Free chapter · Read without an account
35
🧟♀️ *WATA SOYAYYAR!* 🧟♀️
*_Labari/Rubutawa_*
*AMINA ABUBAKAR YANDOMA*
( _Meenat A Yandoma_ )
tare da
*ZAINAB MUHAMMAD*
( _Indian Girl_ )
*NOTE*
_Labarin nan zamu rubuta shi ne a yadda yazo, duk abinda kuka gani mun rubuta a haka aka tsara labarin._
*GARGAƊI!*
_A guji yi mana amfani da labari ta ko wace hanya sai tare da izinin mu_
*PROMO! PROMO!! PROMO!!!*
🥳🥳🥳
*Zumar ƙiba da ta Hips wadda kuka sani a 3500 yanzu ta dawo 3000🤩, ga kuma garin ƙiba 3in1 muna sai da ƙwara ɗaya 3500 bokiti kuma 4500 a cikin sauƙi promo muke💃🏻, ga kuma maganin infection me aiki sadidan wanda ake sha da lipton akan 1000, Hanzar ta ki mallaki naki yar uwa domin neman ƙarin bayani ku tuntube mu akan wannan number ***, Siyan na gari meda kuɗi gida.*
*PAGE 6️⃣3️⃣&6️⃣4️⃣*
...Mahaifiyar Jidda kuwa wata mata ce ta sameta ta haye ruwan cikinta ta shiga jibga tamkar Allah ya aikota, banda ihu Mariya babu abinda ke tashi a cikin gidan, sauran mata kuwa ganin an kayar da mariya ƙasa ya saka su mara ma ƴar uwarsu baya suka ci gaba da Jibgar Mariya suna cizo.
Jidda kuwa haka Jaririyar nan ta shiga ya kushinta da zaƙwa-zaƙwan faratan ta tana me babbaka dariya tamkar zata shiɗe.
Mahaifin Jidda kuwa yana kasuwa ji yayi sam hankalin shi ya ƙi kwanciya ya rasa meke ma shi daɗi babu abinda yake buƙata kamar ya ganshi cikin gidan shi, shagon shi ya kulle tare da nufar gida cikin sauri tamkar zai tashi sama.
Tura ƙofar gidan yayi bakin shi ɗauke da sallama, wannan sautin sallama da matan suka ji ita ce ta daki dodon kunnuwan su, gani yayi sun dafe kai tare da jero atishawa duk wadda ta dawo cikin hayyacinta sai dai kaga ta zabga da gudu ta fice, Mahaifin Jidda kuwa cike da mamaki yake kallon Mariya dake kwance magashiyan fuskarnan ta ji bugu tayi sutu-sutu le6e ya haye, ganin matan sun fice ya saka shi matsowa kusa da mariya.
"Subhanallahi! Me nike gani haka, Mariya da wane ƙaton kikayi dambe yayi maki wannan bugun har haka"?.
"Malam ba ƙarti bane wallahi matan da ka gani sun fita yanzu sune suka yi mani taron dangi."
Da mamaki Mahaifin Jidda ke kallon ta jin yadda ta zage sai zuba take.
"Ga irin abinda nike faɗa maku nan tun farko sai da nace kada kuyi taron sunan nan saboda lalurar jinjirin amma kuka ƙeƙashe ƙasa kuka dage sai kunyi; yanzu wa gari ya waya"?.
"Nidai malam ka yafe mani wallahi nabi Allah na bika ba zani sake yi maka gaddama ba ka ceci rayuwata ni yanzu na dawo daga rakiyar bokaye ka samo mana Malami yayi ma Jidda ruƙiyya domin al'amarinta akwai ban tsoro wallahi Malam na daku ba kaɗan ba ji yadda lebena ya haye yayi suntum."
"Yanzu ita Jiddar tana ina"?.
"Muje ɗaki mu duba ko zamu ganta."
A tare suka shige ɗakin nan suka yi tozali da Jidda a halin suma ga jaririnta kwance saman gado yana rarraba ido, kan Jidda suka yi suna kiran sunan ta amma shuru, da ƙyar suka samu Jidda ta farka; kuka ta hauyi tana furta a kira ma ta Yazid yau zata bayyana duk wani abu da suka jima suna boyewa kodan samun lafiyar ta.
Ba'a jima ba Yazid ya shigo gidan a birkice yana tambayar ba'asi.
"Baba ka taimake ni ka nemo mana malami domin ayi komi a gabanshi.
"Kinyi ma kanki karatun ta natsu domin yau ce rana ta ƙarshe da muka fidda maki kodai ki bayyana gaskiya ko kuma kema kwananki ya ƙare."
A rikice suka ja da baya ganin Jinjirin Jidda dake saman gado ya zama wata zabgegiyar yarinya da a ƙalla zata kai shekaru goma.
"Baiwar Allah! Mi kike nema wurin mu, me muka aikata maki da kike azabtar da ruhin bayin Allah-n nan haka"?.
Mahaifin Jidda ya faɗa a nutse.
"Ba zan faɗi abinda suka aikata mani ba sai kun nemo malamin da zamiyi komi a gabanshi domin ya ji irin cutar da wannan baiwar Allah-n tayi mani."
A gaggauce Mahaifin Jidda ya kirawo Malamin da ya fara duba Jidda a baya.
Babbar tabarma aka shimfiɗa a tsakar gidan kowa ya zauna.
"Jidda ce ta fashe da kuka tare da fara labarin abinda ya faru a baya."
*SHEKARU UKU DA SUKA WUCE*
..."Jidda Nifa so nike bikina ba sai anyi wata bidi'a ba kawai wa'azi ma ya wadatar sai kuma walima."
Hafsa ta fada tare da kallon babbar aminiyarta wato Jidda.
Ya mutsa fuska Jidda tayi;
"Ke fa har yau baki waye ba Kin taba ganin anyi bikin yar boko wadda ta waye ba tare da an chashe ba"?.
"Jidda nifa Albarkar auren nan nike nema ba wani bidi'a ba."
"To ai kuwa kinyi ƙarya domin ni zani samu Yazid in sanar dashi irin Events ɗin da zamuyi."
Dariya Hafsa tayi domin tasan halin jidda da son bidi'a.
Kamar Yadda muka tsara Yazid ne yazo da yamma shida abokin shi Yusuf, falon gidan suka shigo dasu nan na shammaci Hafsa na shafa wani turare tare dayin murmushin da ni ɗaya nasan ma'amar shi.
Falon muka shiga tare da kayan marmari a hannunmu, ni nayi saurin shan gaban Hafsa na ajiye tiren dake hannu na a gaban Yazid, tunda Yazid ya shaƙi turaren Jikin Jidda ya ji duniyar ta fara juya ma shi, a hankali Yaji wata iriyar ƙaunar Jidda ta kama shi.
Hafsa kuwa tunda ta shaƙi turaren taji gabanta yayi wata irin mummunar faɗuwa wani irin ciwon kai ne yayi mata dirar mikiya, a gaggauce suka shirya duk wasu abubuwa da suka kawo su Yazid ya fice tare da baƙon al'amari na ƙaunar Jidda.
Ni kuwa murmushi nayi domin nasan tarko na ya kama tsuntsuwa.
"Hafsa yadai; ko jikin ya motsa"?.
"Jidda kai na ke mani wani irin ciwo wanda ban taba jin irin shi ba."
"Ayya! Sannu bari in baki maganin."
Buɗe jikkata nayi na ɗauko ma Hafsa wani ƙullin magani nace ta shafa a kanta.
Yaddar da Hafsa tayi dani ce ta saka ta shafa maganin ba tare da tunanin komi ba, da Hafsa tasan wane irin magani na bata da koda wasa ba zata yi gigin shafa shi ba.
Jim kaɗan barci yayi awon gaba da Hafsa, kallon ta nayi tare da sakin ƙayataccen murmushi.
"Kinyi kuskure Hafsa ya za'ayi ina ji ina gani zan bari ki auri Yazid bayan dani yafi dacewa, dole ne a fasa auren nan ayi shi dani bayan kin sheƙa.
Fitowa nayi tare dayin sallama da mahaifiyar Hafsa na nufi gida.
Da murna mahaifiyata ta taso tana tambayar lafiyar Hafsa domin tasan maganin mu ya fara aiki, nan na kwashe kaf abinda ke faruwa na sanar da ita, tuntsurewa tayi da dariya.
"Yau bikin ta saura kwana biyar ita kuma a gobe ne maganin zai kasheta kinga dole Yazid ya dawo wurinki ya aure ki."
"Haka ne Umma domin kaf duniya babu abinda nike ƙauna kamar Yazid dole ne in mallake shi kota halin ƙaƙa."
"Kada ki damu in dai ina Numfashi dole ne ki mallaki Yazid."
Da wannan murnar muka kwanta barci asubahin farko waya ta tahau ruri lalubawa nayi tare da kara ta a kunne na, jin Muryar Mahaifiyar Hafsa tana sheƙa kuka tamkar ranta zai fita a firgice na tashi zaune ina sauraron abinda zata sanar dani...
***
...Alkhamis kuwa nan yayi zaune yana dakon tashin Fatima zuciyar shi ce ta zagule tunani iri-iri suka riƙa dawo ma shi.
"Haka ka tsara rayuwar ka, haka kake so ka mutu ka koma ga Allah, sau nawa ka kai kukan ka wurin Allah ka sanar dashi damuwar ka domin yayi maka maganinta, ka taba tunanin kai matar ka wurin wani malamin addini domin a duba lafiyar ta,bokaye kaɗai ka sani dasu ka tashi kaga mahaifiyar ka na tu'ammali kai ma ka take mata baya, ka taba tsaida lokaci ka bautama Allah-n ka yadda ya kamata, shin kodai abanza kazo duniya zaka koma a wofi."
Wata zuciya ta shiga bashi shawara; furzar da wani iska me zafi yayi tare da furta.
"Dole ne in gyara Allah nagode maka daka tunatar dani kafin lokaci ya ƙure mani domin koda ina yaro ban san hanyar islamiyya ba sam mahaifiya ta bata nuna mani ita ba,yanzu lokaci yayi da zani gyara domin samun tsira a gobe ƙiyama."
Fatima ce ta farka tare da buƙatar ruwa bayan ya bata sannu ya ruƙa jero mata.
Ba tare da sanin Fatima ba Alkhamis ya samu wata islamiyya da wani babban malami ke koyarwa duk bayan magriba ya shiga, bai 6oyema malamin komi ba dan haka ne ma ya ƙarfafama malamin yin jihadi ya fa ra koyar da Alkhamis, a cikin mako ɗaya alkhamis ya fara fahimtar addini ya gane a can baya ashe yayi hauka duk rayuwar shirme ce yayi.
Babban abinda ke damunshi shine kullum Fatima na ƙara rikitar dashi tana jefa shi cikin kogin tunanin anya mutumce wata ranar idan ciwonta ya taso har ciwo take ji ma shi domin juyewa take ta koma sak marigayiya Fatima.
A yau ne ƙwadaga zata dawo domin tuni ta sanar da Alkhamis tana hanya kuma a gidan shi zata sauka domin ganin amarya.
Shirye-shirye suke yi na abinci iri-iri wani irin walwala da farin ciki Fatima keyi da ita kanta ta rasa na miye.
Wayar Alkhamis ce ta hau ruri dubawar da zai yi sabuwar Number ya gani ɗauka yayi tare da kara ta a kunne.
Mahaifan Fatima ne ke sanar dashi sun shigo gari.
Nan ya sanar da Fatima domin shi yanzu zai fice ya taro su.
Tunda suka shigo gidan suke kalle-kalle cike da mamakin irin daular da Fatima ke rayuwa ciki.
Cike da Murna Fatima ta rungume mahaifiyar ta tare da gaida mahaifinta.
"Baffa nayi kewar ku."
"Muma munyi kewar ki Fatima"
Nan fa suka hau labarin yaushe gamo, uwar tsaraba ce irin ta mutan ƙauye suka yo ma Fatima ga uban nonon Shanu da suka kawo kaya guda.
Abinci suka baje masu Alkhamis kuma ya fita zai tarbo ƙwadaga .
Bayan fitar Alkhamis nan suka tambayi Fatima ko akwai matsala.
Aa tace masu domin ita bata da wata matsala da mijinta sai wadda ta hango zata faru a yau.
Ko sallama babu haka ƙwadaga ta faɗo ɗakin cikin tafiyar ƙasaita tana wani girgiza.
Juyowar da Jauro zai yi nan idanunshi suka sauka cikin na ƙwadaga, a gigice ya miƙe tare da furta "ƙwadaga!"
"Jauro "
Shine abinda Ƙwadaga ta furta.
Da mamaki mahaifiyar Fatima ta kalli mijin nata
"Dama ka san ta ne"?.
"Ƙwarai kuwa."
Jauro ya furta tare da kallon Ƙwadaga da tayi zaman ƴan bori hawaye nabin fuskarta.
"Ƙwadaga kada kishe mani wannan yaro ɗan ki ne shima"?.
"Ɗa na ne"?.
Ƙwadaga ta furta hawaye nabin fuskar ta.
"Mun shiga ukku Alkhamis ƙanwar ka kake aure."
Tamkar saukar rugugin aradu haka Alkhamis ya ji maganar lokaci ɗaya duhu ya mamaye idanunshi, sai gani suka yi ya yanke jiki yaa faɗi, a kiɗime suka yi kan shi suna kiran sunan shi...
*MEENART............✍🏻*