Free chapter · Read without an account

CHAPTER 13 (UNEXPECTED)

by Khadeejah Bint Ismail · WANI RABON........

WANI RABON.........🦋🦋🦋


Khadeejah Bint Ismail ( deejasmah)


In dedication to all single ladies out there........


Wattpad @deejasmah15

Arewabooks @ deejasmah


WhatsApp @***


N.B WhatsApp only not call😁



Chapter 13(Unexpected)


Wannan shafin gabaɗayan shi sadaukarwa ne ga Aunty Nazeefah Nashe na yaba nagode sosai da kulawarki soyayyarki daban take a zuciyata Allah ya k'ara girma da arzik'i ya kuma albarki zuri'a ya kuma rayasu ya shiryasu bisa tafarkin gaskiya 

Allah ya bar k'auna❤💕


Grill🔐

Appreciate hard times, Someday they'll just be another chapter in your success story.


Misalin biyu na dare na farka daga baccin da ya d'aukeni bud'e idona nai a hankali cikin sanyi ina mai addu'a tareda kallon gefena Areepha ce kwance daga gani bata san bacci ya kwashe taba duba da yanayin da tai baccin mik'ewa nai na taho gabanta da niyyar gyara mata kwanciya zuruf ta mik'e tana kallona "Addah ya jikin?" ta furta cikeda kulawa "Alhamdulillah " na bata amsa ina nufar toilet


Alwala na d'auro kafin na fito a zaune na sameta ban ce mata uffan ba na tada sallah har na idar idonta biyu saidai sab'anin d'azu da take kan bed yanzu tashi tayi ta nufi gefen gadon inda suka ajiye flask "Addah zaki sha tea ne ko kuma in dafo miki indomie " girgiza kai nayi ina baro kan dadduma saida na zauna a gefen gadon kafin nace " black tea issokay banjin wani yunwa kuma bacci nakeji " ok tace tareda had'omin tea d'in godiya nai mata kafin na kafa baki na fara shan tean 


Saida na kammala na koma na kwanta kafin itama ta kwanta cikin k'ank'anin lokaci bacci ya d'auke ta niko idanun na lumshe na dad'e a hakan kafin baccin ya sake d'auka na kiran sallahn asuba ya sanya ni bud'e idanu cikin jin k'warin jikina ya dawo hamdala nayi jin na dawo dai-dai ba tareda na tashi Areepha ba kasancewar nasan ba sallahn zatayi ba na nufi toilet wanka nayo tareda d'auro alwala kafin na fito riga na zura ina tada sallah jin an shiga masallaci ina lazumi naji shigowar Mamie ganin abinda nakeyi ne yasata komawa ba tareda ta shigo ciki ga bad'aya ba saida na idar da lazumi kafin na tashi na isa gaban mirrorn namu shafa nai a sauk'ak'e sannan na bud'e wardrobe d'ina 


Wine colored fluffy skirt na d'auko tareda wata cream colored long sleeved shirt akan stool na d'aura kayan sannan na ciro wani wine colored plain asma veil sai undies farare shiryawa nai tsaf ina kallon gashin kaina daya ke buk'atar kulawa a raina na kud'ire saidai weekend kuma dan gobe kam daga office gidan bestie zan zarce dan nayi kewarta ga kuma mitan da tayi min jiya a lokacin ma ina office 


Inner cap na nemo cream color ina suturta kan nawa kafin na koma sofa ina mai d'aukan tab d'ina wacce take d'auke da tambarin MATAWALLLE GLOBAL na bud'e schedule d'in ranar na duba ina sake tsarawa kasancewar jiya ban duba ba ko kad'an addu'a nai Allah yasa nayi kasanceawar ban taba presenting schedule d'inba but based on the little knowledge i have da kuma abubuwan da muke dasu a ranar na shirya iya abinda zan iya dukda dai ance baa iyawa shi boss d'in 


To do list d'ina na shiga tareda tsara na ranar gudun shiga lokaci ko kuma mantawa sannan na saita reminder ta kafin na d'auko files d'in da na tara reports na ayyukan d akayi sanda baya nan dubawa nakeyi gudun ko na manta wani abun ban rubuta ba a daidai lokacin Mamie ta sake shigowa d'akin cikeda mamakin ganina ina aiki kamar ba patient ba da sauri na d'ago ina kallonta 


"Good morning ma'am " na fad'a ina dariya zama tai kusa dani tana cewa "ai dole kiy dariya kema keda nai tunanin zaki huta yau a gida tunda ba wani dad'i kike jiba " murmushi nai tareda cewa " ai na warware Mamie dama stress ne na aiki kuma yanzu alhamdulillah " gyad'a kai tayi tareda amsa gaisuwa ta tana mai tambayata jikina y'ar fira kad'an muka tab'a kafin na maida komai mazauninshi 


Tashi nai na kammala shirin fita ganin har almost 17 minutes to 7 turarena na fesa mai sanyin k'amshi kafin na dauk'i veil d'in ina rolling kaina dashi ina sa pin mai k'ananun stones suit na d'auka cream color ina d'aurawa akai "omooo see hajiyar ofis " na jiyo muryar Areepha tana fad'i hararar ta nayi ina cewa "meye kuma hajiyar office ana zaman lafiya ?" dariya suka fashe dashi ita da Mamie da itama ni take kallo tasowa tai tana cewa " ai ke d'ince tubarkallah wallahi wannan had'uwa haka " 

"Shine zaki wani kirani hajiyar office, hmmm k'azama wuce toilet jare" k'ara sautin dariyarta tai jin yadda nai maganar kamar wacce take wari kafin ta shagwab'e face ta nufi wurin Mamie " sweetheart kinji ta ko wai nice k'azama " ta fad'a tana kwanciya a jikin Mamie " k'yale hajiyar ofis auta na ai kowa yasan ke ba k'azama bace "


 Itama Mamien ta fad'i hakan turo baki nai ba tareda na kallesu ba na kunna data ina neman uber kasancewar in na biye musu latti gaishe da Mamie tayi kafin nima ta gaisheni amsawa nai ina d'aukar backpack d'ita ina nufar k'ofa sakamakon an sanar dani motar zata iso nanda 5 minutes ganin haka yasa Areepha nufar toilet tana cewa "sai kin dawo Addah Allah ya tsare " Ameen na fad'a ina cewa in wancan sarkin baccin ya taso kice ina gaisheshi fitowa mukai daga d'akin da Mamie shoe rack dake corridor d'in namu na nufa loafers cream na zurawa k'afata kafin na k'arasa dining inda Mamie ta had'omin abinci a wata lunch box godiya nai mata ina pecking cheeks d'inta sallama nai mata kafin na nufi k'ofa jin horn alamun drivern ya iso 


Kusan 7:15 na iso office d'in ko mota d'aya babu a harabar wurin saidai akwai k'arin securities a dan saida suka amshi ID card d'ina suka duba kafin suka barni na shiga babu kowa a reception knocking nai a cubicle d'in k'awata Raheena da mamakina sai gata ta taso tana mai hararata "yess?" da alamun tambaya ban kalleta ba nace "you obviously know what Im here for " turo baki tayi tareda mik'omin book d'in signing nayi tareda time d'in kafin nace mata "have a nice day " 


Ina mai nufar elevator har floor d'inmu babu kowa sai janitors guda biyu dasu keta aikin su gaishe su nayi tareda bud'e office d'ina d'aya ne ya shiga ya gyaro ciki ni kuma nai zama na a wata doguwar waiting sofa dake gaban office d'in ban damu ba don banson inyi lattin zuwa a samu matsala shima mai gyaran bai wani dad'e ba ya fito nikuma na shiga ciki data na kunna bayan na zauna ina mai duba messages d'ina kasancewar jiya I wasn't active replying wainda duke buk'atar hakan nayi kafin nai offing datar ina mai concentrating a aikin gabana 



7:55


Na fara jiyo siren yana tashi lek'owa nayi ta window ina mai kallon harabar companyn a daidai time d'in motoci uku suka shigo ciki ta farko da ta k'arshen dukansu bak'ak'en TUNDRA ne sai ta tsakiyar kuma Lexus ce silver gyad'a kai parking sukai ainda aka tanada domin parking d'insu daga haka ban sake ganinsu ba komawa nai na zauna inajin raunin yana dawowa cikin mintuna da basu shige uku ba naji alamun isowar su floor d'in gyara zama nai Ina mai fuskantar inda nasan zan gansu domin dai glass ne maraba kawai kuma na tinted bane both na ciki da kuma na waje zasu iya ganin juna 


Sanye yake da wata grey colored Tuxedo Grain De poudre suit sai shirt black da straight black trousers sai k'afarshi dake saye cikin black crespo crystals studded leather shoes daga k'afan shi na fara kallo izuwa fuskarshi dake sakaye da black shade dogo ne sosai babu laifi saidai ba mara k'wari ba cos he's well sculpture like an Italian god kyakkyawane ba kuma irin mai mugun kyaun nan ba kalar jikinshi golden brown ne saidai gyara da kuma hutu ya k'awata hakan


Yana da dogon hancin saidai ba wani siriri sosai ba sannan kuma ba faffad'a ba saida ace matsakaicin girma sai lips masu kauri da tudu idonshi manya ne k'wayar ciki ba bak'i bane kalar brown ce sai lashes mai yawa da kuma brow da ya k'awata idanuwan nashi kasancewar cikarsu da kuma bak'insu fuskarshi da saje wanda ya kusan had'ewa da gemunshi mara tsawo da cika sosai sai gashin kanshi da yasha gyara anyi styling d'inshi in a unique and elegance way gefen shi Sahal ne d'ago min hannu yai hakan yasa nai murmushi in response PAn shine yake take musu baya 


Saida sukai wurin 30 minutes da shiga kafin na nufi k'ofar office d'in d'auke da file knocking nayi " yes" aka fad'i da wata murya da bansan mai ita ba bud'e k'ofar nai na shiga da sallama amsawa sukai a tare su biyu ne yanzu daga shi sai Sahal rungume file d'in nayi cikeda tsoro na nufi gaban table d'in a hankali na d'ago kai ina kallonshi " good morning sir " na furta ina kawar da idanuna daga kallonshi a hankali cikeda aji yace " morning " 


Cikin kame-kame na tambayeshi hanya "Alhamdulillah " ya furta a tak'aice satar kallon Sahal nayi gyad'a min kai yayi kafin yace " ammm Buddy meet Faheemah A.Sadauki your new secretary " kallon tsaf yai min da brown orbs d'inshi daga sama har k'asa kafin yace " welcome to Matawalle Global miss Sadauki........ " 


D'an murmushi nai tareda cewa "thank you sir" gyad'a kanshi yai yana daga inda yake a zaune file d'in da na shigo na mik'a mai hannunshi mai dauk'e da agogo k'irar kamfanin hublot yasa tareda k'arba yana bud'ewa nan kyakkyawan rubutuna ya bayyana kallon rubutun yai sannan ya kalleni duk'ar da kaina nayi cikeda nutsuwa na fara mai bayanin abinda ke ciki shikuma yana gyad'a kai har na kammala ajiye file d'in yayi kan table d'inshi yayi tareda cewa " I'll go through it again you can go " 


"Thank you sir" na furta ina kallon Sahal murmushi yai min akan lab'b'anshi yace " bravo alaiki bestienmu" murmushin nima nai tareda nufar k'ofa na fita inda na barsu suka cigaba da tattaunawa basu wani jima ba saiga Sahal ya shigo sake gaisheshi nayi zama yayi yana cewa " what a great presentation " thanks nace ina tambayar shi bestie bai wani dad'e ba ya fita ya barni ina aikina


Shiga na sakeyi da schedules d'in shi na ranar duba yai yana cewa inyi canceling wasu wasu kuma in barshi fitowa nai ina sake zama a haka dai har ranar ta k'are 5 dai-dai na nufi gida cikeda gajiyar zaryan da nasha daga nawa office d'in zuwa nashi dan haka ban iya moruwa ba ko kad'an saidai hakan bai hanani mamakin boss d'inba domin ban zaci tarbar da na samu daga gareshi sakamakon irin labaranshi dana samu tunanina ko korata zaiyi wanda hakan ne yasani zazzab'i amma yanzu kam banda wani fargaba a zaman office d'in...............


Godiya gareki hafsat hassan your comments keeps me going thanks for the love and care Allah ya bar zumunci I also love you too❤

#vote

#comment

#share

#add

Love y'all😍


Deejasmah🦋🔐❤

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol