Free chapter · Read without an account

Missing

by Azizat Hamza · ZAYTOONAH


*Chronicles of*

*...... ...... .......ZAYTOONAH*

Rubutawa.....Azizat

Wattpad@Azi_zat

*Free page*

*16-Missing*

Bismillahir Rahmanir Rahim

T J bai tashi ba sai chan yammaci. An hana mutane shiga wajen sa saboda ba a son abun da zai tada ma sa hankali. Auwal ne kaɗai ya shiga ɗakin ya duba shi.

Yana ganin sa yai murmushi mai ciwo yayinda maganganun Maryam ke sake ma sa yawo a ƙwaƙwalwarsa. Ba abinda ya tsaya ma sa irin furucin da ta yi na danasanin haɗuwa da shi da ta yi har ta fara son shi.

"Daddy ya jikin?" Ya tambaya yana danne hawayen da ke shirin zubowa.

"Mommyn ku tana nan?" Ya faɗa a hankali

Auwal ya girgiza kai, sai ga hawaye ya silalo daga idanun TJ.

"Muna tareda ita tuntuni, ta je gida ɗauko kaya ne" yai saurin faɗa saboda hawayen da ya gani a fiskar TJ. Maryam kam da su ka dame ta da kira ma kashe wayar ta yi.

Ya san ƙarya ya ke yi Maryam ba ta nan, da tana nan ba abinda zai sa ta koma gida ba tareda ya farfaɗo ba.

Kenan da gaske ta tsaneshi, ta tsani zama da shi. Abinda ya faɗo ma sa rai kenan.

"Dan Allah ka ce Mommyn ku ta zo ina son ganin ta"

Auwal ya rasa ya zai faɗa ma sa abinda ke faruwa yana tsoron kar hankalinsa ya kuma tashi. Anje gida ba ta nan, office ɗin ta ma a kulle ya ke ba chan ta je ba.

Ya dai fita dan kaɗan ya rage yai kuka. Yana fitowa Iya ce ta fara tambayar sa ya jikin sa ya ce ma ta da sauƙi. Itama ɗin da ita aka yi zaman jira ta ƙi komawa gida ita yadda aka kawoshi da safe ma ta ɗauka ba zai yi rai ba.

Har dare ba Maryam ba dalilin ta. Auwal kam sai cewa T J yai ciwon Sadiq ne ya tashi Maryam ɗin ke tareda shi a Asibiti saboda ana buƙatar jini. Ya dai ji ne amma ya san ƙarya ne.

"Ta tafi ko?" Auwal yai saurin girgiza kai yana faɗin " Allah Daddy tana wajen Sadiq ne, zuwa gobe da safe za ta zo tunda Likita ya ce mutum ɗaya ne zai zo wajen ka"...

Maryam hotel ta wuce ta kama ɗaki ta shiga ta durƙusa ƙasa tana kuka. Tun kafin ta iso hotel ɗin ake kiranta lokacin da ta karanta text ɗin da Auwal ya tura har ta karya kwana za ta je Asibitin sai ta fasa.

"Akwai mahaifiyar sa akwai matar sa tareda shi za su ba shi kulawan da ya dace" abinda zuciyarta ya raya ma ta kenan ya sa ta fasa zuwa Asibitin.

Sai da ta sha kukan ta sannan ta je ta yo Alwala ta yi sallah ta zauna tana yiwa T J addu'ar Allah ya bashi lafiya.

Ba za ta taɓa yafewa kan ta ba idan wani abu ya sameshi. So mugun abu ne, duk yadda ta ke kurin rabuwa da T J soyayyar sa na maƙale a ran ta kuma tana jin idan ta rabu da T J tamkar ta rasa farinciki a rayuwar ta ne. Ba ta da identity idan aka cire T J a rayuwar ta.

Tana son zuwa ta duba shi amma ba ta san da wani ido za ta kalle shi ba after abubuwan da ta faɗa ma sa. Ga uwa uba ba ta son haɗuwa da Iya.

Chan bayan Maghrib da ta ka sa haƙuri ta kunna wayar ta ta kira numban T J ta sani wayar ba zai wuce yana hannun Auwal ba. Shi ɗin ne ya amsa wayan lokacin ma ya fito daga masallaci kenan zai koma cikin Asibiti.

Tambayar sa ta yi jikin T J ya ce ma ta da sauƙi.

"Mommy ina kika shiga? Daddy yana son ganin ki, yana buƙatar ki kusa da shi" Auwal ya faɗa kaman zai yi kuka.

"Ka kula da shi sosai Dan Allah. Idan yana buƙatar matar sa ka kira ma sa Hajjo" daga haka ta katse kiran ta kashe wayan gaba ɗaya.

Ta riga ta yi waya da Maman Fawaz akan su Zaytoonah za su kwana a wajen ta dan ta yi tafiya dan haka ba ta da matsala da yaran.

Ba ta iya bacci ba saboda damuwa da ya isheta, tun 1am ta tashi ta fara sallah tana roƙawa T J lafiya. Zuwa ƙarfe 3 kuma ta ɗauko ƙur'ani ta fara tilawa. Da safe ko abinci ba ta ci ba ta wuce office zuwa lokacin ta fara jin sanyi a zuciyar ta gameda abinda ya faru.

Da safe ma dai sai da T J ya tambayi Maryam amma babu ita. Dan haka ya ce Auwal ya kira ma sa Yayan sa a kai wa Goggo zai yi magana da ita.

Auwal ya kira Mahaifin sa ya sanar da shi T J ke son magana da Goggo. Ba a jima ba aka kai wa Goggo wayan. Auwal ya sawa T J a kunne su ka fara magana...

Duk da Goggo na fama da ciwon ƙafa hakan bai hana Goggo zuwa Zaria a ranan ba. Maganganun T J ya tada ma ta hankali musamman ma da ta ji cewa a Asibiti ya ke.

*"Goggo Dan Allah ki faɗa min gaskiya, kin san da cewa Mukhtari na son Maryam kafin auren mu?"*

*"Barkindo a ina ka ji wannan maganan?"*

*"Ki faɗa min gaskiya Goggo dan gaskiyar ce za ta ƙwaci Mukhtari a hannuna. Ba zan taɓa yafe ma sa ƙoƙarin ketawa matata haddi da yai ba"*

*"Ya subhanallahi! Barkindo wannan ba maganar waya ba ce. Zan shirya na taho yau yau ɗin nan"*...

Kusan ƙarfe uku Goggo ta iso Asibitin wanda Auwal ne ya je ya taho da ita daga park, tare su ka taho da wani jikan ta mai suna Al'amin ɗan Zahra ƙanwar T J.

Ganin T J kwance a gadon Asibiti ya sa jikin Goggo yai sanyi. Ta so ta ƙi faɗa ma sa gaskiya akan sai ya warke za ta faɗa mi shi komai amma ya dage shi a lokacin ya ke son sanin komai dan hankalin sa ba zai taɓa kwanciya ba.

Labarin komai ta bashi tun daga Lokacin da Muntari ya fara yiwa Baffah maganar yana son auren Maryam tun tana Mary Nkirun ta har zuwa rikicin da aka yi har ta kai ga aka ɗaura auren Tijjani da Maryam a cikin Fadan Ringim. Ta haɗa da cewa tana zargin auren na su da aka yi ne ya sa Muntari barin gida har shekara shabiyar kafin ya dawo.

T J ya sunkuyar da kai yana hawaye yana maimaita Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun saboda ya samu sassauci a zuciyar sa dan har lokacin bai dena jin zafi a zuciyar sa ba.

"Ka yi haƙuri ka da ka ɗaga hankalin ka Dan Allah, zan samu Maryam na ba ta haƙuri"

Ashe dalilin da ya sa Muntari yai wa Maryam kyautar mota lokacin saukanta kenan, saboda bai haƙura da ita ba.

Wani irin so ne wannan ace mace ta auri Yayan ka shekara ishirin da ɗaya amma ka kasa haƙura da ita. Anya kuwa Muntari na da cikakken hankali ?

"Itama Aishatun da ta ke ɗaurewa Muntari gindi zan je na sameta. Har yaushe za ta yi hankali ta yadda da ƙaddara ta bi duniya a sannu?" Muryan Goggo ya katse shi daga tunanin da ya ke yi.

"Goggo dan Allah ki tayani roƙon Maryam, ki roƙeta ko da minti biyu ne ta zo ta duba ni dan na nemi yafiyar ta"

Da wannan maganar su ka rabu da Goggo. Auwal ya raka ta gidan Muntari dan ba ta san gidan ba yayinda Al'amin ya zauna da T J.

Hanne ce ta nunawa Goggo ɗakin Iya wacce tunda ta dawo daga Asibiti ta shige ɗaki ko abincin rana ba ta ci ba. Da safe da ta shiga duba T J kalma ɗaya bai ma ta ba lokacin da ta ke ma sa ya jiki sai hawaye da ya ke yi.

Sai dai ta ƙi gaskiya amma duk cikin 'ya'yan ta Tijjani ke ma ta biyayya ɗari bisa ɗari kuma ba ƙaramin darajata ya ke yi ba. Duk yadda ta ke ja baya da shi baya fushi.

Sai da Goggo ta zauna a kujeran da ke ɗakin sannan ta kalli Iya da ke zaune bakin gado ta ce " a matsayina na 'yar uwar ki zan ba ki shawara Aishatu. Kin san dai Baffah ya rasu ba maganar shekara ɗaya ko biyu ba, kuma duk inda ya ke ina da yaƙinin yana cikin rahamar Ubangiji saboda kyawawan halayen sa da ya rayu da su har mutuwar sa. Aishatu ina miki tuni da cewa inda Baffah ya je ko ba daɗe ko ba juma za mu je muma. Yadda ya ke kwance ƙarƙashin ƙasa muma haka za a rufe mu da ƙasa mu je mu amshi sakamakon ayyukan mu na duniya. Ki shuka alkhairi Aishatu, ki shuka Alkhairi, duniya ba matabbata ba ce. Kuma ina so ki sani yadda Allah ya ce 'ya'yan da mu ka haifa su mana biyayya haka muma ya ce mana 'ya'yan mu amana ne a garemu. Aishatu Allah zai tambayeki amanar 'ya'yan ki, banbanta Muntari da Tijjani da ki ke yi shi ya kawo su ga wannan hali yanzu. Tun farko kin riga kin dasawa Muntari hassadar ɗan uwan sa kuma har yanzu shi ke bibiyar sa. Ki kula da amanar Tijjani da ke hannun ki, dan Allah zai tambayeki, tun yana yaro kike tsangwamar sa saboda ni yanzu kuma ya girma ma ba ki bar shi ba. Ni da Maryam ba mu muka haifi Tijjani ba ke ce kika haifi kayan ki, dan haka duk abinda ya sameshi dalilin mugun halinki ki kuka da kan ki. Zan ƙara jaddada mi ki,Tijjani amana ne a gareki kuma Allah zai tambayeki game da shi. Ita kuma Maryam duk abinda ki ka yi ma ta Allah zai saka ma ta, ina ba ki shawaran ki nemi yafiyar ta ko kuma ku haɗu a gaban Sarkin da ba ya zalinci"

Da wannan ta miƙe ta fita daga ɗakin ta bar Iya zaune jiki yayi laƙwas. Maganganun Goggo sun shigeta sosai...

Lokacin da Auwal ya kira Maryam ya ci sa'a wayan ta a kunne, ba ta ɗauka a kiran farko ba sai a na biyu tana sallama kuwa Goggo ta amsa.

"Maryam ki zo gidan ki ina jiran ki"

"Goggo ki yi haƙuri bazan tashi daga office da wuri ba"

"Ba na son musu Maryam, ki zo gida kawai"

Ba yadda ta iya dole ta amince za ta zo ɗin. Goggo uwa ce a gareta, ita ce matar da ta ke gani ta manta cewa uwar da ta haifeta ba ta raye.

Kusan ƙarfe biyar sai ga ta a gidan. Su Zaytoonah da Salman na tareda Goggo dan Auwal ya koma Asibiti.

Zaytoonah da Salman ba su san Daddyn su ba lafiya ba dan Auwal ce mu su yai da Daddy da Mommy sun yi tafiya.

Shi ba yaro ba ne, ya fahimci kafin rashin lafiyar T J sun samu matsala da Maryam, ga kuma conversation ɗin Goggo da Tijjani da ya saurara ɗazu da safe.

Da sallama ta shigo yaran su ka yi kanta da gudu suna ma ta oyoyo. Har da tambayarta ina tsaraban su.

A ɗakin Maryam su ka yada zango saboda su samu damar tattaunawa da kyau.

"Maryam Dan Allah ki yi haƙuri. Shehu ya gaya min komai kuma na sani ba a miki adalci ba. Amma Maryam bai kai kiyi watsi da mijinki a lokacin da ya fi buƙatar ki ba."

"Goggo na haƙura da shi, na gaji da matsalar mahaifiyar sa, kowa yai hanyar sa kawai" ta faɗa tana goge hawaye

"Tun da Shehu ya kawo ki wajena ya damƙa mini amanar ki na ɗauke ki a matsayin ɗiyar da na haifa. A matsayina na uwa ina ba ki haƙuri bisa laifuffukan da aka miki tun auren ki da Tijjani har yau. Ba sai na gaya miki Tijjani na son ki ba kema kin fini sanin hakan. Ina so ki san wani abu guda, rabuwar ki da Tijjani babu alkhairi a ciki. Ba za ki samu kwanciyar hankaliba kazalika shima ba zai samu ba. Kin dai san yana da hawan jini kuma na san kin san yanzu ma yana kwance a asibiti, saboda ke ne Maryam saboda ke"

"Goggo..." ta faɗa cikin muryan kuka

"Ka da ki sa baƙin ciki ya kashe Tijjani, ki koma gareshi ku cigaba da rufawa kan ku asiri. Shekaru ɗaiɗaiɗai har ishirin ba wasa ba ne, ta ina za ki ma fara raba kan 'ya'yan ki? Wa ki ke da shi da ya fi Tijjani? Waye zai so ki fiye da Tijjani?. Kiyi haƙuri ki cigaba da haƙuri. Ilimi da kyakykyawar zuciya da Tijjani ke da shi shiyasa ya ke takatsantsan da maganar mahaifiyar sa. Ki godewa Allah da ya ba ki miji irin sa, ki cigaba da haƙuri da shi har su rabu da mahaifiyar sa lafiya"

Goggo na magana Maryam na kuka. Duk abinda ta faɗa gaskiya ne. Ba ta da wanda ya fi Tijjani amma Iya Iya Iya. Anya za ta iya cigaba da haƙuri da baƙin cikin Iya?

Haka dai Goggo ta cigaba da yi ma ta nasiha har ta haƙura da zancen rabuwa da za su yi.

Banɗaki ta shiga ta yi wanka ta fito ta shirya cikin wata doguwar riga shadda kalar blue wanda ya sha aiki. Ta yafa farin gyale wanda ya ke da duwatsu blue a jiki. Ta ɗan yiwa fiskarta kwalliya kaɗan har da sa janbaki pink wanda ya amsheta sosai saboda ita fara ce. Yaran ta ɗauka su ka wuce Asibiti Goggo ba ta bi su ba.

A hanya ta faɗa mu su Daddy za su je su gaisar ba shi da lafiya. Zaytoonah har da sha alwashin za ta yiwa Auwal rashin mutunci da ya mu su ƙarya.

Sun zo shiga Asibitin su ka hango Hajjo da Auwal suna fitowa da alama Auwal ɗin ke son tare ma ta abin hawa.

Bayan sun fito daga mota su ka jira har Auwal ya zo ya same su sannan ya mu su jagora zuwa ɗakin da aka kwantar da T J, suna tafiya Zaytoonah ta ɗira ma sa dundu a baya tana faɗin ladan ƙaryan da ya mu su, za ta ma ƙara ma sa wani dundun Maryam ta hana ta.

Sun samu yayi bacci amma hayaniyar su Zaytoonah ya tada shi. Yana ƙyalla ido ya ga Maryam ya ji wani farin ciki ya mamayeshi. Yaran duk su ka yanyameshi da shagwaɓa Zaytoonah har da kukan sakalci. Maryam dai zama ta yi a kujera tana bin su da kallo cike da tausayin mijin na ta har lokacin akwai nasal canula a hancin sa wanda ke daidaita numfashin sa maganar sa ma a hankali a hankali ya ke fita. Shima ɗin lokaci zuwa lokaci yana juyawa ya kalleta, idan su ka haɗa ido sai yai saurin kau da kai.

Bayan maghrib Auwal ya tattari yaran zai mai da su gida su ka ƙi Zaytoonah har da kuka wai a wajen Daddyn ta za ta kwana. Maryam ta zare ma ta ido dole ta bi bayan Salman su ka tafi. Auwal ne zai kai su da Motar Maryam dan shima ba laifi ya iya, a ƙiriniya ya koyi mota a wajen wani abokinsa da ke sato motan Babansa yana fitowa da shi idan baya nan.

Ɗakin yai tsit bayan fitan yaran. Kusan minti biyu ya wuce kafin TJ ya ɗago ido ya kalli Maryam wacce itama shi ta ke kallo ya ce " ki yafe min, ban san da maganar Mukhtari ba, ban san komai ba. Ki yi haƙuri na kasa ba ki farincikin da na miki alkawari a farkon auren mu, ki yafe min"

Tasowa ta yi a hankali ta rungumeshi. Tana tsaye yana zaune ya kwantar da kan sa a cikinta ya ƙanƙameta.

"Na yafe ma ka"

"Da gaske Maryam?"

Ta gyaɗa ma sa kai.

Cikin i'ii'ina ya ce " kin janye maganar rabuwa da ni?"

"Ina da wajen da zan je ne idan na rabu da kai?"

"Na gode Maryam" ya faɗa sai ga hawaye na zubo ma sa. Maimakon ta yi magana sai ta manna ma sa light kiss a bakin sa.

"Ka ga ka kwantar da hankalin ka. Likita ya ce ban da kuka, ban da sa damuwa a rai"

"Ke ce likita na Maryam and you know it. Tunda kika shigo ɗakin nan duk ciwon da na ke ji ya yi sauƙi"

"Allah ya baka lafiya"

"Janbakin ya mi ki kyau idan da hali a bani na shanye"

"Naughty Man" ta faɗa tana murmushi kafin ta rankwafo ta haɗe bakin su...

Ita ta kwana da shi su ka wuni suna nunawa juna kulawa. Duk yadda ya so su tattauna abin da ya faru tsakaninta da Muntari ta ƙi ta ce sai an sallameshi tukunna. Ta yi hakanne dan ba ta so ya ji abinda zai ƙara ɗaga ciwon sa.

Washegari da safe da likita ya zo ya dubashi aka cire ma sa nasal canula ya kuma yiwa Maryam bayanin yadda za a dinga kiyayewa da duk abinda zai ɗaga ma sa hankali. Sun ce idan sun ƙara ganin yanayin yadda ya samu sauƙin ciwon ƙirji za su sallameshi dan har yanzu any shock ko wani extreme excitement zai iya sa shi a risk ɗin wani heart attack ɗin. Shi kuwa T J tunda ya farka dama ya lazimci addu'o'in saboda ya samu sauƙin raɗaɗi da zafin da ya ke ji a zuciyar sa.

Ba ta so tafiya office ba dan yadda T J ke narke ma ta hadda cewa ta ma sa rawan Atilogwu ta yi dariya ta ce za ta ma sa idan ya koma gida. Su Zaytoonah ma kafin su je makaranta sai da su ka zo su ka gaida mahaifin su.

Ƙarfe tara na safe Hajjo ta zo ta karɓeta hakan ya sa Maryam ta koma gida ta shirya ta wuce office. Ƙarfe shabiyu kuwa ta koma gida ta yi wanka ta shiga haɗa abincin da za ta kaiwa T J a asibiti.

Tana cikin juya abincin a food warmer wayarta yai ringing. Numbar T J ne dan haka da sauri ta ɗauka. Ɗazu tana office ya kirata sun fi minti shabiyar su na hira inda ya ke ƙara jaddada ma ta soyayyar shi gareta.

"Hello Mommy ba a ga Daddy ba. Daddy ya ɓata" Auwal ya faɗa cikin kuka.

"Ban gane ba a ga Daddy ba, ina ya je?"

Kukan Hajjo da ta ke ji ne ya sa jikinta ya hau ɓari ta yi saurin kashe wayar ta je ta rarumi gyalenta ta fita da sauri. Tare za su tafi asibitin da Goggo amma ko ta kan ta ba ta bi ba...

Zuwanta Asibitin ta tarar da mummunan labari. Lokacin da T J ya gama waya da Maryam ya kwanta bacci yana bacci Hajjo da ta je ɗauko ma sa kaya ta shigo. Ganin yana bacci ya sa itama ta kwanta a kan tabarma a ƙasa a haka Auwal ya shigo ya sameta, ganin T J ba ya kan gado ya sa ya tashi Hajjo yana tambayarta ina T J tunda ya leƙa banɗaki baya nan.

Wasa- wasa sai ga shi sun duba ko ina a asibitin babu T J ba dalilin sa. Maryam zama ta yi daɓas a ƙasa tana hawaye lokacin da wata mai shara ta ce ta ga lokacin da T J ya fita a ɗakin sa har tana ma sa ya jiki amma ko juyowa bai yi ba balle ya kulata. Mutane biyu ma su ka kuma jaddada cewa sun ga fitan T J daga asibitin.

Da farko Maryam ta ɗauka Muntari zai je nema saboda abinda ya faru amma ai ya san Muntari baya gari.

Ranan dai tashin hankalin da Maryam ta shiga ba a magana. Kuka ma kasa yi ta yi, bacci kam kasa yi ta yi dan duk inda ake tunanin T J zai je an nema ba a same shi ba ba akuma samu wanda ya gan shi ba bayan fitan sa daga asibitin.

Washegari da safe aka je police station aka ba da report na ɓatan T J.

Wasa-wasa kwana biyu su ka shige ba a ga T J ba ba a san inda ya je ba. A rana na uku Muntari ya dawo gida ya tarar da ɓatan T J yadda ya ke salati yana salallami ka ɗauka bai san mi ke faruwa ba, ka ɗauka ya fi kowa damuwa da ɓatan T J. Har Kaduna ya raka Maryam aka kai cigiya gidan talabijin da gidan radio. Tun ana cewa kwanan sa biyu da ba a gan shi ba har aka fara irga sati ɗaya sati biyu sati uku kenan yanzu. Zuwa lokacin Maryam tamkar mahaukaciya ta koma, ita ne nan itane chan ko bacci ba ta iya yi. Koyaushe ɗaurawa kan ta laifi ta ke yi a ɓatan T J musamman da Likitan T J ya ce ƙila damuwa ce ta sa shi samun taɓin hankali...


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol