Free chapter · Read without an account
KADDARATA CE Page 1/2
Allah ka sa yanda na fara lafiya,na gamashi cikin koshin lafiya
*BANYI DAN CIN ZARAFIN WATA KO WANI BA, IDAN KINGA YAYI KAMA DA NAKI RAYUWAR TO ARASHI NE*
``` na sadaukar da wannan labari ga dukkan masoyana,Allah ya bar ƙauna one love my fans❤️```
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم*
01\01\2023
*F~ PAGE 1/2*
__________________
Hada-hadarsu suke a babban gidan yarin da ke cikin garin Kano, wani kyakkyawan saurayi ne ɗauke da gudumar bugun dutse, HAFIZ kenan wanda ƙaddara ta kawo shi prison ɗin da ke unguwar Kurmawa a garin Kano.
Zama ya yi yana sharce gumin da ya yi, a kan wani babban dutse dan hutawa, "Ustazu ya dai?" Killer ya faɗa ya na dafa kafaɗar Hafiz, cikin gajiya ya ce "Ibrahim i'm felling thirsty (ina jin ƙishirwa) wanda ake kira da killer ya juya yana son ganin wana ganduroban ne a kusa, ganin, Usman ne ke nufo inda suke da zabgegiyar bulala a hannunsa, "kai su waye anan su ka zauna" ganduroban ya faɗa ya na muzurai, killer ya ɓata rai,ya na juyowa, Ganduroba Usman ya ce " killer ya haka? kar oga ya ganku a zaune ku ci gaba da fasa dutsen mana kun san dai ance dole sai an gama da wannan a yau ko?"
Cikin nuna tsan-tsan iskanci da ƙwarewa killer ya ce " ruwa za mu sha"ganduroba ya juya yaga kowa ya na ta aikinsa da sauri ya ce" nawa za ka ba ni in kawo muku?" Killer ya ce" ba ka da matsala idan mun koma zan sa a baka 2k" da sauri ganduruba Usman ya juya, Hafiz da ya ke tunanin rayuwar da ya tsinci kan shi a ciki, wacce bai taɓa zata ko tsammani ba, hawaye ne ya gangaro daga idanunsa ya na tuno Innarsa da sauran ƴan'uwansa.
Killer zai yi magana kenan sai ga Usman ɗauke da ruwa pure-water har guda huɗu, ya miƙawa Killer da sauri ya karɓa ya na faɗin "ustazu ga shi"
"nagode" Hafiz ya faɗa ya na bismillah haɗi da shan ruwan, sai da ya sha guda biyu sannan ya ji daɗi, ya saɓi gudumarsa ya ci gaba da fasan dutse,killer kuma ya juya dan komawa nasa ɓangaren,haka nan ya ji yana son Hafiz tun zuwansa gidan yarin.
wata ƙararrawa aka buga wacce ta ke alama ce ta aje a karɓi kokon safe,
Ganduroba Isya ne ya ke faɗin "minti goma kuje ku karya wallahi idan ku ka wuce sai jikinku ya gaya muku, riga-rigan saukowa daga dutsen suke don zuwa karɓar kokon kar ya ƙare, dan indai baka samu ba dole ka haƙura sai ƙarfe uku na rana kuma.
Cikin nutsuwa Hafiz ya sauko tare da sauran fursinonin da aka yanka musu aiki mai tsanani, su ka nufi ciki.
Rana ya kallah ganin takwas ta wuce ya san lokacin sallar walha ya yi, idan ya ce zai bi layi dan karɓar abun kari ba zai samu damar yin sallar ba, hakan ya sa ya nufi ƙaton drum ɗin da ake ajiye musu ruwa, ruwan jajir da shi duk ƙasa wata molallaliyar bottle ya gani a ƙasa ya ɗauka ya ɗauraye ya zuba ruwan,"kai! kai!! kwashe ruwan za ka yi ɗan iskan mazinaci a haka kamar na Allah nan kuwa shegen fajiri ne" mai kula da su ya faɗa, ya na hararar Hafiz. Mai da ruwan da zai ƙara a jarkar ya yi, ya na matsawa gefe ya fara alwala, anan ya tayar da sallah ya na idarwa ya ɗaga hannunsa ya na addu'a "Ya Ubangijin sammai da ƙassai, ya ubangijin Annabi Muhammadu(S.A.W)Allah ka bayyanar da gaskiya,ya ubangiji na san wannan ƘADDARATA CE, ina godiya a gare ka ya Allah ka san ba ni nayi ba,Allah ka bayyana gaskiya a cikin wannan al'amari, ka wanke ni daga zargin da ake min ya Allah" ya shafa ya na mai tashi, Sani wanda ake kira da kure da kuma killer ne suka zo, ɗauke da koko cikin kofi baƙiƙirin da shi, da wasu manyan ƙosai masu kama da dutse tsabar tauri, a roba su ka ce "Ustazu ga naka"
da Murmushi Hafiz ya ce " ku zauna to mu ci" wanda ake kira da killer ya girgiza kai ya na ɗauko wata ƴar kwallah a cikin wandonsa na ciki,dan duk blue ɗin kaya ne a jikinsu ya buɗe ya shanye abun ciki ya na bubbuga kansa ya ce "ni na ƙoshi Ustazu" ya bar wajen, kure ya zauna dan ganin Hafiz ya ci wani abu, tun da aka kawo shi cikinsu, suka san shi ba fashi ya ke ba, ganin yanda ya ke cikin damuwa, sun so ya sanar da su dalilin da ya kawi shi gidan yari sai dai ya ce "KADDARATA CE"
duk da ba su da imani dan killer bai san komai ba sai kisa,kashe mutum ba komai ba ne a wajensa, ɗaurin rai da rai aka yanke musu, su uku ne a cikin ɗakin duhun da suke aka kawo musu Hafiz, kwarjinsa da cikar haibarsa ya sa suka kasa cutar da shi, ƙauna ce tsakaninsu.
Hafiz da ya ga yanda Kure ya kafe shi da ido ya na ta tunani ya ajiye kokon ya ce "Sani lafiya dai?"ajiyar zuciya kure ya sauke ya ce "Ustazu me ya kawo ka gidan nan, mutane nawa ka kashe da aka kawo ka cikin mu, yau shekararmu biyu a gidan nan babu mahaluƙin da ake haɗamu da shi ba mu aika shi ba,sai kai Ustazu kullum muna son sanin waye kai,am...."
Gudun fursinoni ne ya katse musu hirar lokaci ya yi dan komawa aikin fasa dutse, kamar wasu shanu ana bin su da bulala, kure ya kare Hafiz ya na muzurai dan da a daki Ustazunsu gwara a da ke shi, da sauri Hafiz ya janyo hannun kure su ma su ka hau gudu dan komawa kan aikinsu..........
***********
Wani gidan ƙasa ne a cikin tsohuwar unguwar Zage da ke Kano, Baffa da ke zaune kan buzu ya haɗa kai da guiwa ya na jan carbinsa da ganinsa ya na cikin damuwa, wata mata ce ta fito daga ɗaki ba wata babba ba ce ƴar ƙimanin shekara 40 ta kalli Baffa ta girgiza kai, ta ɗauko kujerar tsakar gida ta ajiye kusa da Baffa ta ce "Malam, dan Allah ka sanyawa ranka salama akan wannan al'amarin, da sanin Allah kuma baya bacci idan Yayansu ya na da gaskiya watarana zai fito daga kurkukun nan"
Ajiyar zuciya ɗan dattijon ya sauke ya ce " yau she kuma, bayan anyi shari'a an yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara goma, ni nasan Hafizu ba zai aikata wannan abu ba, sharri akayi masa"
Inna ta ce "ni dai dan Allah ka sassautawa kanka mu ci gaba da addu'a Allah ya bayyana gaskiya" da ameen Baffa ya amsa ya na mai ɗaukan buta dan zagawa bayi.
Sallamar Walida ƙanwar Hafiz ce ta katse tunanin da Inna ta shiga yi, da fara'a ta amsa ta na faɗin " wa'alekissalamu Walida ke ce tafe da safen nan" wacce ake kira da Walida ta fashe da kuka ta na faɗawa jikin Inna ta ce "Inna na shiga uku Amadu ya ce ba zai zauna da ni ba, wai abun kunya ne a ce Yayan matarsa ya na prison an same shi da laifin aikata fyaɗe a bayan gari, ya kore ni ya sake ni"
"innalillahi wa'inna'ilaihirrajiun,allahumma ajirni fi musibati wa'aklifni khairan minha"
Abinda Baffa ya furta kenan jin abinda Walida take faɗi, Yarinyar da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe.
Zakiyya da ta dawo daga islamiyya hannunta ɗauke da jakar leda ganin iyayen nata cirko-cirko ga Yaya Walida na ta kuka ya sa ta tsaya a bakin ƙofa, Isma'il ƙaninta ya shigo da sauri ya na tambayar ba ta da lafiya ne.
Babu wanda ya iya tankawa, bayanta kawai Inna take shafawa alamar rarrashi harshenta yayi mata nauyi ta kasa furta ko da kalma ɗaya, Alhamdulillah ala kulli halin kawai ta kai maimaitawa a ranta, Baffa ne ya ja ƙafa daga bakin bayin da ya ke tsaye ya zo ya tsaya ya ce" to ya isa haka nan Walida Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi,share hawayenki ki ɗauki wannan a matsayin ƙaddara"
Zakiyya ta zare paper da ke hannun Yaya Walida ta buɗe ta shiga karantawa da ƙarfi " Ni Ahmad Bukar na saki Matata Walida saki ɗaya, dan ba zan iya zama da iri irin na gidan masu ci da addini ba...." Kasa ƙarasa karatun tayi, ganin irin cin mutuncin da Mijin Yayar tasu yayi musu.
Baffa ya ce"ba ni takardar nan" ya karɓa ya nufi ɗakinsa jiri na ɗibansa dan ɓacin ran da ya ke ji, Isma'il ya ce " to dan ya sake ki sai me, dan Allah ki bar kuka ai wani hanin ga Allah baiwa ne" take Khadija ta ce ''wallahi kuwa" nan dai ƴan'uwan suka hau rarrashinta har ta fara haƙura, a tare su ka karya, nan suka hau hirar Yayansu Hafiz su na addu'ar Allah ya dawo musu da shi lafiya, ya saka masa sharrin da aka yi masa.
A ranar dai ba su koma makarantar yamma ba dan ɗebewa Yaya Walida kewa ga tsohon ciki kar su barta ta dinga tunani....
***********
"Jawahir,Jawahir, ke Jawahir!!! wata bafulatanan mata ce ta ke tsaye akan wata kyakkyawar budurwa wacce ta lula duniyar tunani idonta na zubar da hawaye, a furgice budurwar ta ɗaga dara-daren idanunta wanda suka yi jajir "na'am Umma"ta amsa ta na share hawayen da ke fuskarta, cikin tausayawa Umma ta zauna bakin gadon da ƴarta ta take ta na mai riƙe mata hannu ta ce " yanzu ba za ki mi ƙa wa Allah lamarin nan ba, ba za ki ɗau wannan abu a matsayin ƙaddara ba?"
Kwanciya Jawahir ta yi jikin Umma wani sabon kuka na ƙwace mata "Umma ya cuceni ya raba ni da mutuncina ko fita na yi sai a yi ta kallona ba zan taɓa ya fe masa ba har abada"
Ƙwallah ce ta cika idanun Umma ta ce " to ya isa haka ki daina damuwa tunda yanzu an kai shi gidan yari ya na can ana gana masa azaba, har ki yi aurenki ki tara zuri'a ma bai fito ba ai ko haka hakkin ki ba zai bar shi ba,ki daina damuwa kin ji ƴar albarka" a jiyar zuciya Jawahir take saukewa, Zainab ta shigo ɗakin ɗauke da ruwa a hannunta ta miƙawa ƙanwarta ta, karɓa ta yi ta sha ta na jin soyayyar iyayen nata a ranta, ba dan Hon.Murtala Gambo Gabasawa ya tsaya musu ba da tuni wanda ya aikata laifin ya na yawo a gari lafiya lau.
Umma ta fita a ɗakin dan ita ma abun ya na damunta yanda aka kawo mata mummunan labarin ya ƙi barin ranta.
Zainab ta ce " wai ke me ya sa baki da tawakkali ne, abu ya wuce amma kullum kina kuka, sai ka ce ba musulma ba"
Jawahir ta yi murmushi wanda ake kira da na yaƙe ta ce " aunty Zainab na san ƘADDARATA CE wannan amma ba zan iya manta abun nan ba, aunty ya zalunce ni ba zan yafe masa ba" Zainab ta ce "eh daman ba za mu yafe ba, amma kar ki ƙara kuka akansa"
Kai Jawahir ta ɗaga alamar amsawa, " oya shirya mu tafi gidan su Amina mu kai mata ankon" da to Jawahir ta amsa ta na mai tashi dan shiryawa,zuciyarta cike da ƙunci dan tunda abun ya faru tayi bankwana da farinciki sai dai yaƙe kawai.
***************
Zaune ya ke a bayan motan da ta sha tinted glass baƙa, ƙirar zamani sai ƙyalli take yi, ya na amsa waya shigowarsa Kano kenan aka ɗauko shi daga airport Hon.Murtala G.G kenan ɗan majalisar tarayya, daga ni naira ta zauna masa.Unguwar Nasarawa suka nufa cikin Lamiɗo cristan gida mai no 209, gate ɗin aka buɗe musu su ka shiga, gida ne wanda tsaruwarsa ya wuce misali tamkar a turai haka gidan yake, sai da su ka kai gate na uku sannan driver ya fito ya na mai buɗe wa Hon.Murtala G.G ƙofa a nutse ya fito ya na mai nufar ƙofar parlour'n.
Da gudu wasu samari biyu suka rungume shi "oyoyo daddy, welcome back" cikin farinciki ya rungume su, ya na mai jin son ƴaƴan nasa, Hajiya Binta na zaune sai murmushi ta ke ganin dawowar mai gidan nata,
"sannu da zuwa Alhaji" ta faɗa ta na tashi dan girmamawa.
Nan suka hau murna kowa ya na ƙoƙarin nunawa daddy yanda suka yi kewarsa tsawon sati ɗaya, jin bai ji su Fatima(ihsan) da Rahma ba ya ce "where is my kids ne? Yusuf wanda yake fitinan ne yai rina gashinsa rabi orange colour rabi baƙi ya sha Dada Barber saloon,ya ce "sun je gidan Uncle Bash wai a can za su yi weekend" murmushi daddy ya yi ya ce "okay dan ban sanar da zuwa na ba ne da nasan ba za su je ba" wayar Yusuf ce ta ke ringing,tashi ya yi ya na sosa ƙeya ya ce "daddy ko akwai kash anan za mu je K/mata studium akwai wasan da za'ayi ne acan.
"Aikin kenan ball" Hajiya ta faɗa ta na zubawa Daddy ruwa a cup ganin ya shanye na ciki, rapper biyu,200k ya ba wa Yusuf ya ce " ga wannan ai ya ishe ka ko?"
"wow common my friend" Yusuf ya faɗa ya na nauyin hannunsa ya karɓa ya sa a aljihun crezy trouser ɗinsa ya fita.
Unguwar Zage ya shiga domin ɗaukar abokinsa Musty su je su shaƙata, wani babban gida ya je ya na kiran musty,wani saurayi ne ya fito age mate ɗinsa shima ya shah askin ƴan iska,tsakiyar kansa ne kawai da gashi cukus ya rina rabi shi ma, gashin a cuccure, ya fito ganin motar da ya zo da ita ya ce " oh my guy wannan fa?"
Cikin farinciki ya ce " daddy na ne ya faso a cikinta" shiga Musty ya yi su ka tafi, tsaki Yusuf ya ja da faɗin "mmtsw gaskiya unguwar nan ba tayi ba,wai me yasa tsohon nan ya zauna a geto area ne?" Musty ya ce "manta kawai"
Su ka nufi stadium dan kallon wasan da Kano pillars za su yi........
Zinariya ce✍🏻