Free chapter · Read without an account
BAKAR FURA CHAPTER 11
by Fadila Lamido · BAKAR FURA
*🕳️ BA'KAR FURA🕳️*
_A true life story_
*Na*
_Fadeela Lamido_
PEN WRITERS ASSOCIATION✍️
Episode 54- 55
Akofar gidan Innawo motar ta tsaya, ahankali suka fara fito da kayan su sannan suka nufi cikin gidan Innawo.
A'a lale lale, kune tafe da yamman nan.
Wlh Innawo tun shekaran jiya muka taso, motar ba sauri.
Afalon suka baje tare da cire mayafin su, Ummi ce tafito daga bayin cike da murmushi ta fada Sadiya tana fadin an girma rabon ki da kasar nan tun kina goye.
Cike da fara'a Aunty Ruqayya tace, aitace girin ku da nisa.
Dariya akayi yayin da Innawo ta juye masu ruwan wanka, bayan sunyi wanka sukayi Sallah magariba domin lakacinta yayi sannan Ummi ta baje masu abinci.
Bayan sun gamaci ne Aunty Ruqayya da 'yarta sadiya suka kwanta nan tsakiyar falon suna hira yayin da Innawo da Ummi suke zaune, hiran suke cike da nishadi suna ta dariya zuwa can Innawo tace, " wai Aliyu ne ya gaya miki ina kiranki koko kawai dai kinzo ne?
Shine ya gaya min Innawo, sau uku yazo musamman ya jaddada min lallai kina son ganina.
Ya gaya miki abun da ya aikata?
Cikin sauri Ummi ta kawar da kanta tare da daure fuska sosai.
A'a me yayi?, nidai yazo kawai yace min ya dawo.
Dan Murmushi Innawo tayi sannan tace ai kanin ki mgn ya dauko mana.
Wacce irin mgn Innawo?, tashi tayi zaune tana kallon Innawo sannan ta juya ta kalli Ummi data hade rai, ko ba'a fada ba tasan Ummi fushi take da Aliyu.
Innawo ce tace, kunyi d'a, danku nan kato nan gidan Umma.
Cike da mamaki tace bangane ba??
Ummii ce tace, yariya yama ciki harta haihu.
Subuhanallahi, Aliyu?🤔
Shifa, Ummi ta bata amsa"
Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, wacce yariya kenan?
Innawo ce tace ita dai wannan yariya Aysha da aka rabashi da ita, kinga rabawar ma beyi amfani ba.
Kashhh, abu beyi dadi ba Innawo, toh wai ita yariya ba annan take ba?
Innawo ce ta kwashe komai ta gaya mata duk yadda akayi, kama bakinta tayi tare da fadin, haba, biri yayi kama da mutum, watanin baya Aliyu ya tashi hankalin sa har nima yazo ya daga min nawa, cikin tsananin damuwa yake zuwa ya kwata min ajiki wai in kwantar masa da hankali kamar yadda Ummi ke masa, sannan sau uku yana sa ranar tafiya har yazo yamin sallama amman washegari saina ganshi ya yazo wai shi ya kasa tafiya gabanshi faduwa yake, ba irin tunanin da tunanin da banyi ba.
Aikuwa dai yanzun anbata da Ummi, dan ta kunkunduma masa zagi manya manya ma kuwa, badan Ina tsakani bama inajin tsine masa zata yi, dan naga kamar tayi niyya.
Idon Ruqayya cike da kwallah tace, ayya Ummi ba halin shi bane fah, dan Allah kiyi hakuri.
Kawar dakai Ummi tayi, yayin da Aunty Ruqayya tace toh aini banga ta zama ba, barin je in dubosu in dawo.
Ki bari saida safe Mana.
A'a Ummi yanzon zani ni daman bansan yariyar ba, yakamata ace komai ya wuce yanzun, mu rungume yariyar mu nuna mata kauna, tunda yana sonta, wlh Ummi zan iya rantsuwa tsautayi ne, kanina ko acen bashi da rawan kai, Baffah ma fada yaketa masa akan yiyi aure, amman wlh ko budurwa bashi da ita.
Cike da taici Ummi tace, " itafa zai yi rawan kai, bayan ya kala rai nan, ai daman hakane, duk matsalar da abun da mutum zai aikata sai ace tsautsa yi.
Mikewa tayi ta yafa gyalenta sannan tace ma 'yarta Sadiya tashi muje.
******
Tundaga zauren gidan sukejin kamshi, sallama sukayi bayan an amsa musu suka shiga ciki.
Umma ce da Maman Sadam suke cin abin ci, gaisawa sukayi sannan sukace, " Aysha suke nema"
Umma ce tace, au Ruqayya ce, da hannun suka nuna mata dakin tare da fadin, " tana nan ciki.
Dakin suka nufa daga yaddda suka mata tasan ba wani shiri suke da itaba, sallama sukayi daga ciki Ayaha ta amsa, dan haka suka shiga.
Gaisawa sukayi sannan Auny tace, nasan baki sannin ba ko?
Eh.
Ni Yaya Aliyu ce daga Nigeria.
Ayya, sannu dazuwa, fuskarta ta dan sake kadan, kallonta Aunty Ruqayya tayi sannan ta kalli akwatin dake gabanta, hijjabinta na kan akwatin, itako harda takalmi akafarta, ga dukan Alamu dai fita zatayi, dan haka Aunty Ruqayya cikin nazari tace, " fitama zakiyi kenan?
Eh wlh, Aysha ta fada tana kawar da ido.
Toh dan bani yaron ingani Mana.
Mikewa tayi ta kwantoshi ta mikawa Aunty Ruqayya sannan ta koma ta zauna.
Ido Ruqayya ta zubawa yaron fuskanta cike da murmushi, tabbas wannan karamin Aliyu ne, idonta akan yaron tace Ina zakije naga harda akwati?
Kawar da kanta tayi yayin da hawaye ya zubo mata tai saurin sharewa.
Da kallo Aunty Ruqayya ta bita zuwa can tace, kin dai san akwai aure akanki bekamata ace kina fita babu izinin mijin ki ba, ko kuwa ya baki dama kije wani waje ne??
Idonta akasa tace a'a.
Shine kike kokarin fita harda su daukan akwati?
Toh aunty yaushe nasan ranar da zai dawo dahar zanzauna Ina jiran Umarnin sa, bakin ciki ne zai kashi kawai, bazan zauna jiranshi ba.
Kallon Aysha aunty tayi tsayon lakaci, damuwa karara afuskanta tagani dan haka tace, kenan wannan kayan da kika hada garin Zaki bari?
Kawar dakai tayi sannan tace a'a.
Eh Mana, toh Ina zakije da daddaren nan?, kina jira mutane su shiga daki ko???
Dagowa Aysha tayi suka hada ido sannan tai saurin mayar da idonta kasa.
Aunty ce tace, " toh wlh karki fara, nasan aiki ne ya tareshi ba wani abu ba, sanda na tahoma baya garin, kiyi hakuri yana nan zuwa ko Kuma ki shirya sai mu tafi tare.
Kawar da kanta tayi can gefe yayin da aunty Rukayya ta sake cewa ki shirya sati daya zanyi sai mukoma tare.
Ni bazani ba aunty, ai shi yama manta dani yanxun, daman ance min bazai dawo ba Kuma ko naje bazai bari in ganshi ba😭
Cike da Mamaki aunty take kallon Aysha sannan tace, duk wadda ya gaya miki haka ya fadane kawai, Aliyu ba haka yaje ba, ninasan zai dawo ba haka Aliyu yake ba.
Kawar dakai tayi sannan tace, wlh aunty haka yake, wancen karon ma cemin yayi wata Uku, Amman bezo ba saida aka kusa shekara, haka yake, beda alkawari, nasan bazai dawo ba ko zai dawo saina kusan mutuwa da wahala, haka yayi min waccen karon, amman bakomai ba laifinsa bane, laifinane, da banje gurin saba da yanxun Ina zaune lafiya da 'yan uwana cikin mutunci, kamar yadda yake zaune da nashi, Ina shan wahala arayuwata, gara min mutuwa da wannan rayuwar, kowa ya juya min baya cikin harda Yaya Aliyun......
A'a kam, kicireshi aciki, nasan rankine ya baci, Kuma shi besan halin da kike ciki ba......
Ya sani, saidana gaya mishi, yace min in basu hakuri, Kuma nata basu har nagaji, basa sona, basa son ganina, saidai in fita in sawo abun da zanci, ruwan wanka kuwa sai dai inje makota in roko, inayin kwana biyu uku banyi wanka ba.
Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, aunty ta fada, sannan ta mike ta mikawa Sadiya dake kuka yaron ta koma kusa da Aysha ta jawota jikinta ta rungume, itako Ayaha fashewa tayi da kuka sosai, tana jinta rungume jikin Rukayya rabonta dataji an rungumeta haka tama manta, ashe rungumewa ma rahama ne, Kara shigewa jikin Rukayya take tamkar zata shige jikinta, ahankali Rugayya tace Aysha Ina mahaifiyar ki take duk wannan abun yake faruwa?
Tana nan acikin gidan nan, amman ita bata cewa komai, sai abun da su Umma sukace, nasan ko bataso yadda suke min bazata iya hanasu ba, Kuma itama bazata kulani ba haka take tuni nasani.
Jimmm tayi, sannan tace, toh kishirya rana ita yau zan kaiki gurin mijin ki.
Cikin sauri ta dago daga jikin aunty ni bazani gurin saba aunty ai yana sane Dani yabarni anan.
Amman Aysha ki masa uzuri mana.
Baya ta juyawa aunty tana wasa da hannunta ganin haka aunty tace shikenan nasani Aliyu yayi laifi, be kyauta ba, yanzun abun da nake rokon alfarma wajen ki, tunda ba xaki gun Aliyu ba, ni kibini ki zauna gurina tunda yanzun inma fitan kikayi bakisan inda Zaki ba.
Cikin kuka Aysha tace Aunty bazani ba dan Allah kiyi hakuri.
Ajiyan zuciya aunty Ruqayya tayi har ga Allah ta damu da lamarin Aysha, hannunta ta daura akan gado bayan Aysha, sannan tace, " yanzun kenan inda Allah be kawo ni yau ba garin Zaki bari?, In kin fita kinbar gida yanzun kinsan hannun wa zaki fada ne?, haba Aysha, shikuma Aliyu idan ya dawo akace mishi ba'asan inda kike ba kina tunanin awanni hali Zaki sashi??
Aunty ni babu abun da ya dameni dashi, ba halin da zai shiga, yana sane yake yin haka, ni daman ban sanshiba arayuwata, tunda nasanshi nake shiga cikin matsala gashi kullum kara gaba take, shikuma janyewa yake, garama mota ta takeni na mutu in huta.
Cikin tsananin tausayawa Aunty tace kibar irin wannan tunanin, Kuma ki daukeni kamar 'yar uwarki, koma uwa kika maidani daidai ne, ko ban haifi kamarki ba kadan ya rage nafahimci kinyi fushi da Aliyu sosai dan haka mu aje zancen Aliyu agefe, ba Ina kareshi bane wannan kibarshi a tsakanin ku, kibini muje gidana ki zauna tare dani.
Amsawa tayi kawai dan takula aunty ta tausaya mata sosai, Kuma yadda take rarrashin ta da Kunya tace mata a'a
Aunty ce ta share mata hawaye sannan tace kin fasa tafiyar ko?
Kai Aisha ta daga.
Yauwa nagode Aysha, yanzun bari muje da Khalifa amishi wanka sai adawo dashi.
Na mishi wanka da yamma ma aunty ko za'a bari da safe?
Toh aini kin banin tsoro ne Aysha, ganin nake kamar idan banje da yaron ba tafiyar ki zaki yi.
A'a ba inda zani Aunty na miki alkawarin bazanje ko Ina ba.
Toh nagode da safe Sadiya zatazo ta dauke shi.
*****
Koda Ruqayya ta koma gida labarta masu halin da ake ciki tayi, sosai Innawo ta tausayawa Aysha, haka kuwa washegari da sassafe Ta tura adauko Khalipa, wanka tamai tamai tana zubar da hawayen tausayin yaron, bayan ta gama shirya shi jikin Ummi ta daurashi tana fadin Ummi ki kalleshi dan Allah kisa mishi albarka ba laifinsa bane ?
Tunda Ummi ta daura idonta akan yaron ta fashe da kuka, shikuwa yaji dadin wanka sai wuntsula kaba da hannuwa sama yake yi, sai rana aka mayar mata dashi, tundaga wanna. Ranar kullum Sadiya take kaiwa Ayaha ruwan wanka sannan ta dauko yaron amasa har suka cika kwana biyar, aranar ne Innawo ta shiga gidan ta kanta ta sanarwa Umma gobe za'a tafi da Aysha gurin Mijinta Nigeria, tana bude baki kuwa tace Allah ya rakata taki gona.
Tun aranar Aysha tafara hada kayan ta, bawani abu me yawa ta diba ba, akwati daya tayi nata Dana Khalifa, haka takejin duk zuciyarta babu dadi, saidai tana matukar son tabar gidan dan ayanzun dataga Umma gabanta har faduwa yake, hakama Maman Sadam garama Aunty Murja mgn ne batayi da ita amman bata gaya mata bakar mgn, washegari ne ya kama ranar da Innawo tace zasu tafi tun safe ta shirya saidai tana balakin son taga mamanta ba gani irin wadda ta saba mata ba, ganinta take son tayi mata ido da ido suyi mgn duk da tanajin zafin yadda take mata amman tana son ganinta.
Sai dai data fita saitaga maman Sadam na mata wani mugun kallo wadda tasan ko taje gaban mamanta indai maman Sadam na wajen bazata mata mgn ba.
Misalin karfe 6 na yamma Innawo da Sadiya suka shigo, a tsakar gida ta samu maman Sadam da Umma bayan sun gaisa tace nazo tafiya da Aysha.
Toh Allah ya taima ka, Sadiya ce ta shiga ta dauko akwatin ta fice yayin da Aysha ta fito sanye da hijjabi Innawo kuwa khalifan ta dauko.
Aysha kuwa kasa daga kafarta tayi daga kofar dakin dan haka Umma tace kije kiyi sallama da maman ki.
Maman Sadam ce tace a'a tayi bacci, Innawo ce tace eh kotana macci ta shiga haka.
Aysha bata jira amsan suba tashige dakin, yayin data samu Mama kan Sallaya, tsugunawa tayi gabanta, cikin fashewa da kuka, yayin da Innawo take tsaye saman Aysha take fadin, Aysha zata tafi gidan mijinta kisa mata albarka
Ahankali Umma ta motsa bakinta tace, Allah ya bada sa'a.
Innawo ce ta amsa da Ameen, sannan ta dago Aysha suka fito tana waiwayen mahaifiyar ta, suko su Umma har Aysha ta fita agidan maganganu suke marasa dadi wadda ke nuna sun yake zumunta da Aysha har abada.
Sosai Aysha take ganin bakinsu cikin ranta, badan Mamanta da Daddyn taba da zata iya fushi dasu da tace ita da gidan har abada, gidan Innawo suka nufa, Ummi da Aunty Rukayya ne a falon,, Innawo ce ta mikawa Ruqayya yaron sannan ta nunawa Aysha gurin zama tana fadin, kiyi hakuri kinji ko, insha Allahu wata rana sai labari.
Aysha ta dade kudun dune cikin hijjabi sai bayan Sallan mangariba ta sarara da kukan, saidai ko mgn bata iyawa, washegari sunyin sallah asuba suka kama hanya, har tasha Ummi da Innawo suka rako su duk da cewa babu fara'a afuskan Ummi amman ta masu fatan sauka lafiya, harma ta ziro hannun ta cikin motar ta gyara daurin hulan Khalipa tana fadin a gyara shi kada iskan mota ya sashi mura, har ma ta Kara da cewa aunty Ruqayya karbe shi ne.
Hanya suka kamo yayin da Aysha takejin babu dadi cikin ranta, sunyi tafiya me nisa sannan ta tuna da Babanta ko tantama batayi yayi tafiya ne da bazai taba daukan wannan lokacin bezo ba.
*****
Oyoyo Uncle Aliyu.
Tohowa sukayi gaba dayan su yaran maza da mata suka rungume shi, cikin wani irin yanayi yake daga kananan sama sannan ya Isa kujera ya zauna yana fadin, " Inna aunty?"
Wani Dan saurayi ne da bazai wuce shekara 16 yace tana Cameroon.
Lumshe ido yayi sannan yace, " yaushe ta tafi??
Yau kwananta 8.
Ta gaya muku ranar da zata dawo??
A'a
Mikewa yayi yasa hannun sa cikin aljihu ya ciro kudi ya mika ma yaron yana fadin, "kabawa Yaya Fahat Ina sauri ne, idan aunty ta dawo daga nan zuwa gobe da daddare komai dare kazo ka gaya min.
Gida ya koma cike da damuwa saidai yana shiga falon cikin daga murya Baffah yace,
" Ina Ruqayya?"
Sunkuyar dakai yayi yace bata nan.
Ina wasa dakai ne???
Wlh Baffah bata nan yaranta ne kadai agidan sunce tana Cameroon.....
***
*🕳️ BA'KAR FURA🕳️*
_A true life story_
*Na*
_Fadeela Lamido_
Episode 56- 57
Komawa Baffah yayi ya zauna yana cike da bacin rai, yayin da Momy take fadin, " kayi hakuri kabi komai ahankaali.
Aliyu kuwa kansa akasa ya juya ya koma dakinsa tare da fadawa kan godo yai ruf da ciki yana fadin, koma me Baffah yake zargina dashi nasan bazai wuce kan wancen auren bane
dan haka sosai yaji hankalin sa ya tashi, addu'a yake Allah yasa aunty ta dawo, domin yasan dole Innawo zata aikota gurin Baffah, sai dai itama besan yadda zata dauki zancen ba.
Washegari tashi yayi da matukar zazzabi sabo da yadda yake Jin damuwa sosai, gashi agobe yake son zuwa Cameroon amman Ina, yana tsoron yadda zai fad'awa Baffah.
Daker ya iya daurewa da yamman ya fito misalin karfe 5, bemasan inda zashiba kawai dai fitowan yayi, motarsa ya shiga ya zauna yana kokarin tadata yaga an bude gate din gidan, motar gidan su aunty Ruqayya yaga tana shigowa, take ya sake ajiyan zuciya batare data sani ba, domin yasan duk yadda akayi aunty ta dawo kenan.
Jira yake yaga danta Abba ya fito amman abun mamaki ita da kanta ya gani tana saukowa.
Cike da zullumi ya bude motar ya sauko, ya nufeta, yayin da tana ganin shi ta sake murmushi.
Dafda ita ya tsaya aunty yaushe kika dawo?
Jiya da Yamma, ance min kaje, Ina ta Allah Allah karka kama hanya.
Gobe nake da niyar tafiya, wani aikine ya taidani.
Ka makara matarka nata fushi dakai.
'Dan kawar takai yayi domin zuwa yanzun yasan tasan komai, cike da sonji yace, " kinje ne?"
Eh bama sau daya ba.
Sunanan lafiya ko?
Lafiya Lau, to Kai yaushe ka dawo?
Jiya da safe, nadawo ma nasamu Baffah sai fad'a yake yi, yana nuna wai yana zargina bani da gaskiya, jiyan ma shine yace in Kira masa ke.
Dan takatawa tayi da tafiya tana fadin, wani ya kawo masa labari ne?
Shine ban sani ba Aunty.
Jimmm tayi zuwa can tace, " ai yana gida yanzun ko?
Yana nan.
Barin je karka shigo, idan ba kiranka yayi ba .
Amsawa Aliyu yayi sannan ya koma cikin motar sa ya zauna.
Ruqayya ko ciki ta shiga cikin fara'a Momy ta tareta, bayan tace mata gurin Baffah tazo aka kaita har falon sa, Baffah na sauke ajiyan zuciya suka gaisa da Ruqayya, sannan yace mata, daman Ina son ganin ki, jiya na aika Haydar ya kiramin ke yace kinyi tafiya.
Eh Baffah Ina Cameroon, jiya da daddare muka shigo, toh daman Innawo ta bani sako tace Ina dawowa inzo in isar mata da sakonta gurin ka.
Toh toh naji, nima Ina son nai mgn dake, amman kafin nan bani sakon na Mama.
Shiru Ruqayya tayi tama rasa ta Ina zata fara, zuwa can tace, nima zuwa Cameroon din kirana tayi, tunda naji kira nai saurin tafiya, toh daje sai take min bayanin cewa akwai yariya data sauka a agidan nan watannin baya, wadda Aliyu yazo da ita.
Eh tabbas matar abokin Aliyu ko?
Eh toh, Innawo tace kayi hakuri kuma ka fahimci zancen dakyau dan Allah.
Inajin ki, muje, muje Ruqayyatu.
Toh Baffah wannan yariyar ba matar abikon sa bace kamar yadda ya gaya maka.
Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, Baffah ya fada sannan ya tsare Rukayya da idon sa yana fadin inajin ki.
Baffah wannan yariya ta dalilin ta Ummi ta koro Aliyu daga can Cameroon ya dawo nan da zama, domin sun nuna suna son juna, Kuma anyi anyi su rabu sunki, a yadda suka bani labari family yariyar ba inda basukai mgnr ba har kotu anshiga, amman sunki rabowa da juna, dan haka ta turoshi gurin ka kawai.
Subuhanallahi, kinji irin abun ko?, amman da Aliyu yazo nan, ba yadda banyi dashi ba inji dalili yaki fada min, daga karshe nabarshi kawai tunda Naga bason fada yake ba.
To Kuma Baffah sai gashi ya kumayin wani kuskuren agaba, domin da yariyar ta biyo shi nan kasar bayan shekara biyar da rabuwan su Ya kamata ya sanar maka sabo da abashi shawaran abun da ya sace.
Shiru Baffah yayi yana jinjina zancen, cikin ransa zuwa can yace, " a'a ikon Allah, bana mantawa lokacin na mishi fada akan zuwanshi da ita, amman saiya rufemin baki da fadin ajiyansa aka bashi Kuma ma matar Aure ce, toh abun da yasa ban damu ba lokacin, yariyar cikin su Meenat ya barta, daga baya yace min Mijinta ya dawo, tazo tamin sallama na mata alheri, duk ta saba da yara, yanxun haka ko jiya sunata cewa zasu zasu Cameroon gurin ta.
Ai Baffah da yace maka Mijinta ya dawo mota yasata ta koma gida, Innawo tace dan Allah Kai hakuri karka dauki zancen da zafi dan kafin ta koma gida wani abu ya shiga tsakanin sa da yariyar........
Batakai ga karasawa ba Baffah ya dafa kansa yana fadin Innalillahi wa inna ilaihir raju'un.
Yana rike da kansa aunty Ruqayya tace Baffah dan Allah kayi hakuri abun da suka guda kenan suka turoshi nan, amman dake kaddara ta riga fata soyayya najanta, saida ta biyo shi nan, bayan Kuma ta koma da wata uku iyayenta suka gane tana dauke da ciki, wadda aka rasa inda ta samushi, domin bata kula kowa, Baffah saida yariyar ta haihuwa aka tabbatar d'an na Aliyu ne, domin jinin sa ya nuna sosai Koda yariyar bata fada ba yaron yayi kama dashi kamar an tsaka kara.
Motse baki Baffah yayi idon sa akasa sannan ya dauke gilashin sa dake gefen kujera yasa a idon sa, daker ya iya bude baki yace, shikenan sai ya aureta kawai.
Jimmm, Aunty tayi sannan tace, " eh bayan yaje lokacin ta haihu kotu suka kaishi, nan ta kwashe komai ta gaya masa har tahowan da tayi da yariyar.
Bayan ya gama sauraron Ruqayya yace, " shikenan Ruqayya bakomai, ni musulmi ne dole in amshi kaddara mekyau da mara kyau, ni daman naji kishin kishin din yayi aure a Cameroon, naji daga wani abokina da nake bawa sako na musashi, ganin wani ya sake min mgn nace barin tuntube ki, su Kuma iyayen yariyar ai bekamata suyi watsi da ita ba, wannan auren da akayi shine maganin abun, Kuma wannan ya Isa yasa zuciyar su ta huce, Amman fa laifin na Aliyu ne, inda ya gaya min tunfarko da ke zan nema kisata agaba ki mayar da ita gaban iyayenta, su Kuma iyayen idan suna da hankali lokacin zasu gane auren shiyafi dacewa dasu.
Ai Baffah iyayen yariyar nan banjin kome za'ayi zasu bada ita.
Toh shikenan, abun da ya faru ya riga ya faru, yanzun abun da za'ayi tunda Aliyu beda gurin zama, besa zaiyi aure ba bare ya nema, wancen part din daman can danshi na gina shi, yariyar tazo ta zauna aciki amman fa duk abun da zanma Aliyu yanzun zan masa domin yariyar ne, domin yariyar ce abun tausayi idan bata samu farin ciki ba akwai matsala dole Aliyu ya riketa dakyau, idan har yana son in huce dashi ya kyautatawa yariyar nan, akanta zan bashi mamaki matsawar yace zai wulakantata. Tun shine silar lalata mata rayuwarta, Ina da 'ya'ya mata idan aka masu bazanji dadi ba, dan haka itama yariyar nasoko cikin yarana idan ya nemin ya wulakantata zan rufe idon incimai mutunci, wannan shine sharadina.
Cike da farin cike Aunty tace toh mungode Baffah insha Allahu zasu zauna lafiya.
********
Aliyu taganin tahowan Aunty ya fito cikin motar, yadda yaga fuskanta yasashi ya sake murmushi yana fadin, " kungama?"
Eh, ya fahimta, amman kasan dole zaiji babu dadi, ya Kuma ce babu wulakanci, Kuma a kanta zai iya saba maka, yana nufin dai beson rigima, yana son ka rike ta amana.
Ba rigimar da zamuyi aunty, ko munyi ma babu meji kanmu.
Murmushi tayi sannan tace Allah yasa, amman ai koni yanzun najiku, tunda Aysha bakaramin fushi take dakai ba, samunta nayi fa ta hada akwati zata shiga duniya, sabo da fushin da take dakai.
Nashiga uku, ya fada yana zare idon, tare da fadin, har kin Kara min tashin hankali, Anya kuwa baxan tafi yau ba?, toh aunty kinji dai nayau, amman insha Allahu wannan ne nafarko da kikaji kanmu kuma na karshe.
Dariya aunty tayi sannan tace, zafi kowa farin ciki da hakan kuma lokacin ne zan tabbatar daku masoya ne, Aysha kuma daker na dakatar da ita, Amman zakazo gidan mu da daddare ko?
A'a kam, muyi sallama kawai yanxun?
A'a kaxo.munyi da ita zam bada sako ka Kai mata.
Kansan ya sosa kadan sannan yace saina zo toh.
Motar ta shiga suka bar gidan yayin da Aliyu ya koma cikin gida yana sauke ajiyan zuciya.
Misalin 8:00pm Aliyu ya fito da nufin zuwa gidan aunty saidai yana son ya sanar da Baffah gobe zai wuce Cameroon dan haka ya fara zuwa falon sa, da sallama ya tura kofar ya shiga, Islam da Meenat ne suka amsa Baffah ko juyar da kansa yayi can gefe.
Zama yayi agefen sa yana fadin Ina wuni Baffah.
Lafiya, kawai ya iya cewa fuskan sa babu alamar walwala, Su Meenat ne suka gaidashi ya amsa sannan ya sake kallon Baffah yace, " gobe zanje Cameroon.....
Tun be rufe baki ba Baffah yace, " ka gaishe su.
Kasa tashi yayi domin ba haka suka saba sallama ba idan zaiyi tafiya, ya dade zauna sannan ya tashi jiki ba kwari ya fito.
Baffah kuwa Aliyu ta nafita ya mikawa su Meenat key din part din da Aliyu zai zauna yana fadin, " ku rike wannan masu aiki zasuzo gobe su karba.
Baffah na meye ne key din?
Na wancen part din ne, yayan ku zaizauna aciki da matar sa.
Baffah zaiyi aure ne??
Yamayi a Cameroon.
Idon suka zaro saidai sun kula kamar Baffah bayajin dadi dan haka sukayi cikin gida.
Basu dade da fita ba Momy ta shigo lokacin Baffah yana dafe da kansa, kallon sa tayi sannan tace Alhaji wani lbr naji abakin yara, wai da gaske Haydar yayi aure a Cameroon??
Eh, yayi.
Amman Alhaji kana nuna min iyakata agidan nan, wato sabo da banice uwar shi ba bazaka gaya min komai da ya shafe shi.
Kiyi hakuri, cikin bacin rai nake, abu me dadi shi kake rawar jikin gaya, Ina wannan yariyar da ya taba sauka agidan nan?
Eh naji matar abokin sa.
Karya yamin kawai matar sa ce.
Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, lallai ma Aliyu.
Baffah da beson zancen yai nisa mikewa yayi kawai ya nufi dakin gidan mahaifiyar sa.
******
Ai danaga har 08:30pm baka zoba na dauka baza kazo ba.
A'a aunty, na tsaya gurin Baffah ne, kince ya fahimta amman naga daker yake min mgn.
Cikin ido ta kalleshi sannan tace karka damu da wannan, Kai inda ace da yariyar da 'Dan kazo mishi ai da kun kwasa 'yan kallo, karka damu ai abun ma yayi kyau, kama godewa Allah, har cewa yayi fa ga guri nan ka zauna kafin ka nemi wani.
Karyar dakai Aliyu yayi yana fadin, toh yanzun aunty bani sakon in wuce sauri nake yi"
Toh shiga daki yana nan gefen gado ka dauko.
Mikewa yayi yabi hanyar data nuna masa, be taba shiga dakintaba amman Kai tsaye ya tura kofar.
Babban dakine me dauke da wawakeken gado, idon sa ya sauka akan wani yaro dake ta wasa da kafarsa da hannunsa, sai kushin kushin yake, tsintan kansa yayi da saurin karasawa, saidai idon shi na sauka akan yaron yaga kamar gizo ne dan haka yasa hannun sa yana kokarin daukan yaron tare da saurin juyawa yana Kara kallon yaron.
Cak ya atsaya alokacin da yaga Aysha ta fito daga wanka towel daure bisa kirjinta yayin da ta yafa wani a kafadanta.
Binta da kallon yayi sosai yake mamaki yana Kuma tsareta da ido.
Itako Aysha ganinsa ya sata daure fuska sosai, tasan dole ne yasan tana gidan Amman bata zaci zasu hadu da wuri haka ba, ganin inda yake binta da kallo tundaga sama har kasa yasa tai saurin komawa toilet din yayin da yai saurin takowa tare da mika hannun sa, adaidai wannan lokacin ta bugo kofar tare da fadin, wayyo aunty!!!
Runtse idon sa yayi saboda zafin da yaji sosai kofar ta matse hannun sa, yayin daya kara rike Khalipa dakyau da hannun sa daya yana fadin, "Aysha menene haka?, daman kun taho tare?, Aysha ki bude kofar mana"
Arikece Aysha ke Kiran sunan aunty ganin haka Aliyu yace, " ki bude ki fito, kibar kiran aunty haka.
Nika fita, bana son ganin ka.
Ni din?
Eh.
Haba Ayaha nine fa yaya Aliyu malamin ki, daman d'aliba tana fushi da malaminta ne???
Toh bakai bane saikamin alkawari baka cikawa dan kawai kaga bana gurin, ka manta dani😭
Nidin?, akasi ake samu Aysha, tayaya zan mance ku, arana bana iya kirga so nawa nake tuna ku, kiyi hakuri kinji.
Ni ba kalmar da zaka gaya min.
Toh naji, yanzun fito ki amsa Khalipa.
Ka ajeshi inda ka ganshi.
Toh zan ajiyeshi, sai yaushe zan ganki to??
Ni karka sake min mgn.
Kawar da kansa yayi daga kallon kofar, Khalipa ya zubawa ido sannan yace, naji bazan sake miki mgn ba, amman kibani rana da lokacin da zan miki mgnr.
Jinta shiru yace mgn nake fah.
Ni babu ruwana dakai
Lumshe ido yayi sannan yace, aure muka yi fah Aysha, kinta ganin mata tace babu ruwanta da Mijinta alhalin tana karkashin ikon sa??
Wannan karon batace komai ba,dan haka yaci gaba da cewa, ," baya ga haka Kuma ke dalibata ce, Kuma har yanzun ni malamin ki ne dan haka ki fito kawai.
Yana gama fadin haka ya koma bakin gadon ya zauna yana me zubawa kofar ido, zuwa can yajita cikin kasa da murya tace, " ka dan miko min hijjabina.
Akwai yaro a hannuna kizo ki dauka.
Ka ajeshi mana
A'a, ya fada sannan ya dauke kansa yana cigaba da fadin, Idan sabo da nine na juya baya na ki fito abun ki.
Lekowa tayi taga ya juya bayan kamar yadda yace, dan haka ta fito tai saurin daukan hijjabinta ta sanya, shiryawa tafara, yayin da Aliyu ya maida hankalin sa kan Khalipa tsayon lokaci sannan yace, " idan kin gama zan wuce.
Can kasa tace nagama.
Juyawa yayi ya kwantar da Khalipa tare da tufa masa addu'a sannan ya mike har ya wuce ya miko hannunsa ya jawota ya hada ta da kirjinshi ya rungume.
Sosai ya rungumeta tamkar wani zai kwace ta, ajiyan zuciya yake saukewa da karfi yayin da numshin sa yake sauka a tsakar kanta lokacin daya yake kewaye duk ilahirin jikinta, nan danan taji jikinta na amsawa, bata so ta sauko da wuri haka ba dan haka ta kokarin ta dake, daker take iya turesa take kaimasa duka.
Duk inda ta nemi ta kubce rokota yake, gashi tanayin abun ne cikin kuka gaba daya.
Aysha kiyi hakuri, bason bacin ranki nan, gaba zaki tabbatar da haka, Ina tsananin sonki fiye da tunanin ki, kuma zanyi kokarin insaki farin wadda ba'a iya kwatantawa, kibar zargina akan rashin cika alkawari, na farko nasan da gangan nayi, saboda tun ranar da kika gayamin jiya kika gama al'adarki na rubuta na ajiye, Kuma saidana kirga wata tara sannan na kamo hanya, amman wannan karon akasi aka samu, dan Allah ki nutsu ki gaya min matsalar ki ayanzun dani, nikuma zanyi kokari in gyara komai, zama nake son muyi mekyau, Ina son ki bani hadin kai, ya kasance ni dake har abada babu mejin kanmu, ko wani abu ya faru tsanin mu ne kowa banson wani yaji, nasan halin ki kinsan nawa, nasan kina da taurin Kai, ni Kuma ina da zafi idan raina ya baci, yanzun kinsan me nake so dake???
Tana kwance akirjin sa ta kirgiza kanta.
Bani shawaran hukuncin da zan dinga miki idan kin kureni da taurin kanki, nikuma zan baki shawaran abun da ya kamata kiyi idan fushina ya tashi har kika rasa inda zakiyi dani......