fama da jure zama da Madam Talatu wacce ko sau ɗaya ba ta taɓa burgeshi ba, yayi komai ne domin ta kuma ya tabbata yanzu ya mallaki abinda ko Tijjani zai shekara talatin yana aikin albashi ba zai samu rabin kuɗin da ya ke da shi ba.

Saura lokaci kaɗan ya koma gareta, ma su ginin sun ce ma sa cikin wata biyu za'a kammala komai. Ba shi da matsala da wannan zai iya jure wata biyun nan, musamman ma da ya ke da yaƙinin kafin wata biyun nan za ta kasance cikin kaɗaici, cikin tsananin buƙata...

Ba ƙaramin kewar mijinta za ta yi ba idan ya tafi, ɗawainiya zai ma ta yawa idan baya nan amma tafiyar tana da muhimmanci. Gwamnatin tarayya ne ta turashi Oxford dan yai digirin digirgir wato Phd na shi.

Tun kwana uku daya wuce ta gama haɗa ma sa kayan sa, tafiyar kawai ake jira. Daɗinta ma ranan tafiyar zai faɗo a kwananta ne.

Wani littafi ta ke karantawa lokacin da Salman ya shigo ɗakin da gudu.

"Mommy..."

"Ba na hanaka shigowa ɗaki ba sallama ba?" Ta daka ma sa tsawa

Salman da gulma ke cinsa ya koma bakin ƙofa da sauri yai sallama. Maryam ta amsa ta ce ya shigo,

"Mommy Adaeze is eating cake in the kitchen"

"O'o ni 'yar nan ina za ta kai kwaɗayi ne" ta furta a fili tana miƙewa tsaye, ta bi bayan Salman da ya fita da gudu yana so ya ga yadda Mommy za ta punishing yayar ta sa.

Cake ne Mommy ta yi saboda birthday ɗin Salman da za ayi nan da kwana bakwai amma saboda tafiyar Daddyn su shiyasa za ayi shi gobe. Da safe ta baking cake ɗin akan da yamma zuwa dare za ta decorating ɗin sa ashe acicin gidan ta je ta hau kai.

A karo na biyar Zaytoonah ta sake buɗe fridge ɗin ta ɗauko cupcake ɗin da ke ciki, wai za ta yiwa Mommy wayo sai ba ta taɓa babban cake ɗin ba amma cupcake guda shida da ke kusa da shi duk ta rarike sama saman ta cinye.

Wannan karan za ta cinye ɗaya ne idan Mommy ta tambaya ta ce guda biyar ne ba shida ba.

Tana cikin ci ta ji an ja kunnenta ana murɗawa. Tsabar daɗin cake ba ta san yaushe Mommyn ta shigo kitchen ɗin ba.

"Ba kya jin magana Zaytoonah, sau nawa ina hanaki ɗaukan abu ba tareda kin tambaya ba"

Zaytoonah ta ɓare baki sai kuka shi kuma Salman sai dariya ya ke ma ta.

"Na hanaki kwaɗayi Zaytoonah ba kya ji. Do you want me to beat you?" Tana maganar tana cigaba da murɗa ma ta kunne

"Kin fara ko, kin fara ko" ta tsinkayi muryan shi a kitchen ɗin.

"Kai ka ke ɓata yarinyar nan, jiba yadda ta dawo fa, kalleta fa"

Ya kamo hannun Zaytoonah yana tambayar miya faru. Salman ya shiga ba da bahasin abinda Zaytoonan ta yi.

T J ya je ya buɗe fridge ɗin ya ɗauko cupcake guda biyu ya miƙa ma ta ya ce "dena kuka kinji, zo mu je ki ci wannan idan bai isheki ba zan ƙara miki"

Aikuwa ta dena kukan da ta ke ta karɓi cupcake ɗin ta fara ci. T J ya ja hannunta su ka bar wajen.

Maryam ta girgiza kai kawai ta koma wajen fridge ɗin dan taga ta'adin da Zaytoonah ta yi. Ta ci sa'a ma ba ta taɓa cake ɗin birthday ɗin ba...

Da dare tana decorating cake kusan ƙarfe takwas na dare sai ga T J ya shigo yi mu su sallama dan ba a gidan ta zai kwana ba.

"Sannu da aiki Uwargida ran gida"

"Sannu da lallashi" ta faɗa tana murmushi

Ya lakato buttercream icing ɗin a hannun sa ya lashe.

"Dear kai dai da shan zaƙi"

"Ya zanyi, abinda ya fito damu daga ƙauye kenan"

Dariya ta fara shima ya tayata yi.

"Zan missing ɗin ku sosai Maryam" ya faɗa bayan ya dena dariyan

"Muma haka"

Shiru ne ya biyo bayan abinda ta ce. Sai chan T J ya ja dogon numfashi ya ce

"Maryam ba dan hali na ba, ba kuma dan halin Iya ko Hajjo ba Dan Allah zan bar miki amanar Humairah da Sadiq musamman ma Sadiq, ki yi haƙuri ta kula min da su"

Shekara ɗaya bayan Maryam ta haifi Salman Hajjo ta sake haihuwa itama ta samu Abubakar Sadiq kuma still shi ɗin ma Sickler ne, sai dai shi har yanzu yana raye. Shekara biyun farko sun ɗauka ba zai yi rai ba dan yadda ciwon sa ke tashi a kai-a kai amma yanzu da ya cika shekara uku abin ya zo ma sa da sauƙi dan yanzu ma ana son sashi a makaranta idan an shiga sabon term.

Bayan haihuwan Sadiq T J ya kai Hajjo aka ma ta planning saboda yadda Hajjo ke saurin ɗaukan ciki ba zai juri samun 'ya'ya SS ba, yaro ya wahala suma su wahala.

Murmushi ta yi ta ce " kar ka damu, Allah zai kula maka da mu gabaɗaya har ka je ka dawo"...

***

Bayan tafiyar T J gidan ya ma ta faɗi. A da kullum sai ta gan shi, ko da ba ita ke da girki ba zai zo ya duba ta da yaran da safe da kuma dare wani lokaci har da rana amma yanzu shikenan ba za ta sake ganin sa ba har sai ya shekara. Ya ce zai yi ƙoƙarin zuwa mu su bayan wata shida amma ta sani da wahala hakan ya yiwu.

Yaran ma kewar sa da su ke yasa kwana biyu sun nitsu ba sa damunta da rigima. Zaytoonah kuwa ta zama babbar banza dan kukan rashin Daddynta da ta ke yi ƙaninta Salman bai yi ba.

Kullum sai ta tambayi saura kwana nawa Daddy ya dawo Maryam ta ce ya kusa dawowa.

Bisa amanar 'ya'yan sa da ya bar ma ta koyaushe tana zuwa gidan Hajjo ta duba su. Iya dai har yau ba ta amsa gaisuwan Maryam itama Maryam ɗin tana yi ne kawai dan ta fita hakkin ta.

Humairah kufulancin Iya ta ɗauko shiyasa ba ta son Zaytoonah da Mommy kaman yadda ake kiran Maryam. Shi kam Sadiq da ya ganta zai fara murna.

Makaranta ɗaya Humairah su ke zuwa da Zaytoonah amma ajin su ba ɗaya ba, duk da haka ba sa jituwa.

Wani lokaci idan Maryam ta yi abin marmari tana aika mu su ta ce a bawa yara.

Iya a ba ta son Maryam ɗin still idan Hajjo ta yi kaso ba ta raba da ita ba za ta ce ina nata. Hajjo kuwa sai ta ma ta tsiya kafin ta ba ta, dan ba ta da zuciya haka za ta ci. Ana kawo abinci daga gidan Maryam za ka ji falon ya buɗe da ƙanshi mai daɗi.

Ita kuwa Maryam kullum ta zo sai ta yi mamakin yadda su ka fara ɓata gidan T J. Falon gaba ɗaya ba kyan gani, ga wani wari-wari da ake ji ta rasa na minene, banɗaki da ba sa wankewa akai akai ne ko na rashin shara da moping da ba sa yi. Daga ka ga rigan yara a kan kujera sai ka ga an bar kwanukan da aka ci abinci ba a tattare ba. Wani lokacin ruwa ko kunu zai zube ba za a goge ba.

Tunda su ka raba gida indai T J zai yi baƙo ko gidan Maryam zai saukeshi ko da ba ranan girkinta ba ne idan ba hakan yai ba ba ƙaramin kunyata shi Hajjo za ta yi ba...



Tafiya ta ke da sauri sauri kaman za ta kife, so ta ke ta yi sauri ta kai abincin ta koma su ci na su abincin. Tsoronta kar kafin ta dawo sun kusa cinyewa.

Tana riƙe da kwandon abinci ta yi sallama sannan ta tura ƙofar falon gidan.

Iya ce a falon da Humairah su na kallo Iya na yiwa Humairah tsifa.

Ta tsani Iya, ba ta son ganinta ita ba dan Mommy ba ba abinda zai sa ta dinga zuwa gidan.

Ta ƙariso wajen glass centre table ɗin da ke falon ta ajiye kwandon abincin. Ta juya za ta tafi Iya ta ce " zo nan"

Zaytoonah ta juyo ta ƙura ma ta ido.

"Shegiya haka uwar ki ta koya miki rashin kunya ki shigo ba za ki gaida ni ba"

Ta turo baki ta ce "ni ba shegiya ba ce"

Iya ta tashi za ta make ta sai Zaytoonah ta sa gudu za ta fita sai gashi ta buge kwandon da ta ajiye a center table dama a baki-baki ta ɗokana shi.

Miyan dai sai gashi ya zube

"Iya ki ga ta zubar mana da abinci" Humairah ta faɗa kaman za ta yi kuka

Iya ta ƙarisa ta damƙo Zaytoonah ta wanketa da mari. "Ba ki da hankali ko?"

Zaytoonah ta fashe da kuka

Hajjo da ke ɗaki ta leƙo tana Hamma. Gandar girki ta ke yi shiyasa ta zauna a ɗaki tana tsammanin girkin Maryam dan ta san yau Jummu'a jazaman ne za ta aiko mu su da abinci.

Tunda Sadiq ya ce ta dinga kawo mu su abinci kullum saboda abincinta ya fi daɗi yanzu kusan kullum sai ta kawo mu su. Idan ba a kawo na rana ba za a kawo na dare wani lokaci da na rana dana dare duk tana aikowa.

Ganin abinda ya faru ne ya sa Hajjo ta ja tsaki ta ce " yanzu gaba ɗaya miyan ne ya malale?"

Humairah ta ce "akwai saura kaɗan"

"To wallahi ku ɗebe dan ba zan sake wani miya ba"

Iya ta zunguri ƙeyar Zaytoonah ta ce ta wuce ta ba su waje. Zaytoonah ta fita tana kuka.

Sai da ta kusa isowa gida ta ƙara volume ɗin kukanta, daga bakin ƙofa Auwal ya jawota jikin sa yana tambayan miya faru.

Ganin Mommy ta tsura ma ta ido ya sa ta ce "Iya ce ta mare ni"

Maryam ta san ba za ta yi ƙarya ba dan ba tarbiyyan da ta mata ba kenan. Amma kuma ba abinda za ta ce tunda ta san anyi hakan ne dan ta yi magana.

Maryam ta ce"Je ki wanke hannu ki zo mu ci abinci"

"Mommy" ta faɗa tana fashewa da wani sabon kukan

Maryam ta ce Auwal ya saketa ya zo su ci abinci. Tarbiyyan da ta ɗaura mu su shine dukkan su suke haɗuwa su ci abinci a tray ɗaya, ko T J na nan ma duk ranan girkinta indai yana nan dukkan su ke haɗuwa su ci abinci tare. Indai ta ware mu su abinci to Zaytoonah ne ta dameta da kukan yunwa sai ta zuba ma ta nata. Wani lokaci bayan taci idan sun zo za su ci na su itama za ta sa hannu a ci da ita.

Tana tsaye tana kukan sakalci ta ga Mommy ta serving abincin sun fara ci.

Ta dinga bin bakin su da kallo yadda su ke cin abinci hankali kwance, ganin Salman ya ɗau ƙatuwar hanta yana ci hakan ya sa ta ka sa haƙuri ta zo da gudu ta zauna. Za ta sa hannu Maryam ta daka ma ta tsawa dan haka ta yi hanyar kitchen a ɗari. Da ta dawo kuwa ta fi kowa ƙaton loma tanaci da sauri-sauri kaman abincin zai ƙare.

Tuwon shinkafa da miyan egusi daya ji naman kayan ciki da pomo ne sai ƙanshi miyan ke yi.

"Zaytoonah ki ci a hankali mana"

Auwal ya faɗa yana kallon yadda ta ke zare ido saboda ta cika bakinta da abinci kuma tuwon da zafi.

"Bar ta, idan ta ƙware za ta yi hankali"

Maryam ta faɗa tana kau da kai shi kuwa ya miƙo ma ta ruwa a kofi ta karɓa ta kora...

Tundaga marin da Iya ta ma ta ta dena kai abinci gidan, idan an bata abinci sai ta fita da shi sai ta tsaya a ta lungun da Almajirai ke zama suna cin abinci ta juye mu su sai ta ɗan tsaya kaɗan kafin ta wuce gida. Wani lokaci idan ta juye abincin a kwanon almajiran ko kafin ta juye taga nama dumu-dumu sai ta tsaya ta zaƙolo naman da ke ciki ta ci kafin ta juye mu su ta wuce gida.

Ta sawa ranta ba za ta ƙara kai wa su Iya abinci ba.

A ranan na huɗu ne da Maryam ta je duba su Sadiq sai Hajjo ke ma ta habaici wai dan ta ga Sadiq ya damu da girkinta ne shine ta ke ja ma sa rai kafin ta aiko. Ta yi maganan ne saboda missing daddaɗan girkin Maryam da su ka yi cikin kwanakin.

Maryam ba ta gane zancen ba amma ta dake ta ce "Sadiq duk lokacin da ka ke son cin abinci ka zo gida ka ji" yaron ya gyaɗa ma ta kai. Dama yana son zuwa Hajjo ke hanashi, ita a nata tunanin idan ya je ya ci a gidan Maryam ba za ta aiko musu ba. Tunda dai abincin da ta ke aikowa ba abincin da Sadiq kaɗai zai ci ba ne tunda ko tuwo ne leda biyu manya ta ke sawa.

Zuwanta gida ta samu Zaytoonah na yin assignment a falo.

Sai da ta zauna ta ce " Adaeze zo nan"

Zaytoonah ta taso da sauri dan ta san indai Mommy ta kirata da Adaeze ko Princess to za'a lallasheta ne da abun ƙwalama. Ɗazu da rana ta fasawa Mommy plate sai Mommyn ta sa ta kneel down ta ɗaga hannu ta rufe ido na kusan minti shabiyar.

Maryam ta ɗaura Zaytoonah akan cinyarta tana shafa kitson chuku da aka ma ta wanda jelar sa ya sauka har kafaɗanta. Maryam da T J duka suna da gashi sai dai Zaytoonah yanayin gashin T J ta ɗauko baƙi mai tsantsi ba kaman na Maryam ɗin da ya ke brown kuma kinky hair ba.

"Adaeze a wa kike kai wa abinci idan na aike ki gidan Iya?"

Nan da nan idonta ya kawo ruwa.

"Ban ce ki min kuka ba, gaskiya kawai za ki gaya min. Idan ma kin yi ƙarya zan gane kuma dukan ki zan yi"

"Mommy i'm sorry" ta faɗi tana fashewa da kuka

"Zubar wa ki ke yi?"

Ta yi saurin girgiza kai

"Ya kike yi da shi?"

Sai da ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce "Almajirai na ke kai wa"

Maryam ta ƙura ma ta ido dan ta gane ko ƙarya ta ke ma ta amma gaskiyar ce dai ta faɗa. Ta sani saboda abinda Iyan ta ma ta ya sa ta ɗau wannan matakin. She wont blame her tunda Iya ce ta creating wannan ƙiyayyar tun farko.

Ta sa hannu ta goge ma ta hawaye ta ce shikenan daga yau za ta dinga aikan Auwal idan baya nan za a nemi ko Almajiri ne ya kai mu su. Zaytoonah ta gyaɗa kai...

***

"Maman Bola, Maman Bola" Humairah ta dinga faɗi lokacin da su ka fito daga cikin school ɗin za su je wajen Manu mai mashin wanda ke kawo su makaranta.

Maman Bola suna ne da wata 'yar ajin su Zaytoonan ta sa ma ta saboda kullum itace da takarcen ciye-ciye idan ta zo school. Tsab-Tsab za a shiryata zuwa makaranta amma kafin a tashi ta ɓata jikinta. Idan ba ka ga uniform ɗin ta ya yi dumu-dumu da kayan ƙwalama ko maiƙon abinci ba zaka ga ya ɓace da ƙasa. Tana zaune a aji tun ma kafin a fita break za ka ga ta fara buɗe food flask ɗinta tana cin soyayyen dankali ko ƙwai, idan ta ɗebi loma ɗaya biyu ta ga za a ganta sai ta yi saurin rufewa ta goge hannunta na maiƙo ajikin uniform ɗin. Zaytoonah kenan.

Humairah ba ta san da sunan ba sai da yau suna fitowa Habiba 'yar class ɗin su Zaytoonan ta kira ta dashi. Shine kuma Humairan ta samu sai tsokanarta ta ke yi. Zaytoonah ba ta kulata ba dan Mommy ta hanata dukan Humairah kullum ta kawo ƙaran ta sai ta riƙa cewa ita ce Babba ta yi haƙuri. Ita kuma Maryam ba ta son ƙara ingiza wutar gaban da Iya ta kunna ne tsakanin yaran.

Daidai wajen ɗalibai dayawa da ke jiran a zo a ɗaukesu Zaytoonah ta yi wuf ta cire hulan Humairah. Ƙitson chuku aka ba su a satin kuma shi ke kan Humairan amma da ke ba ta da gashi sai chukun ya ƙi haɗuwa balle ma har a haɗe shi a dunƙule kamar yadda na Zaytoonah yai.

Zaytoonah ta fara " ku ga Humairah me ƙwaƙwuyayyen gashi, ƙwaƙus, ƙwaƙus ƙus, ƙus, ƙus"

Haka ake tsokalar yaran da ba su da gashi a class na su kuma abun na sosa mu su rai har ka ga suna kuka, wani lokaci sai Aunty ta tsawatar ake denawa.

Itama Humairan kuka ta fara musamman da ta hango wasu ɗaliban sa'anninta na dariya.

Har Manu ya saukesu Humairah ba ta dena kuka ba. Ta shiga gida da gudu tana kuka, straight ɗakin Iya ta wuce tunda ba ta ganta a falo ba...

Mommy ba ta dawo daga office da wuri ba yau dan haka gidan maƙotan su Maman Fawaz su ka wuce dan su jirata, da ke Auwal sai ƙarfe biyu zai dawo saboda a JSS 2 ya ke. Idan kuma ya rigata dawowa zai karɓi key a wajen Maman Fawaz ya buɗe mu su gidan.

Su na zaune a falo suna wasa da yaran Maman Fawaz ɗin sai ga Iya ta yi sallama hannunta riƙe da Humairah.

"Iya ga ta nan, dama nan su ke zama idan Mommyn su ba ta nan" Humairah ta faɗa tana nuna Zaytoonah.

"Zo nan dan Uwar ki"

"A'a Iya ke ce a gidan na mu" Maman Fawaz ta faɗa da fitowanta kenan daga kitchen.

Ba ta kula Maman Fawaz ba ta je ta finciko Zaytoonah.

"Dan Allah ki yi haƙuri kin san sha'anin yara..."

"Ba ruwan ki jikata ce" Iya ta katseta

Zaytoonah na kuka haka Iya ta ja ta su ka bar gidan. Direct gidan Hajjo su ka wuce wanda tun a hanya Iyan ke ta surfa masifa.

Suna zuwa kuwa ta ɗauko almakashi ta danneta ta fara aske ma ta gashi tana faɗin gaba ta ƙara yiwa Humairah Shalele dariya ƙwandala za ta ma ta.

Humairah na dariya ganin yadda dogon gashin Zaytoonah ke zubewa a ƙasa.

"Iya kin san dai Maryam ba za ta yi shiru ba ko?"

Hajjo ta faɗa bayan ta fito daga kitchen jin kukan Zaytoonah.

"To ko Ubanta yana nan ya isa yai magana balle uwarta Inyamura"

Hajjo ta taɓe baki ta koma kitchen ɗin. Jikarta ce dan haka ba ruwanta da abinda ta ke yi.

Bayan ta aske gashin wanda ya saura kaman irin low-cut ɗin nan sannan ta riƙe kunnen ta ta ce " duk ranan da kika sake tsokanarta sai na ɓaɓɓallaki"

Har gara Salman sau dubu a wajen Iya akan Zaytoonah wacce kamanninta da Maryam ya ƙara sa ma ta baƙin jini a wajen Iyan. Banbancinta da Maryam kawai farin fata ne wacce ita Zaytoonan ta ɗauko baƙin fatan T J.

Da gudu Zaytoonah ta fice a falon wanda tsabar bata ganin gabanta sai da ta bugu da ƙofa. Ko zafin bugun bai dameta ba ta fice daga gidan tana kuka.

A hanya ta haɗu da Auwal da ke shirin shiga gidan Maman Fawaz.

"Zaytoonah wa ya dake ki? Ina ki ka je? Iya ce ta dake ki ko Umma Hajjo?"

Duk tambayoyinsa ba wanda ta amsa ma sa sai kuka kawai...

A bakin ƙofa ta tsaya tana kuka tana jiran Mommynta, Auwal yayi-yayi ta shiga gida ta ƙi dan haka shima ya tsaya bakin ƙofan yana cigaba da lallashinta, shi bai ma lura da kanta ba saboda akwai hula a kanta.

Salman ma ganin yadda Zaytoonah ke ta kuka ya sa shi fara kukan, su na yawan faɗa da Addar ta sa amma yana son ta sosai.

A haka Maryam ta dawo daga office kusan 2:30pm ta same su.

Tana saukowa daga mashin Zaytoonah ta je ta faɗa jikinta tana kuka tana Mommy.

"What happened?. Auwal miya sameta?"

"Nima ban sani ba amma ina tunanin Iya ce ta dake ta"

Ta ɗan sunkuya dai dai tsayin Zaytoonan ta ce " Adaeze waya dake ki?"

Zaytoonah ta sa hannu ta cire hulan kan ta tana cigaba da kuka.

"Iya did this to you?"

Ta gyaɗa ma ta kai.

Rarrashinta ta fara yi amma inaa ta ƙi yin shiru hakan ya sa ta ɗauketa duk da girmanta a hakan ta shiga da ita cikin gida.

Yau duk kayan ƙwalamar an ma ta tayin su ta ƙi ci sai kuka. Daga baya ne ma Maryam ta lura da fashewar da gefen goshinta yai. Ta goge jinin da ya bushe ta shafa ma ta magani.

A jikinta ta kwanta tana shafa bayanta har ta yi bacci, sannan ta kwantar da ita a gado.

Ranta idan yai dubu to ya ɓaci, ba za ta bari a cigaba da cin zalin 'yar ta ba dan haka ta wuce gidan Hajjo cike da ɓacin rai.

Spaghetti ce akayi dafa dukan ta wanda yai yi wani irin dahuwa sosai ya caɓe. Amma a haka su ka zauna suna ci, Humairah dai wasa ta ke yi da shi dan abincin bai ma ta ba. 'Yar indomie noodles ɗin nan Ummanta ba ta dafa ma ta yai kyau kaman na sauran 'yan ajin su.

Sallama da ta zama dole Maryam ta yi lokacin da ta shiga falon.

Duk su ka tsura ma ta ido, Sadiq ne kaɗai baya wajen dan yayi bacci a ɗaki.

"Wallahi Wallahi duk ranan da wani a gidan nan ya sake taɓa min lafiyar 'ya ta sai hukuma ta rabamu, ko da kuwa uwar da ta haifi uban ta ne. Cin zalin ya isa haka, ya isa haka, i repeat ya isa haka. Idan ba a son 'ya ta a bar min ita ina son kayana. Idan kunne ya ji jiki ya tsira" daga haka ta fice a gidan.

Har ta gama magana ba wacce ta yi magana. Ita kan ta Iya yadda Maryam ke magana da ƙarfi sai da ta ɗan tsorata.

Daren ranan sai da Zaytoonah ta kwana da zazzaɓi saboda kuka da ta sha.

***

Exams yaran ke yi dan haka da wuri su ke dawowa gida. Yau ma sun jima da dawowa suna ta damunta da rigima ta tura su gidan su Fawaz. Shi kuwa Auwal ya je aski. Ba ta jin daɗi ya sa ta dawo daga office tun ƙarfe shaɗaya na safe. Laulayi ne ta ke wanda ba ta san tana ɗauke da cikin ba sai sati biyu da su ka wuce wanda ya kama satin T J shida da barin ƙasar.

Jin ana buga ƙofa ne ya sa ta tashi daga baccin da ta ɗan farayi.

"Zaytoonah? Salman?" Ta fara kiran sunan yaran amma shiru dan haka ta sa a ranta ba su ba ne.

Doguwar riga ce ajikin ta dan haka gyalensa kawai ta yafa ta fito.

Jin yana ta buga ƙofa ba a amsa ba ne ya sa shi buɗe ƙofan ai kuwa ya ji shi a buɗe. Ba tareda wani shayi ba ya kutsa kai cikin gidan.

Ko'ina tsab-tsab a falon sai ƙanshi ke tashi. Yai murmushi dan ya san Maryam ce da wannan gyaran.

Fitowan da za ta yi a ɗaki ta ga wani guntun mutum a tsakiyar falonta ya ƙurawa hoton su da ke jikin bango ido. Hoto ne da su ka yi duka gidan ranan birthday ɗin Salman na cika shekara huɗu a duniya.

"Malam lafiya za ka shigo min gida ba tareda izinin ma su g..." maganar ta kafe lokacin da mutumin ya juyo.

Shekaru shabiyar rabon da ta sashi a ido , ita tama manta da batun sa. Saɓanin wancan da ta sani da ya ke yaro ɗan ƙauye mai kusan shekaru ishirin, wannan ya ƙara girma da wayewa ga alamun hutu ya ratsa shi.

"MUNTARI!" Ta furta cike da mamaki

"No no no no. Its ALHAJI MUNTARI"


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol