Free chapter · Read without an account

BAKAR FURA CHAPTER 1

by Fadila Lamido · BAKAR FURA

*🕳️BA'KAR FURA🕳️*

   _A true life story_

*Na*

_Fadeela Lamido_

  PEN WRITERS ASSOCIATION✍️

*✍🏻✍🏻BAKAR FURA lbr ne da yafaru da gaske, wanda yake dauke da Soyayya me kayatarwa, ga tarin Nishadi, ban al'ajabi tare da ban tausayi, gameda fadakarwa, wadan da abun ya faru dasu muna nan muna cigaba da rayuwa tare dasu cikin wannan duniyar tamu,Allah yabani ikon isar da sakon yadda ya dace.*

              *Episode 1- 2*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

              Cikin kasar CAMAROON (1995)👈

                        

_Alif dubu daya da dari tara da casa'in da biyar_

Ke!! Ke!!! dakata maza ki tattara kafafuwan ki ki koma gida.

   Cak yariyar da ake dakawa tsawan ta tsaya cikin yanayin rashin jin dadi.😔

       Wasa ta shigayi da fararen yatsun ta, tare da zuba masu ido, saidai ko motsi batai ba bare ta juya kamar yadda matar dake zaune gefenta ta bukata.

           Cikin fullaci matar ta sake mgn kamar yadda tayi da fari tace, " wai badake nake mgn bane kika min tsaye"?

         Har yanzun yariyar na tsaye bata juya ba, ko motsi ma batai ba, fitowan wata dattijuwa tana fadin yaya akayi ne?, yasa su duk suka kalleta"

    Itako wannan matar kawar dakai tayi can gefe.

   Kallo tattijuwar tabi matar dashi sannan ta kalli kyakyawar yariyar dake tsaye tayi murmushi ta matsa gefenta tana fadin *Aysha* zo ki wuce.

      Cikin sunkuyar dakai yariyar ta wuce, tana waigen wannan matar, bayan ta kulle ne matar tabi bayan yariyar da harara ganin dattijuwar na kallonta tai saurin dauke kanta can gefe cikin yanayin jin kunya.

      Matsowa dattijuwar tayi kusa da matar tana fadi cikin harcen fullaci, " Fatima kibar kyaran ta"

        Batare da matar ta juyoba tace " Innawo kina kallon fa yadda 'yan gidan su suke nunawa baro baro basu son shigowar ta.

   Duk cikin harcen fullacin suke mgnr da alama fullacin kawai suke ji bisaga la'akari da yadda ya rike bakin su.

          Me ya dame ki?, wani ne yaje ya kirata ne?, inace ita ta kawo kanta?, babu ruwanki, idan har basaso su dakatar da ita daga can.

      Batare data juyo ba tace shike nan.

      Zama sukayi suka cigaba da hira har tsayon wani lokaci, zuwa can *Aysha* ta fito hannunta dauke da littafai, inda suke ta kalla cikin sakin fuska tace, "natafi"

    Innawo ce kadai ta amsa sannan ta wuce ta fita.

      Hira Innawo sukaci gaba dayi, zuwa can na hango wani zafgegen saurayi, wankan tarwada shiba fariba Kuma ba baki ba, dogo, kwantancen saje gewaye da fuskarsa, kananan kaya ne ajikin sa yana takawa da karfi irin na jajartattun maza, idon sa tubarkallah, mayya ne, ko ince wadatattu, tafe yake fuskarsa kadaran kadaham, shiba fara'a yake ba, Kuma ba daureta yayi ba, wuce su Innawo yayi yana kokarin barin gidan yaji ance zonan"

      Cak ya tsaya tare da dawowa baya yana binsu da kallon kasan ido yace gani"

       Naga ka wuce ne kamar bakasan damu agurin ba?

    Naga ganku, nace sannu ku ai"

     Cikin lumshe ido matar tace bamuji ba.

   Innawo ya kallah sannan yace Innawo kema bakiji ba?....

    A'a babu ruwana, wannan mgnr ku ce naga dai kamar ka motsa leben ka ko?

         Kawar da kansa yayi sannan ya juyo ya kalli matar data daure fuska sosai ya hadiye yawu tare da fadin, toh Ummi sannu ku"

    Kawar dakai tayi batare data amsa ba, ganin haka ya dan sake kallonta yana sake fadin, bari naje na dawo"

       Ahankali tace adawo lafiya"

     Allah yasa, yafada sannan ya juya ya fita.

        *******

*Aysha!!!*

   Na'am Mama!

    Mikewa tayi ta fito da littafanta a hannunta da alama karatu take yi"

      Jikin mahaifiyarta ta fada cikin nuna tsananin so ta rungumeta tacin fullacin tace"

        *Aysha* baki gajiya da karatu ko?, yau ko abinci banga kinci ba fah"

  Mama banjin yunwa"

   Inafa zakiji yunwa tunda kin rike littafai"

    Karatu nake mun kusa fara jarabawa"

     Littafin dake hannunta ta karba ta duba cikin yamutsa fuska tace"

      Wannan ba rubutun ki bane, bayan littafi ta duba sannan ta kalli *Aysha* tace, littafin naki ne, rubutun fa na waye?

       Dagowa tayi daga jikin mahaifiyar tata tana me kallon cikin idonta cikin alamun rashin gaskiya tace"

         Ya *Aliyu* ne ya rubuta min.....

     Cikin zafi ta make bakin Aysha tana fadin, yaushe kika sirare kika fita?, wato ke bakijin mgn ko?

    Rike bakin Aysha tayi idonta na tsiyayan hawaye tace, Mama idan banje ba waye ne zai koya min karatun?

    Mama ta bude baki zatayi mgn wata tsohowa ta fito daga wani daki tana fadin"

        Ai sai kinyi da gaske idan kina son ki raba Aysha da yaron nan, ai ina kallonta sanda ta fita zuba ido kawai nayi, tun dake kin bari ni yaya zanyi?

      Nifa Umma bahaka bane, ai dole sai kun tayani, idan anga tayi abun da ba daidai ba a kwaba mata"

    Cikin kawar dakai tace shikenan, abin da yafi Sam ahana ta shiga wannan gidan, gaba daya, idan mu kin rainamu baki tsoron mu nasan dawa zan hadaki, gaba daya yayyen uwar ki zan sanar abun da kike yi"

     Ganin Inda Umma ta Kura mata ido ta kalli mama sannan tai kasa da kanta.

      Umma kuwa haka taita maganganu yayin da Mama ke taya ta, *Aysha* kuwa saurare kawai take"

       Washegari da misalin karfe 2 *Aysha* ce ke tube kayan makaranta sannan ta saka yar karamar riga da siket dinta daidai guiwa, irin me budewa gaba daya, littafinta ta ciro guda daya tare da biro ta zauna tana fakan idon su Umma dake aikin girki can bakin kitchen, ganin sun maida hankalin su sosai kan aiki ta wuce suf suf ta fice"

           *******

  Ahankali ta tura kofar bakinta dauke da sallama.

     Dagowa saurayin yayi ya kalleta sama da kasa sannan yai saurin dauke idon sa ya maida kan yariyar dake zaune gaban sa tana rubutu cikin littafin dake gaban ta"

    Karasowa tayi kusa da yariyar ta zauna yayin dataga saurayin ya sake dagowa ya kalleta akaro na biyu, kallo ta bishi dashi yayin dataga kamar yana motsa lebensa, kallo taita binsa dashi Kamar yadda shima yake binta dashi saidai bata ankara ba taji ya buga wata irin tsawa me rugugi wadda yasata sakin littafin da biron batare data shiryar ba, bata ankara ba sai ganinta tayi akofar gidan cikin yanayin haki ta tsuguna tana maida numfashi"

        Dariya taji asaman kanta dan haka tai saurin dagowa ta kalli yariyar sannan tayi ajiyan zuciya tace"

      Husna me namai?

    Cikin matsanancin dariya wadda aka Kira da suna Husna tace yace kizo"

         A'a nikam bazani ba"

   Dariya Husna ta sake yi sannan tace tashi muyi sauri mukoma karyace mun dade, muje ba abun da zai miki"

    Cikin rashin fahimta tace mena mai toh?

     Ke dai muje mana"

     Wlh Husna masifar tsoron wannan tsawar tasa nake"

   Jikin Aysha Husna ta kalla yadda jikinta ke buga uban rawa ta kara fashewa da dariya tana fadin, " aikuwa kina da aiki"

    Daker Aysha tace kemafa kina firgita idan yayita"

   Ina firgita amman jikina baya rawa, waigawa tayi ta kalli fokar gidan nasu sannan tace kitashi muje.

   Ahankali suka shiga dakin, Husna agaba *Aysha* nabinta abaya cikin tafiya ahankali har suka isa gaban shi"

       Zama sukayi duk su biyun yayin da *Aysha* ke Satan kallon shi, ganin da tayi Kamar bashi ne ma ya buga tsawar dazon ba tayi ajiyan zuciya adaidai lokacin da yace, matso ke"

        Cikin tsoro sosai ta matsa gabansa, wani irin radadi taji a tsakiyar kanta, dan haka tai saurin runtse ido tare da yamutsa fuska cikin yanayin dake nuna tanajin zafi"

    Shikuwa Aliyu kalabar dake kanta ya rike tsoro biyu tun daga tushen su yake fadin meyasa baki rufe kanki ba?

     Macewa nayi ya *Aliyu* kayi hakuri.

  Mantuwa fa kika ce?, Shekarun ki nawa?

        Dan Allah kayi hakuri bazan Kara ba"

   Tambayan ki nake ai, shakaran ki nawa?

   Kasancewar yana Kara matsewa hakan ke Kara sata rikecewa cikin sauri tace, goma sha uku"

   Kawar dakai yayi batare daya saki kan nata ba yace, toh kinji goma har sha uku, amman kika iya tsallako gida nawa kika taho ahaka, gida nawa kika tsallake kafin kikazo nan?

     Wayyo Allah, dan Allah kai hakuri kaji"

     Sakin kan yayi da sauri yana fadin nayi hakurin, amman karna Kuma ganin ki ahaka"

     Kanta ta gyada tare da kokarin share hawayen ta.

     Aliyu kuwa Husna ya kallah yace, kuje kibata zani da hijjabi, Amman kuyi sauri fita zanyi"

    Cikin kankanin lokaci suka dawo sannan yai masu karatun kamar yadda suka saba, cikin lokacin dabe wuce awa daya ba suka gama, a tare suka fito cikin sauri yabar gidan yayin da *Aysha* ma ta nufi gida.

           *******

 Innawo!!!

  Gaban Innawo ne ya yanke ya fadi jin Kira cikin fada da hargowa, fitowa tayi tana zare ido ganin Umma tsaye atsakar gidan yasa tace"

  Au kece?, Lafiya kika shigo babu Sallama?🤔

      Kashedi na kawo miki, *Aliyu* ya fita harkar *Aysha*, idan ba haka ba kuwa wlh zan dauki mummunan mataki akan shi"

     Subuhanallahi, to wai me yake faruwa ne?

   Babu komai kawai ni alakar tasu ce banaso"

      Ai basu da wata alaka, Umma ki kwatar da hankali ki, inace *Aysha* gurin Husna take zuwa, so da yawa zatazo tasamu Aliyu nama Husna karatu dan haka itama tafara zuwa da dan littafin ta, ni banga abun tashin hankali ba anan"

      Kece baki ganshi ba, nikam na ganshi, banso ne Sam idan ba haka ba duk abun da ya faru karkuga laifina"

        Babu abun da zai faru sai alheri, kuma jikarki indai baki son ta shigo gidan nan ki tare ta acan gidan ki dan nikam ba me gadin ki bace......

     Muryan Ummi sukaji tace, "Umma jeki duk ranar da *Aysha* ta shigo gidan nan zan mata korar wulakanci"

        Aikuwa dakin birgeni, juyawa tayi tanacigaba da fadin maganganu yayin da Ummi ta Kara kulewa sosai"

   

             **********

         Tsayon kwana biyu aka kwasa *Aysha* bata shigo gidan ba, yayin da duk Husna taji wani irin, domin ta saba kullum zasu hadu bayan sun dawo makaranta, gaba dayan su zaune suke a tsakar gida har Aliyu, Ummi ce ta kalli Husna tace, "waike meke damun ki?"

       Ahankali tace babu komai"

    Aliyu ne ya kalleta ta gefen idon sa tsayon lokaci kafin yace, ke me yake faruwa?

      Ummi da Innawo ta kalla ganin basa kallon ta tai kasa da muryar tare da fadin, kwana biyu *Aysha* batazo ba, Kuma Ummi ta hanani fita"

       Kallon Husnah yayi sosai sannan ya maida hankalin sa gurin kallon su innawo yana fadin jeki Kira min ita.

         Wa za'a Kira maka?, Innawo tayi tambayan tana tsaresa da ido"

    Kai tsaye yace *Aysha*"

   Aysha?, *Aliyu* Aysha fa iyayenta bason shiguaarta gidan nan suke ba, ko shekaran jiya bayan kagama masu karatu nan kakarta tashigo taita fadar maganganu marasu dadi, ku fita harkar yariyar nan"

         Wai akan me take mgnr wai, ya fada yana kallon fuskan Innawo"

     Au tambaya keke ne?, Ana cemaka ku fita hanyarta kana tambayan dalili? Ummi ta fada hakan cikin tsare sa da ido, dan haka yadanyi kasa da kansa sannan yace

       Naga ai karatu ne ke kawota ba wani abu ba, amman ni meye nawa, shiguwar tata mezata kara min?

    Mikewa Ummi tayi tana fadin nima abun da nagani kenan"

          **********

   Abincin dake gabanta take ta juyawa tare da fakan idon aunty Murja dake gefen ta, tana bude jakar makarantar ta ahankali ta jawo littafin ta wadda tasaba zuwa dashi karatu kowanni lokaci, rigarta ta daga ta tura shi cikin siket dinta, agogo ta kalla domin tasan ya Aliyu 3 yake fita gashi yanzun biyu har da kwata"

   Aunty Murja taita satan kallo daga can taga ta mike ta shiga dakin Umma dan haka tai saf saf ta fice agidan.

        *********

Babu kowa a tsakar gidan cikin siririyar muryarta ta shiga sallama daga can Husnah ta amsa mata.

    Falon taji Muryan Husna dan haka can ta nufa inda ta hangesu Husna zaune akasa yayin da Ya *Aliyu* ke zaune kan kujera idonsa akan littafin Husna dake hannun sa"

      Har Aysha ta zauna beyi mgn ba, Kuma be dago ido ba, ahankali Aysha tace " Ya Aliyu ina yini"?

     Lafiya lau ya fada batare daya dago ya kalleta ba"

*Gyara adon mace, komai yanason gyara, idan kina dakyau kira da wanka, dan haka mata atashi agyara, akwai kayan gyara lada da kala sai wadda kika zaba domin gigita me gida, sabbabin amare ina da irin naku, yan mata masu shirin shiga daga ciki kuma akwai naku na musamman cikin rahusa mai sauki, ina aikawa kowanni gari, ina da tabbaci akan kayana, idan kika gwada saikin dawo insha Allahu, gamasu bukata su tuntubeni ta wannan no ****

       Bayan yagama duba littafin Husna yace matso, gaban shi ta isa ta zauna, cikin nutsuwa yake Kara fahimtar da ita saida ya tabbatar ta gane sannan ya tura mata littafinta yana fadin, *Aysha* muga naki"

   Mika masa tayi tunda ta shigo har yanzun beko kallesu ba, duk bayanin da yake idonsa nakan littafi, cikin kankanin lokaci ya tura mata littafin bayan ya tattabar itama ta fahimta, sannan ya mike yana sauke ajiyan zuciya.

       Aysha!! Aysha!!! Jin wannan Kiran yai matukar firgita Aysha, mikewa tayi da sauri ta koma bayan Ya *Aliyu* tana zare ido.

      Tsuhuwar ce ta sake fadin Aysha bazaki fito bane saina shigo na rafke kafafuwan naki sun dagargaje??

      Juyawa yayi ya kalle bayan sa da Aysha take lebewa, kallo daya ya mata tai saurin fitowa ta isa gaban kakarta, yayin da tai saurin rike kunnenta ta murdeshi tana cewa, " ke wato kunnen ki nakashi ne ko?, kullum ana gaya miki mgn bakiji ko?, Ko kullum ba gaya miki ake ki kiyaye wannan abun ba?

       Cikin kuka take kokarin kwace kunnenta yayin da Husna take fadin Umma kiyi hakuri dan Allah.....

  Ke dallah rufe min baki, da hakurin ta mutu Sadakan nawa kika bada?, ni kujimin mara kunyar yariya wai wani Umma yi hakuri, inyi hakuri in saki jikata sakaka saikace goyon gwauro ?, ba tsari ba lissafi dake ni fitsarriya ce, duk cikin harcen fullaci take mgrn tana iza keyar Aisha

      Fitowa Aliyu yayi batare daya kalle inda Umma take ba yake kokarin ficewa daga gidan cikin tsawa Umma tace, "kai!! tsaya yaro"

     Cak ya tsaya batare daya juyoba.

  Waishin bakaji sakona bane?, nace bakaji sakona bane?, kake wani lumlumshe min idanun ka narashin da'a, nagaya maku gaba daya gidan nan ku fita hanyar jikata, idan baso kuke nai maku rashin mutunci ba"

      Lumshe ido yayi sannan ya fara takawa yana kokarin barin gidan, ganin haka Umma ta fara fadin, " ninake mgn kana tafiya, lallai bakasan halina ba, amman zan gwada maka duk ranar da ka Kara kuskura ka kula jikata saikayi daka sanin zuwanka duniya, wawa kawai mara mutunci me zubin 'yan wuta.

    Tafe yake tana binsa abaya tana surfa masa zagi harya bude motarsa ya shiga ya zauna yana jiyo ihunta, hankali kwance, yana motar yana me kallon gabansa kamar yadda ya saba, cikin gidan Umma ta koma ganin haka Aysha ta kwace hannunta ta nufi gida.

         Kan Husna ta koma ta inda tashiga batanan take fita ba, saida tagaji Dan kanta tabar gidan"

       Sosai ran Husna yake abace, ita kadaice agidan dan haka tasa kuka"

      Kusan minti 30 tana kuka sannan su Innawo suka dawo, Ummi ce agaba yayin data tsare Husna da ido, cikin tuhuma tace' " meya sameki kike kuka"?

       Umma ce tazo taita zagina"

   Cak suka tsaya, yayin da Ummi ke fadin, " zagi"?, akan wanni dalilin me kika mata?

   Akan *Aysha* ne Innawo, har ya Aliyu tabi har waje tana zagin sa"

   Cikin rashin kwarin jiki tace, " *Aysha* ta shigo ne "?

   Eh ta shigo"

    Dattijon dake bayan su ne yace wacece Aysha?

     Innawo ce tace nan makwaftamu take, kawar Husna ce, gun Husna take zuwa idan taga Aliyu suna karatu da Husna take shiga itama ayi da ita, shine kakar tata bataso, fitinan yau daban nagobe daban"

    Cikin tsananin bacin rai Ummi tace, ai Innawo duk laifinki ne, inda kin barni ko hanyar gidan nan akace *Aysha*ta kalla bazata biyo ba, Kuma bari ta sake shigowa gidan nan saina tsintsinka mata mari"

    Da sauri wannan dattijon yace kul, karki Tama masu yariya, badai gurin Husna take zuwa ba, kawai Husna ta hado kayanta muje gida"

    Shikenan kuwa, Husna dauko kayanki kibi ubanki, cewar Innawo taname cire mayafinta

     

               Lallai yanzun sabo da wata can sai adauke Husna anan?

    Cikin nutsuwa dattijon yace wani lokacin zata sake zuwa ai, yanzun dai kam haka ne kadai mafita, Kinga itama kawar tata zatai zamanta agidan su, da haka ne hankalin kowa zai kwanta, daman Husna ai bakuwa ce"

    Badan ran Ummi yaso ba ta nufi dakinta cike da bacin rai, domin yayanta alhaji Umar kaifi daya ne.....

     Fadeela Lamido✍️


*🕳️BA'KAR FURA🕳️*

   _A true life story_

*Na*

_Fadeela Lamido_

  PEN WRITERS ASSOCIATION✍️

                      *Episode 3 - 4*

   Aranar Abban Husna ya wuce da ita kamar yadda yace, sai dai sosai hakan ya bata ran Ummi dan tare suke kwana gado daya da Husna"

  Washegari gidan yai masu tsit daman husnan ce kadai yariya, misalin karfe 08:30am Aliyu ya fito cikin Shirin fita bayan ya gaidasu Innawa ya mike yana fadin, " ina Husna"

      Ummi ce ta bashi amsa Husna takoma gidan su"

    Da saurin sa ya kalli Ummi yana fadin, "sabo dame"?

     Sabo da Aysha mana, koba jiya kakarta tazo ta kare maku zagi kaida Husna ba?

   Jimmm yayi sannan yace, " saboda tsohuwar kuka tura Husna gida?, rikicin tsofa ne kawai ke damun matar nan ba wani abu ba"

    Aliyu taje can tayi rikicin tsofan nata Amman ba anan ba, yadda nake ganin yanayin matar nan masharranciya ce gara mubita asannu"

     Duk cikin harcen fullaci suke yin zancen nasu, tafiya Aliyu ya fara yana fadin, " zanje indawo da Husna"

    Ficewa yayi yayin da Innawo da Ummi sukacigaba da tattaunawa akan halin kakar Aysha"

          Bayan kwana biyu, Aysha ta nufi gidan su Husna kamar yadda ta saba, cikin sallama yayin da Ummi ta amsa sallamar sannan ta mike ta fito tana gyara daurin Dan kwalinta.

   Ido ta zubawa Aysha, ganin yadda Ummin Aliyu ta tsareta da ido yasa ta kasa kallonta cikin sauri tai kasa da kanta tare da wasa da fararen yatsunta.

     Ke dago idonki ki kalleni nan"

   Ahankali ta kalleta kamar yadda tace' sai dai cikin sauri ta sake yin kasa da kanta"

     Ke Aysha!!

  Cikin faduwan gaba ta sake kallon Ummi akaro na biyu sannan ta sakeyin kasa da kanta"

     Kibude kunnen ki dakyau kiji abun da zan gaya miki, daga yau karna sake ganin ki cikin gidan nan, tunda ba gidan ubanki bane, ko an hada da kwandala ta ubanki kafin aka gina gidan nan??

   Ahankali ta girgiza kanta tare da fadin a'a"

Toh maza ki tattara kafafuwan ki kibar gidan nan tunkan na karya wannan kafar taki me kama dana tantabara"

     Juyawa tayi idonta akasa, yayin datajiyo muryan Innawo tana fadin, Aysha kidinga zama a gidan ku Husna ma takoma gidan Babanta"

      Fita tayi batare datace komai ba, sai dai tana fita kofar gidan hawaye ya zobo mata, tana rungume da littafinta a kirjinta, ajiyan zuciya kawai take, yayin da hawaye ke zobo mata tana sharewa, sosai take shashshekar kuka tana tafe gefen hanya"

          **********

Me aka mata take tafe take kuka haka?, Allah yasa ba mutuwa akayi ba, Aliyu ke wannan tunanin alokacin daya hangi Aisha na tahowa tana kuka"

      Ganin tsayuwar mota gabanta yasa tai saurin dagowa ta kalleshi sannan tai kasa da kai tana me share hawaye"

      Lebensa taga ya motsa Dan haka ta kalleshi kawai ta sake share hawaye"

    Cikin tsawa tare da daga murya ya sake cewa badake nake mgn bane wai, me aka miki??

     Fashewa tayi da kuka saboda Kara rudewa datayi, cikin matsanancin kuka tace, Ummi ku ce ta koreni, tace karna kara zuwa gidan"

   Jimmmm yayi yana kallonta tsayon lokaci sannan ya dauke kansa tare da fadin, " daura dan kwalin ki"

   Cikin sauri ta dauki dankwalin dake wuyanta ta daura akanta"

   Umarni ya sake bata akaro na biyu cewa ta share hawayen ta"

        Sharewa tayi kamar yadda yace sannan ta dan kalleshi kadan"

      Me kikajeyi agidan toh?, taji ya jeho mata tambaya batare daya kalli inda take ba"

   Karatu 😭😭

    Waigowa yayi ya kalleta nace kibar yi min kuka ko?

    Jikina rawa ta fara share hawayen"

  Ta gefen ido ya kalleta sanannan yace, baki san kawarki bata gidan ba?

   Nasani, mun hado amakaranta ta gaya min"

      Jimmm yayi, sannan yace toh me kika je yi gidan??

    Wahawayen ta ne suka karo, yayin da suka balle kamar famfo harda majina, duk abun da take Aliyu na kallonta ahankali ya sake cewa ko gurina kikazo nai miki karatu???

     Cikin sauri ta daga kanta"

  Murmushi yayi kadan, sannan yace, ke baki da Yaya ne??

     Kanta ta daga tare dajan majina"

             Kannai fah?

      Nikadai ce mamana ta haifa"

   Wanni irin kallo yai mata na sama da kasa sannan yace toh nawa zaki dinga biyana duk wata.

      Dagowa tayi ta kalleshi yadda fuskarsa take daure ya tabbatar mata shine yai mgnr, ni bani da kudi, saidai in dinga baka rabin kudin makaranta na kullum"

   Lumshe idon sa yayi tare da tsotson sweet din da baya rabo da bakin sa, yana fadin shikenan na amince, amman fa ki dinga rufe gashin ki banson ganin gashi sam"

       Tam, tace ahankali"

      Tada motar yayi yana fadin muje, gaba tayi yana binta da motar ahankali, kusan atare suka isa yayin data bude motar ya fito ya rike hannunta suka shiga gidan"

              ******

   

Kai!! kai!! Aliyu saki hannun yariyar nan tabar gidan nan"

     Ummi karatu tazo, ya fada yana cigaba da tafiya"

     Falon ya zauna sannan ya kalli Aysha yace zauna"

      Zamanta yayi daidai da lokacin Ummi ta shigo falon tana fadin, " maza maza kizo kibar gidan nan ko bakijin yaren da nake ne, juya harce tayi daga fillaci zuwa french take fadin yi gidan ku"

     Hawaye ta share yayin da Aliyu ya kalli Ummi yace, "haba mana Ummi kibar koranta karatu ne yake kawota ba wani abu ba"

      Wani irin kallo Ummi tamai sannan tace waikai baka gudun zuciya ne?, Aliyu duk fa irin maganganun da kakarta take kasan dasu, me zaisa mubarta ta zauna, itafa take karuwa damu bamu ke karuwa da itaba, sannan azo ana gaya mana mgnr banza da wufi.....

    Nidai bakomai Ummi, duk surutun da zata yi Babu abun da ya dame ni, Ummi yariyar zaki duba tana son karatu sosai fah"

        Wani irin kallo ta masa afusace sannan tace, amakaranta ya cancanta tai karatu ba annan ba, Kuma ma wai meye naka tunda iyayenta basa so??

    Zuwa wannan lokacin idon Aliyu ya fara canza launi daga fari kar zuwa jah dan haka ya lumahe ido kawai yana me lasan leben sa na kasa"

    Meye naka Ummi ta sake tambaya?

      Lebensa ne ya motsa, sarai tagane me yace amman sai tace ka bude baki kamin mgn"

     Sumar kansa ya shafa sannan yace cewa nayi yariyar nason karatu.

    Kallo tabishi dashi sosai dan haka yai kasa da kansa, ganin haka Ummi ta juya gun Aysha tace ke Kuma bace min dagani wawiyar yariya kawai me zubin mayo, banson naci wlh"

     Ficewa Aysha tayi tana share hawaye sosai, bayanta Ummi tabi tana cigaba da gayawa Aysha duk wani abun da yazo bakinta, tanemejin tsananta har cikin ranta"

     Aliyu kuwa cikin tsananin baccin rai ya nufi dakinsa ko kallon inda aka aje masa abincin ranar sa bayi ba.

            *******

  Toh fah, subuhanallahi"

 Meya faru Innawo?

  Yau waya taba min megida na, Kinga abincinsa narana beciba, gana dare ga Kuma nakarin kumallo Babu wadda yasa hannun sa akai"

       Jimmm Ummi tayi sannan tace kada Allah yasa yaci, dan Allah Innawo daga yau karki Kuma bashi abinci, ai ba ubanshi ya kawo mana ba bare yace zai gwada mana taurin kai"

    A'a nikam banson rigima, kowa da irin sa ai, Kuma nasan da akwai abun dake damun sa duk yadda akayi jiya kin masa fada"

    Babu fadan dana mai Innawo, kema kinsan gaba daya halin Bello ya kwaso, har nema ma yake ya zarta shi"

      Kema danaki ai, bari ya dawo naji dalilin kin cin abincin nashi"

       ********

 Misalin 3 na rana Aliyu ya dawo gida, afalo yacin musu kamar kullum yai masu sannu sannan ya wuce su, binsa Ummi tayi da kallo harya kulle sannan ta tabe baki"

  Itako Innawo abincin sa ta dauka tabi bayan sa, itama binta da kallo Ummi tayi har taga shiganta dakin Aliyu"

       Kusan bayan awa daya ta fito rike da kulan abincin, fita tayi tsakar gidan ta aje kulan sannan ta dawo ta zauna kusa da Ummi tana fadin, " kinsan abin da nake so dake"?

        Kai Ummi ta girgiza tare da fadin a'a"

    Ko sau nawa Aysha zata shigo gidan nan Babu ruwanki da ita, karki sake koran ta"

  Jimmm Ummi tayi cikin ya mutsa fuska tace Innawo biye mishi zaki yi?, yariyar nan macece fa bana miji ba, Kuma iyayenta sun nuna basa so, dole ne??

    Ba wannan zaki duba ba, yariyar nason karatu, Kuma guda nawa Aysha take da zasu kasa tsareta agida, mu subarmu da yi masu gadi?, Kuma yariyar nan tana zuwa muna korarta bakin mu zata dinga gani har girmanta, yaro be manta abu, tunda sune basa so, su dakatar da ita da kansu.

     Cikin tsananin bacin rai Ummi tace nidai Innawo bakomai, taga bakin nawa, tana shigowa gidan nan wlh tsanarta karuwa yake azuciya, ko Husna da suke kawance tahakura bareshi, meye nashi ne aciki wai, dan Allah Innawo kirabu dashi, ai gaba muke dashi bare yace yafimu hangen nesa.

     Mikewa Innawo tayi cikin ya mutsa baki tace' toh me d'a, nafa manta ke kika haifeshi dole yabi Umar nin ki, ke kuma daga sama kika fado, sai kiyi abun da kikaga dama, ficewa tayi yayin da Ummi ta zaro idonta waje tare da mikewa da sauri tai waje, cikin kitchen ta samu Innawo dan haka tabita ciki tana cewa, " Innawo kiyi hakuri naga ranki ya baci, ba haka nake nufi ba, naga su duk yara ne ba......

    Katseta Innawo tayi da fadin, ke guda nawa kike???

  Lumshe idon Ummi tayi sannan tace shikenan kiyi hakuri toh"

    Cigaba Innawo tayi da aikin ta cikin yanayin fushi dan haka Ummi ta sake cewa Innawo nace kiyi hakuri dan Allah, wannan karon ma shiru, dan haka Ummi ta nufita ta amshi tsintsiyar dake hannunta tafara karasa inda Innawo tafara sharewa tana me Satan kallon Innawo dake kokarin shiga falo, ajiyan zuciya Ummi tayi dan ta tabbatar yanzun Innawo ta hakura"

       Sai yamma Aliyu ya fito sannu yai masu kamar yadda ya saba Innawo kadai ta amsa har yakai kofar gida ya dawo, daf da Ummi ya tsaya Ummi nai miki laifi ne??

        A'a tafada kai tsaye"

  Naga nace muku sannu baki amsa ba"

      Bakaji bane na amsa"

     Lumshe ido yayi sananna ya sake cewa to natafi kinji Ummi"

    Daga murya tayi da Dan karfi tace adawo lafiya"

     Allah yasa yafada sannan ya juya ya fice"

                    Bayan sati daya

   Misalin karfe biyu na rana Innawo ta hango farin hannu yana rike labulen falon, adaga arufe har kusan sau biyar dan haka cikin daga murya tace waye nan?

     Ahankali cikin wani irin zazzakar murya tace nice"

     Kecewa?

    Sakin labulen tayi ahankali tace Aysha ce"

      Au Aysha kece kike leke, shigo mana"

    Labulen ta daga ta shigo tana share hawayen fuskanta, gaida Innawo tayi sannan ta juya barayin Ummi tace, Ummi ina yini?

   Lafiya Ummi tace cikin kawar da kanta tare da kirne fuska"

   Innawo ce ta sake cewa Aysha kwana biyu, ya mamaki?

   Lafiya lau"

 

   Madallah, Innawo ta fada sannan ta sake cewa ai Kuna haduwa da Husna amakaranta ko?

   Kai ta daga tare da fadin, " Innawo Ya Aliyu na nan inason ne zai dubamin wani abu?

       Aliyu baya nan Aysha amman nasan ya daf daf da shigowa.

    Idonta cike da hawaye tace tam, juyawa tayi tare da fadin sai anjima.

    Abakin kofar fita sukaci karo da Aliyu yana kokarin shigowa gidan

  

  Cikin sauri ta kauce ta bashi hanya ya wuce yayin data shiga wasa da yatsun hannunta, ganin yana kokarin wucewa abun sa yasata saurin cewa ina wuni cikin fullacin daya rike bakinta ram

     Kallonta yayi yayin data karayin kasa da kanta yace, " lafiya ya gida"

     Lafiya lau"

   Kallon sama da kasa yai mata sannan yace, " meyasa kwana biyu bakizo ba"?

     Kanta akasa yayin data tsananta wasa da hannun ta, kur ya mata tsayon lokaci sannan yaga ta saki hannunta tare da dagawa takai daya tana share hawayen fuskanta, tsayon lokaci ya dauka yana nazartanta zuwa can ya mika hannun sa ya zaro littafinta guda biyu dake tsakankanin kirjinta da cinyar hannunta, fuskarta ya sake kallo har yanzun hawaye ne ke tsiyayowa tana sharewa, dauke idonsa yayi sannan ya bude littafi ahankali ya fara duba shafukan, abun da ya lura dashi tun daga lukacin da tabar zuwa akwai ci baya a yanayin Makin da take samu lokacin da take zuwa bayan ya kare bude shafukan da akwai rubutun ta akai ya rufe littafi sannan yai mata wani irin kallo ya mika mata ta amsa tare da zuba mata rankwashi akanta sannan ya bude daya littafin kamar ba shine yai rankwashin ba.

     Hawayenta ne ya karu, yayin da suke zubowa Babu kaukautawa.

   Rufe littafin yayi domin shima dai irin dayan ne mika mata yayi ta amsa sannan ya fara takawa da sauri da sauri yana nufar kofar da zata sadashi da falon.

     Cikin sauri tabi bayansa cikin kokarin son ta cin masa harsai da ta hada da gudu amman dun da haka kafin tashiga babban falon gidan har ya shige dakin sa.

        Hake take sosai lokacin da tabbatar ya shige dakin sa, tsaye tayi tsakiyar falon sai yanzun ta kulla da hararan da Ummi ke zabga mata afakaice, cikin sauri ta dauke kanta ta mayar da hankalin ta kan kofar dakin Aliyu.

      Ba jimawa ya fito ya zauna afalon, ahankali Itama Aysha ta zauna Dan nesa dashi akasa, Kamar kullum ya shiga yimata bayani cikin nutsuwa da daukan hankali"

*Gyara adon mace, komai yanason gyara, idan kina dakyau kira da wanka, dan haka mata atashi agyara, akwai kayan gyara lada da kala sai wadda kika zaba domin gigita me gida, sabbabin amare ina da irin naku, yan mata masu shirin shiga daga ciki kuma akwai naku na musamman cikin rahusa mai sauki, ina aikawa kowanni gari, ina da tabbaci akan kayana, idan kika gwada saikin dawo insha Allahu, gamasu bukata su tuntubeni ta wannan no ****

    Ummi dake gefe ma kallo tabi Aliyu dashi saboda yadda yake mata bayani daki daki dole nema mutum ya fahimta sannan daya fara yi mata bayani cikin harcen french yake baya taba sako kowwanni yare, har suka gama karatun Ummi na kallo Kuma tana saurare, murmushi tayi har cikin zuciyarta sanan ta sake dagowa ta kalleshi, tunda ya zauna agorin har yanzun idon sa nakan littafin ko sau daya beyi kuskuren dago idon sa ya kalli wani guri daban ba, gani tayi ya rufe littafin tare da mikewa yana kokarin shiga dakinsa yake fadin shikenan kije gida sai gobe kuma.

     Itama Aysha littafinta ta dauka sannan ta mike ta kalli inda Ummi take tace, Ummi sai anjima"

   Tsintan kanta tayi da amsa mata, bayan ta wuce ta bita da kallo, me kama da harara"⅝

               *********

    Ai saidai ki koma inda kika fito tun da ke kince kunnen Kashi gareki.

      Mama karatu naje fah"

    Wa kika gayawa wa da kika tashi fita??

   Mamma kona tambaya ai ba barina kuke yi ba ke da Umma"

    Cikin fada Umma tace shine ai aka ce miki ki koma inda kika fito, badai gidan Innawo ba?, ki koma can ki zauna tunda kince ke sarakan yan naci ne ke"

       Mama kiyi hakuri kinji?

    Tsawa Umma ta buka mata, bace a gurin wuce kibamu guri marajij mgn kawai.......

     Afakaice Aysha ta harari Umma tare da fadin, Umma ba ruwan ki"

       Au Babu ruwana ma kike cewa, takalmin dake kamafarta tacire tafara dukan Aysha dashi duk da cewa bawani da karfi take bugawa ba amman sosai Aysha ta hade fuska tare da kallon fuskar mamanta, gani tayi mama ta dauke kanta daga kallon su yayin da Umma kecigaba da fadin, ko tsinken ki karki barmin ki koma gidan Innawo"

       Afusace Aysha ta mike ta nufi dakin mama jakar makarantar ta ta goyo tazo ta wuce su ta fice daga gidan"

          Hanyar gidan Innawo ta kamo, idonta bushe, saida tazo kofar gidan sannan ta tuna fuskar Ummi, cak ta tsaya, ahankali ta juya ta kalli gidan su, hawaye ne taji suna sakkowa kan idonta, yatsun hannunta ta zubawa ido yayin da take matsa yatsun nata da daya hannun ta tayi tana dagowa tana kallon gidajen guda biyu wadda tasa su a tsakiya.

  

      Hawaye ta share afili tace, bazan iya shiga gidan Innawo ba, haka Kuma bazan koma gidan mu ba, wani shashine na zuciyarta ke tambayanta ina zakije toh?, Kara matsa hannunta tayi sannan tace"

    Bansan ko inaba sai makaranta, hawaye ta share sannan ta nemi wani dan tudu ta zauna tare da fadin anan zan zamana gobe inje makaranta......

           

         Fadeela Lamido ✍️


*🕳️BA'KAR FURA🕳️*

   _A true life story_

*Na*

_Fadeela Lamido_

  PEN WRITERS ASSOCIATION✍️

              *Episode 5- 6*

 Zama Aysha tayi agurin tsayon lokaci, wani irin haushi Umma ke bata domin tasan idan babu Umma Mama bazata koreta ba.

 Yamma ce tayi sosai kasancewar yanayin damina, tuni hadari ya hadu sama na shirin zubo da ruwa amman Aysha ko ajikinta, tana zaune jakar makarantar ta goye a bayan ta kananan kaya ne ajikin ta riga da siket, sai hular dake kanta wadda ya matse tarin tudun gashinta a tsakiyar kanta, kasancewar ta farar bafulata cikin bakaken kaya yai matukar fitar da kyanta, Babu abun da take sai raba idon ta tana kallon mutane da motocin dake ta rige rige wucewa dalilin iskan hadarin dake tasowa, bakajin komai sai Karan iska hadari da Karan motoci.

          **********

  Agoje yake Jan motar domin isa gida akan lokaci, bayan ya faka motar akofar gidan nasu ya sakkowa tare da waiwayowa bayan sa yana kallon yariyar dake zaune nesa dashi.

      Cikin zafin nama ya fara takowa domin tabbatar da abun da yake tunani, gabanta ya tsaya tare da fadin, ke!!!

     Azubure ta mike tsaye tare da tsallaka kwatar dake gurin batare data sani ba.

      Cak ta tsaya, kanta akasa.

  Cikin kausasassar murya yace me kike anan gurin??

       Umma da Mama suka kore ni"😔

  Idonsa akan hadarin dake shirin sakkowa yace me kika musu?

      Wai dan nazo kamin karatu"

   Lumshe ido yayi sannan yace tun yaushe?

  Sai yanzun ta dago ta sata kallon sa tana fadin, tun da nadawo gida"

    Kallonta yayi cikin ido yayin da tai saurin yin kasa da kanta, yawu ya hadiye sannan yace, kika kasa basu hakuri Kuma?

    Na basu fa amman sun ki"

      Hannun sa yasa daya cikin aljihu sannan yace sau nawa kika basu hakurin"

        Uku ta fada tare da gyra siket dinta da iska hadarin ke kokarin yayewa"

         Ke! Ya sake cewa karo na biyu bayan ta dago idonta ta kalleshi yace, " ki wuce ki koma gida ki basu hakuri"

     Kwal kwal tayi da idonta cikin shirin yin kuka, tana nifa na basu hakuri basu hakura ba, ni nan zanyi zamana gobe innaje makaranta sai in zauna acan"

    Lumshe idon sa yayin jin ta ambaci makaranta, zuwa can ya bude idon nasa tare da fadin, " ke wai ina wasa dake ne, ki wuce gida ki basu hakuri nagaya miki, kina nufin anan gurin zaki kwana??

      Cikin sauri ta daga kanta"

    Wani irin kallo yai mata sannan yace shikenan, juyawa yayi ya nufi gida, binsa da kallo Aysha tayi harya kule sannan sannan ta koma ta zauna"

     Zuwa can ta hangosa ya Kuma fitowa cikin sauri ya nufa masallaci"

*Gyara adon mace, komai yanason gyara, idan kina dakyau kira da wanka, dan haka mata atashi agyara, akwai kayan gyara lada da kala sai wadda kika zaba domin gigita me gida, sabbabin amare ina da irin naku, yan mata masu shirin shiga daga ciki kuma akwai naku na musamman cikin rahusa mai sauki, ina aikawa kowanni gari, ina da tabbaci akan kayana, idan kika gwada saikin dawo insha Allahu, gamasu bukata su tuntubeni ta wannan no ****

    Zamanta tayi tana kallon duk wani me wucewa, zuwa can aka fara fitowa masallaci dauke idonta tayi dan gudun kar karsu hada ido da Aliyu, muryar sa taji daga dan nesa da ita yana fadin, " kina da taurin kai ko"?

          Mikewa tayi ta shiga wasa da hannunta Kamar yadda ta saba kanta akasa tace, " ni a'a fah kaine kace in zauna"

         Ni Kuma?, ke baki san gatse ba?

        Shiru tayi idonta akan yatsun hannun nata

   Domin batama gane me yake nufi da gatsen ba, duk da cewa cikin fulatanci suke mgnr

              Kara daure fuskan sa yayi sosai sannan yace, " ke kin sanin kuwa?, maza kije ki basu hakuri nasake fotowa naganki anan gurin saina baki kashi wlh, kinji Kuma na rantse"

          Tafiya ta fara yayin dayai tsaye agurin yana kallon ta, itako tafe take tana waiwayen sa saida Aliyu ya tabbatar ta isa kofar gidan nasu sannan ya nufi gida, cikin ikon Allah yana shiga gidan ruwan saman daya dade yana hada hadari ya sakko, ruwa ne ya kece sosai.

               *********

   Dadin yanayin da ake cikin na ruwan sama yasa Aliyu zama cikin su Ummi yaci abinci, Koda ba mgn yake yi ba, Amman yana sauraron hiran Innawo da Ummi saidai in sunyi abun dariya yai murmushi har yagama cin abincin ya mike yana fadin, saida safe"

          Amsa masa sukayi sannan suka cigaba da hirar su.

      Aliyu kuwa bayan ya shiga daki wanka yayi 

     Sannan yai shirin bacci ya kwanta tare da rufa cikin bargonsa me shigen laushi, addu'ar bacci ya karanta sannan ya lumshe idonsa yana mejin saukan ruwan saman da aketa zugawa"

     

   Sosai yakejin dadin yanayin idonsa alumshe yanajin saukan ruwan saman daketa kwaranya, hiran Ummi da Innawo ya tuna dan haka yadanyi murmushi tare da gyara kwanciyarsa"

    Bacci ne ya dauki sa, yayin da can cikin baccin yakejin hayaniya sama sama, ahankali ya bude idonsa har yanzun ruwan ake zubawa sannan ga hayaniya yanaji wanda be sanin me ake cewa, tashi yayi ya zauna yana me Kara baza kunnen sa, yaye bargon yayi gaba daya ya sauko ya nufi window tare da yaye labulen, Kakar Aysha yagani tare da mahaifiyarta da wasu maza biyu manya sai masifa suke cikin tsakiyar ruwan sama  duk sun jike, cikin sauri ya saki labulen tare da nufar kofa, karo sukaci da Innawo cikin yanayin rudu tace kai *Ali* kaga Aisha wai??

             ***********

               JIGON LABARIN

  *Aliyu* dane ga Alhaji Bello Kano, shahararren dan kasuwa Kuma masu fada aji, mahaifiyar Aliyu mutuniyar Cemaroon ce, bafulatana, yar asalin kasar Camaroon, sun hadu da Alhaji Bello ne a kasar Camaroon alokacin dayaje domin kasuwanci, Soyayya ta kullo tsakanin su har takaisu ga aure, saidai kafin aurenta da alhaji Bello ta taba aure har da yaranta biyu namiji da mace wadda alokacin ita macen me sunan Ruqayya an auren da ita tana zaune da mijinta a Kano Nigeria, dan haka da Alhaji Bello ya nuna ra'yin sa akanta tai farin ciki domin zata zauna kusa da 'yarta, shiko Alhaji Bello irin mazan nan ne wadda suka jima basuyi aure ba, sai akan Fatima, cikin farin ciki Fatima ta taho aure Nigeria tabaro Babban danta Fahat can CAMAROON gurin mahaifiyarta, Fahat shine yayan Ruqayya, sai dai shi yana da lalurar tabin hankali, sai dai Allah be kaddara dogon zama tsakanin Fatima da Alhaji Bello ba, domin kuwa tana da cikin Aliyu wata daya suka rabo, dan haka ta tattaro ta dawo CAMAROON anan tayi rainon cikin ta, bayan wata 8 ta Haifi danta katon gaske saidai bashi da hasken Fata kamar na Fatima, mahaifin sa Alhaji Bello yazo ya ganshi, inda yai masa huduba da Aliyu, sannan yayi duk wani abu da yadace uba yayi alokacin da aka haifan masa da, sannan ya koma Nigeria"

    Fatima tacigana da rainon Aliyu cikin so da kauna, hakama mahaifiyar ta Innawo tana nuna tsananin soyayyarta wa Aliyu, bayan Aliyu yafara girma suka sanyashi makaranta sosai yake maida hankalin sa kan karatun sa, bayan ya kara girma ne suka kula da wasu dabi'u nashi, yana da son yara kanana, sannan Koda yaushe fuskarsa sake take amman mgnr sa ya kanyita ne ciki ciki kuma bada kowa yake mgn ba sai yaga dama, ta wani bangaren ana iya kiransa miskili, shidin kaifi daya ne, yana sa gabansa ne kawai abun da yasa gaba sannan baya daukan raini, idan ransa yabaci kuwa be iya fushi ba, ahaka Aliyu ya taso cikin kulawan dagin mahaifiyarsa lokaci bayan lokaci mahaifin sa nazuwa ganin sa, sannan akowanni lokaci yana aiko masu da sako babu laifi"

    Aliyu yana da kimanin shekara 10 yayar sa Ruqayya ta kawo masu ziyara CAMAROON lokacin data tashi komawa ta nemi da abata Yayanta Fahat ta tafi dashi Nigeria domin neman masa magani, komai sai an masa baya iya yiwa kansa komai, haka kuwa akayi Ruqayya ta tafi da Fahat, yayin da Innawo da Fatima suka maida hankalin su gaba daya akan Aliyu, a yanzun haka Aliyu yana daf da kammala karatun sa na gaba da secondary, Aliyu matashin saurayi ne meji da kansa, wadda bazai wuce shekaru 25 ba, yana da matukar kokari amakaranta yana da tsanin tafta wadda har take son ta wuce misali, Kuma har wannan lokacin Fahat yana gurin kanwarsa Ruqayya kullum cikin nema masa magani take amman har yanzun ba'a dace ba

   Kasancewar Fatima Bafulatana ce ita da danginta yasa fullanci ya zauna bakin Aliyu sosai, dan yanzun haka duk wata magana da zasuyi cikin harcen fullaci sukeyi duk da cewa Fatima tanajin hausa kadan kadan hakama Innawo tana gane wasu abubuwan, haka Kuma abangaren makaranta boko anayin amfani ne da french dan haka ya kejin french sosai, saidai Aliyu mutum ne meson jin yaruka da yawa dan haka ya nemi ajin English tun yana secondary School yana hadawa dashi, ayanzun haka Aliyu yana jin yaruka 4 Hausa Fulatanci English    French.

               Wannan kenan.

        Abangaren Aisha kuwa, iyayen Aisha gaba dayan su Mutanen CAMAROON ne uwa da uba, yayin da mahaifiyar Aisha ta kasance Fulani, maifinta Kuma kirista ne, kaddara ta hadasu aure wanda basu jima tare ba, Aisha nada shekara uku suka rabo, kasancewar sa ba musulmi bane tai zafin naman tattaro diyarta ta rike gunta, duk da cewa me kudine sosai Babban ma'akacin gwamnati, Bilkisu wato mahaifiyar Aisha kyakayawace sosai fara tas hakama Aysha ta dauko farin fatan da kyau gurin uwarta, Koda shima mahaifin Aisha fari ne tas, Kuma yana tsananin son Aisha tare da kawo mata ziyara duk lokacin da yaso ganin ta, bata nemi komai ta rasa ba, domin mahaifinta tsaye yake akan karatun ta bashi da wani buri daya wuce yaga Aisha cikin farin ciki"

  Haka itama Aisha tana son Daddyn ta sosai da sosai har bata iya banbance wadda tafi so tsakanin sa da Maman ta, tun da ta taso yariya ce meson karatu sosai, fiye da tunanin me karatu, na boko dana bangaren addini, hakama Mamanta da kakarta Umma suna bata kulawa gurin karatun nata, Aisha yariya ce meson wasa da dariya Kuma me jajircewa akan abun da tasa gaba, yanzun haka tana aji daya na secondary School, Aisha yaruka biyu kawai take iyaji, fullanci sai Kuma french wada da dashi ake masu karatu amakarantar boko

               *CIGABAN LABARIN*

 

    Lumshe idonsa yayi sannan yace, "eh naganta dazon"

     Ka ganta?,🤔 Ina take toh??

      Kafin ya bude baki Umminsa ta karaso ta kure sa da ido, inda Innawo ta sake cewa ina jinka"

     Innawo nace miki dazon naganta zaune a kofar gida nace mata ta Koma ta koma gida"

   Wani irin kallo mahaifiyar tasa ta masa me cike da tuhuma sannan tace bayan Kun gama karatun ina ka kaita?

      Ni?

  Eh kai fah"

   Ummi nifa tasowan hadarin nan da nadawo nasameta awaje ne kawai, Dana mata tambaya tace min Koranta akayi agida sabo da ta zo karatun daker nasata ta koma gida, Kuma banbar gurin ba har saida naga shiganta gida"

   Cike da bacin rai Ummi tace zo ka fita kaje ka fito masu da yarsu"

   Wani irin kallo Innawo tama Ummi ya nemota a ina?, kinaji yace saida yaga shiganta gida, suje can su nemeta suna sonta ai basa koreta ba, yar karamar yariya kamar Aisha tun rana basu tashi nemanta ba sai yanzun?, wannan shiri ne kawai"

       Innawo ai shima yanzun bashi da mafita fah, tunda an gansu tare"

       Yana dashi da karfin ikon Allah"

    Juyawa Aliyu yayi ya nufi dakinsa ba jimawa ya fito cikin sauri yana kokarin gyara wuyan rigarsa daya sanyata yanzunan yana me motsa labban sa, tare da nufan kofar da zata sadashi da tsakargidan nasu"

   Zo nan me kake cewa?, Ummi ta tambaya bayan ta tabbatar daya yayi mgn"

      

     Lumshe idonsa yayi sannan yace cewa nayi saina zane ta"

     Cikin yanayin dake nuna taji mamaki tace sabo da kaine ka haifeta?

    A'a saboda ta fidda ni acikin ruwa Kuma saida nace ta koma gida, kenan kunnenta bamejin mgn bane.....

   Toh waye ya aikeka fita cikin ruwan?, Innawo ta jefa masa tambayan bayan ta tsare sa da ido"

   Kansa ya dan shafo kadan sannan yayi wuf yashige cikin ruwan saman dake sauka kamar da bakin kwarya"

      Koda ya fito kofar gidan yan gidan su Aysha ne duk acikin ruwan saman sai haske haske suke yi tare da surutai wadda bayajin me suke fada saboda Karan ruwan saman da ake kwararawa"

     Bebi ta kansu ba ya wuce abun sa, tafiya yake yana duba Aysha duk wani lungu da sako saida ya duba, gaba daya ya jike sharkaf yana tsiyayan ruwa, gaba daya unguwar ya gama zagawa babu Aysha babu alamarta

gashi dare nakara nisa, baban abun da yafi tayar masa da hankali kankantar shekarun ta, ko wani hali take ciki yanzun duk wannan ruwan da ake ina take?, ta fakewa ruwan ko bata fake ba?, jikinsa ya kallah yadda ya jike sharkaf gawani irin iska wanda yakejin tamkar zatai sama dashi, sosai hankalin sa ya kara tashi, ruwa yaki tsayawa tsayon lokaci, gashi baya tunanin akwai inda be duba ba lungu da sako nacikin unguwar, dan haka yayi tunanin komawa gida watakila zuwa yanzun Aisha ta koma gida"

    Zuwa wannan lokacin babu kowa alayin nasu dan haka yaji sanyi cikin ransa yana me tabbacin anganta, sai dai yana daf da shiga gidan ya hangi su Innawo da Ummin sa sunfito daga gidan su Aisha duk sun gama jikewa, kasa hakuri yayi ya karasa yana fadin, " an ganta"?

       Inafah, suna nan sun kafe cewa ka fito masu da 'yarsu"

   Lumshe ido yayi batare da yace komai ba ya juya ya shiga gida"

  Koda Innawo ta shigo babu abun da take kira sai sunayen Allah "

      Sosai hankalin Ummi dana Innawo ya tashi, baban burin su ayanzun be wuce ganin Aisha ba, Innawo tagumi ta zuba lokaci bayan lokaci tana fadin, "munshiga uku"

      Fitowan Aliyu cikin kananan kaya tare da katuwar rigar sanyi yasa duk suka dago suka kalleshi, ina zaka?, Ummi ta fada?

   Zan dauki mota ne in kara bincikata"

    A'a kazauna agida, tunda sun tura kanin Mamanta ya kira police"

     Lumshe ido yayi tare da Kara tura hannunsa cikin aljihun rigarsa sanyin dake jikin sa sannan ya fara takowa ahankali, daf da Innawo ya zauna tare da daukan kafarsa daya ya daura kan daya, ahankali ya fito da hannun sa na dama daga cikin aljihun sweet ya shiga barewa sannan ya jefa abakin sa ya shiga tsotsa ahankali"

  Ummi ce ta bishi da kallo yadda yake tauna cigam dinsa bakace wani abu na damun sa ba har wani dan girgiza kafarsa yake yi, kwayar idon sa fari karrr gawani farin ruwa kwance acikin sa, kwayar idon kawai kake gani suna juyawa, motsin da Ummi taji a tsakar gidan nasu yasata maida hankalin ta ga kofar falon, mamakin da taji yasata kallon agogo karfe 01:15am.....

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol