Free chapter · Read without an account

Chapter 1

by Halimatou Khabir · ZANEN ZABUWA

*ZANEN ZABUWA*


        *©️ Nana Haleema.*




_Godiya ga Allah subahanahu wata'ala da ya bamu ikon ganin wannan sabuwar shekara cikin k'oshin lafiya da kuma kwanciyar hankali, ya Allah muna rok'on ka ka sada mu da dukkan alkhairin da yake cikin ta ka kuma nesan tamu da dukkan sharrin da yake cikin ta, ka saka mu yi ido hud'u da halak muyi sab'ani da haram, ka cika mana dukkanin burukan mu na duniya da na lahira a cikin ta, ka zauna da k'asar mu lafiya ka kuma zab'a masa shugabanin na gari a cikin ta, Amin._


_ina godewa Allah da ya bani damar sake d'aukar alqalami nake rubuta wannan labari cikin kwanciyar hankali da kuma nutsuwa, ya Allah ina rok'on ka ka bani ikon kammala shi lafiya kamar yadda na fara shi, Amin._


_Wannan labari it's created bai faru a gaske ba, duk wani abu da akayi karo dashi a ciki wanda ya faru da wani ko wata a gaske ayi hak'uri rashin sani ne._


⚠️ _Warning: ban yadda wani ko wata su canja min labari zuwa wata siga daban ba ba tare da izini ba._


*Page 1*





*Bayero University Kano (B.U.K).*

*Old side.*


Makaranta ce babba dake unguwar k'ofar kabuga dake garin Kanon dabo Nigeria, babban makaranta ce mai d'auke da dalibai daban-daban wanda ya had'a da y'an gayu, y'ay'an manya, y'ay'an talakawa. Makaranta ce wacce babba gari guda mai d'auke da b'angarorin karatu da dama, kamar b'angaren kimiya science kenan da kuma b'angaren zane-zane da sauran su. A cikin ta akwai wanda karatu ya kaisu da kuma wanda shashanci ne ya kaisu da wanda kuma suka had'a biyu.



Kamar koda yaushe zaune Jannat take a kan mazaunin da aka tanada dake cikin makaranta tana kallon agogon wayar ta da alama tana jiran wani ne domin yanayin ta ya gwada hakan. iska ta fesar lokacin da ta d'ago da kanta daga kallon agogon tana kallon mutanen dake ta kai kawo a wajan kowa yana harkar sa wasu suna shiga wasu suna fita.


Jannat yarinya ce y'ar kimanin shekara ashirin a duniya, bak'a ce irin bak'in nan mai kyau wanda yake su6ul babu tabo ko kurji a jikin ta, fuskar ta har golden-brown take bayarwa sabida yadda kalar ta ta amshi jikin nata, doguwa ce ba irin sosai din nan ba zata shiga cikin tsakatsaki. Tana da manyan idanu farare zagayayyu masu kyau da kuma d'aukar hankalin masu kallon su, hancin ta siriri ne mara tsaho sosai da fad'i, lips d'in ta jajaye kamar na labarawa k'ananu masu kyau da kyawun kallon.


Juya k'wayar idon ta tayi alamun gajiya lokacin da ta hango wacce take son gani taja k'aramin tsaki tana hararar ta tare da fad'in, "daga zuwa siyo kunun aya sai yanzu?". Zama tayi a kusa da ita tana bud'e murfin robar tace, "Kin cika k'orafi wallahi, ya bai zo ba har yanzu?". Rausayar da kai tayi tace, "bai zo ba gashi ina ta kiran sa kuma baiyi picking call d'in ba". "Wata k'ila ko wani abun ne ya tare shi amma kin san yana hanya ai." Bata ce komai ba ta mayar da hankalin ta kan wayar ta tana cigaba da kiran layin sa har lokacin bai d'auka ba, mik'ewa tsaye tayi ta juya baya tana kallon Nafisa tace, "kodai na tafi kawai?". Nafisa ma ta mik'e tace, "A'a kin san baya son kina hawa keke napep ki jira shi yazo d'in".


Zata yi magana kenan taji an bangaje ta wayar hannun ta ta fad'i haka littafan hannun ta tayi gaba zata fad'i Allah ya taimaka ta dafa abinda suke zaune, a fusace tayi saurin juyowa dan taga waye da wannan aikin haka, bayan sa ta gani da alama wuce ta yayi ba tare da ya tsaya ba hakan ya saka tace, "malam baka gani ne ko kuma kai makawo ne?" Ta fad'a yadda zai jiyo ta fuskar ta a had'e. Da saurin Nafisa ta mik'e tare zare ido tace, "ke Jannat me kike yi haka?" Juyawa tayi ta kalli wanda ya tsaya cakk sabida jin abinda Jannat d'in tace Nafisa tace, "kayi hak'uri bata san kai bane". Jannat a fusace tace, "akan me zaki bashi hak'uri bayan shine yayi min laifi? Ina ruwa na da ko waye shi da zaki ce wani ban san shi ba? Ubana ne shi?" Ta fad'a tana hararar Nafisa.


Kafin Nafisa tace wani abu Jannat ta sake cewa, "aikin banza wanda bai san darajar d'an adam ba, a haka za'a k'are kuma wallahi komai kake tak'ama dashi ni dai-dai da kai nake mtswwww." ta fad'a tana sunkuyawa ta d'auki jakar ta da littafan ta da wayar ta da screen d'in ya tsage.


D'agowar da zatayi ta ga idon sa a kanta yana kallon ta ta sake jan dogon tsaki tana hararar sa tace, "in kana yiwa mutane suna k'yale ka ni baka isa na k'yale ka ba, in taqamar ka rashin kunya na dame ka na shanye wallahi stupid man". Hannun sa ya d'aga da niyar zabga mata mari yaji an rik'e hannun daga baya hakan ya saka shi kallon wajan nan suka had'a ido da wanda ya rik'e hannun a lokacin da ya zagayo wajan yace, "Kar ka kuskura hannun ka ya tab'a jikin ta." ya fad'a yana sakin hannun sa, kallon sa yayi shima yace, "in na dake ta d'in akwai abinda zakayi ne?."

"Gargad'i nake maka akan hakan dan sai kayi zaka ga abinda zanyi d'in".

"Kai kasan waye ni?."

Murmushi Imran yayi yace, "ban damu da nasan waye kai ba ina fad'a maka ne kar kayi kuskuren dukan ta".


Kwafa Muhsin yayi ya kalli Jannat zaiyi magana wayar sa ta d'auki ringing ya kalla ganin mai kiran ya saka shi yace, "ki jira had'uwar mu ta gaba ba'a fad'a min magana, ba kuma a d'aga min murya." yana gama fad'ar hakan ya juya da sauri ya bar wajan zuciyar sa ta wani irin d'aci sabida b'acin ran da yake ciki, shi mutum ne da ya tsani rashin kunya musamman ma daga wajan talaka, talakan ma kuma mace, macen kamar Jannat wacce yana da tabbatacin k'anwar sama ta girme ta, inda motar sa take ya k'arasa ya shiga tare da bata wuta ya bar cikin makarantar.


Jannat ta kalli Imran cikin shagwa6ar da ta saba yi masa tace, "shine baka zo da wuri bako?." Fuskar sa tamke babu ko alamun murmushi yace, "wuce muje." Kallon sa tayi a tsorace jikin ta yayi bala'in sanyi ganin yadda ya had'e rai ta kalli Nafisa tace, "Nafisa sai gobe." Itama d'aga mata kai kawai tayi dan yanayin Imran itama kanta ya tab'a ta dan shi mutum ne mai fara'a da kuma wasa da dariya.


Yana gaba tana binsa a baya a tunanin ta zata ga babur d'in da yake zuwa d'aukar ta kamar koda yaushe amma sai taga ya nufi mota kirar civic one door ash kala ya bud'e mazaunin driver ya shiga itama ta bud'e gaba ta shiga tana sake kallon motar, bai kula ta ba ya kunna motar suka fita daga makarantar har lokacin bai kalli inda take ba sai fuskar sa da ya sake had'ewa kamar bashi ba.


jikin ta yayi bala'in sanyi hankalin ta ya tashi zuciyar ta ta fara wani irin bugu kamar zata fito daga k'irjin ta ganin yadda ko kallon ta yak'i yayi sai ma had'e fuska da ya kuma yi, "Yaya Iman." ta fad'a muryar ta na rawa kamar zatayi kuka.



Bai kula ta ba sai hankalin sa da yake kan titi yana tafiya cikin nutsuwa, hawaye taji ya fara bin kuncin ta ta sunkuyar da kanta ta fara kuka sosai tun baya fita har ya fara fitowa, gab da zai shiga underpass ta k'ofar gadon qaya ya faka yace, "kin san bana son wannan kukan naki ko?." Kanta na cikin cinyoyin ta tace, "ba kaine kak'i ka kula ni ba." 

'Ai kice kika b'ata min rai, Jannat mai ya kaiki fad'a da namiji kina mace?."


Sai a lokacin ta d'ago tace, "banfa sanshi ba kawai ina tsaye yazo ya bangaje ni waya ta tafi kalli kaga har ta fashe ma kuma yayi wucewar sa ko kallo na baiyi ba shine fa nayi masa magana." ta fad'a tana nuna masa wayar. Kallon wayar yayi yace, "da kin sani kin k'yale shi ai komai na duniya hak'uri ake yi."


Turo baki tayi tace, "kai komai ayi hak'uri shine fa da laifi bani ba." Gyara zaman sa yayi ya fuskance ta yace, "Amma da banzo ba kinga da ya dake ki ai ko?." 

"Ai wallahi da sai na rama ai ba haifa ta yayi ba."

Zaro ido waje yayi yace, "ki rama fa kika cee?."


Turo baki tayi bata ce masa komai ba sai kuka da ta sake fashewa dashi, "is okay Jannat ki bar wannan kukan dan Allah, za'a canja screen d'in wayar shikenan hankalin ki ya kwanta?." Share hawayen ta tayi bata ce komai ba har lokacin ya sake cewa, "amma dan Allah kar ki kuma sauraren sa kinji k'anwa ta, bana so wani abu ya same ki ko kad'an."


D'aga masa kai tayi tace, "insha Allah Yaya na bazan kuma ba kayi hak'uri na b'ata maka rai." Murmushi yayi mata mai kyau yace, "baki min laifi komai ba kawai naji haushin ganin ki da wani ne." Murmushin jin dad'i tayi tace, "Yaya na sarkin kishi." "Yess ina kishin k'anwa ta sosai ma" ya fad'a yana kunna motar suka hau kan gadar.


"Yaya na wannan motar fa?". 

"Tawa ce ita naje karb'owa shiyasa na jima banzo ba, kin ganta tsohuwa ko?."

Zaro ido waje tayi tace, "Da gaske Yaya na motar kace?." Kallon ta yayi kad'an yafin ya mayar da kansa titi yace, "da gaske nake mana."

"Alhamdulillah Yaya na yayi mota, kai yau abin farin ciki ya same ni ni Jannat." Baice komai ba sai murmushi da yayi yace, "Jannat bana so naga ina d'auko ki a machine tun daga nan har gida maza suna kallon ki raina yana b'aci sosai wannan dalilin ya saka kud'in nan da nake tarawa kawai na d'auke su na siyi wannan kinga ai ba sabuwa bace ba."


Cak ta tsaya da farin cikin tace, "Amma Yaya na kud'in fa jari naji kace zaka k'ara a kasuwa fa." 

"Jannat bazan iya ba na kasa jurewa na dinga ganin ki a machine ina yawo dake". 

"Amma Yaya jarin yafi siyan motar, dan kak'i yadda ne amma da sai na dinga dawowa na napep tunda baka so nake hawa machine d'in. " Girgiza kai yayi yace, "ba gwara na cigaba da d'auko ki a machine d'in ba da ki hau napep, masu keken da suke combining maza da mata a ciki, Jannat yadda aka tara wannan kud'in a hankali shima na jarin zai taru kinga ai ina aiki komai zai zo da sauk'i sosai." 


Ajiyar zuciya tayi tace, "kana so kace ko su Umma ma basu san ka siyi motar nan ba?". 

"A'a Umma tasan da maganar badai taga motar ba yanzu zata ganta." Shiru tayi ta kasa cewa wani b'angare na zuciyar ta na farin ciki da siyar motar wani b'angaren kuma tana jin rashin jin dad'in hakan.


"Ya fuskar ki ta canja kuma?" Ya fad'a yana Langwa6ar da kai, murmushi tayi kad'an k'aunar yayan nata na sake shiga jikin ta tace, "babu komai kawai gani nake kamar hakan baiyi dai-dai bane, amma naji dad'i wallahi sosai Yaya na."


Bai sake cewa komai ba ya shiga da tuk'in sa a hankali har suka K'arasa unguwar shard'a ya tsaya a k'ofar gidan su ya kalle ta yace, "toh a daina wannan fushin Jannaty na Allah zai shiga lamarin kinji?." Kai kawai ta d'aga masa bata ce komai ba sabida jikin ta yayi sanyi sosai hakan ya haifar mata da kasalar da ta kasa magana, ganin ta kasa magana yace, "kije ki huta nasan kin gaji zan shigo gidan wajan Gwaggo in anjima." Batace komai ba ta d'auki littafan ta da suke cinyar ta ta bud'e motar ta fita ta shiga gida shima ya gyara zaman motar dake layin nasu yana da girma sosai ya fito ya shiga nasu gidan dake jikin wanda Jannat ta shiga.


Da sallama ya shiga tsakar gidan nasu wanda aka mulmule shi da siminti yayi tasss babu ko tsinke a kansa sai d'aukar ido yake yu, mutum uku yaji sun amsa masa sallamar hakan ya tabbatar masa da yayyen sa mata guda biyu suna nan tare da mahaifiyar su, fad'ad'a murmushin sa yayi ya shiga gidan yana fad'in, "yau muna da manyan bak'i kenan a gidan." ya fad'a yana K'arasa inda tabarmar take a shinfid'e suna zaune su uku suna hira, "zuwa nayi daman yau ka cika min jaka ta dan baza tafi ba sai naji na kasa d'aga jakar tawa." d'aya daga cikin su ta fad'a tana kallon sa da murmushi. Murmushi ya sake yi ya zauna a gefen tabarmar yana cewa, "indai jaka za'a cika miki baki da damuwa babbar Yaya". "Sannu Imran yau ka jima baka dawo ba." Umma ta fad'a murmushi tana kallon d'an nata da kulawa. 


Murmushi shima yayi yace, "na biya na d'auko Jannat kuma daman akwai albishir babba da nazo muku dashi." Dogon tsaki d'aya daga cikin su taja tace, "dallah malam mu zancen ka muke so kayi mana ba wata Jannat ba, kai komai Jannat ba za'a tab'a hirar arzuk'i dakai baka saka zancen yarinyar nan ba?." Sakk yayi yana kallon Yayar tasa kafin ya langwa6ar da kai kamar k'aramin yaro yace, "Yaya wai mai Jannat tayi miki ne haka dan Allah?." Tsaki Umma tayi tace, "kai ka kula ta ma har kake tambayar ta abinda tayi mata, ina jinka meye abin albiishri d'in?."


Duk jikin sa yayi sanyi ba kamar d'azu ba yace, "mota na siya gata can a waje." Zaro ido Anty Surayya tace, "mota fa kace k'ani na? Da gaske kake ko wasa?." "Da gaske nake mana Anty, tana k'ofar gidan nan." Ai bata jira wata magana ba ta mik'e da sauri ta zari mayafi tayi waje da gudu, tsaki Yaya Binta tayi tace, "kenan sai da y'ar gold d'in taka ta riga mu ganin motar?."


"Ke bana son shirmen banza, me yarinyar nan ta tare miki ne bakya son ta haka?" Umma ta fad'a cikin fad'a tana kallon ta.


Tab'e baki tayi kawai ta kawar da kai gefe a lokacin Anty Surayya ta dawo tana fad'in, "gaskiya mota tayi kyau Imran, Allah ya tsare ya kau da idon mak'iya ya kawo wacce ta niinka ta sau d'ari biyar." Sosai yaji dad'in addu'ar yayar tasa yace, "Amin Anty na nagode sosai." Umma ma tace, "Allah ya tsare ya baka kariya a duk inda kake". "Amin Umma".


"Asslaamu alaikum" sallamar Jannat ta katse masa maganar da yake niyar yi, "Amin, wa'alaiki salam maraba da Khadijah" Umma ta fad'a da murmushi a fuskar ta tana kallon Jannat da itama take murmushi tare da k'arasowa tsakar gidan, "Jannaty yanzu kika dawo daga school fa, me ya fito dake ko hutawa bakiyi ba?." Imran ya fad'a yana kallon ta bayan ya d'an had'e fuska, turo masa baki tayi tace, "to ni ba su Anty nazo gaishewa ba."

"Meyasa baki bari sai anjima ba? Kofa abinci baki ci ba ga magariba tana neman zuwa."

"To sai ka d'auke ta ka mayar da ita tunda y'ar gold ce ba'a so tasha wahala." Yaya ta fad'a tana hararar su duka biyun dan ba k'aramin takaici ya shek'a mata ba.


Babu wanda ya tanka mata Jannat tace, "Umma ina wuni". "Lafiya lau Jannat ya Gwaggon naki?". "Tana nan qalau, Yaya ina wuni, ina wuni Anty" duk ta fad'a a jere tana kallon su, Anty ce tace, "Lafiya lau Jannat, ya makaranta?". "Alhamdulillah" ta bata amsa jikin ta a sanyaye dan a rayuwar ta in akwai abinda ta tsana bai wuce ta gaida mutum yak'i amsawa ba bayan kuma yaji. 


Mik'ewa tsaye tayi tace, "Umma bara na koma, Anty ku gaida gida a gaishe mu dasu Ihsan". "Zasu ji insha Allah, kwana biyu baki lek'o mu ba ai." Murmushi tayi kad'an tace, "dana samu hutun makaranta zan zo". "Allah ya kawo ki, ki gaida Gwaggon". Da to kawai ta amsa ta fita daga gidan Imran ya bita da kallo har ta b'acewa ganin sa kafin ya sauke numfashi ya dawo da kallon sa ga Yaya da take aikin sakar masa harara baice komai ba ya mik'e kawai ya fita daga cikin gidan ransa a b'ace. 


Dakalin k'ofar gidan su ya zauna zuciyar sa na wani irin zafi sabida b'acin ran da yake ciki, in akwai abinda yake saurin b'ata masa rai bai wuce yaga wani ko wata sun tab'a masa Jannat, yana saurin tunzura a akan hakan duk hak'urin sa baya iya hak'uri akan abinda ya shafi Jannat dalilin da yasa shi baro gidan kenan dan in ya zauna zai iya yin b'arin zance ga yayar tasa, "Imran ya." aka fad'a daga bayan sa tare da zagayowa aka zauna kusa dashi, hannu ya bawa wanda ya zauna d'in suka gaisa yace, "normal Nura." "Kace normal na ganka haka." Ajiyar zuciya yayi yace, "raina ne a b'ace wallahi, ga mota ta can fa" ya fad'a yana nuna masa mota da yatsa a inda take ajjiye. "Shege mutumi na har an siyo kenan." ya fad'a yana mik'ewa tare da k'arasawa wajan motar yana kallon ko ina kafin ya dawo ya zauna kusa dashi yace, "wallahi tayi kyau sosai Allah ya sanya alkhairi ya tsare." Imran ya amsa da fad'in, "Amin nagode Nura." Nura yace, "sai munzo d'ani." Murmushi kawai yayi baice komai ba ya mayar da kansa kallon hanya.


   "Wai me yake damun kane haka?". Ajiyar zuciya yayi yace, "Yaya ce wallahi ban san me Jannat ta tsare mata ba sam bata son ta, yanzu fa zuwa tayi gaishe su amma ta gaishe ta tayi mata banza shine duk raina ya b'aci wallahi." 


Nura yace, "To ai hak'uri zakayi ka danne abinda kake ji ba ka zo ka zauna a nan ba". Nan ma bai ce komai ba yayi shiru yana kallon hanya, "wai sabida ita d'in ka siyi wannan motar?". Kallon sa yayi kad'an kafin yace, "Uhum bana so na dinga d'auko ta a machine kowa yana kallon ta, hawa machine bana mace bane shiyasa kawai na siyi wannan."


Girgiza kai Nura yayi yace, "Imran in nace maka son Jannat kake sai kace A'a kawai shaquwa ce a tsakanin ku, abinda baka sani ba wannan shaquwar ta koma soyayya meyasa baza ka yadda ba?."


   A dai-dai lokacin da Jannat ta sako kai zata fito daga gida taji abinda Nura yake cewa ta tsaya cak tana so taji mai Imran zaice, "Nura ni babu soyayyar Jannat a zuciya ta indai ba soyayyar yaya da k'anwa ba, ina son ta bakayi k'arya ba amma ba wai irin wannan soyayyar aure ba soyayya nake mata ni irin ta y'an uwa wanda suke ciki d'aya." 

"To babu so me ya kawo kake kishin ta haka?".

"Sabida ta kasance k'anwa a gare ni dole nayi kishin ta don ina son ta sosai."

"Imran kana da taurin kai wallahi, kowa yaga yadda kake yiwa Jannat yasan ba iya shaquwa ce a tsakanin ku ba akwai soyayya."



"Masu karancin tunani irin naku sune suke d'auka hakan amma ni babu wata soyayya ta aure dake tsakani na da ita, nine zan aurar da ita na kaita har gidan mijin ta matsayi na na yayan ta guda d'aya tal a dunjya." Girgiza kai Nura kawai yayi tare da yin murmushi yace, "To Allah ya kaimu lokacin ya kuma bamu lafiya." Da amin ya amsa kawai suka bar zancen.


   Jannat da taji komai hankalin ta yayi bala'in tashi jikin ta soma wani irin rawa kamar an jona mata shocking hawaye suka fara ambaliyya daga idon ta, zuciyar ta ta fara bugu mai k'arfi wanda sai da ta dafe saitin zuciyar ta sabida ji take tana barazanar fitowa waje, da gudu ta juya ta koma cikin gidan su ko Gwaggo bata kalla ba da take tsakar gida ta shiga d'aki a guje tana kuka sosai.


Kan gadon Gwaggo ta fad'a ta fashe da kuka mai cin rai tana fad'in, "Me nayi masa baya sona? Meyasa bazai fahimci ina son sa bani? Meyasa bazai fahimci soyayyar sa tayi min mugun kamu ba? Meyasa bazai gane ni ina qaunar sa ba? Ya kasa gane shaquwar mu ta koma soyayya mai k'arfi, ya kasa gane da soyayyar sa na rayu, ya kasa gane ina son sa. Wayyo Allah na ya zanyi da raina ina zan saka kaina naji dad'i?" Ta fad'a cikin kuka mai tsuma zuciya tana birgima akan gadon sabida yadda take jin jikin ta kamar ana soka mata allura in ta tsaya waje d'aya. 


*☆☆☆*


*Senator Al_Mustapha Bashir Bukar residents.*


A haukace ya banka k'ofar falon ko sallama babu ransa a mutuk'ar b'ace, "Muhsin lafiya na ganka haka?" Wanda yake zaune a falon ya fad'a yana kallon sa da kulawa, kama k'ugu yayi sannan yace, "Daddy meye manufar ka na tura ni waccan banzar makarantar na zauna matsayin dalibi?."


Wanda aka kira da Daddy ya mik'e tsaye ya k'araso inda Maheer d'in yake tsaye yace, "calm down, Muhsin zauna nayi maka bayani."


Ba musu ya zauna shima ya zauna kusa dashi yace, "Kasan siyasa ta matso kuma ina da burin sake maimaita wannan kujerar shiyasa na tura ka cikin talakawa mutanen gari su ganka kana karatu a cikin su hakan zai saka su amincewa dani har su sake zab'a ta a zab'e mai zuwa."


Kallon Daddyn nasa yake kafin yace, "Akan siyasar ka shine za'a cutar dani? Nayi makaranta har matakin masters akan meye zan kuma komawa sabida kawai mutane su ganni a zab'e ka?." Murmushi Daddy yayi yace, "Baza ka gane ba Muhsin shiyasa kake cewa haka ai." 


   "Daddy yau a cikin school d'in nan wata banza y'ar talakawa ta kira ni da stupid man, sannan wani shashasha yayan tane ko waye ya rik'e min hannu a lokacin da nake k'okarin yi mata hukunci, Daddy kasan hali na bani da hak'uri meyasa zaka kaini inda zan d'auko maka magana? Me zai saka ka kaini inda zan b'arar maka da siyasar ka, domin wallahi ido na idon yarinyar nan sai nayi mata abinda baza ta tab'a mantawa ba."


Zaro ido Daddy yayi yace, "tace maka stupid? Wacece ita y'ar gidan uban waye? Me take tak'ama dashi da zata ce maka haka?." Mik'ewa tsaye yayi yace, "Ba y'ar kowa bace face y'ar talakawa, mara gata, mara galihu, amma zanyi maganin ta kaima kasan bazan barta ta zagi banza ba, zata banbance tsakanin aya da tsakuwa, ba irin mu ake tab'awa a zauna lafiya ba." yana gama fad'ar hakan ya shige cikin gidan ya bar Daddy a zaune shima ransa a b'ace jin a zagi gudan jinin sa wanda yafi so a duniya.


Free page😁



_Wannan labarin na kud'i ne ki biya naira 300 kacal ki karanta wannan chakwakiyar da aka faro ta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Domin biya tuntub'i wannan number but only WhatsApp ***._

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol