Free chapter · Read without an account

14

by Safiyya Haruna · HATSABIBAN TSIBIRI

Hatsabiban Tsibiri

By Mrsjmoon.


Adabi Writer's Association.


14.


"Dan Allah Dr. Neerah ki taimakeni na sami amincewar yaya Sadauki domin shi ne muradina mahad'an ruhina a bisa igiyar aure."


Sabbin zantukan Zuhrah suka dawo da Neerah hayyacinta, sai da ta saita kanta kafin ta soma magana cike da kamewa "Kiyi hak'uri, Muneerah bata cikin sokayen matan da so ke kaisu aikin zubar da k'ima dan haka kai tsaye bazan iya taimakonki ba, hausawa suka ce iya ruwa fidda kai, tunda kin iya kamuwa da ƙaunarsa ai banjin tunk'ararsa domin fayyace masa karatun ruhinki zai zamowa abin wahalarwa ba da har sai kin kama ƙafa da ni saboda tsaban kin rainamin hankali, foolish girl, mitcheww!."


Ta kai ƙarshen maganar ranta a mugun b'ace tana maijin tamkar zuciyarta zata faso k'irjinta saboda zugi da takeyi maka.


"Hey Malama me ye na b'ata rai har da zagin cin mutunci daga neman alfarma."


"Kanki a jeji sokuwa kawai kuma wallahi kada ki sake tarana da wannan maganar banzan idan kuma kina son ranki ya ɓaci ne to ki sake jaraba tarana da maganar." 


Daga haka tayi gaba, duk da Part dinsu taso tafiya amma sai ta nufi Part din Mami Fulani tama haɗa hanya domin bata ganin gabanta sosai. Ita kanta mamakin zafin da ta ɗauka akan maganar Zuhrah takeyi, anan ta sake gasgata ƙaunar da takeyiwa Sadauki. Tana shiga suka d'ago suka zuba mata ido da sauri ta sauke kai ƙasa ta iso gaban Mami ta zauna gefen ƙafanta ta riƙo hannunta tana sauke numfashi da sauri da sauri.


"Lafiya kike kuwa Muneerah?"


"Mami ina s...


Sai kuma ta fashe da kuka ta mik'e da sauri ta nufi d'akin Lailah, ta faɗa saman gado tana cigaba da rera kuka tamkar wacce akayiwa dukan tsiya domin tanajin idan batayi kukan ba jininta zai iya hawa.


"Babana jimin wani shiri-rita dai."


Shafo sajensa yayi cikin jin rashin daɗin ganinta a damuwa, ganin Mami na dakon cewarsa sai ya saita kanshi ya tab'e baki ya ce "Ita ta sani ai, tunda ita ba yarinya ba ce sannan tafi kowa sanin illar jefa kai a damuwa dan haka ki barta har sai ta sakko da kanta tanemi kiji damuwarta amma dan Allah kada ki saka kanki a sokancinta hawan jininki ya motsa."


" A she baka da imani Babana?"


Da sauri ya kalleta ta zabga masa harara zaiyi magana ta d'aga masa hannu "Gara da hakan ya faru na gane waye kai, daga yau Jabir ko Junaid zan soma kira baya goya marayu, Ubannin k'annensu ba kai ba."


"Mami wai me na...


"Sai da safe Babana zan tafi jin damuwar d'iyata yanzu bazan fahimci tatsuniyar nan naka ba."


"Innalillahi wa inna ilaihin raji'un, wai me nayi da zafi ne haka Mami?"


Tashi ta yi ta barshi da baki buɗe. Sosa goshinsa yayi cike da mamakin zafin da Mami ta ɗauka akan abinda bai kai ya kawo ba. Maimakon ya tashi sai ya gyara zama ya jingina da Cushing d'in da ta tashi sautin kukan Neerah nayi masa amsa amsa kuwa a cikin kunni hakan ya ƙara dagula masa lissafi inda ya tashi da sauri ya nufi wurin da zuciyarsa keyi masa jagora, tura k'ofar yayi a hankali idanunsu ya sarke da juna wacce take lafe a kafad'ar Mami na taping bayarta da ido yake tambayarka me ke damunta tura baki tayi tare da lumshe ido, k'ofar ya ɗan buga saboda ya lura Mami b'ata san da shigowarshi ba dan ta bama k'ofar baya.


"Babana ko maciji ka zama ka shigo a silale kana tunanin ba zan san da isowarka wuri ba ne?"


"Mami affuwan na janye kalamaina."


"Ya wuce Babana amma ga kanwarka nan ka tabbatar da ta sanar da kai abinda ya sakata kuka."


Daga haka ta fice, da ido suka raka bayanta sannan suka kalli juna na seconds, Sadauki ne ya d'age mata hira cikin tambayar kurame na meye damuwarta. Harara ta cilla mashi tare da hayewa saman gado ta rufe jikinta da bargo har saman kanta.


"Kin hutar da ni yanzu zan tafi in sanar da Mami kishin wanda baisan kina dakon son shi ba kikeyi."


Ai kafin ya rufe baki ta diro daga gadon ta cukumeshi ta baya tare da fashewa da sabon kuka mai sauti wanda ya janyo hankali Mami ta shigo a hanzarce ganinsu haka sai ta nuna Sadauki da yatsa cikin gargad'i batare da ta furta kalma ba. Murmusawa yayi ya janyo Neerah ta dawo gabanshi ya kalli Mami dake cillo masa harara ya kauda kai tare da cewa "Kiji tsoron Allah Doctor N ki sanarmin da gaskiyan damuwarki in har ba akan kishi ba ne"


Duka ta soma kai masa a k'irji ya kalli Mami ta watso masa dak'uwa tare da barin wurin ganin Neerah bata lura da wucewar Mami ba sai ya saki Murmushi mai sauti tare da janyota ya jefa cikin k'irjinsa ya matse da ƙarfi dan ji yake tamkar ya tsaga k'irjinsa ya tura ta cikin zuciyarsa.


"Wash! my boobs."


Ta ambata tana mai son kubcewa.


Sassauta riƙon yayi mata ta zame ƙasa ya bita suka zauna saman rug, ta tura kanta tsakanin cinyoyinta sai lamarin ya bashi dariya, ya kai bakinsa daf da kunninta ya hura mata iska ta zabura ta mike tsaye ya nunata da yatsa nayin dariya mara sauti mai bayyana cikar kamalarshi a fili.


"Yaya Yarima me ye haka? Allah bana so."


"I love you so much Dr. N, do you love me?"


Idanu waje take kallonsa ya tsare gira tamkar bai taɓa dariya ba ya sake maimaita tambayeshi cikin dakon jin amsarta, tayi tsit kanta sunkuye tana miƙa godiya ga Allah na jin furucin bakinsa.


"Baki so na saboda na zamo mai sauri saki ko?"


Da sauri ta d'ago ta zuba masa idanunta har lokacin ta kasa furta kalma, girgiza kai yayi cike da damuwa kana ya mik'e da sauri ya fice tare da bugo k'ofar da ƙarfi. 


"Your are stupid Neerah."


Ta ambatawa kanta hakan tare marin fuskanta cike da takaicin barin damar da ta samu ya kufce mata.


"Amma ai kunyarshi naji."


"Kunyar Babana ko saurayin da kike kishi?"


A firgice ta kalli Mami ta gyaɗa mata kai cikin rashin walwala tare da shigowa d'akin ta kamo hannunta suka fito ta nufi ɗaya daga cikin d'akunar barcinta.


"Shiga kiyi wanka ki fito mu kawo ƙarshen maganar munafuncin nan taku."


"Kaina ciwo Mami kuma barci nake ji kuma walalhi bamuyi munafuncin komi ba ki yarda dani Mamina."


"To kwanta zuwa gobe mayi maganar kuma ki tabbatar da gaskiyan ruhinki zaki sanarmin domin ta nan ne zan gane abinda ya kamata inyi akai duk da ba'a son raina lamarin ya zo a haka ba."


Kai ta motsa tana kulle ido sanyin ac na son saukar mata da zazzaɓi sannan ruhinta cike yake da tambayoyin inda zantukan Mamu Fulani suka dosa na abinda take ambata da ba a son ranta zai faru ba.


Ac Mami ta kashe tare da rage mata hasken wutan dakin ta fice, ajiyar zuciya ta sauke natsuwar ruhi na rab'arta saboda yarda kalaman ina sonki sosai Dr N, shin kina so na? Ke amsa kuwwan a cikin kunnuwarta, juyi tayi tare da furta "I love you too Yaya Yarima."


Tana rufe baki taji motsin tafiyar wani abu a jikinta daidai saitin zuciyarta ta lalibo da sauri sai ga ƙatuwar kunama jajur da ita, ta tsira mata ido sai kai da kawo takeyi tsakanin tafin hannunta zuwa tsin-tsiyar hannunta ba tare da tayi mata illar komi ba, murmushi ta yi tare da matseta da ƙarfi tana jin yarda bugun zuciyarta ya k'aru, ta lumshe ido tana mai furta "Where are you Yaya Yarima? Dan nasan kana kusa da ni tunda ga kayanka a hannuna."


"Yes I'm here my Doctor."


Da sauri ta kalli bakin k'ofan cikin hasken da bai wadaci d'akin ba, shi ne tsaye yana kallonta fuskansa ba d'igon annuri, murza idanu tayi dan tabbatarwa sai taga wayam ba kowa komawa kwance ta yi ta tsirawa kunaman nan ido da ta koma jikin bango tana ta shawagi sai sanja color takeyi from black to red, yellow, blue, brown and so on dan wani color d'in bata taɓa ganinsa ba tsawon rayuwarta. Murmushi kawai take binta da shi, har bata san sadda barci ya ɗauketa ba ta kife ruf da ciki barcin da su Mami ke yak'in ta daina yi saboda rashin alfanunsa ga Bil'adam.


***

'Na yarda da zancen Bokanki Mamma hak'ik'a ya sanar da ke gaskiya cewa ina da kishiya a kusa da ni, in ko haka ne wallahi sai dai kowa ya rasa Yaya Sadauki domin bazanyi kishi da ke Neerah ba kamar yarda nasan kema bazakiyi da ni ba saboda girman zumuntarmu ya wuce wasa, kai bama zai yiwu hakan ya kasance ba, tabbaas kai nawa ne Yarima Aliyu, ruwa da iska banga mai yimin shamaki da aurenka ba, Neerah wahalar banza kikeyi, ke da Yaya Sadauki sai zumunci na yan uwantaka da Allah ya haɗamu.'


Duk cikin zucci Zuhrah keyin zantukan idanunta na kan sashin Mami Fulani tana auna masa mugun kallo tamkar shi ne Dr. Neerah. Cin tayar mota da akayi yasa ta kalli wurin a hanzarce hango Ƴaƴanta Hud cikin maye yasa ta buɗe robar ruwar hannunta wanda ke da sanyi ta nufeshi a fusace ta watsa masa ya saki a jiyar zuciya yana kallonta idanu jajur sake juye masa ragowar ruwan tayi a fuska aikam ya rarumota ta kwasa da gudu ya rufa mata baya yana huci.


"Mamma kizo danki mara amfani zai illata miki ni."


Abinda take ambata kenan tana

maimaitawa sadda tayi nasarar shiga falonsu, Mamma ta fito zani na kufcewa dan tunda tajiyo kalaman Zuhrah ta san ita da Hud ne wanda tayi imani ya koma ruwane na shigowa Masarauta cikin maye lamarin da Zuhrah ke adawa shi kuma hakanne yasa tayi mugun rainashi duk da ba ita ce sak'onshi ba domin a kwai mutum biyu tsakaninsu kafin ita.


"Me yasa ne Hud? kamanta tijarar Abbanku Chiroma ko? Shin kana ganin wannan gaulancin zai kaika zuwa ga hawa karagar Sarautar Birnin Mungaye?"


Da sauri Zuhrah ta anshe da "Ina kuwa domin wallahi ko ni sai na yi sanadin rashin hawarsa domin mu ba 'yan maye ba ne balle ya hau ya maida giya ruwan fanfommu duk mu lalace, kanmu ya kwance kamar yarda nasa yake a kwance."


Tama rufe baki ta k'wallah ihu domin a fusace ya jefota da zobbesa mai kama da k'ashi, ya ko sameta a goshi a take jini ya wanke mata fuska, Mamma ta yi kanta tana rafka salati fadi take "Hud kiramin Dr Neerah ta bata taimakon gaggawa domin ban son Masarauta susan wannan abin kunyar da ka aikata."


"Sai dai ta mutu wallahi Mamma indai sai na kira an bata taimako ne."


Ya ambata cikin rabewar murya irin na 'yan maye.


Wani a shar Mamma ta mulmulo ta antaya masa ko ajikinsa sai ma ya kwashe da dariya ya tura kai d'akin Zuhrah ya faɗa saman Cushing yana sunbatun sai ya illata rayuwar Zuhrah tunda ta rainashi, daga haka barci yayi gaba da shi.


"Mamma jijiyar idanu zasu tsinke kiyi wani abu kada na rasa idanun gani, wayyo! Na shiga uku na lalace, walalhi ba zan yafewa ɗanki mara amfanin can ba."


A gigice Mamma ta kamota tare da tara d'ankwalinta a goshin tana zabga salati gami da toshe mata baki dan ta daina aibata ɗan uwanta tare da gudun kada wani ya jiyo.


"Mamma kaini Mungaye Clinic kada in rasa idanu cikar ado da k'walliyar duk kan mutane musanman mata."


Bata da zaɓi zai fito da ita zuwa Clinic duk da bata so hakan ba saboda bata son labari ya fito cewa Hud ne ya jima shalelenta ciwo domin a bayyane nakasu ne gareshi akan burinta na ganin ya haye karagar mulkin Mungaye.


***

Tsibiri.


Iskan bai tsaya a ɗauke masu gani ba har da halaka jama'a, a cikin abinda bai wuce mintoci biyar ba ya halaka mutane masu yawa. Tsibiri ya hautsine da iface-iface na neman dauki, cikin fushi Sarkin yaƙi wato mahaifin Buda ya aika sak'o cikin aikin alk'aliman sihiri zuwa ga Abun akan su dawo Tsibiri zai kama da wuta sannan ya soma ƙoƙarin tsaida guguwan cikin kwarewar tsafi sai dai lamarin ya sha ƙarfinsa, suka taru suka haɗa ƙarfi kamar yarda sukayima na farko nanma bata sanja zani ba sai kawai suka soma neman matseta tare da bawa jama'a taimakon wurin b'uya. 


Rugugi ne ya doso Tsibirin abinda ya sanya iskan nan lafawa, tamkar k'iftawar ido iskan ta ɓace, zuwa can Lina ta bayyana fuska a daure, kafin su ankara ta soma huro sanyi wanda ke fitowa daga bakinta na shiga jikkunar Jama'a inda ke warkar masu da raunin da suka ji tare da tashin wanda suka jikkata, ta ɗauki tsawon mintoci goma tana huro iskan kafin ta dakata tana kallon al'umman da duk suka samu natsuwa suka sakata a tsakiya suna yi mata kirari da Gimbiyarsu mai tausayi.


"Kuyi hak'uri da matsalar da 'yar uwana ta janyo muku, yanzu ku tafi ku kauda wanda suka mutu tare da cigaba da harkokinku zanyi bakin iyawata wurin kare lafiyarku domin wannan shi ne burina kuyi rayuwar 'yanci wata rana."


"Mungode shugaban gobe, Sarautar Tsibiri naki ne Gimbiya Lina."


Suka ambata a tare cikin daga murya.


Jinjina kai tayi ciki da alfahari da su. Suna watsewa Abun ya bayya tare da Buda, Lina na jin alamun takunsu ta ɓace ta bayyana cikin Bukkan Kaka Gunu inda ta sami Lima sunkuye kan Mah tana aikin ceto ranta.


"Sakacinki ya janyo Mah zata mutu, wannan bak'ar ranar nake jiye mana har na umurceki da ki kula da ita amma saboda son zuciya irin naki kin kasa zama da ita kin taho neman cikar burinki, to ki zauna a nan tare da ita domin fitowarki kiran ajalinki ne domin Jama'an Tsibiri sun fusata da kashe masu dangi da kikayi sanadi sannan Abun yana farautanki kamar yarda yake faraunata da Mah."


"Me kike nufi da Abun na farautanmu? Alhalin mu ne kaɗai sanyin idanunsa."


"Lima yanzu Abun ya sanja dan shi ne ke wasa da rayuwar Mah domin ya samu hankalina ya dawo kanta inda zai hilace ni ya mallaki Zoben da ke hannuna wand zai bashi damar samun ƙarfin tsafin da ya zarce na kowa dake zamanin nan haka ya fiki burin son mallakan Ruwan Albarkan Kaka Gunu domin shima na ɗauke da sirrika masu girma akan tsafi da cikar mulki, ki sani a yanzu mu ne damuwarshi akan haka ya kudiri halakamu baki ɗaya indai zamu kawo masa tangarda a samun tsawon rayuwa akan mulki."


"Ta ya zan yarda da gaskiya kike sanarmin ba yaudarar da kika saba yimin ba ne? "


"Ifritu Mutuwa zai gasgatani."


"Tabbas zantukan yar uwanki Lina ba ƙarya duk da itama tana son shan ruwan albarkan domin ta sake finki komi dan hawa karagar mulki, ko ba haka ne manufarki ba ya ke Gimbiya Lina?"


"Tabbaas haka ne kuma har a yanzu ina cikin muradin rigaki mallakan ruwan albarkan sai dai ba yanzu shi ne a gabana ba domin haka kaima Mutuwa dole ka dakata da taimakonta na mallakan Ruwan har sai na kammala da abinda ke gaba in yaso sai kayi mana k'uri'a duk wanda ya ci shine mai mallakin gadon Kaka Gunu."


"Baki isa ba Lina, ni ce ke da gadon Ruwan Albarkan Kaka Gunu dan haka ki fitar da ranki akansa."


Murmusawa Lina ta yi batare da ta furta kalma ba ta isa gaban Mah da ke shimfida tamkar gawa ta sunkuya ta shafi fuskanta wani haske ya sauka a fuskan zuwa ilahirin jikinta aikam sai ta soma tari tana kiran sunar Abun da ya zo ya taimaketa.


"Mah kina tare da 'yan biyunki kuma bisa kulawarsu kika tsira daga baƙin iskan da Lima ta yi jagoran shigowarsa cikin al'umma, yanzu zan barki a wannan Bukar ta Kaka Gunu Lima zata kula da ke zuwa sadda zan dawo na maidaki inda duk ƙarfin tsafin matsafi yayi kaɗan ya iya zuwa wurin."


"Ki dawo lafiya Ruhin Sarki Goma ya baki kariya."


Motsa kai tayi tare da mik'e ta kalli Lima da ta tsare giran sama da ƙasa ta hurama fuskanta iska kan dole ta murmusa saboda tunowa da lokacin baya da take azabtar da Lina da iskan bakinta.


"Yawwa kin tuna muguntarki na baya ko? To ki natsu kiji me zan sanar da ke, ki zauna a nan kamar yarda na sanar da ke a farko, ki kulamin da Mah, Ifritu Mutuwa zai kula da ku sannan zan batar da Bukkan Kaka Gunu a idanun Abun wanda ke nufin isowa bada jimawa ba."


Lima zatayi magana Lina ta daga mata hannu tare da cewa "Kada kiyi yunkurin barin Bukkan nan dan zuwa watsewarki domin yin hakan wasa da rayuwarki ne domin kina fita zaki tsinci kanki a akurkin sihiri ko na Abun ko na Ifritu Baushe kuma ki sani bana da lokacin taimakonki saboda lamarin Mah d'ita ya fiyemin komi, in kinji gargad'i ruwanki, ni zan wuce ba zan jima ba zan dawo dan bana son na wuce kwanaki biyu rak ban kammala abinda naje yi ba."


Kafin Lima ta furta kalma Lina ta zama farin hayaki ta b'ace kallonta ta sauke kan Ifritu Mutuwa sai ya jijjiga kai tare da bude tafin hannunsa saiga wurin ya sanja, ya dawo dauke da kilisai masu laushi da makeken gadon alfarma, jinjina tayi masa ya gyaɗa kai tare da b'acewa, ta doshi gadon ta hau ta kwanta ba jimawa barci ya dauketa cike da burin sai ta fita wurin nan taga abinda zai faru. Mah itama gadon ta hau cike da tarin damuwa.


Lina na fitowa ta jiyo takun Dokin Buda sai ta zama balbela ta haye saman bishiya suna wucewa ta sakko ta watsa haske a baki ɗaya Bukkan ta lula sararin samaniya.


***

Abun tsaye a turakansa yana kai da kawo cikin tarin damuwa zuwa can ya ja iska ya fesar tare da zama akan k'ok'on kan Giwa ya na cije lebe, ya sharce Gumin da ya feso masa a goshi tare da mikewa a fusace ya kaiwa bango duka cikin ambatar "Ƙarya ne, saina Mallaki Zoben hannunki Lina sannan yar uwanki zata kasheki a gaban mahaifiyarki, a yanzu bana da abokiyar gaba sama da ke, zan nuna miki ta yaro kyau take amma bata k'arko, ki sani ba zan barki ki Mulke ni ba alhali ina rayuwa, tabbaas a yau na musanta kalman cewa bazanyi fito na fito da ke ba haka na gasgata kalamin Kaka Gunu da ya ce samuwarki cikinmu masifa ce domin zaki karya k'adarinmu ki sanja tarihinmu ki watsa mana Martaban Tsibiri hak'ik'a dana sani na bashi dama a can baya ya sanya kinbi rariya ya zamo Lima kawai zata zo duniyarmu."


Momyn Haske ne 🥰 


*Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad. Yana maganin Infection, asma, limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon mara, kaikayin jiki dana matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida ɗaya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. ***. Yarda ake amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha. Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da man ayu su shanye. Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah ya ƙara mana lafiya Amin.*


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.