Free chapter · Read without an account

Chapter 21

by Ummulkhair Abba Muhammad · MIJIN MACE ƊAYA PART ONE


MIJIN MACE ƊAYA Part 2

Book by Ummul khair Abba Muhammad.


MU ƘARU DA JUNA




Warin hammata abu ne wanda yake zuwa mostly da puberty..Wani warin hammatan kuma rashin wanka da kyau ke kawo shi..Wani kuma naturally haka Allah ya halicceshi da shi.

Aske gashin hammata yana ƙarawa jiki lafiya..da kariya daga kamuwa da cututtuka..

*Coconut oil*

Coconut yana dauke da sinadarin ƙara haske da kuma vitamin E..

Ki dinga shafa man kwakwa kullum a hammata ya yi minti 15 kafin ki shiga wanka..bayan hakan sai a wanke shi da sabulu da ruwa mai ɗumi.


Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai.





HAFSAT BAYAN TA KOMA GIDA

Hajiya Maryam da Alhaji Abdullahi, iyayen Hafsy zaune suke a parlour a gaban dining table sai ga 'yar aiki ta shigo cikin rutsunawa ta gaishe su, kana ta ajiye abincin ta fice.

 Sallama Hafsy ta yi riƙe da ice cream a hannunta, sai duk hankalinsu ya karkata ga bakin kofar, fuskarta cike da fara’a Daddynta na gwaninta ya ce, "To,yau Daddy’s girl me ya faru ne ana ta fara'a haka?"

 Mahaifiyarta ce ta ɗan rage volume na TV da ake wani series film a Zee world.

Bayan ta zauna ta gaishe su tana murmushi ta ce, "Daddy yau fitan da na yi ba...." Sai ta yi shiru, "Daddy’s girl faɗa mini mana."

  Ta langaɓe wuya, "I will tell you later but now ka taɓa abin da na zo da shi ta ciro ice cream ta mika masa."

 Ya karɓa tare da cewa, "Thank you my lovely daughter, zan sha but sai na kammala da cin abinci."

Mahaifiyarta ta gyaɗa kai, "Yana da kyau, ni da a ka ce mini supermarket zam za a kawo mini amma kina ganin daddynki kin manta da ni ko na gode."

 Ta miƙe ta zo daf da mahaifiyarta, "So sorry Mummyna, na isa na manta da ke, i apologize." Ta ƙarashe maganar tana murmushi.

"Rabu da ita my daughter, ta manta sunanki Daddy’s girl a ke ce miki ba Mummy’s girl ba. Ta yaya ba za ki fara da ni ba."

"Abin ma gori ne ko, to Allah ni ma ina roƙonƙa ka arzurta ni da ɗiya na samu Mummy’s girl, idan ta zo duk sai na yi maganinku."

 Dukkansu suka tuntsire da dariyar maganarta.

Hafsy ta ciro cake ta dubi Mummynta, "Mommy ki yi haƙuri na san ki da son cake ki ci shi, ke da dad duk matsayinku ɗaya yake a gare ni, next idan na zo da abu da ke zan fara, sai ma kin koshi zan waiwayi Dad kin hakura."

 Ta dubi mijinta ta yi masa gwalo. "Ka dai ji next da ni za a fara." Hafsat ta sa wa mahaifiyarta cake a baki ta gutsura bayan ta cinye ta ce da 'yar ta, "Na hakura my daughter, koma wajenki mu zauna mu fara dinner."

 Mahaifinta ya miƙe, "Daddy’s girl a gaban nawa ki ke faɗa mini haka, shikenan, bari na ba ku waje ke da Mummyn naki."

  Ya mike ya nufi bedroom, haba dad ita ma ta bi shi a guje ta dinga rarrashinsa tare da marairaice murya suka dawo falo suka ci abinci.

 Bayan sun kammala cin suka ƙara volume na television hankalinsu na ga kallon kowanne daga cikinsu na cin tuffah.

 Hafsat ta fara miƙa da hamma ta yi wa iyayenta sallama ta nufi sashenta.

 Ta faɗa gado tana murmushi ta ɗauki wayarta ta yi try number Mus'ab a ka ce da ita currently switch off, ta miƙe tana zazzagaye ɗakin bayan kowace daƙiƙa sai ta kuma try amma a kashe a ke ce mata kawai ta jefar da wayar ta faɗa gado ta kwanta ruf da ciki a zuciyarta ta ce, "Me ya sa zuciyata ta damu da wannan guy ɗin ne?"

 Ta juya rigingine, "Tsarinka na burge ni Mus'ab da za mu kwana muna hira da kai ba zan gajiya ba."

Ta tashi ta zauna haɗe da yin tagumi, "Ban san soyayya ba, ban san mene ne so ba, amma lamarinka na tasirantuwa a zuciyata. Ba abin da zuciyata ke so kamar ta dinga tuna ka hakan na sa ta farin ciki."

 Mus'ab na kwance a jemammiyar katifarsa ya ce, "Na yi wa Hafsat karya zan kira ta a waya alhali ban da waya, me ya sa ban fito fili na faɗa mata gaskiya ba."

Ya mirgina, "Tun da ta ba ni number ta bari na je ko da wurin Idi mai shayi na ƙira ta a wayarsa."

 Ya miƙe ya nufi wurin Idi mai shayi ya shaida masa wayarsa ko na flashing babu ya duba aljihunsa ya yi sa'a akwai gudan 100 ya je ya sayo katin ya sa yana saka number da ya ƙira ya ji ya shiga daɗi ya maimaye zuciyarsa.

Hafsat na kwance da ta ji ƙira ta jawo wayar nata da ta ga number da ba ta sani ba ta ja dogon tsaki ta ki picking.

Mus'ab da ya ga an ƙi ɗagawa ya kuma retrying sai a ƙira na huɗu tukun ta ɗaga tare da cewa, " Please who am speaking with."

Ya ce, "Ranki ya daɗe, kina magana da Mus'ab ne."

Murmushi ta yi tare da lumshe ido, "Mus'ab, ina ta trying number ka ana ta ce mini switch off."

"Eh haka ne mai chargy da na ba wa ne ya rufe shagonsa ina ga ya tafi wani uzurinsa ne wannan wayar abokina ne na ƙira ki da shi."

 Ta kashe ta ƙira da wayarta sun shafe lokaci mai tsawo suna hira, kana ta buƙaci ya faɗa mata inda za ta same shi gobe sai su wuce gidan Zoo, ya kwatanta mata sannan suka ajiye time.

Bayan sun gama wayar ta saki tattausar murmushi ta ce, "Tabbas na kamu da son wannan bawan Allah, Allah ya sa idan na furta masa kar ya watsa mini ƙasa a ido." Ta lumshe ido, "I love you Mus'ab."

 WASHE GARI

Hafsat ta cancanɗa kwalliya ta zo gaban mahaifiyarta ta durƙusa, "Mummy da ma Zakiyya Umar ce ta ƙira ni take shaida mini Safiya Musa ba ta lafiya ya kamata mu je mu duba ta shi ne na zo neman izini." Ta ƙarashe maganar tana sosa keya.

Ta numfasa, "Hafsat, da wata ce ba Safiya ba ce ba inda zan bar ki je, don yarinyar tana da mutunci, ni ban son yawace-yawace jiya kin fita yau ma haka. Na amince amma kar ki daɗe."

  Ta miƙe, "In sha Allah Mummyna na gode."

 Ta ɗauki mukullin mota ta fice.

A inda suka yi za su haɗu tana zuwa ta hango Mus'ab tsaye na sanye da kayan da kana gani ka san talaka ne, ta tsaya daf da shi ta buɗe mota, "Bismilla, ka cika alƙawari." Tana maganar ne tare da murmushi Mus'ab ya shiga ta ja mota.

 HAFSAT DA MUS'AB A GIDAN ZOO

 Bayan sun shiga ta biya kuɗin da ake bayarwa yayin da aka shiga gidan Zoo, suka zazzagaya suka kalli dabbobi.

 Daga nan suka wuce wani keɓaɓen wuri mai sanyi wanda jama'a ba su fiye wuce wa ba suka zauna suna fuskantar juna, ɗan nesa da su Wild animals ne da aka katange.

 Hafsat ta taho musu da drinks masu sanyi, yayin da ta kurɓa ta ajiye ta zuba masa dara-daran idanuwanta sai ta ce cikin ɓacin rai

 "Mus'ab ka yi mini laifi." Ya zaro ido, "Laifi kuma Hafsat da yaushe na yi shi?"

 Ta ya mutsa fuska, "A yau ka yi shi kuma a cikin gidan Zoo ɗin, Mus'ab na yarda da kai ka ci mini amana. Ina yi maka kallon mutumin kirki ashe ba haka kake ba. Ina ga ba ka san ni 'yar wa ba, za ka gama rayuwarka cikin gidan yari."

Fuskarsa cike da tashin hankali, "Don Allah ki faɗa mini abin da na yi."

 Cijan laɓɓanta ta yi tare da miƙewa, "Ka yi mini satar babbar abu na san ko ban ambaci sunan abin ba kana sa ne." Ta harare shi, "Ɓarawo!"

 Cikin ɗaga murya da zafin rai ta ci gaba da cewa, "Kar ka kuskura ka musa saboda ka san daga ni sai kai babu wanda ke tare da mu da zan zarge shi."

Mus'ab jikinsa ya shiga rawa kamar mazari, saboda bai taɓa tunanin Hafsat za ta yi masa irin wannan sharrin ba, a zuciyarsa ya ce, "Da ma kin shigo rayuwata ce dan ki ɗana mini tarko? Ta Allah ba ta ki ba."


Ta kyalkyale da dariya,  "Mus'ab!"

"Na'am." Ya ce da ita idanuwansa a ƙasa.

"Ka ɗago fuskarka ka kalli kwayar idona, me ya sa ka fita hayyacinka cikin kankanin lokaci?"

 Da kyar ya iya ɗago kai ya kalle ta, "Ko za ka iya faɗa mini me ka gani a cikin ƙwayar idona?"

 Bayan ya sunƙuyar da kai ya ce, "Gaskiya ban ga komai ba."

 Ta miƙe ta zo daf da shi tana murmushi, "Ka ce ba ka ga komai a ƙwayar idona ba. Abin da ke cikin ƙwayar idona shi ne tsantsar soyayyarka, shi ne babbar satar da nake nufi ka yi mini duk wanda ya sace zuciyar mutum da kuma ruhinsa akwai irin satar da ya kai shi a doron duniya? Ina son ka ina kaunarka, Mus'ab daga kallo ɗaya da na yi maka a jiya na kamu da ciwon son ka, ban taɓa sanin so ba, ban taɓa sanin so na shiga cikin zuciya lokaci guda ba sai a kanka, Mus'ab, ka sace zuciyata ka hana ta sakat a lokaci guda, ina dai fatan satar da ka yi za ka adanata a waje mai sanyi mai inuwa ba a wajen da za ta kuntata ba. Daga ƙarshe ina mai ba ka haƙurin razanar da zuciyarka da na yi."

Ta durƙusa guiwowinta a ƙasa, "Ka yafe mini my dear."

 Mus'ab mekewa ya yi yana ja da baya ya ce, "Ki yi haƙuri ba zan iya karɓar wannan soyayyar ba."

Cikin sanyayyir murya kamar za ta yi kuka ta ce, "Mus'ab don Allah ka karɓi soyayyata, kar ka kunya ta ni, ina mace na ajeye matsayina ta mace na furta so a kanka, don Allah dan soyayyarka da Manzon Allah ka so ni."

 Ta yi shiru shi kuma ya ka sa cewa komai.

Ta katse shirun, "Ina sauraronka fa."

Ya sauke ajiyar zuciya "Ki ba ni lokaci na yi nazari."

Murmushi ta yi, "Ba damuwa, Allah ya sa zuciyata ta ji abin da za ta ji daɗi ba wanda zai tarwatsa ta ba."

Haka suka miƙe ta kai shi har unguwarsu suka yi da juna bayan kwana uku za su kuma haɗuwa.

Mus'ab tun da suka rabu da Hafsat maganganunta ke kai wa da dawowa a zuciyarsa ya gaza samun nutsuwa.

  Ya rafka tagumi ya ja numfashi mai ƙarfi ya ɗaga idanuwansa ya dubi agogon da ke maƙale a bangon ɗakin 2: 30am ya furta a fili, "Yau ni ne har warhaka ban runtsa idanuna ba?"

 Ya miƙe ya je ya yi alwala ya shiga yin nafilfili.

 WASHE GARI

Bayan ya yi wanka ya shirya tsaf ya je ya gaishe da mahaifiyarsa, daga nan ya miƙe ya nufi wurin abokinsa Mansur don ya labarta masa halin da yake ciki kuma ya ba shi shawara.

 Zaune suke bisa kan wani dandamali Mus'ab ya zayyanewa Mansur halin da yake ciki kana ya dube shi, "Abokina wanne shawara za ka iya ba ni?"

 Shiru ya yi na some seconds then ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Shin zuciyarka na son ta, ko kuma za ka karɓi soyayyarta don tausaya mata da kuma matsayinta ta 'yar attajirai."

Ɗan ƙara gyara zamansa ya yi sannan ya ce, "Tabbas zuciyata ita ma ta kamu da son baiwar Allahn nan don jiya saboda tunaninta na gaggara runtsawa sai bayan asuba bacci ɓarawo ya sace ni."

 Ya numfasa ya ci gaba da cewa, "Abokina, ba don komai zuciyata ta so ta ba, sai don ta siffantu ta ɗabi'antu da abubuwan da mutum zai so mutum don su, a iya haɗuwa da muka yi na fahimci tana da kamala da kamun kai, ga ta da saukin kai babu jiji da kai ko raini na 'ya'yan attajirai."

Ya dafa shi ya ce, "Abokina, ka karɓi soyayyarta tun ka yaba da halayenta ta cancanci a so ta, sannan ita da kanta ta furta kalmar so a gare ka, to ka sani ka taka babban mataki a zuciyarta, ina muku fata na alheri Allah ya dafa maka."

 Ya amsa da amin suka yi sallama Mus'ab ya nufi wurin buga-bugarsa.

 BAYAN KWANA BIYU.

 

Mus'ab ya amince da shawarar da abokinsa ya ba shi amma ya kudirta a zuciyarsa ba zai yi accepting nata lokaci guda ba sai ɗan ba da lokaci.

 HaƊUWAR HAFSAT DA MUS'AB

Zaune suke cikin mota tana wasa da key motarta a hannunta Mus'ab ya ce da ita.

"Ko me ya ja hankalinki game da ni kika buƙaci soyayyata?

 Murmushi ta yi, cikin siririyar murya ta ce, "Abubuwa da yawa kaɗan daga cikin: kana da kamala da kamun kai sannan na fahimci kai abin duniya bai dame ka ba, wannan ɗabi'u naka shi ya burge ni har na tsinci kaina da kwaɗayin son ka, kasancewa da irin ka babban nasara ce a rayuwa."

 

 Ta yi murmushi ta ci gaba da cewa, "Ni na san ba za ka taɓa watsa mini ƙasa a ido ba, za ka amince za ka karɓi soyayya ta saboda..."

  Ya datse ta ya ce, " A'a Hafsat kar ki amsa abin da ni nake da ikon amsa shi, kar mu yaudari junanmu, ni da ke kwarya ta bi kwarya. Ba zan iya soyayya da ke ba ni talaka fitik ne, kowa ya je ya nemi daidai da shi. Kin san an ce kowace ƙwarya da abokiyar gurminta."

 Yana dasa ayar a maganarsa ya kalli cikin kwayar idonta, "Ko zan iya tafiya?"

Wani irin gumi ne ya yanko mata ta sa handkhieif ta goge ta fara magana kamar mai son yin kuka, "Mus'ab shin ba ka san shi so maƙaho ba ne, baya gani, baya banbance talaka da mai kuɗi baya bambance mummuna da kyakyawa shi dai idan abu ya masa to ya yi, ko da bai yi wa wasu ba, SOYAYYA gamon jini ce. Ya kamata ka fahimta. So haɗuwar jini ce ba ruwansa da kyau, kuɗi, ko mulki, nasaba, ko cancanta duk soyayyar da ka ga tana duba bisa abubuwan da na lissafo to ba so na gaskiya ba ne."

 Ta fashe da kuka, "Mus’ab ya kamata ka so mai son ka. Ban taɓa jin son wani ɗa namiji ya ɗarsu a zuciyata ba sai a kanka. Ni a baya ma ina daga cikin waɗanda suka jahilci so haɗuwa ta da kai na fahimci soyayya gaskiya ce duk wanda ya faɗa tarkonta ba zai taɓa samun nutsuwa a rayuwarsa ba sai ruhin da ya kamu da son ya karɓi soyayyar don Allah don fiyayyen hallitta don soyayyar da kake wa iyayenka ka ce kana so na za ka rayu da ni za mu zamo ma’auratan juna."

Shiru ya yi kamar wanda ruwa ya cinye ta dube shi, "Ya ka yi shiru? Kai fa nake sauraro."

 Tunani mai zurfi ya shiga maganarta ce ya katse tunanin nasa ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Hafsat ba zan iya furta su ba ƙarya da ciwo ko da na ce ina son ki, batun aure ba ni da ƙarfin yin sa, saboda ba ni da sana’a ko aiki takamaimai, ko duba muka yi a musulunce ma Allah ya ce shi aure ga wanda ya na da iko ne, ni kuma kin ga ban da iko."

 "Allah zai ba ka iko, ni dai kawai ka karɓi batuna ka furta cewa ka amince ka na so na. Mus’ab zuciyata ba za ta taɓa samun nutsuwa ba idanuwa na baza su iya runtsawa ba, ba tare da ta ji amsar da zai fito daga bakinka ta kasance da na ta iri ɗaya ba. Kai fa ka alƙawarta mini ga shi kana ƙoƙarin ka saɓa kuma ka san girman alƙawari."

 "Hafsat ki rarrashi zuciyarki abin da kika zo da shi ne karɓar shi da a cikin ƙanƙanin lokaci akwai kuskure, ban son na yaudari zuciyarki na mata ƙarya na fi so nayi mata gaskiya a kodayaushe duk abin da zan furta ya zama tabbas hakan, idan kika yi haƙuri za ki ji hairan. Yanzu abin da nake so mu kulla da ke kawai friendship."

Shiru ta yi sai ta tuna wata maganar da ake cewa, first step of love is friendship shi kenan ta nuna masa ta amince, kana ta ce da shi me ya sa number da ya ba ta tana trying kullum ana cewa a kashe, nan ya faɗa mata gaskiyan lamari an sace masa wayar ya yi welcomeback har yanzu Allah bai hore masa kuɗin sayar wani ba.


Ya ce, "Yanzu kin fara fahimtar waye Mus’ab ko? Talaka fitik da ke rayuwa ba waya."

 Ta tauna lips ɗin ta, "Ban son kana faɗan haka, ka sani da talaka da mai kuɗi duk Allah ne ya yi su kuma ya ce ba wanda ya fi wani a gare sa sai wanda ya fi tsoronsa."

 Ta ja mota, wurin da ake sai da wayoyi ta je ta sauka ta ce ya tsumaye ta ta sayo waya bayan ta shiga ta zauna ta damƙa masa waya ya ki karɓa ta kaɗa ta raya ya nuna sam shi fa ba zai karɓa ba ta nuna matuƙar ɓacin ranta, a take fuskarta ta sauya ta ce, "Mus’ab, me ya sa kake son bakanta zuciyar mai son ta dadaɗa maka? Ka fi so ka yi ta azabtar da zuciyata ko? Saɓa mini da kake tamkar azabtar da ni kake, ya kamata ka tausayawa zuciyar da ta ce tana son ka, kana ba ta haɗin kai. Haba wanda ya ce yana son ka fa ba ka da tamkarsa." Ta ajeye masa waya bisa cinyoyinsa. "In ba ka yi amfani da shi ba, ba zan taɓa yafe maka ba a rayuwa. Ni ba wai na ba ka don ka gaza ba ne, na yi ne don kyautatawa."

Da ya ɗaga kai suka kalli juna ya fahimci tsananin ɓacin rai sun bayyana a allon fuskarta na game da kin karɓar kyautar da ta yi masa, ala dole ya karɓa ya jujjuya wayar sai ya ga ya fi na hannunta ma tsada, ya nuna mata matuƙar godiyarsa haɗe da nuna jin daɗi. Ta sake tattausar murmushi da dimple nata suka motsa, tare da cewa, "Ko kai fa, hakan ya dace ka yi mini tuntuni." Daga nan ta ja mota ta kai shi unguwarsu ta sauke shi.

    

Mus'ab al'amarinsa da Hafsat yakan ba shi mamaki gani yake kamar a shirin film kwance yake yana kallon silin zuciyarsa na kai wa da komo wa game da ita, tabbas yana son ta amma idan ya tuna matsayinsa da matsayinta sai ya ji da kamar wuya don wutsiyar raƙumi ta yi nisa da ƙasa. Ya san wannan soyayyar zai iya fuskantar ƙalubale a tafiyar don mafi aƙasarin 'ya'yan attajirai iyayensu ba sa so kwata-kwata 'ya'yansu su auri 'yan'yan talakawa sai dai a yi ƙwarya ta bi ƙwarya. Lallai idan haka ne akwai ƙura, amma akwai ƙalilan daga cikin su duk abin da 'yan'yansu suka zo musu da shi suka nuna suna so suna accepting. 

A fili ya ce,"Ya Allah ka sa ni ma iyayen Hafsat suna daga cikin irin waɗannan iyayen. Duk wani ƙalubale da zai kasance a tsakaninmu ya kawo cikas Allah ka kawar da shi tun kafin ya afku. Idan kuma za ka jarabce ni da shi ka ba ni ikon cin nasara a wannan jarabawar."

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol