Free chapter · Read without an account
06
06
Tafiya na ƙara nisa inda zuwa lokacin Aliyu Malle ya tara iyali mai yawa dan ya auri bafullatanan da ta yi makuwa mai suna Mero haka ya nemi aure a wurin wani Buzu shima da ya fito ci rani yaga dajin Mungaye ya zama maraya sai ya zauna da iyalinsa, sannan ya koma Asalinsa ya auro 'yar uwarshi Kanuri inda ya auro har guda biyu, a lokacin danginsa suka soma nuna masa ƙauna tunda suka gansa cikin rufin asiri musamman sarautan da yake da shi yanzu na matsayin Sarkin Birnin Mungaye. A wannan komawa danginsa da yayi wasu daga ciki suka biyoshi tare da iyalansu sai Masarautan Mungaye ya sake cika da al'umma. Daga nan auratayya ya cigaba da kulluwa tatsakanin kabilun uku wato Barebari, Fulani da Buzaye.
Wannan auratayya da ya kullu tsakaninsu sai ya tsakud'a ya fitar da wata kalan al'umma masu kyawun sifa gami da kyawun launin fata, fuska dana sura. Kowa ka gani a cikin birnin Mungaye mai kyawu ne musanman 'ya'yan gidan sarauta domin Sarki da matarsa masu tsan-tsar kyau ne, wasu masu hasken, wasu mai sirki da ja da kuma masu haɗi da duhu kaɗan amma duk wanda ka kalla mai kyau ne a Masarautan dan har akanyi masu kirari da Birnin Mungaye mai kyawawan Mata.
Birnin ta sami wayewa bisa ziyartan turawa inda suka gina makarantun Boko tare da kawo malamai suka riƙa koyar da su ilimin zamani duk dama can akwai masu Ilimin daidai misali musanman Sarki Aliyu Malle tare da danginsa, sai dai hak'ar Turawa bai cimma ruwa ba na samun nasarar rabasu da addinin da suka samesu akai wato Musulunci wanda burin sanja masu tunani ne su koma bin addininsu ya sanya suka shigo birnin sai suka samu Sarki Aliyu Mallae ya yi namijin kokari akan al'umman shi na ganin sun ginu akan turban gaskiya na kaɗaita Allah Subbahanatu Wa Ta'alah gami da riƙo ga sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, shi yasa har izuwa yanzu Birnin Mungaye cike ya ke da musulmai, malamai gami da tsirarun mabiya addinin Yahudu da Nasara wanda suke zaman lafiya da juna domin tun tarihin kafuwar Birnin babu abin tashin hankali da ya taɓa kawo matshi ziyara ko riciki a bisa bambancin Addini ko wani tarzoma na daban sai dai su jiyoshi a makwaftansu saboda sunyi imani da Allah ɗaya ne kuma suna masu jajircewa wurin zaman addu'o'in samun kariya ga Birnin tare da zaman lafiya tsakaninsu suma sauran k'abilun nayin irin tasu addu'ar awurin bautarsu. Wannan tsarin ginin tubalin zaman lafiyar duk ya samune bisa jajircewar mai Mungaye wato Malami, Sarki kuma Limamin Birnin Aliyu Malle wanda ya rasu shekaru masu yawa sai tsa-tsonshi sukayi ta gadan Sarautar har zuwa kan sarki na yanzu Sarki Abdul Hakam. A dalin jagora tamkar 'yan uwanshi da suka gabata sai dai shi ne Sarki mafi wayewa domin dan Boko ne na gaske wanda ya taka har zuwa matakin Professor, shi yasa hawa karagar mulkinsa ya zo da sauyi wurin shigo da abubuwan Zamani fiye da sarakunar da suka gabace shi.
Abin burgewa ga wannan ƙasaitacciyar masarauta shi ne riƙon Addininsu domin har zuwa yanzu sarakunarsu sune Limamai kuma masu gabatar da tafsirai a lokacin Azumin Ramadan dan haka babban masallacin Juma'a na garin a kofar Fada take kamar yarda mafi yawan masarauta aka sani da gina Masallatai da ake sallar Juma'a a Fadar su, saidai wannan a cikinta ake sallar Idi dan takasance mai girma tamkar wata Masarautan kaso sake ginawa haka a gefen Masallacin wani daji ne da aka killace shi aka cika shi da shuke-shuken kayan marmari wanda ina mutum ya shiga zai dauka a wani yanki na daban ya ke saboda yalwar bishiyoyi tare nisan tafiya kafin a isa k'arshenta, aka ba wurin suna da Mungaye Garden.
Wannan ak'idar da Masarautar ta ginu da shi na son Musulunci da Musulmi shi yasa jama'anta suka kasance masu karamci ga bak'i masu zuwa fatauci da zama na mundun rai. Dan ƙasar Mungaye Allah ya hore mata kyawun fitar tsirrai (Amfanin gona) shi yasa Manoma suka cika garin ta ko wani sassa da ke makwaftaka da ita, lamarin da ya kara daga darajar Birnin ta zamo abar yabo ta ko ina haka duk inda ɗan Masarautar ya shiga yana da alfarma.
Mai martaba Abdul Hakam na da Matan Aure biyu. Uwar gida Hajiya Hafsatu (Umma Babba) da Amarya Hajiya Murjanatu (Mami Fulani) da yara maza da mata sai dai 'ya'ya matan ne manya domin wasu sunyi aure tare da albarka zuri'a. A yanzu Mai martaba girma ya soma kamashi, babban burinshi ya yi murabus ya dank'a mulkin hannun ɗaya daga cikin zaratan matasan 'ya'yanshi wato Ahmad (Sardauna) da Aliyu (Saudauki) Sai dai ƙurar da ke hangowa ya sa ya tsuke bakinsa akan ayyana wanda zai zamo magajinsa cikinsu, ya zuba masu ido yana sake lak'antar halayyan kowa tare da wanda Jama'a sukafi nuna k'aunarsu da ya zamo jagoransu makar yarda mahaifinsa ya yi sadda aka bashi mulkin duk da baida ra'ayi amma jama'ar gari suka nuna shi ne zaɓinsu kuma ba jayayya 'yan uwansa sukayi masa mubaya'a sai dai a wannan lokacin baijin shi zai sami sauk'in dank'a mulki da ɗaya daga cikin 'ya'yan nasa ba saboda kowa yana nuna mulkin ya ke so bakin rai bakin fama.
A fannin Yarimomin Mungaye kuwa duk sun can-canci hawa karagar mulkin sai dai jama'ar gari sunfi nuna ra'ayinsu akan Sadauki sama da Sardauna duk kuwa da matsalar da ke ga Sadaukin na auri saki domin a shekaran da ya gabata sukayi auren fari amma zuwa yanzu ya mata huɗu ya aura ya saki batare da sanin laifin da suke aikata masa ba domin ya k'i yin bayanin da yasa ke aikata sakin haka suma matayen idan an tambayesu amsar ɗaya ce suke bayarwa ita ce basuyi masa laifin komi ba ya sallamesu ba tare da ya haɗa shimfida da su ba.
Cikin matar na ya saka akwai ta farko 'yar kanwar Sarki mai suna Mubina wacce aka aura masa tana da k'arancin shekaru domin kammala secondary dinta kenan a ka yi mata aure cikin rashin son ranta inda shi kuma Sardauna aka aura masa 'yar Waziri wanda shima ya ke kani ga sarki kuma har wayau k'anwa ce ga aminin Sadauki wato Abubakar ana yi masa alkunya da Imam, wacce ta kasance babba mai yalwar komi na cikar halittar mace sama da Mubina, wannan bambancin da ke tsakanin matan nasu yasa sadda Sadauki ya saki Mubina a washegarin kaita gidanshi yasa hankali bai wani tashi ba musamman da ita Mubinar ta yi ta murna har aka ɗora laifin akanta ganin yarda ta yi ta boren bata son auren sai ake zargin ita ce ta nemi sakin da kanta.
Matarsa ta biyu 'yar Aminin Sarki ne wacce ta zamo mai wayewa domin ita tana da degree har biyu amma kwanarta uku a gidanshi ya saketa hankali ya tashi a wannan karon amma Sadauki ya nuna ko a jikinsa, akan haka Mai Martaba ya ce ya gama samo masa matar aure. Bayan watanni Mamie Fulani ta matsa sai ya amince da auren 'yar aminiyarta inda ya amince bisa takurashi da tayi saidai shima auren kwanarshi daya ya bata sallama inda kafin ta isa cikin Masarautar da labarin ya tsere gidanshi da ya gina a b'oye da ke dajin Tekun Kabobo wurin da ba wanda ya sani sai amininsa Imam da turawan da sukayi aikin. Bayan wasu watanni ya dawo ya sha faɗa tamkar Sarki zai dukeshi ya yi ta basu hak'uri, anan suka rutsashi sai ya sanar masu da matsalarshi Amma yak'i magana akan dole suka rabu da shi, daga nan bai sake aure ba sai wata ɗaya da ya wuce inda Na'ibin Sarki ya bashi sadakar d'iyarshi mai wadataccen ilimin addini sai dai yana jin labarin ya hankalinsa ya tashi inda Mami Fulani ta rufe shi da faɗa tare da gargadi akan kada ta sami labarin ya saki yarinyar inko ya kuskura ya aikata mai rabata da shi sai Allah wannan kalma ya hura wutar jin rabuwa da Sakina wacce a ranar da aka kawo mashi ita ya bata saki wanda faruwar haka ya saka Masarauta zama akanshi a karan farko tun soma wasa da auren da keyi gami da son zubar da Martaban Masarautar su domin lamarin na taɓa ran manyan masarautar musanman Baba Chiroma da yafi kowa zafi haka ansha mamaki da har zuwa lokacin bai nemi ganawa da Sadauki ba shi yasa yanajin sakon kiran da yafito daga bakin sa sai ya gudu mab'oyarshi tare da gargadin Imam akan kada ya sake ya tona inda ya ke. Sai da ya sami wata ɗaya da kwana biyar wato sati biyar kenan sannan ya dawo inda ya ke kan fuskantar fushi daga mahaifanshi ya yin da dan uwanshi Sardauna ke yi masa shagub'e na kiranshi da kalman mai auri saki mara godiyar Allah, duk da kalaman nayi masa ciwo amma ko kallo bai isheshi ba balle ya tsaya bashi amsa wanda ke kallo a matsayin bata lokaci sannan duk da hakan kauanrshi ga Jama'ar gari bai rage komi ba wannan lamari ya rage masa damuwar da ke ciki na fushi da mahaifanka keyi da shi. Duk da b'oye halin da ke ciki da ya keyi amma kallo ɗaya zakayi masa ka gano yana cikin matsanancin damuwa wanda Amininsa Imam ke aikin bashi baki.
***
Aliyu Sadauki.
Tsaye ya ke a bakin window dake bedroom dinsa inda ke kallon kai da kawon hadimai bisa alamu manyan baƙi ne zasu halarci Masarautan. Bushe-bushen da aka soma ne ya sashi barin wurin ya koma saman sofa ya kwanta idanunsa na kallon sama zuwa can ya tashi zaune ya furzar da iska mai huci tare da kaiwa k'irjinsa duka ya rintse ido da hanzari jin yarda zafi ya ziyarci wurin da ya duka. Ya juya kai cikin furta "Why ta zamemin masifa a rayuwa? Shin aina zan sake ganta? Shin ita din mutum ce ko aljana? Me yasa na aikata mata haka? Shin har sai yaushe zan fita daga wannan rayuwar na fitinuwa da son kasancewa mace amma ko ta zo gareni sai naji banda mak'iya irinta?"
Kwalla ne ya taru a kwarmin idanunsa ya kai hannu ya goge tare da tsirawa ruwan hawayen ido da ya shafo.
"Narantse duk ranar da na sake ganinta sai na wulak'antata fiye da yarda take kan wulak'antani yarda zatayi jinya tare da shiga damuwa sama da wanda ta jefani ciki."
"Wacece ita Aliyu?"
Kallon Imam ya yi wanda bisa alamu ya jima tsaye bai sani ba.
Ganin da Imam ya yi ba zai sami amsar tambaya ba sai ya tako ya zauna gefenshi ya kamo hannunsa cikin sanyin murya ya soma magana "Please Sarkin gobe ka daure kayimin bayani yarda zan fahimta wanda zai fitar da su Mamie Fulani daga zargin sihiri akayi maka wanda ba dare ba rana suke mik'a kukansu ga mai warware k'ulli batare da gajiyawa ba akan abinda ke jikinta ya fita ka yi aure ko saga jininka kafin su koma ga mahalicci su."
Shiru bai tanka ba saima kwanciya da ya yi yana jin mararsa na kartawa tamkar yarda ya saba ji duk in ya shiga tunanin sanin wacce ke alak'anta silar rashin zamanshi da matarsa na aure.
"Yar gidan waye? Me ta ke tak'ama da shi? Shin zan iya samun wadannan tambayoyin daga bakin Aliyu Abdul Hakam?"
"No."
"Why?"
"Imam ban santa ba haka ban san me zance maka akanta ba."
"Ikon Allah, wato ta tabbata Aljana dai kenan?"
"Ina tunanin hakan."
"To aina ka gamu da ita?"
"A Barci."
Ya samu kanshi da ambatar hakan alhalin ya san ba hakan ba ne.
Shiru Imam ya yi na kallonshi ya yin da shi kuma ya kauda kai gefe,murmushi ce ta kufcewa Imam har da zarcewa da guntun dariya lamarin da ya fusata Sadauki ya mik'e ya nuna masa kofar fita sai kawai ya kulle bakinsa da tafin hannunshi ya cigaba da dariya har da fitar kwalla.
"Na haukace ko Imam?"
"No Brother kawai dariya k'aryar da ka yanko ne ya bani domin k'arara ka tona kanka ba gaskiya ka ambatamin ba."
"Me kake nufi da kalamanka?"
"Nothing, but sit and tell me the truth, dan wallahi ba zanyi kaffara ba, ba gaskiyan kenan ba."
"Nagode da maidani mak'aryaci da kayi kuma ka fice alamarina, bana son sake ganinka kusa da ni, yes na amince na rayu cikin kaɗaici kamar yarda Mamie ta furtamin, Abba ya bawa sokon danshi mulkin Mungaye, Umma ta cigaba da kirana mara amfani."
"Innalillahi! Sadauki yaushe Umma ta ambata maka wannan mugun kalman?"
"I said get out! Malam."
Ya ambata tare da jan hannun Imam ya mik'ar ya soma ja har zuwa bakin falonshi sannan ya sakeshi ya koma saman Cushing ya zauna ya rik'e kanshi gam wanda ke jin tamkar zai fice daga muhallinsu.
"Affuwan A...
Hannun da ya daga masa yasa Imam gintse ban hak'urin da ke nufin bashi.
Tsawon mintoci uku ba wanda ya yi magana sannan Sadauki ya mik'e ya doshi hanyar bedroom saida ya tura kofar sannan ya yi magana cike da izza ya ce "Ka shirya idan anyi sallah zaka rakani sake bawa su Abba hak'uri a turakarshi dan yau Mamie ke da girki kamar yarda Lailah ta sanarmin."
"Ok Allah ya kaimu."
"Amin."
Ya amsa can ƙasar mak'oshi wanda ko Imam bai jiyoshi ba.
***
Durk'ushe suke gaban Mai Martaba Abdul Hakam da Mamie Fulani. Imam ne ke ta ban hak'uri ya yin da Sadauki yake ciccira hawaye nayi masa zarya na bak'in cikin jin kalaman da Mamie Fulani ta ambata sadda ta ganshi gabanta.
'Ban son sake ganin fuskanka Babana domin k'unci nake shiga a duk sadda ka ziyarceni dan haka kada ka sake zuwa inda nake na rok'eka.'
Toshe kunnuwansa ya yi tuno kalaman, ya d'ago kanshi hawaye wani na bin wani duk da zamowarshi mara saurin kuka amma kalaman Mami ya sakashi kasa jurewa. Ya sarrafa cikin sarsarfa ya isa bagan Mamie Fulani ya sauke kanshi a saman k'afafunta yana furta "Ki yafemin Mamiena wallahi ina cikin iftila'in rayuwa ne domin fushinki guba ne gareni dan ba zan tab'a sake yin tasiri ba har abada."
Sai ya fashe da kuka mai sauti wanda rabon da ya yi irinsa ba zai tuna ba. Ganin haka sai Imam ya tashi ya fice da sauri yana goge hawayen tausayin Amininsa.
Momyn Haske ce🥰