Free chapter · Read without an account
chapter 9-10
GE 9&10*
________________Sapna kam ta zama yar gida domin kuwa ko kadan bata boye wa Naina damuwan ta, kyawon ta ya kara fito, ta kara fresh daman ita kyakyawa ce wahalar gidan su ne ya chanza mata kammani,
Sosai ta kara kyau, sharp dinta ko ya fito coca-cola sak za Masha Allah, domin kuwa idan ka kalle ta kallo daya bata ishe ka ba, sai ka sake kalla, yar karamar yarinya sai diri,
Naina ce ta fara magana "Yar kwarai zo nan, na aike ki, da dan saurin ta taje tace "Gani Naina ina zaki aike ni ne, kin ga fa ban san ko ina ba a fadar nan, cewar Sapna, Dan murmushin gefen baki Naina tayi tareda cewa "eh karki damu tare da Uwale zaku je, ungo wannan Gimbiya Khadija zaki bawa, maganin Yarima ne,
Sapna hannu biyu ta sa ta karbe maganin a ladabce tareda cewa "toh shikenan, Naina kwala wa Uwale kira tayi ko second 2 ba'a yi ba Uwale ta fito daga cikin kitchen, ga Sapna ki raka ta, sashen Gimbiya Khadija cewar Naina
"Angama ran ki shi dade, cewar Uwale Sapna hijabin ta ta saka har kasa, sallama dauke abakin ta suka shiga parlourn taso tayi kauyanci amma babu hali domin kuwa tun shigowan su sarki ya dinga kallon su,
Durkusawa tayi har kasa tana kwasan gaisuwa, Sarki amsa mata yayi fuska sake, yana mai saka mata albarka, sosai ya yaba da natsuwa yarinyar, sai dai ya lura kamar tanada damuwa
Maganar Uwale ce ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya lula, "Mai martaba daman Naina ce ta aiko mu, Uwale ta fada tareda maida kallon ta ga Sapna, "Eh daman Naina ce tace na kawo ma Gimbiya maganin Yarima" Sapna ta fada kamar bata son yin magana,
Sarki nuna mata dakin Yarima yayi tareda cewa "ki shiga Gimbiya tana ciki sai ki bata, godiya ta yi masa ta nufa dakin da ya nuna mata, ita kuwa Uwale wucewar ta tayi abun ta,
*****************
Sapna dakin ta shiga sadaf-sadaf kamar wata mara gaskiya, sallama dauke a bakin ta, Gimbiya Khadija da ke shafa wa Yarima magani a jikin sa amsawa tayi tareda cewa "Au ke Naina ta aiko kenan?" Sannu yar albarka, Sapna maganin hannun ta ta mika mata tareda cewa "Mommy ashe Yarima Sapwan babba ne, ni fa a tunani na nazata karamin yaro ne, Ubanjigi Allah ya bashi lafiya Mommy zan dinga masa addu'a sosai,
Gimbiya Khadija har cikin ran ta taji dadin kalaman Sapna, kuma taji dadin sunan da Sapna ta kirata amsa mata tayi da "Ameen yar nan, kema Allah yayiwa rayuwar ki albarka.
"Ameen tace," kafin ta zauna bakin gadon tana kallonshi, abin abin tausayi ganin yarda yake zalalar da miyau.
hanky, dinta mai kanshi tasa ta fara goge mishi miyau, shi kuwa kafeta ya yi, da ido kamar yasan mai ake ciki, ita kuwa Gimbiya Khadija kallonsu takeyi cike da burgewa tare da kauna, kodan bata taɓa haihuwar Ƴa mace ba , kuma Prince din ma shikadai gareta shiyasa taji kaunar Sapna sosai.
fira suka fara, sunayi tana goge mishi miyau,tare da gyara mishi kanshi dake langaɓewa.
sai gurun 9pm kafin ta koma, part din Nainah.
*****************
"Yan iskan Yara masu bakin jini, kunanan ko dan mai mashin kunkasa samowa sai , shegen kaudi da sa jan baki, kamar karuwa", Inna ta fada da hargowa.
Abasiyya, ce ta juyo tana cewa ,"gaskiya Inna ni ki daina zagin mu, koma menene ai ke kikaja, dan haka Wallahi karki kara zagin mu", ta fada tana murmura ido.
ai kafin ta maida idanunta lafiya lau ji kake kauuuui, Ummi ta wanke ta da mari, zafin marin da ya ratsata, itama ta dauki hannu ta rama.
ai kuwa fadane ya kachame, Abasiyya harda daukar muciyar tuwon Inna, Inna ce tazo raba, aikuwa a rashin sa'a Abasiyya ta rangwala mata muciyar hannunta wani ihun azaba ta saki, tare da durkushewa kasa, tana dafe baya.
da sauri Ummi tayi kanta Abasiyya kuwa waje tayi, tana hura hanci.
da kyar, Ummi ta iya taimakawa Inna ta tashi tashiga ɗaki, ruwan ɗumi ta diɓo a cikin wanda Inna ta daura zatayi tuwo , rigar Innar mai kamar tsunma ta cire kafin ta samu wani dan kyalle, ta fara daddanawa Inna bayan.
har ta gama , ba laifi taji dadin bayan, hakan yasa Ummi tashi, ta nufi ɗakinsu, ita kuwa Abasiyya ko a jikinta , wai an tsikari kakkausa.
*****************
"sai yanzu kike dawowa ", cewar Naina tana kallon Sapna dake zama kusa da ita.
"eh Wallahi Nainah, sai yanzu na tsaya munyi fira da Mommy kuma daga nan, naga Prince wai dama Ashe babba ne, nifa na dauka karamine", ta fada tana kallon Nainah tare da rike baki kamar wata babbar mace.
abin ma dariya ya bawa Nainah, kafin tace "eh mana Babba ne, shine Yaron Sarki na farko", ta fada tana kannanɗa dogon gashin na Sapna dake kwance kan kafarta, dan yanzu ta sabar mata da zama jikinta inda suna zaune.
"aikuwa na ganshi, ya bani tausayi, kuma daga yanzu kullum zanna zuwa ina kulla dashi , ai zaki barni ko?", ta fada tana kallonta.
ita kuwa Nainah, gyada mata kai kawai tayi tana mamakin yanda ta iya zaro magana haka.
******************
"Mai martaba, mai zai hana tunda har yanzun ba'a samowa Prince mata ba, ka naima mishi Auren Yarinyar nan, tunda naga tana da hankali, ga tausayi, ba kaga yarda ta dunga kula dashi, ba Wallahi da miyau ya fito ta goge, kanshi na langaɓewa take gyara mishi", ta fada tana kallonshi.
wani shu'umin murmushi ya saki kafin yace ".............
*muje zuwa........*
*ZAKU IYA TURO DA KUƊINKU TA WANNAN ACCOUNT DIN👇*
*1499884120 UMMA SALMA SANI ACCESS BANK*
*KO KUMA WANNAN ACCOUNT DIN 👇*
*2153892190*
*U.B A BANK*
*MARYAM YUSUF*
*IDAN KUN TURO TO KU TURO MANA SHAIDAR BIYAN TA WANNAN NUMBER DIN👇*
***
*KO KUMA WANNAN NUMBER DIN👇*
***
*ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚♀️🧚♀️🧚♀️ , TARE DA SAHIBAR ROYAL💫💫*