Free chapter · Read without an account

38

by Amina Abubakar Yandoma · WATA SOYAYYAR

🧟‍♀️ *WATA SOYAYYAR!* 🧟‍♀️



   *_Labari/Rubutawa_*


*AMINA ABUBAKAR YANDOMA*

    ( _Meenat A Yandoma_ )

         tare da

   *ZAINAB MUHAMMAD*

      ( _Indian Girl_ )



*NOTE*

_Labarin nan zamu rubuta shi ne a yadda yazo, duk abinda kuka gani mun rubuta a haka aka tsara labarin._



      *GARGAƊI!*

_A guji yi mana amfani da labari ta ko wace hanya sai tare da izinin mu_




*PROMO! PROMO!! PROMO!!!*

🥳🥳🥳


*Zumar ƙiba da ta Hips wadda kuka sani a 3500 yanzu ta dawo 3000🤩, ga kuma garin ƙiba 3in1 muna sai da ƙwara ɗaya 3500 bokiti kuma 4500 a cikin sauƙi promo muke💃🏻, ga kuma maganin infection me aiki sadidan wanda ake sha da lipton akan 1000, Hanzar ta ki mallaki naki yar uwa domin neman ƙarin bayani ku tuntube mu akan wannan number ***, Siyan na gari meda kuɗi gida.*



*WANNAN PAGE ƊIN SADAUKARWA NE GARE KU*


Abubakar Ak saraki

Prince

Ƙamaruddin 

Safwan 

Akhairin Allah ya kai maku har gadon barcin ku🥰


*PAGE 6️⃣9️⃣&7️⃣0️⃣*


*END🔚🔚🔚*


...A rikice Mahaifiyarta tayi kanta tana kuka.

"Malam ka taimake ni kada ƴata ta mutu, wani kallo na zaki gane kuren ki ya watsa mata ba tare da yace komi ba ya fice mata daga gidan.


Tunda Jidda ta farfaɗo babu abinda take sai kuka ta ƙi cin komi magana ma sai ta zama dole take yin ta, mutane kuwa tuni suka samu abun faɗa cewa Jidda ta kashe ɗiyar ta lokaci ɗaya unguwa ta haɗe da labarin kowa da irin abinda yake faɗa.


Mahaifiyar Jidda ta yi nadamar aikata duk wani abu da tayi a baya wata irin nadama ce ta shige domin kuwa ta gane duniya ba matabbata bace.


Yazid kuwa kai tsaye gidan Iya ya wuce yana zuwa faɗawa yayi saman gadonta tare da sakin kuka me tsuma zuciya.

"Yazidun lafiyar ka kuwa zaka faɗo mani gida ko sallama babu, ko wani abu ya samu jika na"?.


Kasa magana yayi sai ma tura kan shi da yayi a cikin pillow, ɗago jajayen idanun shi yayi.

"Iya Jidda na saka".


"Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un! Yazid lafiyar ka kuwa zaka saki Jidda kuna zaman ku lafiya, kuma in dan matsalar dake damun ku ne in kayi haƙuri komi ya kusa zuwa ƙarshe."

"Abinda ta haifa ya rasu, Iya ina me roƙon ki da kada ki takura mani akan sai na faɗa maki dalili."

Sallallami Iya ta hau yi cike da damuwar wannan al'amari, amma koma miye a yanzu ta kyale shi domin ta lura bai son maganar da ta danganci Jidda.


Yazid kuwa Allah ne kaɗai yasan yadda zuciyar shi ke ma shi ƙuna bada son ranshi ya saki Jidda ba babu yadda zai yi amma Allah ne kaɗai yasan yadda yake ji, ya boye ma Iya gaskiya ne domin in har ta ji abinda ya faru shi yasan ya rabu da Judda har abada ba zata bari ya sake auren ta ba.


Haka rayuwa ta riƙa tafiya yau da daɗi gobe babu Jidda tayi baƙi ta fita hayyacin ta babu wanda ke zuwa neman auren ta ga mahaifinta daya dawo cikin hayyacin shi wurin dangin shi ya nufa, Mahaifiyar ta tayi kukan fili da na boye domin tasan kome ya faru i ta ce sila hatta abinda zasu ci wahala yake masu dole mahaifiyar Jidda ta fa ra sana'ar wainar gero da safe ita suke ci har da rana sauran kuɗin a auno gero a samu abinda aka ci da dare.


Ta fannin Yazid ma rayuwa tayi ma shi kunci ya rasa matar aure domin duk wadda yaje nema kamar abin asiri sai an fara magana se magana tazo ta wargaje, bangare ɗaya ga soyayyar Jidda dake addabar shi ya kasa cire ta a cikin ranshi dan haka yau alƙawali ya ɗauka zai je domin yaga halin da take ciki.

Tunda ya shigo unguwar yake jin gabanshi na faɗuwa nutsuwar shi ya tattaro tare da tsayawa ƙofar gidan su Jidda.


Zaune suke ita da mahaifiyar ta suna gyara geron da zasu yi wainar gobe, yaro ne ya shigo yace ana sallama da Jidda.


"Kace bata nan."

Jidda ta faɗa.


"Jidda ba'a haka kamata yayi ki fita ki ga waye ke kira, kai kace gata nan fitowa."


Badan Jidda taso ba sai dan matsawar da mahaifiyar ta tayi mata haka ta fita jiki a sanyaye, tun daga zaure ta jiyo kamshin turarenshi Ƙamshi da ko cikin duba tasan wannan kamshin Yazid ne, hawaye ta ji sun cika mata ido tana fitowa ta ga shi ne ji tayi ƙafafunta sun kasa ɗaukar ta dole ta tsuguwa tare da fashewa da kuka, ganin irin kukan da take ji yayi tamkar an soke shi da kibiya matsowa yayi kusa da ita.

"Baki ji daɗin gani na ba ko Jidda, ki daina kuka idan baki son gani na zan tafi amma ki daina kukan nan domin yana ƙona mani zuciya."


"Kada ka tafi, dan Allah Yazid kada ka tafi ka barni, ka yafe mani bazan iya cigaba da rayuwa ba in babu kai."


Har cikin zuciyar shi ya ji daɗin abinda Jidda ta fada domin kuwa soyayyar ta na nan cikin zuciyar shi kuskure ne dai sun riga da sun yi sai dai addu'ar ubanginji ya gafarta masu.

"Jidda na dawo ne wurin ki bada wasa ba domin kuwa na dawo ne in meda ki ɗakin ki mu gyara kuskuren da muka tafka."

"Yazid ka yafe mani ko da zan samu salama cikin rai na."

"Jidda na Yafe maki ki daina dawo da abinda ya wuce baya."

Gidan suka shiga ya gaisa da Mahaifiyar Jidda tare da sanar da ita ƙudurin shi na mayar da matar shi, da ƙyar dangin Mahaifin Jidda suka amince ya dawo gida domin kuwa sunce ba zasu bari Mariya ta kashe masu dan uwa ba tunda ya dawo cikin hayyacin shi dole ne ya ƙara aure.


Jin zai mata kishiya ba karamin kuka tayi ba cike da nadamar abinda ta aikata, tana ji tana gani haka aka ɗaura auren Mahaifin Jidda tare da na Jidda.


A ranar Jidda ta tare gidan su na ainahi da suka baro domin kuwa yanzu gida ya gyaru tunda sun gano matsalar su.


Mahaifiyar Jidda tana ji tana gani aka kaao mata amarya dole tayi haƙuri da ita domin kuwa ta lura tsaf zai iya sakin ta tunda asiri ya ri ga da ya warware haka ta cigaba da zaman haƙuri tare da yin istigifari.


Jidda kuwa zaman lafiya suke da Yazid tamkar babu wani abu daya taba faruwa a tsakanin su abu daya ne ke damun su bai wuce rashin haihuwa ba wanda sun fitar da ran cewa zasu sake haihuwa.


Ko wane bawa da irin tashi ƙaddarar dan haka sun riga da sun haƙura da haihuwa, islamiyyar matan aure Yazid ya saka Jidda shima ya shiga wata da ake yi bayan sallar Magrib.


Rayuwa suke gudanar wa cikin tsafta da haƙuri da juna sai dai muyi masu fatan kara wani haƙurin na rashin haihuwa su kuma ƙaddarar su kenan.


           *** 

...Tura ƙofar ɗakin Alkhamis yayi gabanshi na faɗuwa domin kuwa bai san abinda zai taras ba; cikin kusurwar ɗakin ya iske ta tana ta faman soshe-soshe tamkar wata tababbiya tana ganin shi ta matso inda yake.

"Alkhamis ka yafe mani domin kuwa nasan wa'adina yayi mutuwa zanyi, nasan na cutar dakai domin kuwa ban zama uwa ta gari a wurin ka ba; ban baka tarbiyyar data kamata ba dan Allah ka yafe mani, sannan akwai wata laya dana saka kasan akwatin ka, amfanin layar shine indai kaso mace dole ta soka ko bata son ka, na saka maka ita ne ba tare da sanin ka ba."

"Umma kina nufin duk soyayyar da Fatima tayi mani sanadin wannan layar ne"?


"Alkhamis bazan boye maka ba soyayyar Fayima daga Allah ne laya bata isa ta saka ta so ka har haka ba Alkhamis, ka yafe mani Alkhamis, sannan ka koma garin Dan janku dangin mahaifinka da nike boye maka suna can."

Tana gama maganar sai gani yayi ta hau babbaka dariya tana nuna shi da yatsa.


Wasu hawaye ne suka zubo ma shi na tausayin mahaifiyar shi domin ɗa da uwa sai Allah.


Su Jauro kuwa sha tara ta arziƙi mahaifan Fatima suka haɗa masu har gida aka mayar dasu domin yanzu Usman da Umar duk sun gama karatu har sun fara aiki.


Fatima kuwa har cikin ranta tana ƙaunar mijin ta biyayya kaɗai take ma iyayenta domin ita ta ɗauki mutuwar ƴar uwarta a matsayin ƙaddara wadda bawa bai iya kauce mata.


Wasu canje-canje Inna Habiba ta fara gani a jikin Fatima tana so ta gasgata zarginta amma dai tayi shuru, wani irin zazzabi ne ya kama Fatima lokaci ɗaya sai amai, kafin a ɗauki lokaci ta galabaita asibiti suka nufa, nan aka tabbatar masu Fatima na ɗauke da juna biyu zuciyoyin su a dagule suka dawo gida.


"Baba wannan cikin fa zubar dashi za'ayi domin Fatima ta baro gidan Alkhamis har abada bamu buƙatar haɗa jini da Alkhamis."

Umar ya faɗa a zuciye.


Gaban Fatima ne yayi wata mummunar faɗuwa kuka ta fara tana harbe-harbe.

"Kada ku kashen mani aure dan Allah ina son mijjna baba kada ku yi man haka."

Cike da zallar mamaki suke kallon Fatima sun kasa furta koda kalma ɗaya ce, abinda suke tambayar kawunan su shine kodai Fatalwar tsohuwar Fatima ce bata bar jikin ta ba, domin sak ta rikice ta koma masu marigayiya fatima.


Wasu yawu Inna Habiba ta haɗiye ji kake ƙut! 


Murmushi Mahaifin Fatima yayi

"Kada muce zamuyi jayayya da ikon Allah mu bar Fatima ta koma gidan mijin ta domin wannan aure bamu muka haɗashi ba Allah ne ya haɗa shi dan haka mubar yarinyar nan ta koma gidan mijinta kada fa tarihi ya maimaita kan shi."


"In sha Allahu ma bazai me-meta kanshi ba."

Inna Habiba ta faɗa.


Nan suka yi amanna da maganar Mahaifinsu.


Alkhamis kuwa yana barci mahaifiyar shi ta sulale ta fice hauka tuburan ta riƙa yi saman bola duk wanda ya matso inda take zata rike ka ta hauka da bugu tamkar zata raba ka da rayuwar ka, babu yadda Alkhamis ya iya haka ya bita da addu'a.


Wurin abokin shi Riyo ya tafi domin Riyo ma ya shiryu tun lokacin da suka je Rugar su Fatima, magana suka gama akan zuwa kauyen su Alkhamis domin haɗuwa da dangin su, sai da suka tsayar da maganar ranar da zasu tafi sannan ya nufi gida.


Tun daga nesa yake ganin mutanen cike da unguwar sai da ya matso kusa nan ya taras da gidan su ya kama da wuta duk ƙoƙarin kashe wutar da ake amma abun yaci tura sai ya zamana tamkar ana ƙara zuba mata makashi ne; wutar bata mutu ba sai da ta lashe duk wani abu dake cikin gidan.


Tashin hankalin da Alkhamis ya shiga bai misaltuwa domin babu abinda suka tsira dashi ga shi gobe zasu yi tafiyar nan.


Jiki ba kwari haka ya koma wurin Riyo nan ya sanar dashi abinda ya faru, kwantar ma shi da hankali yayi cewa komi ya faru daga Allah ne.


Asubar fari suka ɗauki hanyar garin su Alkhamis, da kwatance har Alkhamis ya isa ga danginshi, ba karamin daɗi suka ji ba domin kuwa har sun fitar da ran cewa zasu sake tozali da Alkhamis, koda suka tambaye shi kwadaga shuru yayi.


Sai da suka kebe shida mahaifinshi sannan ya sanar dashi kaf abinda ya faru.

"Ubangiji ya bata lafiya amma Ƙwadaga ta cutar dani mafi munin cutarwa, halin matsi na karayar arziƙi dana shiga shine ya saka kwadaga ta sako ni gaba sai da na sake ta lokaci ɗaya muka ne meta muka rasa ashe guduwa tayi da kai, jim kaɗan bayan tafiyar ta Ubangiji ya buda mani abinda na rasa ya dawo mani kai fiye ma da abinda na rasa a baya, kada ka damu In sha Allah Matar ka zata dawo maka domin ba laifinka bane ni kai na na neme ku amma ban same ku ba har ta kai na fidda rai da sake haɗuwa da kai."


Gidajen dangi aka rika bi da Alkhamis ana nuna mashi, kwanan su biyu mahaifinshi ya biyo shi domin ganawa da mahaifan Fatima.

Tarba me kyau aka yi masu domin mahaifan Fatima sun haƙura sun manta da abinda ya faru a baya.


Ba ƙaramin daɗi suka ji ba musamman da suka ga Mahaifin Alkhamis koba komi yanzu dai suna da tabbacin Alkhamsi ba shege bane.


Sun yanke shawarar Fatima zata koma gidan Alkhamis nan mahaifin shi yayi godiya da irin karamcin da akayi ma shi.


Wasu Shanu mahaifin Alkhamis ya siyar ya ba shi kuɗin ya ja jari domin yanzu akwai nauyin iyali a kanshi, har da kuka Alkhamis yayi domin sai yanzu yake jin yayi rashin Mahaifin shi a baya.


Fatima ta koma gidan ta zaman lafiya suke ita da Alkhamsi domin bai bar zuwa islamiyya ba hatta Fatima ma ya saka ta.


Bikin Umar da Usman aka saka ba'a ɗauki dogon lokaci ba aka yi shi lokacin cikin Fatima nada wata tara, karku so kuga yadda Alkhamis ke ririta ta ko aiki da kyar yake bari tayi shi.


Kwadaga kuwa har gida Alkhamis ya kai ta ya zuba yan aiki suna kula da ita amma sai wayar gari aka taras ta gudu, bata jima da bata ba aka tsinci gawar ta an yanke mata kai da wasu sassan jikin ta.


Alkhamis yayi kuka ba kaɗan ba da haka har ya haƙura tare da roƙama ta rahamar Ubangiji.


Fatima ta sauka Lafiya ta samu ɗiyar ta mace, ta ko wane bangare murna ake hatta mutanen ruga sai da suka zo cike da farin ciki.


Yarinya ta ci Suna Fatima domin har abada Alkhamis bazai taba mantawa da marigayiya Fatima ba.


Sai dai fatan Ubangiji ya tsare mu da aikata aikin dana sani ya Nisanta mu da afkawa cikin WATA SOYAYYAR.



*ALHAMDULILLAH ANAN MUKA KAWO ƘARSHEN WANNAN LITTAFIN NAMU ABUBUWAN DA MUKA FADA DAI-DAI DA WANDA MUKA YI KUSKURE UBANGIJI YA GAFARTA MANA, ALLAH YASA MUYI AIKI DA ABINDA YAKE DAI-DAI WANDA YAKE KUSKURE KUMA UBANGIJI YA NISANTA MU DA AIKATA SHI, GODIYA TA MUSAMMAN GA ƳAN WATA SOYAYYAR FANS GROUP DAMA DUK WASU MASU KAUNAR LITTAFIN NAN COMMENT ƊIN KU DA SAƘONNIN KU SUNA ƘAYATAR DANI UBANGIJI YA BAR ƘAUNA, MU HADE A SABON LITTAFINA ME SUNA....... BAZAN SANAR DAKU BA DOMIN TAFIYAR TA MUSAMMAN CE KUDAI MU KASAN CE A SABON LITTAFI NA*





*MEENART..........✍🏻*

***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol