Free chapter · Read without an account

04

by Safiyya Haruna · HATSABIBAN TSIBIRI

Page 04.


Sai dai abin da basu sani ba Lina ta yi yaƙin k'wato masu 'yanci ne domin kanta saboda gudun kada mahaifinsu ya gano tanayin nisan zango zuwa wani yanki batare da saninsa ba haka tana da burin shiga ta alfarma kamar yarda take ganin a masarautun da take zagayawa da ke birane daban daban sannan tana da burin samo ilimin tsafin da zai bata kariya daga zalinci Lima tare da samun damar shiga fadar da jama'a ke turu-ruwan shiga musaman ranar juma'a suma taga wani kalan bauta sukeyi tare da iya yarensu mai ratsa zuciya. (Masallacin Juma'a da karatun Alqur'ani Lina take magana)


Burinta ya cika inda ta cigaba da fita yawo duk inda taga dama a kuma sadda ta so dan har ta kan kwana a can amma bata wuce kwana ɗaya zuwa biyu duk tanayin tafiyar ne bisa amincewar Abun tare da neman albarkan Mah.


Lima hankalinta ya tashi sadda ta fahimci yawon da Lina ke fita wani sabon ilimi take samowa wanda nan gaba zai iya zama bara zama a gareta, sai itama ta soma yin nisan zango saidai ita ilimin zalunci take sake koyowa inda zata dawo tayi ta azabtar da bayi tare da jama'ar gari hakan kuwa na faranta ran Kaka Gunu domin alamomin gadar karagar mulki na ta ƙara bayyana a gareta, sai ya ƙara mara mata baya tana cigaba da zalintar wanda basu ji ba basu gani ba, har saida Abun ya tsawatar mata tare da nunawa Kaka Gunu illar hakan ya ce a bari ta hau mulkin zaifi wannan kalamin nasa ya fusata Kaka Gunu har ya ce ba wanda ta gaji ruwan tulun albarkansa sai Lima sai Abun ya rokeshi da ya b'oye zancen zai cika masa wannan wasiccin.


A cikin wannan tsakani Kaka Gunu ya mutu, Abun ya tafi dan mallakan Ruwan Tulun da sauran sirrikan tsafi amma ifritan da ke gadin Bukkan suka hana shi da ya matsa sai suka nemi halakashi kan dole ya hak'ura amma yana cike da burin mallakan wannan ruwa na albarka.


Bayan wasu shekaru burrin Lina ya cika domin ta samo ilimin da take burin mallaka wato tsafin da ya doke na Lima wanda yanzu take shirya fito na fito da wanda ya nemi kawo mata cikas a cikin manufarta na zamowa magajiyar karagar kujerar HATSABIBIN TSIBIBI domin shimfid'a mulkin adalci gami da samar masu da abin bauta su daina zama kara zube, su sami ilmomi mabambanta haka tana burin ganin wayewar su ya zarta na biranen da take shiga tana ganin cigaba da suke tare da shi mai burgewa haka babban burinta shi ne su sakko daga kan Tsibirin (Tsauni) su gyara dajin ya zamo birni mai zaman kan shi tare da kayan more rayuwa in yaso saman tsibirin ayi masa gyara ya zamo wurin shakatawa na musamman da jama'a daga birane daban-daban zasu riƙa zuwa yawon buɗe ido kuɗin shiga na halal na samuwa ga Tsibirin daga nan ƙarshen zalincinsu ya zo su kowa rayuwar 'yanci mai cike da farin ciki tare da zumuncin ga kowa, baƙi su zamo abar karramawa a tsibirin. Tarihin Hatsabiban Tsibiri da Sarki Goma ya gina ya zamo ya tarwatse sai wanda ta ingana da kanta, sunarta ya zagaye Duniya da tambarin Adalci. Saidai a gefen Lima duk kishiyar burin Lina shi ne nata wanda a kullum da shi take kwana da tashi.


*Wannan shi ne asalin labarin Tsibirin da rayuwar jama'ar cikinsa gami da burikan tagwayen Gimbiyoyin.*


Cigaban labari.


***

Lima a Bukkan Kaka Gunu.


Ta tura kai cikin Bukkan bayan ta yi amfani da alkaliman sihiri k'ofar bukkan ya buɗe, cikinsa katon wuri ne da ya cika da k'okunar kan namun daji kala daban-daban a can daga nesa wani kilisa ne mai daukan ido samansa da kujerar na alfarma ce, wurin Lima ta nufa ta hau saman kujeran ta zauna tana fesar da iska cikin nuna izzar jinin sarauta.


"Barka da isowa uwar gijiyata, me ke tafe da ke?"


Kallon tsamurmurin tsohon ta yi cike da mamakin bayyanarshi ba neman iso daga gareta.


"Affuwan uwar gijiyata na kasance zaune a wannan bigire shekaru masu yawa domin tun sarki na biyu nake a matsayin hadimisa sannan nine sirrin dukkanin sarakunan da suka shude dan haka kema nine idonki akan komi umurninki kawai nake jira yanzu kiga aiki da cikawa."


"Me ye sunarka?"


"Tsidau uban yan binciken wannan fada."


"Madallah, yanzu na zo ne domin sanin abin da 'yar uwata Lina ke boyemin game da tafiyarta da duk abin da ya faru gareta tun kafin tafiyar har zuwa yanzu."


"Kwanta ki huta uwar gijiyata kina tashi na yi alkawarin bayyana miki duk abin da ya shige miki duhu akan Gimbiya Lina."


"Tsidau bana jin barci domin bashi na zo yi ba."


"Dole kiyi shi uwar gijiyana."


"Kada ka kawomin wargi na hukunta ka y kai Tsohon wofi."


"Tuba nake Sarauniyar Gobe, fushinki kukan yaro."


Tana shirin sake magana ya hura mata iskan bakinsa a take ta zame daga kujerar kanta langabe alamun barci ya ɗauke ta, da yatsarshi ya nunata sai gata kwance saman kilisar ta yi matashin kai da wani filo mai zanen fatar jakin daji.


"Shin ta ina zan soma boye miki sirrin abin da kika zo bincike?"


"Bar wurin don ka gama aikinka kafin ta farka na nade sirrin da aka barmata gado."


Muryan Lina ya ratso.


"Na barki lafiya Gimbiya mai jiran gado."


"Ko da yake kafin nan zauna da ita ya kai amintaccen hadimin Sadauki Gauɗu bari in koma na sallami wancan lalataccen kada maikon kogin da ya yi jagorar samar da shi ya halaka shi."


"A dawo lafiya ya ke adalar Sarauniyar Duniya."


Murmushi ta yi tare da b'acewa shi kuma ya gyara zama gaban Lima ya tsirawa hawa da saukan numfashita ido tamkar mai irgawa. Rugigi ya ji a bayanshi kafin ya tantance dalilin afkuwan lamarin Bukkan ya ɗauki rawa wani gaton dutse ya d'ago daga ƙasa inda ke zaune ya nufo inda ya ke yana fesar da koren wuta, tamkar walkiya Tsidau ya b'ace a daidai lokacin Lima ta farka a firgice sai dutsen ya koma mazauninshi tamkar bashi ba. Abun ne ya shigo a rikice ta tashi da hanzari ta isa gabanshi ya rik'o hannayenta ya soma magana.


"Ya ke farin cikina wannan binciken yafi karfinki dan haka ki lamuncemin amsar gadonki domin na samu damar taimakonki."


"Abun zan iya, kabarni da kayana."


"Bazaki iya ba tunda ga shinan an sakaki barci bisa hila wanda saninki da ilimin tsafi bai amfana miki komi ba a wannan gab'an."


"Abun waye Tsidau?"


"Hadimin ne ga 'yar uwanki Lina."


Ware ido ta yi cikin cewa "Lallai Lina ta shiryawa taran aradu."


"Biyoni kawai domin sanin ta inda zaki bullowa lamarin."


Biyo bayanshi ta yi cike da zantukan zuccin wanda ta sanyawa ranta sai ta nemo sanadin afkuwansu dan hatta Abun ta soma wasi-wasin a kansa.


***

Lina ce tsaye a saman ruwan Tekun Kabobo fuska a haɗe ta watsa wani haske da ya fito daga babban yatsar hannunta na dama,a take maikon da ya b'ata ruwan ya soma tafiya har ya b'ace amma launinsa na yellow bai sanja ba. Ta sake tsuke fuska tana fitar da huci zuwa can ta yi gunji ta soma tafiya a saman ruwan a hanzarce har ta isa tsakiyarshi kujerarta ga gold ya baiyana a saman dutsen da ke tsakiyar Tekun inda wasu halittun ruwan sukayi dandazo domin gudun hijira daga halaka, ta zauna tare da tsirawa ruwan Tekun ido da ya ke sake komawa yallow mai duhu, zuwa can dokin Buda ya taso sama ruwa ya yi tartsi tare da fitar haniniyarshi mai firgitarwa inda halittu suka sake rudewa da neman mafaka sai kuma ya koma ciki tsundum! Tamkar an janyoshi, kimanin mintoci biya ya sake tasowa sama wannan karan Buda na kwance saman bayarshi tamkar Gawa, tafiya yasomayi a saman ruwan cikin jan ƙafa saidai kafin ya kai bakin gab'a wani igiya daga kasan ruwan ya fito kamar walk'iya ya maidashi ciki sai ruwan ya sake rukid'ewa zuwa bak'in-k'irin tare fitar k'ugi tamkar rugugin hadarin damina.


Lina da ke kallon komi ta mik'e tsaye da sauri tare da kulle ido ta nuna ruwan a ta ke dokin da Buda suka taso sama ta tura hannunta gaba suka tafi a guje tamkar tsintsaye suka zube a saman yashi da ke gefen Tekun. Ta sauke numfashi ta re bud'e hannayenta ta nuna ruwan ya dawo launin shi fari k'al yana murdewa yarda ya keyi a tun farko, ai kafin kwabo Halittun nan sun soma rige-rigen komawa muhallinsu, ido ta zuba musu tana sakin murmushi ta sunkuya tamkar zata fad'a cikin ruwan sai kuma ta tashi tsaye tana mai shafan gefen fuskanta cikin cewa "Na sami cikar burina na taimakon dabbobin ruwa tare da sokon can Buda, mulkin Adalci ya soma sauka daga hannuna, godiya gareka Sadauki Gaud'u da kayimin komi na ganin na mallaki ilimin tsafin da ya zarce na ko wani matsafi dake nahiyar nan harma da waje ta, hak'ik'a zanyi aiki da Adalci tamkar yarda hakan shi ne cikar burinsa, ganinan tafe zuwa mik'o gaisuwa ga ruhinka abar girmamawata, tabbas idan na zama Sarauniyar Tsibiri kogon da kabarinka ya ke nan ne wurin bautarmu."


Tana kulle baki ta rikid'a zuwa k'aramar tsuntsuwa mai shegen gudu ta lula sararin samaniya ta ɓace tamkar kibiya sai dai tana sauka a cikin kogon dutsen da kabarin Sadauki Gauɗu yake idonta ya sauka kan Hadimi Tsidau kansa sunkuye cikin tsantsar ladabi ya soma magana.


"Uwar gijiyana ayimin gafara lamarin ne ya sha gabana domin na kusa halaka kuma a faruwa hakan na gano ma'adanar tulun sirrin da kike burin mallaka sai dai zamowa mallakinki da kamar wuya saboda manyan iffiritai ne ke gadinsa kuma mahaifinku shima na burin mallakan tulun ya tura 'yar uwanki ne domin ta binciko Tulun sai ya tabbatar ta nemo sai ya taho ya amshe cikin hikima saboda ya san iffiritan da ke gadin Tulun ruwan albarkan baza su yi mata komi ba sabanin da in shi ne zai iya rasa ranshi dan ya taɓa jaraba mallakansa ya sha da k'yar."


Numfashi Lina ta sauke tare da buɗe idanunta da suke kulle tun soma maganar Hadimi Tsidau ta kalleshi na sakonni ta jinjina kai batare da ta furta kalmar ba ta matsa gaban Kabarin Sadauki Gauɗu ta russuna gabansa ta miƙa hannunnta na dama ta ɗora saman Kabarin kanta sunkuye, ganin haka sai shima Hadimi Tsidau ya taho da sarsarfa ya russuna a bayan Lina tare da sauke kansa ƙasa, ta sami mintoci goma sha biyar a haka sannan ta mike tsaye shi kuma Hadimi Tsidau na nan sunkuye cikin girmamawa. Murmushi ta yi kana ta soma magana cikin tsantsar isa da mulki inda kallaman ke fita ɗaya bayan ɗaya.


"Tsidau zanyi aikin da kaina domin ina tare da Zobben sihiri na Sadauki Gauɗu duk da saka Zoben tamkar na yafa mayafin mutuwana ce ga rayuwata amma akan cikan burina zanyi wannan kasadan saboda da in mutu a hannun Lima gara na ƙare rayuwa a matsayin baiwa a masarautar Sarki Gamji ko ba komi shi ɗin mahaifi ne ga shugabana Sadauki Gaud'u."


"A'a Uwar gajiyana banayi miki fatar shiga hannun azzalimin Sarkin nan wanda har 'ƴa'ƴan cikinsa bai bari ba saidai kafin ina baki labarin hatsarinsa zanso sanin sirrin da Zoben ke tare da shi da na kasa ganowa tun sadda mai gidana Gaud'u ke sanye da shi."


"Tsidau bana buƙatar jin komi daga masarautar Sarki Gamji domin Sadauki ya sanarmin da komai sannan Zoben da zan fito da shi yana ƙasan Tekun Kabobo sirrinshi mai faɗi ne domin duk wanda ke tare da shi a cikin yatsarshi yafi ƙarfin duk wani matsafi haka duk abin da ya tunk'ara sai ya samu nasara komin wuyar lamarin, in barka haka."


"Tafdijan amma Shugabana yana da wannan Zoben ya yi sake mugun nufin mahaifinsa ya yi nasara akanshi?" 


"Ya sanarmin ya wuce shekaru bakwai da cire ainihin Zoben a yatsarshi jabun ke sanye da shi tare da boyewa mahara Zoben gano jabun ne ke yatsarsni cikinsu har da mahaifinsa domin burinsa ya mallakamin."


"Shugaba ya sanki da jimawa kenan?"


Jim ta yi domin bata son ambatar ƙaddarar da ya taɓa afka mata wanda ya kasa b'acewa a ranta haka ta kasa maida hankali akan gano dalilin faruwar lamarin kamar yarda tak'i amincewa ruhinta a hukunta mai laifin duk da tarin damar da take da shi na aikata masa komeye da ta so amma ganin Tsidau na dakon amsarta sai ta amsa a takaictda " Eh."


"Affuwan Uwar gijiyana, ban gamsu da amsar nan ba a matsayinsa na sirrintaccen Hadiminki bai kamata ki riƙa bani bayani a dunkele ba dukda ina aljani zan iya gano kome kika boye saidai alkawari nayiwa Shugabana cewa bazan taɓa binciko sirrinki ba kamar yarda ban taɓa gigin binciko nashi ba bisa alkawarin da na daukan masa wanda wannan lamarin yasa aka kawo masa hari batare da na nasan meke faruwa ba dan haka a yau ina neman alfarman ki amince alkawarin da na ɗaukawa Shugabana ya zamo tarihi inda zan riƙa sanin abin da zai sameki na kangin rayuwa kafin ya iso na tareshi na maidawa wanda yayo aiken."


"Godiya nake ya kai Tsidau amma ban amince ka zamo cikin marasa cika alkawari ba, ina son ka yarda komi nawa kada ka binciko sai wanda na baka dama, ka dauwamma a aikinka na ɗan aike tare da rakiya zuwa inda nake da muradin tafiya da kai."


"Angama ya ke Uwar gijiyana, Gimbiyan gobe bisa amincin mahaliccin tsuntsaye da tsirrai."


"Tsidau ina yawan jin kalaman nan a bakin Sadauki Gauɗu sannan duk in ya furta na kanji kaina ya yi girma basirana ya toshe inda nake hango kaina cikin wani duhu tare da haske daga nesa can, shin me hakan ke nufi?


"Uwar gijiyata rayuwar Shugaba na tarin ababen al'ajabi domin duk nacina akan ya bayyamin sirrin da ke cikin kalaman nan ya k'i dan haka ban san komi akai ba domin harshesa nake kwaikwayo har na ambata miki hakan sai dai ina ta tabbacin wani abin bautane mai girma da ƙarfin mulkin da ya doke wanda su Sarki Gamji ke bautamawa."


"Zanzo sanin shi ko da kuwa hakan zai iya zamowa ajalina ne."


"Uwar Gijiyata kidaina ambatar mutuwa baki zamo Shugaban Tsibiri ba wacce adalcinta zai kewaye Duniya."


Murmushi ya kubce mata sannan ta fuskanci Tsidau tana mai cewa "Ya kai amintaccen Hadimina hakika mun kusa rabuwa domin da zarar na sanya Zoben zan bacewa ganinka na har abada haka zaka tsinci kanka cikin jinsinka cike da yanci daga nan kazamo mai yantacce daga bawa ni kuma zan mallaki Tulun sirrin saidai ba zan jima ba akan karagar mulki Sarki Gamji sai aikomin da sako walau irin wanda ya aikowa Sadauki Gauɗu ya halaka ko ya ɗaukeni daga yankin zuwa kurkukunsa na karkashun ƙasa na tabbata a can har zuwa mutuwa ya riskeni dan haka zan koma Tekun Kabobo in d'auko Zoben, ina godiya da taimakon da ka riƙa bani na duk abin da nake son ci da sha tare da sutura, gaisuwata mai yawa zuwa ga iyalenka."

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.