Free chapter · Read without an account
Page 33
🧟♀️ *WATA SOYAYYAR!* 🧟♀️
*_Labari/Rubutawa_*
*AMINA ABUBAKAR YANDOMA*
( _Meenat A Yandoma_ )
tare da
*ZAINAB MUHAMMAD*
( _Indian Girl_ )
*NOTE*
_Labarin nan zamu rubuta shi ne a yadda yazo, duk abinda kuka gani mun rubuta a haka aka tsara labarin._
*GARGAƊI!*
_A guji yi mana amfani da labari ta ko wace hanya sai tare da izinin mu_
*PROMO! PROMO!! PROMO!!!*
🥳🥳🥳
*Zumar ƙiba da ta Hips wadda kuka sani a 3500 yanzu ta dawo 3000🤩, ga kuma garin ƙiba 3in1 muna sai da ƙwara ɗaya 3500 bokiti kuma 4500 a cikin sauƙi promo muke💃🏻, ga kuma maganin infection me aiki sadidan wanda ake sha da lipton akan 1000, Hanzar ta ki mallaki naki yar uwa domin neman ƙarin bayani ku tuntube mu akan wannan number ***, Siyan na gari meda kuɗi gida.*
*PAGE 5️⃣9️⃣&6️⃣0️⃣*
...A gigice Alkhamis ya taka birki suna neman hanyar ficewa daga motar sakamakon Fatima da suka ga jikinta na wata iriyar lanƙwasa tamkar macijiya.
Riyo da bai taba tozali da al'amari irin wannan ba firgicewa yayi ya hau kurma ihu yana jijjiga murfin motar da ya datse ko motsi ya ƙi yi, dariyar da suka ji Fatima ta babbake da ita ce ta saka Riyo sakin fitsari jikin shi na wata irin kyarma.
"Masoyina kuma uban ƴa'ƴana barka da sake haɗuwar mu a karo na biyu, bazan tafi in barka ba saboda ina sonka ina ƙaunar ka zan rayu dakai Alkhamis ka taimaka ka soni ka rayu dani."
Fatima ta ƙarasa maganar cikin wata iriyar murya tana amsa amo, fashewa akayi da wani irin kuka tamkar ba za'a daina ba, sai kuma ta tuntsire da dariya a hankali kuma dariyar ta fara yin ƙasa har ya kai basu jin komi.
Duk da dunƙulewar da suka yi wuri ɗaya bai hana Alkhamis ɗago kanshi ya dubi Riyo.
"Ka taimake mu ka duba ka gani Aljanar yarinyar nan kodai ta fice daga motar nan"?.
Riyo daya haɗa gumi ta ko ina hannu yasa ya yarfe zufar goshin shi tare da kallon Alkhamis.
"Amma kamisu Allah ya isa tsakani na da kai, dama kasan yarinyar nan mayyace amma dan mugunta ka saka ni shiga mota ɗaya da ita, ka cuce ni ka haɗani zama da ƙarfen ƙafa ka buɗe mani mota in fice."
"Ka fita ni ka barni cikin masifa in kaga na bude motar nan to mun isa gida ne, sannan kuma maganar an saka ka masifa bata taso ba domin kai ne wanda ka zugani muka zo garin nan domin neman matar aure kaga ko nine ka cuta, tunda naga yarinyar nan na lura kaman nin su ɗaya da Fatima jikina ya bani wannan yarinyar Fatima ta ce."
Alkhamis ya ƙarasa maganar tare da yin ƙarfin hali ya leƙa inda Fatima ke zaune, a kwance ya hango ta barci ya ɗauke ta, ajiyar zuciya ya sauke tare da tayar da motar.
"Wai da kasan da haka amma ka amince aka ɗaura maka aure da Aljana, Alkhamis ka cuce ni daka bari na tsoma kai na cikin wannan harkar."
Alkhamis kuwa bai bi ta kashi ba ya fizgi mota suka fita daga karkarar domin baisan yadda zata kaya ba in fatima ta farka, abu ɗaya ya saka ma ran shi shine koda Fatima Aljana ce bazai taba sakin ta ba domin yadda yake jin soyayyar ta in ya rasa ta zai iya rasa rayuwar shi..
***
...Tun bayan bacewar su Fatima su Jauro suka koma cikin Rugar labari ya bazu cewa sun aurar da ɗiyar su ga mutanen burni hasalima ba'asan su waye ba, abunka da Rugar Fulani haka aka fara yi masu tofin ala tsine akan sun siyar da ɗiyar su ga ƴan yankan kai.
Takanas mata Rugar suka wanke ƙafa suka zo har gida suka tultulema inna habaici da Allah wadai na abunda suka aikata, tun bayan ficewar matan mahaifiyar Fatima ke faman kuka ita da ƙanwar Fatima a haka har Jauro ya taras da ita.
Abinda bai taba ba sunan ta taji ya kira, ɗago kanta tayi da jajaten idanun ta tana me goge hawaye.
"Nasan kina cikin baƙin cikin abinda danginki da kuma mutanen gari suka zo har gida suka yi maki, nayi wannan abun ne badan komi ba sai domin gyara rayuwar Fatima shin kin manta da abinda ya faru a baya ne"?.
A firgice ta dube shi tare da furta.
"Ban manta ba na roƙe ka mu bar maganar nan domin kuwa magana ta ƙare Fatima dai tayi nisa damu."
"Shiyasa nike so ki kwantar da hankalin ki domin yaron nan bai bar rugar nan ba sai da ya rubuta mani lambar salula da suke amfani da ita tare da rubuta mana kwatancen gidan shi a tarkarda ina me tabbatar maki Munyi kuskuren aura ma shi ita ba tare da bincike ba amma munyi hakan ne domin bamu da wata mafita, ina me sake jaddada maki ranar da suka cika mako biyu da tafi a ranar zamu bisu burni domin muga inda suke rayuwa.
Jin wannan bayani na Jauro ya matuƙar faranta ran mahaifiyar Fatima dan haka ji tayi ta samu rangwamen abinda take ji cikin ranta...
***
...Matar dake hawayen jini kuwa wata mahaukaciyar tsawa ta daka ma jaririyar dake gefen ta.
"Me ye dalilin daya saka kullum in na bayyana sai na ganki a tare da waɗan nan mutanen; ko a tunaninki zaki iya taimakon su ne"?.
Babbakewa jinjirar tayi da dariya sannan ta cira kanta ta kalli matar.
"Abinda ya kawo ki nima shine ya kawo ni fansa nazo ɗauka mummunar fansa a kansu."
"Hhh Wato Jidda kun cika cikakkun mugaye ita ma ɗiyarku ta dawo gareku ne domin kuji a jikin ku, zamu haɗa ƙarfi nida ita domin ɗaukar fansar da zata gigita rayuwarku."
Tana ƙarasa maganar wata mahaukaciyar dariya suka kece da ita ɗakin ne ya fara girgiza sai kuma wutar shi ta ɗauke, jim kaɗan kuma ta dawo.
"Yazid wallahi ina tsoron wannan Jaririn cikin da aka ce mani ya bare yanzu kuma lokaci ɗaya ace ya tashi har na haihu anya babu ƙullalliya a cikin al'amarin nan"?.
"Jidda wace irin ƙullalliya kuma, Ubangiji ya bamu yaro wanda muke matuƙar buƙata amma ki fara wasu surutai na banza yanzu shiryawa za ki yi muje asibiti domin duba lafiyar ki."
Badan Jidda taso ba haka ta haƙura ta shirya suka je asibiti.
Shi kan shi likitan ya gigita da ganin wannan yaro domin idanu ne dashi tamkar balan-balan ga wani irin rafkeken kai, kan shi yafi jikin shi girma nesa ba kusa ba, an tabbatar masu da jaririn da Jidda duk suna cikin ƙoshin lafiya.
Koda suka fito daga asibitin kai tsaye gidan Mahaifiyar Jidda suka wuce; ganin Jidda ta shigo washe baki ta hauyi domin a tunaninta jikin Jidda ne ya tashi an maidota gida ne ayi mata magani ita kuma hanyar samun kuɗinta ta buɗe.
Bayan sun gaisa Jidda ta sauko Jinjirin dake bayan ta tare da mika ma Mahaifiyar ta.
"Na shiga ukki! Jidda yanzu dan baku haihuba sai ki je ki ɗauko wannan aljanin ki riƙe shi a matsayin ɗa Jidda kauda mani fuskar shi kada yasa inji mafarki."
Sai da Jidda ta bari takai aya sannan ta kwashe kaf abinda ya faru ta sanar da ita.
Mantawa tayi da suffar yaron son kuɗi ya rufe mata ido tace babu inda za'a koma da Jidda gida za'a barta har sai anyi suna babu yadda Jidda da Yazid suka iya haka suka haƙura Yazid ya ɗauko ma jidda duk wani abu da zasu buƙata tare da ba Mahaifiyar ta maƙudan ƙudi sannan ya nufi gidan iya dan ya sanar da ita.
Kar kuso kuga murna wurin iya domin ita dama tace bata yarda ba wai cikin Jidda ya bare.
A gaggauce Iya ta shirya ta nufi gidan iyayen Jidda.
Ƴan barka ne cike da gida suna ta tofa albarkacin bakin su domin wasu ma gulma ce ke kawo su don su gane ma idon su.
Iya kuwa kallo ɗaya tayi ma yaron taji cikin ta ya murɗa wani zawo ya kutso kai, ba shiri ta miƙa yaron ta shiga bayan gida; ta jima a ciki kafin ta fito ta koma ɗakin.
"Dukkan wasu alamu sun tabbatar yaron nan Jinnu sun shafe shi dan haka zamu dage da neman magani domin tun wuri sai mun tashi tsaye."
"Magani ai yana buƙatar kuɗi; kuɗi zaku bada mu kuma mu nemo malamai da yan bori har sai yaron nan ya samu lafiya."
Mahaifiyar Jidda ta faɗa.
"To shikenan zani turo Yazid domin ya kawo kuɗi nima kuma ta babgare na zani fara neman maganin."
Iya bata bar gidan ba sai ana gaf da magriba.
Jidda kuwa harga Allah tsoron yaron take domin bata yarda ba cewa shi ɗin jinin ta ne.
Ga yaron sam baiyi kuka ba har yanzu sai dai in ya kafe ka da ido yana kallo sai ka sha jinin jikin ka.
Maƙudan kuɗi Yazid ya kashe domin shirya gagarumin suna na kece raini.
Ranar suna yaro yaci sunan mahaifin Yazid wato Bello.
Da sun san abinda zai faru ranar sunan tabbas da basu shirya wani taron suna ba.
Duk yadda mahaifin Jidda yaso hana taron sunan amma sai da suka yi shi babu yadda ya iya haka ya haƙura yabar masu gidan.
Jidda kuwa an sha kyau na ƙarshe ana ta zuba ƙamshi sai fara'a ake ganin gida ya cika da yan biki.
Mutanen unguwa kuwa ganin irin abinciccikan da aka shirya da kuɗin da aka kashe yasa suka ce wannan banza ba zata wuce su ba, dole ne suzo au ci banza.
Wata makwafciyar su ce ta shigo gidan tana ta washe baki musamman data hango har an fara raba abinci.
Ba zato ba tsammani kawai taji ta kece da mahaukaciyar dariya, kallon ta babbiya mutane suka fara yi mata dan haka wasu dangin Jidda ganin zata bata masu taro yasa suka yi kanta.
Babu zato babu tsammani suka ji su ma sun hau babbaka dariya hada hawaye.
Kafin ka ankara gida ya haukace da mahaukaciyar dariya ta kowane ban gare mata sun hau babbaka dariya wasu ma hada hawaye...
***
...Sai bayan magriba su Alkhamis suka iso gida, ana tsaida mota Riyo ya fito tare da sauke tagwayen ajiyar zuciya yana me jifar Alkhamis da kallon ka jefa ni cikin masifa.
Alkhamis kuwa leƙawa yayi dan ganin ko Fatima ta farka sai gani yayi har yanzu barcin ta take yi.
"Kamisu daga yau babu ni babu kai kada ka kuskura ka sake nema na muddun kuna tare da yarinyar nan domin ni ban shirya faɗa da Aljannu ba."
Yana gama maganar ya fice daga gidan tamkar zai tashi sama.
Babu yadda Alkhamis ya iya haka ya ɗauki Fatima ya shiga da ita ya kwantar da ita a falo.
Gefen ta ya zauna yana jin duk wani abu daya faru a baya yana dawo ma shi ɗaya bayan ɗaya.
Motsin daya ga ta fara ne ya sanya gabanshi yayi wata mummunar faɗuwa, wasu yawun wahala ya haɗiye ji kake muƙut!
Miƙewa tayi zaune tare da nufar inda Alkhamis yake, gaban shi ta durƙusa tare da fara magana cikin muryar da ta saka Alkhamis zare ido bayyanan nen tashin hankali ya sauka a fuskar shi.
"Dan Allah kayi haƙuri kuɗin da ka buƙata ne ban samo ba sai yanzu, kada ka rabu dani kada kace zaka juya mani baya mutuwa zanyi."
Daskarewa Alkhamis yayi lokaci ɗaya jikin shi ya fa ra kyarma tamkar mazari domin abinda ta gama faɗa Fatima ce kaɗai ke faɗa ma shi irin shi, bai sake tsinkewa da al'amarin ba sai da yaji Fatima ta kece da dariya tare da Furta.
"Ka amshi kuɗin domin sune nazo in kawo maka."
Hannun ta ya kalla nan yayi tozali da kuɗi.
Watsa ma shi su tayi a fuska tare da shigewa uwar ɗaka tana dariya.
Alkhamis kuwa duk da sanyi A.C dake tashi amma wani gumi ne ke wanke ma shi jiki.
Tamkar kazar da ƙwai ya fashe mawa a ciki haka Alkhamis ya miƙe ya nufi ƙofar fita; abinci yaje ya samo kasu tare da siyoma Fatima kayan sawa domin kuwa yasa ya ɗebo ruwan dafa kanshi kuma koda zai rasa ran shi ba zai taba sakin Fatima ba.
Koda ya dawo zaune ya iske ta takure a saman kujera tana rarraba ido.
Sallama yayi ta ɗago kai tana murmushi abincin ya bude tare da buƙatar ta sauko suci.
"Sallah zanyi; shin kai kayi kuwa"?.
Shuru yayi domin kuwa yau i ta ce rana ta farko da mace ta fara tuna mashi cewa bai yi sallah ba; a tare suka gabatar da sallar tamkar ba Alkhamis ba wai yau shine dayin sallah akan lokacin ta.
Abincin ya ɗauko masu tare da mika mata kayayyakin daya siyo mata don takai ɗaki ta shirya su.
Bayan sun gama cin abinci wani irin barci ne ya fa ra fizgar Alkhamis Fatima kuwa ɗaki ta faɗa ta barshi nan yana gyangyaɗi.
Saurin mikewa yayi sakamakon jin ana kokawa a ƙurya, kururuwar Fatima ya jiyo tana kiran sunan shi, a guje ya afka ɗakin sai dai abinda majigin idanun shi suka hasko ma shi tuni yaji kafafunshi sun kasa ɗaukar shi ba shiri ya sulale kasa zuciyar shi na bugawa da sauri, idanun shi ya rumtse jikin shi na wata irin kyarma tamkar mazari...
*MEENART..........✍🏻*