Free chapter · Read without an account

9&10

by Rabiatu bashir · DINYAR MAKAHO

*_📲Typing_*.




*_🪁ƊINYAR MAKAHO...!🪁_*

   _(Ta nuna a hannunsa)🍀_






_*UMMU MAHER(MISS GREEN ce)🍀*_


_AREWA BOOK👉🏼_

Rabiattu0444


*GAWURTATTU 5🔥*

------------------------



P. 9&10



............"Hmm Magajiya kenan,kina tunanin a wannan karon zan bar wannan balarabiyar tasha ruwa ne?kema kinsa halina babu abinda ya shafeni a mutu ko kuma ayi rai ni dai bai dameni ba".


 Wata mahaukaciyar dariya Magajiya ta yi sannan ta ce"Hmm Uwar gijiyata mu fa mu kashe mutum ba komai ba,indai har zai shigo gonarmu to zamu gama dashi yanzun nan,ni har mamaki ma nake ta yadda akayi har yanxu balarabiyar nan take zaune agidan da bai cancanta ta zauna ba".?


 Kilishi ta kalli Magajiya sosai ta ɓata fuska tamkar dai bats taɓa wani abu wai shi dariya ba,sannan ta ce"Magajiya duk ranar da kika bari bakinki ya ƙara kuskure faɗar maganganu akan gazawar danayi don barin wannan banzar,wallahi sai dai uwarki ta haifi wata amman ba ke ba".


 Ta faɗi hakan tana karkaɗa mata hannu,tana fito da fici-ficin idanuwanta waje tamkar wata mayya.


 Da sauri Magajiya ta kama wagagen bakinta sannan ta ce"ki yimin afuwa Uwar ɗakina ni dai banason mutuwa yanzu Allah ya gani,ba tare dana yi aure na ga ƴaƴa na".


 Kilishi ta murɗa bakinta gefe alamar ke kika sani, sannan ta tashi ta ɗakko wata takadda fara sol,ta kalli Magajiya sannan ta ce"yauwa wannan takaddar da ki ke ganinta Takadda ce daza ta tarwatsa rayuwar wasu acikin gidan nan,saboda haka kada kiyi min wasa da i'ta,idan ba haka ba ki janyowa kanki masifa".


 da sauri Magajiya ta miƙo hannu zata amshi wannan takaddar,da sauri Kilishi ta amshe ta sannan ta ce"ke!Magajiya ki buɗe kunnuwanki da kyau kisan yadda zaki kula da wannan takaddar haka zaki kula da rayuwarki,akasin hakan kuma to tabbas kina cikin babbar masifa".


 Magajiya ta waro idanuwa waje kamar zata zuga aguje,don wani lokacin idan Kilishi ta juya mata,sai taga tamkar dai wata zaki ce,don Kilishi sam bata tsoron Allah,wai duk akan bata haifi ɗa namiji ba kuma gashi ita ce mace ta farko awajen Sarki Ƴaƴanta goma kuma duk mata ayanzu har tana da jikokinta ma,ƴan mata biyu ne waɗanda bata aurar ba amman har yanzu bata yi hankali ba,rashin imanin na ta ma gaba yake ƙarayi ba baya ba don anason kullum mutum yana girma yana ƙara hankali,amman ita Kilishi kamar kowacce rana ƙara mata rashin imani ake.


 Kilishi ta juyawa Magajiya Baya,tana sanye cikin wata doguwar riga tana jan ƙasa irin ta manyan mata ƴan gidan Sarauta,kana ganin rigar ba sai an faɗa maka ba,tasha kuɗi sosai ba rigar talaka bace.


 Allah sarki talaka,Allah dai ya rufa mana asiri duniya da lahira.



Magajiya na ganin Kilishi ta juya mata baya tasan wannan maganar ba ƙaramin muhimmanci bane da maganar,ta gyara zaman da tayi sosai don jin abinda Uwargiyarta zata faɗa mata.



 "Magajiya!Magajiya!!Magajiya!!!."


"Sau nawa na faɗi sunanki"?.


 Magajiya ta haɗiye wani yawu me zafi,don Magajiya aƙwai tsoro kuma aƙwai rashin imani.


"Uwar ɗakina Sau uku kika faɗa,Allah dai yasa lafiya"?.


 

 "Wannan Takaddar tafi ɓangaren Fulanin Sura da i'ta,Idan kika je tunda ta yarda dake sai ki shiga ɗakinta ki jefar da ita,sai kiyi sauri ki fita daga sashenta,awannan aikin da zakiyi kada ki yarda kowa ya ganki,idan kuma kika bari kika yarda aka ganki to wallahi kinsan sauran".


 Tana faɗar hakan ta jehowa Magajiya wannan takaddar.


 Hannu na rawa Magajiya ta ɗauke wannan Takaddar,ta buɗe bakin zaninta ta ɗaure Takaddar sosai da sauri ta fice daga sashen Kilishi,ta fita ta ƙofar baya tana ɗan waige waige tamkar mara gaskiya,ko da yake ance mara gaskiya ko aruwa ya ke sai yayi gumi.



 *Ahmad Pov*


. . . . . . . .Sosai jikin Zaliha ya yi mugun sanyi ganin abinda ta aikata,gashi kuma duk ta ɓatawa yayan na ta jiki,da sauri ta yo inda yake bata sani ba ta taka ƙwalba,ta shige mata ƙafa ta saki wani irin ihu me firgitarwa don taji zafin ƙwalbar sosai.


 Da sauri Ahmad ya isa inda take,ya riƙeta sosai sai ihu take tana yarfe hannuwa duka biyu tana ƙwalla.



 Zaunar da ita ya yi,a bakin kujerar falo duk hankalinsa atashe,ya ɗaga ƙafar ya ɗora abisa carpet ɗin ɗakin,sosai ya ruɗe ya rasa yadda zaiyi.


 Zaliha kuwa duk da zafin da takeji awajen bai hanata jin wani mugun daɗi ba,ta yadda yayan na ta wanda take matuƙar so kamar ranta,yana bata kulawa ashe daman shima yana sonta kamar yadda take sonshi?.


 Zafin cire ƙwalbarne yasa ra fasa ihu,tana riƙe hannayensa tana kuka.


 Sosai abin ya bashi dariya har yana dungure kumatun Zaliha ya ce"raguwar yarinya kawai".


  Kukan shagwaɓa ta fara yimai tana kuka,anan dai suka lalace yana ta tsokanarta tana biye masa har Hajiya ta samesu alokacin har ya ɗakko box ɗinsa ya gyara mata ciwon.


 Hajiya ta ce"ikon Allah ita kuma wannan me yasa me ta"?.


 Ahmad ne ya faɗa mata duk abinda ya faru,Hajiyar Ahmad ta yi shiru duk jikinta ya yi sanyi da abinda ya faru.



 YAZEED Pov



. . . . .computer ce akan cinyarsa yana aiki,sanye ya ke cikin riga da wando pijamas kayan bacci na maza,dukkanin hankalinsa yana kan aikin daya ke yi.


 Wayarsa ce ta fara ringing,ya kalli wayar ganin me kiran yasa ya cigaba da aikinsa,da aka damesa ma da kira sai ya kashe wayar baki ɗaya.


 Kofin coffie da ke kusa dashi ya ɗauka ya fara sha ahankali har ya gama aikinsa tsaf,don Yarima Yazeed mayan coffie ne,don indai kusa dashi aƙwai coffie to idan zai kai biyun dare yana aiki babu komai don ba zaiji wata gajiya ba.


 Ƙarar bell yaji alamar aƙwai wanda keson shigowa,to shi dai yasan ba shida apointment da kowa don haka ya koma ya yi ƙwanciyarsa,har aka gaji aka tafi don shi Yazeed ɗan ra'ayi ne indai har ba shine ya gayyato ka ba,to babu ruwansa idan kazo gidansa yaƙi sauraranka don Yazeed irin rayuwar turawa ya ke,sam baya son wata damuwa ko hayaniya,abinda yasa har yanzu ya ƙi komawa Nigeria kenan,don sha'ani na gidan Sarauta baza'a barka ka huta ba,zaman fadar sarki ma kaɗai ta isheka shiyasa yanzu sam baya son komawa.



 Washe gari.


Yana tashi da asuba ya yi sallarsa ya ɗora da karatun alqur'ani me girma,cikin zazzaƙar muryarsa abinda zai baka mamaki Yazeed shekararsa goma cif ya sauke alqur'ani me girma,tun kafin yaxo ƙasar France ya sauke Qur'ani don Sarauniya Zulaihat ma ba bays bace wajen karatu haka shima mahaifinsa me Martaba Sarki Abdussalam mutum ne me ɗinbin ilimi don duk ƴaƴansa awajensa suke ɗaukar karatu.



  Yana idarwa ya tsaya ya yi addu'o'i sosai akan Allah ya shiryesa akan wani laifi da yake wa Allah wanda ba kowa ne yasan da hakan ba.



 Buɗe wayarsa ya yi,ya kira number mahaifiyarsa sun daɗe sosai suna hira,har yake gaya mata yau zai yi tafiya zuwa garin da Aliyu da Muhammad suke wato 'Clermont Ferrand' garin da ke gabas ga ƙasar France.


 Sarauniya Zulaiha ta ce"to My son Allah ya tsaremin kai ya kuma kare ka,ka kuma gaishemin dasu sosai tunda dai ku yanzu kum zama ƴan ƙasar France kunyi mana ta wa-ye".


 Murmushin nan nasa ya yi me matuƙar kyau sannan ya ce"haba Ammina zamu dawo fa,kawai dai lokaci ne babu amman insha Allah da mun samu lokaci zamu dawo".


 "Hmm to ai shikken,gashi saura wata biyu bikin ƙannenku Fadila da yusra".


 "To Ummi ni dai idan na ce zanzo na yi ƙarya,saboda ko da zan dawo sai nan da wata 7 haka koma fi,ni dai inason a gama wannan gadar da aka bani ƙwangilarta dana gama zan dawo ma gida baki ɗaya,sai dai in dinga zuwar musu ziyara ko kuma idan wani aikin ya taso".


 "To shikkenan Son Allah ya kaimu,Allah ya bada sa'a akan wannan aikin da aka baka ƙwangilarsa,don nasan ɗana gwarzo ne ba kaɗan ba".


 Murmushi ya yi sannan ya ce"kuma nima uwata gwarzuwa ce ba kaɗan ba,Allah dai ya barni da Ummi na ni kaɗai ban da kowa".


 Dariya Ummi ta yi sannan ta ce"a haba Son ai ba kai kaɗai bane ga ka ga Twins don ni dai nafi sonsu tunda sune mata".


 "To shikkenan tunda kinfi sonsu ni na fasa dawowa ma,zanyi zamana anan France don ƴan France sunfi sona,tunda ma Ummina ba ta so na".


  Ya faɗi hakan cikin shagwaɓa wacce ta xamar masa tamkar jiki,indai yana tare da Umminsa yadda kasan ɗan yaro haka yake.


 Murmushi Ummi ta yi,tamkar yana ganinta sai ta kama kunnenta ta ce"o ni na isa in ɓatawa Prince ransa,ayimin afuwa Yarima Ɗa ga Sarki Abdussalam".


 Wani murmushi ya yi har tana ɗan jiyo sautinsa,sannan ya yi mata wani peck ya ce"bye my mom".


 "Bye my lovely son".


 Cike da farin ciki suka gama wayar Yazeed ya haɗa kayansa acikin wani ɗan ƙaramin troley,sannan ya kulle ko ina ya kashe wutar lantarkin gidan nasa baki ɗaya.



 Gidane me kyau plat ne wanda Ƙasar France ta basa,ba wai don bashi da gidan da Zai zauna ba,a'ah shi da kansa yana da gida har guda biyu a ƙasar france ɗin,amman ba shida sha'awar ya zauna ɗaya daga cikin gidajen nasa yafi sha'awar zama acikin wannan.


  Ko ina shuke shuke ne acikin gidan gwanin sha'awa ya tarar da masu gadin gidan nasa ya basu mukulli,amman ba na ko'ina na cikin gidan ba aƙwai inda sirrinsa ya ke kuma ba kowa ne yake son yaga wannan ɗin ba.


 Bai kula da mutum a bakin ƙofar ba,sai daya duba sosai sai ya hango Fareeda wacce ke rakuɓe agefe,ta haɗe jikinta waje ɗaya sai rawar sanyi take.


 Sosai abin ya bashi mamaki,ya ƙarasa kusa da i'ta cikin tsoro ya ce.


 "Fareed"!.


 Da sauri ta kallesa jikinta sai rawa ya ke,saboda yanayin sanyin Ƙasar France ga ƙanƙara sai faɗuwa take.


 Ya matso sosai inda take,har suna iya juyo numfashin junansu.


 Ya ce"Fareeda me ya kawoki gidana?ban hanaki zuwa ba?kin sani banason zuwanki gidana,a halin da nake ciki yanzu bana son kowacce mace ta raɓi inda nake,saboda bana son ɓatawa mahaliccina".


 Bakinta na rawa ta fara magana kamar haka:



  "haba Prince me yasa ka ke yimin haka?kasan yau ƙwana nayi a ƙofar gidanka,na kiraka awaya kaƙi ɗagawa nazo inda ka ke don ka sharemin hawaye na ka ƙi buɗemin gidanka"?.


 Da sauri Yazeed ya ce"Fareeda don Allah live me a long"!.


 Ya faɗi hakan cikin matsanancin fushi,yana jin wani irin mugun haushin Fareeda na ninkuwa acikin zuciyarsa,don duk Fareeda ita ce 1st na lalacewar rayuwarsa daya kasance me bin mata.


 kamar mahaukaciya ta tashi tazo har gabansa ta kallesa kallon cikin ido sannan ta ce"to prince ka aureni mana?tunda har kana cewa ka gaji da saɓawa mahaliccinka".


 Cikin fushi ya juyo ya kalleta sannan ya ce"Fareeda ni ayanzu babu aure a gabana,kuma ba yanzu na ke da niyyar yin aure ba,har sai na sami macen da ta dace da rayuwata".


 Kamar mahaukaciya sabon kamu ta fara magana cikin fushi ta ce.


 "Prince ni ka ke cewa baza kayi aure yanzu ba?saboda ni ka gama da rayuwata shine zakace baza ka aure ni ba?ka rabani da iyaye na,saboda soyayyar dana ke yi maka na musulunta?amman shine yanzu zakaƙi ni?dube ni da kyau ka gani,Allah ya yimin ƙira me kyau ina da kyau na dai dai gwargwado amman kace baza ka aure ni ba?amman ka cuce ni prince ka lalata rayuwata".


 Ta faɗi hakan cikin kuka,tana tsugunne aƙasa hannuwanta na kan ƙafarsa.


 Sosai Fareeda ta karya masa zuciya,yabi hanyar motarsa tunda ga nesa ya buɗe motar ya shige,Fareeda jikinta asanyaye ta shiga cikin motar tana goge ɗan munafikin hawayenta.


 A hankali ya juyo ya kalli shigar da tayi ajikinta,sai da yaji wani iri ajikinsa sannan da sauri ya juya ya ce.



 "Fareeda idan na samu super market zan tsaya in siyo miki kaya na mutunci ki saka,saboda ba zai yiwu ki dinga yawo da waɗannan kayan ba,alhali kuma kina musulma kuma ni kinga ba mijinki bane"?.


 Yana faɗar hakan yana tuƙinsa,Fareeda ta ƙulu sosai da ya ke ita irin matan nanne masu saurin ƙuluwa sai kuwa ta ce"yanzu prince wannan shigar meye laifinta?kuma naga da a haka nake yawo baka ce komai ba?au sai yanxu zakayi magana saboda na ce ka aure ni"?.


 Banza ya yi mata tamkar ba dashi take ba,don arayuwarsa ya tsani ya yi magana a musa mishi,kuma bayan haka ma shi ba mutum ne me son magana ba,zaiyi wuya kaji ko da tarinsa idan ba da ƙwaƙƙwaran dalili ba.



 to Fareeda da taga ya yi mata shiru tasan halin Prince ɗinta,zai iya jeho ta waje idan bata yi a hankali ba,shiyasa ta yi shiru don tasan yanzu ita ya kamata ta lallaɓasa ba shine ya kamata ya lallaɓata ba,don ita ayanzu burinta bai wuce na auran Yazeed ba.


 Awani super market ya tsaya,sannan ya ce ta biyosa haka kuwa akayi ta biyosa har cikin wajen,waje ne babba sai taga Yazeed ya yi ɓangaren siyarda abaya ta mata masu matuƙar kyau da tsada.

sosai ya jibgo mata su,sannan ya ɗibi hijabai a ƙalla kala goma ya biyasu kuɗinsu sannan ya wuce cikin mota,har yanzu kuma fuskarsa tana a haɗe sosai.


 Kallonta ya yi sannan ya ce"ɗauki hijabin nan ki saka ɗaya idan kuma abayar zaki saka go a head".


 Da sauri ta ɗauka hannunta sai kakkarwa ya ke na tsoron Yazeed,don idan ya juya mata ganinsa take tamkar wani zaki.




 sosai sukasha tafiya,har Fareeda ta yi barci ya juyo a hankali ya kalle ta,tabbas kamar yadda Fareeda ta faɗa ba tada makusa ko kaɗan a jikinta,shi dai kawai yasan baya jin zuciyarsa zata iya daurewa akan aurenta,don shi ayanzu babu tunanin aure aransa,yafi son sai nan gaba shima nan gaban yana fatan ya samu wacce ta yi dai dai da zuciyarsa.


 Har suka isa Fareeda bata tashi daga baccinta ba,shima bai tashe taba don baya son a dame sa ko kaɗan,ita kuma Fareeda idan banda neman tashin hankali babu abinda ta iya.


 Yana zuwa garin ya fara tsayawa ya siyo musu tsaraba,irin tasu inibi da sauransu don garin Allah ya hore musu kayan marmari kala kala.

 Sai alokacin Fareeda ta farka daga baccin da take,kuma lokacin suka isa ƙofar tamfatsetsen gidansu Muhammad.gida ne suma plat amman babbane sosai gashi unguwar shiru,babu ko mutum ɗaya awaje gashi dare ya lula sosai.



  Yana gaba Fareeda na biye dashi a baya,aƙwatinansu na cikin mota don dukkansu sun gaji sosai.


 A hankali Yazeed ke danna bell ɗin ƙofar,sai da yayi kamar sau uku sannan akazo aka buɗe.


 Sosai Aliyu ya yi mamakin ganin Yazeed,cikin murna ya rungumesa yana ce wa"our welcome Bro".shima Yazeed ɗin rungumesa ya yi yana jin wani irin daɗi na ratsasa don rabonsa dasu Aliyu kusan wata biyar kenan,tun wani visiting da suka kawo masa paris.


 Fareeda na tsaye tana kallonsu,Aliyu ya.kalle ta ya ɓata rai sosai ya ce"bro wai daman har yanzu kana tare da wannan shaiɗaniyar yarinyar"?.


 Yazeed bai amsa masa ba ya yi shigowarsa,tare da jiyowa ya kalli Fareeda sannan ya yi mata alama da ta shigo.


 Aliyu yasan Yazeed ba amsa masa zaiyi ba,don yafi kowa sanin waye Yazeed ba kowacce magana yake yi ba,a hakan ma wai don sune shiyasa ma yake ɗaga musu ƙafa awani abin.


 Muhammad na falo yana ganin Yazeed ya taso da sauri ya rungume Yazeed ɗin,shi kuwa bai wani mayar masa da rungumar ba,don duk jikinsa ya gaji bai saba irin daɗewa yana tuƙi ba,wannan ma don ya matsu yazo ya gansu ne,kuma baya sha'awar hawa jirgi yafi son ya ɗan wasa jininsa.



 *****


Noor Pov


. . . . .jiki na ya yi sauƙi sosai,karayar dana yi ce dai bata gama warkewa ba,jiki na ya yi wani irin kyau sai sheƙi ya ke,na yi wani irin fari da ƙiba kumatu na sun cika sosai saboda kulawar dana ke samu awajen Ahmad.

 


 Sai dai wasu abubuwa da suke wanzuwa tsakanina da Ahmad,bai wuce yadda ya ke bani wata irin kulawa ba,gashi sai ya dinga nunawa afili yana jin wani abu agame dani,ki da yake ni fa har yanzu farin shiga ce ban san komai a harkar soyayya ba,wala Alla shiyasa ban gane inda gizo yake saƙar ba.?


 Awasu lokuta da dama idan yazo,sai inga yana ta kallo na idan na kamashi da tuhumar yana kallona,sai inga ya kama kunnensa alamar ban haƙuri,sai dai kawai inyi dariya in cigaba da kallon wani wajen.


 Nima da kai na yanzu na fara jin wani irin abu agame da abubuwan da suke wanzuwa tsakanina da Ahmad ɗin,ita kanta Umna da take mahaifiyata ta fara gano wasu abubuwan sai dai bata nuna ta gane hakan ba.



 Rannan ina zaune muna ta hira da Hadiza harda ƙawata Fatima aminiyata ta boko,muna ta hira har da dariya Umma na ɗan saka mana baki sai mukaji sallama.



 Haɗa ido mukayi dashi ya kashemin ɗaya,da sauri na juyar da fuskata don bana son kallon idanuwan nan nasa firgita ni suke.


 Har gaban Umma yaje suka gaisa,sannan ya kalleni ya ce"Gimbiya ina ƙwana".?


 Kunya ce ta baibayeni saboda gaisheshi ɗin da banyi ba na ce"yi haƙuri yaya Ahmad ina ƙwana".?


 Murmushi ya yi sannan ya ce"a'ah ni dai ƙanwata ba ta laifi,ai nasan mantawa kika yi".


 Sunkuyar da kaina nayi ba tare dana ce komai ba,ina wasa da ƴan ƴatsun hannuwa na.



 Su Hadiza ma suka gaishesa,ya amsa cikin fara'a kamar yadda ya saba amsawa,don shi Ahmad mutum ne me fara'a sosai ko da yaushe fuskarsa tana cikin fara'a ga son mutane,gashi dai yana da kuɗi sosai amman baza ka taɓa cewa yana da kuɗi har haka ba,tunda ba shida wulaƙanta ɗan adam.




 Ahmad ya juya inda Umma take ya ce.



 "Umma daman inason muyi wata magana dake idan babu damuwa".


 Murmushi Umma tayi sannan ta ce"babu komai Ahmad ka faɗi kowacce magana ce daman nan wajen duk ƴaƴa nane."


 Fatima ce ta fara tashi ta kalli Umma sannan ta ce"haba Umma ai aƙwai sirrin da yake son a sirrantasa,don haka gwara muɗan baku waje daga baya sai mu dawo."


 Ɗan murmushi Umma ta yi sannan ta ce"babu komai Fatima ku koma ku zauna kuma ƴaƴa na ne ai".


 Komawa sukayi suka zauna,don da har da Hadiza suka tashi,Na kallesu na hararesu na ce"to su Fatima duk yadda akayi guduwa zakiyi shiyasa ki ke wani sauri."



  Murmushi Fatima ta yi sannan ta ce" a haba yaya za'ayi in tafi yanzu daga zuwa na,ai sai na zauna munyi faɗan da muka ƙwana biyu bamuyi ba."


 

 Ahmad ya ce"Umma daman magana ce akan wannan lalurar taki,munyi magana da wani likita a ƙasar Masar na yi masa bayani agameda komai akan abinda na sani.


 To shine nake son idan har kin yarda in shirya mana tafiya akan zuwa Masar,wani watan mai kamawa kuma inason inyi magana da Baban Noor ma,idan na bar asibitin nan don ya sani da wuri".


 Ƙwalla ce ta fito a idon Umma sannan ta ce"haƙiƙa Ahmad ba nida bakin da zan yi maka godiya,sai dai ince Allah ya saka maka da alkhairi Allah ya ƙara haɓɓaka maka dukiyarka."


 Murmushi Ahmad ya yi sannan ya ce"babu komai Umma ai yiwa kai ne,fatanmu dai albarkar da kuke saka mana ku cigaba da yi mana."


 "Ahmad ai tun ranar da ka taimakeni nake sakaka acikin duka addu'o'i na.saboda irin taimakon da kayi min ba kowa ne zai iya hakan ba."



 "Haka ne Umma na gode sosai."


 Ana cikin hakan ya sayyadi ya shigo,sai dai wani abu daya bani mamaki sai naga Ya sayyadi bai gaisa da Ahmad ba,abin ya ɗaure min kai sosai ko me ya shiga tsakaninsu oho?to sai naga shima Ahmad ɗin bai wani zafafa ba.............✍🏿



 @@Miss green ce🍀🫵🏾




 *Bazan ga ƙaunar da kuke nunamin ba,har sai kun taya ni da share da kuma comments me ratsa zuciya,ina alfahari da masoyana aduk inda kuke.*



 Masu yimin copy na littafi,kuna ɗorawa amadadin ku kukayi,babu komai bazanyi Allah ya ida ba,sai dai in gode muku don na san duk cikin love ne,amman aji tsoron Allah🙏🏼🙏🏼🙏🏼.





_Ummu Maheer_

*DINYAR MAKAHO*



_Miss Hajo_

*KHADIJATUL SABREEN*



_Mrs Bukhari_

*ANGULU DAKAN ZABO*


_Ummu Affan_

*SANDAR MAKAUNIYA*


_Mom Islam_

*TSAUTSAYIN TAUNA*


*Ga tsarin yanda biyan yake*


_Guda d'aya 300_


_Guda biyu 500_


_Guda Ukku 700_


_Guda hudu 800_


_Guda Biyar 1k_



Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.


0037219728

FATIMA RABIU SUNUSI

StanbicIBTC BANK



Shaidar biya ta nan


***


Masu turo kati MTN ta wannan number.


***


Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.


***


Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.