Free chapter · Read without an account

15

by Safiyya Haruna · HATSABIBAN TSIBIRI

Hatsabibin Tsiri

By Mrsjmoon


Adabi Writer's Association.


15 


Ya kai ƙarshen zance cikin ɓacin rai, yana jin tamkar ya dawo da baya ya goge samuwar Lina a cikin zuri'arshi.


"Da girman mulkinka ya mai Tsibiri, ya kamata ka fito dan jajantawa Jama'a masifar da ta afku wanda Gimbiya Lima ta janyo faruwarshi."


Sarkin yaƙi ya ambata daga bakin kofa kansa sunkuye.


Cikin ɓacin rai ya nuna Sarkin yaƙi bakinsa na fitar da tiririn masifa ya ce "Yau she mulkin Tsibiri ya kai ga lalacewar da Sarki mai ikon juya kowa da ke Tsibirin nan zai fito bawa Talakawa hak'uri abisa afkuwan lamarin da ya zamo cigaban Mulkinsa ne, to ka tuna idan ka manta ne Tsibirin nan bai ginu bisa Tausayi ba haka ba zai taɓa haɗa hanya da shi ba, ka ƙara sani, nai alfahari da afkuwan masifar nan domin samun cikar burina na mallakan ababen da ke hannun 'ya'yana sai da zubda jini k irin wannan, lallai aikikinki na kyau Gimbiya Lima, a kullum ina alfahari da zamowarki gudan Jinina tabbaas ke ce magajiyar Tsibiri na sake gas-gata kalaman Kaka Gunu na cewa nasaranmu naga hawa karagar mulkinki ne duk da ina da wani buri akanki amma ba zan k'i yaba miki."


"Ya shugabana ka natsu mu fuskancin masifar da wannan zubda jinin zai haifar domin Dodo yayi fushi ya bar Tsibirin domin Guguwan ta rainata masa mata yanzu haka ya killace kansa a Kogo yana shirin yak'ar Lima shin idan baka fito ka jajantawa Jama'a ba me kake tunanin yi wanda zai sakko da Dodo akan dokin nakin na ya hau?"


"Sarkin yaƙi ka rufemin baki tun fushina bai sauka kanka ba sannan Dodo zai dawo bakin aikinsa kuma fushin-shi na rashin samun damar san Jinin jama'ar da baiyi ba ne, ba wai na nak'asar matarsa ba, shin ko ka manta bata da lafiya a cikin ko wani lokaci zata iya samun rauni, tunda ta saci jiki taje ta sha Jinin wani dan Fulani shi kuma ya soma bin hakkin jinin Ɗansa lamarin da yaso shafar ƙarfin ikon Tsibiri, shin ko mutuwa tayi ai bamu da asara."


"Haka ne ya mai Tsibiri, tabbas na tuna da wannan masifar da muka kasa samun maganinsa sai da k'yar."


"To Dodo fushin karya ya keyi sai dai bazank'i ta bakinka ba zamu ɗauki matakin kare kai kada ya kawo mana matsala saboda ya soma nuna rashin amana wanda hakan zai haifar masa da rasa rayuwarshi ba damuwata ba ne."


"Me zamuyi masa?"


"Cin amanar tun kafin ya samu nasarar cin tamu, wato samo hanyar halakasu cikin dibara."


"Ya mai Tsibiri Dodo ya wuce da saninmu domin ya rayu tun farkon Sarkin da ya raya wannan Tsibirin, yana da nindarai kala kala sama da dubbunnai dan haka shawara mafi samun mafita shi ne anjima da dare zanzo mu tafi wurinsa mu rarrasheshi ya dawo mu cigaba da zaman amana amma ka janye batun halakashi saboda gudun matsala."


Jim Abun yayi daga bisani ya gyada kai alamun aminta da zancen, Sarkin yaƙi za ku saka magana Abun ya d'aga mashi hannu tare da nuna kofar fita, ya ko juya da hanzari ya fice yana mai cike da farin cikin hayewa matakin farko daga cikar burinsa.


Abun d'akin bincikensa ya shige yana mai jin rashin yarda da zantukan Sarkin yaƙi na zuwa muhallin Dodo sai dai burin son nemo hanyar da zai ladaftar da Lina har ya mallaki Zoben hannunta ya shafe binciko abinda Sarkin yaƙin ke shiryawa, sai ma watsar da lamarin da yayi saboda zuciyarsa na bashi tabbacin aminci dake tsakaninsu da juna.


A gafen Sarki yaƙi kuwa gidansa ya nufa inda ya sami ɗansa Jarumi Buda zaine na dakon isowarshi. Yana isa ya rungume Buda yana kyal-kyalan dariya sai da yayi mai isarshi sannan ya tsagaita ya doki kafadan ɗan nasa yana mai koro masa yarda sukayi da Abun, yana dasa aya Buda ya amshe da cewa" Ya Baba ina guje mana afkawa tarkon Lina dan zuwa yanzu na soma tsorata da lamarinta kada garin halaka mahaifinta mu ɗin mu halaka a banza saboda bata bari kayi nasarar halaka mahaifinta ba, ni dai da zakaji shawarata da mun hak'ura da son mulkin nan mu kare namu da muke da shi na Sarkin mayak'a."


Yana rufe baki wani taurari suka gifta a maganansa sakamakon marin da Sarkin yaƙi ya zabga mashi. A gigice ya durk'ushe gami da kwalla ihu wanda yayi amsa kuwwa a Tsibirin lamarin da ya sake gigita Al'umma suka soma fadawa mahallinsu suna kare kai ta hanyar tsaface kansu da 'ya'yansu domin tunaninsu wata masifar ce ta dawo. Ihun Buda ya sauka a kunnin Abun dake tsaka da bincike, tsak ya tsaya yana nazarin abinda ke shirin faruwa sai dai jin takun isowar Lina Tsibirin yasa shi barin komi ya soma shirin tunkararta tun kafin ta hayo, burinsa ya halakata kowa ya huta da ganinta.


Sarki yaƙi yaji rashin jin daɗin abinda ya aikatawa ɗan nasa sai yayi ƙasa da murya yana mai cewa "Kayi hak'uri ya kai ɗana amma ka sani burin mahaifina kenan mu gaji mulkin Tsibiri hakan bai samu ba saboda Kaka Gunu ya katange hanyar shi yasa na rayuwa da burin kawo karshen mai Tsibiri ko da hakan na nufin rasa raina zanyi dan haka kada ka sake ambatamin na ja da baya tunda kai baka son hawa mulki to ni zan hau duk da na soma tsufa."


"Zan hau Babana domin nima ina da burin mulkan jama'armu."


"Da kyau ɗana, ina alfahari da kai."


Kauda kai Buda ya yi yana mai buɗe k'ofofin hancinsa sai kuma ya mik'e a hanyarca, Sarkin yaƙi ya rik'oshi cikin alamun tambayar inda zaije.


"Babana Gimbiya Lina na daf da shigowa Tsibiri kuma ina jiyo alamun zata gamu da matsala dan haka zan kai mata ɗauki."


"Ta mutu mana ina ruwanmu."


"Ina sonta Babana, ka amincemin na kai mata ɗauki saboda sai da ƙarfinta zan samu damar hawa karagar mulkin Tsibiri."


"Kana hauka ne Buda? Lina tafi kowa son mulkan Tsibiri dan haka zan amince maka kaje gareta bisa aniyar kasheta ka riga mai Tsibiri mallakan Zoben da naji yana magana akai wanda ke hannunta."


"In haka ne Baba kaga kenan taimakonta zansoma akan duk abinda ta sanya gaba idan ta aminta da ni cewa masoyinta na gaskiya ne sai na yaudareta na amshe Zoben daga nan sai mu fito mata da manufarmu na yak'arta mu kaudata cikin sauk'i."


"Da kyau fasihin ɗana Buda, tafi gareta da albarka Takobin yaƙina, kai ne ke da nasara kan Gimbiya Lina."


"Godiya nake Babana."


Daga haka Buda ya fice ya doshi inda yake jiyo K'amshin Lina wanda ya kaishi ga fita yankin Tsibirin baki ɗaya. Shima Abun ya nausa wajen Tsibirin inda ke jiyo takon Lina har lokacin kuma ya kasa cimma ta sai ya ƙara k'aimi domin riskanta akan lokaci. 


Sai dai abinda ba su sani ba shi ne duk kansu bayan Lima suka biyo wacce ta fice ta bar Mah na barci, lokacin da zata fita Ifritu Mutuwa ya so hanata amma tuno zaman cika umurninta yakeyi sai ya kyaleta ta fice cike da muradin son ganin abinda zai faru akan fitar nata, mutuwa ce ko rayuwa, nasara ce ko rashin nasara, ita dai burinta yin ido biyu da kalaman Lina domin ji take idan bata fito wajen Tsibiri ba to Lina ta gama samun nasara akanta na zamowa shugabanta tunda gashi nan ta bata umurni kuma ta bi.


Abun, Buda tare da Lima sunata yin nisa da Tsibiri a bisa hanya ɗaya batare da sun gano hakan ba domin Ifritu Baushe ne ya shiryo musu sihirin ficewa daga Tsibirin ta hanyar kusanto masu da takun Lima gami da k'amshinta da ya sauya da irin na Lina sak, saboda Hadimi Tsidau ya sanar masa indai suna cikin Tsibirin to ba zaiyi nasarar shigowa ya ɗauke Mah ba wacce ke son yin garkuwa da ita domin Lina tazo yankinsa da kanta inda zai mallaketa tare da Zoben sihirin hannunta daga bisa ya sadaukarwa da Dodonsa jinin Mah a gaban idanunta, kana yayi mata ciki ta haifa masa d'iyar da zai sha jininta duk akan idonta ya tabbatar da ganan labarinta ya zo ƙarshe dan ko bai halakata da hannunsa ba ya san bak'in ciki zaisa ta had'iye ranta. 


Tunda Tsidau ya farka da barcin da ya kwashe shi sai ifrutu Baushe ya adana shi yana gana masa azaba kala daban daban domin ya fahimci makirci ke son shirya masa ya gudu dan ba zai taɓa kawo mashi Lina Fadar sa ba, yanzu haka yana can kurkukun tsafinsa da ke k'ark'ashin ƙasa cikin tsaron wasu bak'ak'en rindunar Aljannu suna aikin azabtar da shi, wuya yasa shi sanar da Baushe hanyar da zaibi domin samun nasarar shiga cikin Tsibirin har ya samu cikar burinaa wato sai ya kora su Abun sunyi nesa da Tsibiri domin yawan yin nisansu da Tsibiri shi kuma yawan kusanci ga nasararshi na shiga cikin Tsibiri. Yanzu haka Ifritun Baushe ya sami kusanci da Hatsabibin Tsiri saura samun nasarar shiga cikinsa tunda ga su Lima can na cigaba da lulawa cikin duniya ba tare da sun gano sihiri ke d'awainiya da su ba.


***

Masarautar Mungaye.


Cikin ikon Allah su Zuhrah har suka isa Clinic ba wanda ya gansu sai hadimai dake ta mik'o masu gaisuwa. An wanke mata ciwon inda anan aka gano ƙarami ne tsabar rakine ke damunta ta cika masu kunnuwa da ihu, a hanyarsu na dawo ne suka haɗu da Jabir inda ya gaisar da Mamma cikin girmamawa ta amsa tare da yin gaba ta barshi da Zuhrah, shi kuwa ya tsareta da tambayoyi akan sanadin raunin fuskanta batare da jin ko ɗarba ta koro masa bayanin abinda ya faru sai dai ganin ɓacin ran da ya nuna har saida tayi da ta sanin faɗan domin yarda ya rufeta da masifa sai da tayi zaton dukanta zaiyi, ta ja da baya ya fizgo hannunta suka isa sashin Mamma ya turata tare da rufa mata baya. Mamma dake zaune riƙe da robar ruwa tana sha ta mik'e a firgice tana tambayar abinda ke faruwa.


"Mamma ki gyarawa Zuhrah tarbiyya saboda yaya Hud ba sa'arta ba ne, shin taya za'a ce kina kallo ta gama rainashi? A gaskiya da sake, in sha Allah gobe zan sanar da Mai Martaba domin a dauki mataki dan ko me yakeyi ya fi gaban raini a wurin k'aninsa sannan rayuwar dake ciki ƙaddara ce wata rana zai zamo labari dan haka dole Zuhrah ta girmama shi a matsayinsa na babban yaya a d'akinsu."


Ya sauke dubansa kan Zuhrah dake risgan kukan baƙin cikin anayi mata faɗa alhalin ita aka zalunta. Ya nunata da yatsa cikin kaushin murya wanda ya koma irin na Sadauki sak ya ce "Wannan shi ne rana ta ƙarshe da zan ji kin sake aibata yayanki mai ɗauke da matakin uba, idan kuma kince wasa nakeyi to ga fili nan ga mai doki, kin sanni dai sarai magajin Abba Chiroma ne, so be carefull kuma ki hanzarta bashi hak'uri, zan tambayeshi idan naji saɓanin haka na lahira sai ya fiki jin daɗi."


Sai ya russuna gaban Mamma yayi mata sai da safe ta amsa jiki a mace, saida ya fice sannan ta sauke ajiyar zuciya tana ƙara tsirawa hanyar da ya bi da idanu saboda zantukansa sun nusar da ita wani kuskure da take aikatawa na sangarta Zuhrah ya zamo kaf yayunta bata ganin girmansu saɓanin sauran yaran dake kan girmama yayunsu, ta dubi Zuhrah kafin ta furta kalma ta buga ƙafa tare da fashewa kuka mai sauti, Mamma ta nufota ta zille ta fice da gudu tana gunjin kuka, komawa Mamma tayi ta zauna ta dafe kanta cikin sake tsunduma nazarin kalaman Jabir inda take hango cikakken gazawarta wurin tarbiyyan yaranta.


 "Ƴaƴan Fulani dai masu hangen nesa ne, komin hassadan mutum ya zauna da su sai sun shiga ranshi tare da ƙaruwa da su, Jabir nagode da tunatarwa amma duk da haka bashi ne zaisa na janye ga son Hud ya zama Sarkin birnin Mungaye ba, ina nan akan bakana sai na salwartan da Sadauki daga wannan nahiyar."


Tana ambatar haka ta mik'e da sauri ta shirya ta fice zuwa sashin Umma domin kamma aikin da suka soma na birne layun da Mai Martaba zai ambaci sunar Hud a matsayin magajinsa domin Mamma mutum biyu take aikin a kansu wato Sadauki da Sardauna, ta kora Sadauki ya b'ace a duniya shi kuma Sardauna ya nak'asa yarda mulki zaifi ƙarfin shi,a wannan gaɓar mai martaba zai ayyana Hud, duk ta manta idan ba Sadauki da Sardauna a kwai wasu zaratan samarin Junaid da Jabir.


***

Washe gari.


Neerah ce zaune gaban Mami Fulani, tambayar duniya tayi mata akan sanin gaskiyan ra'ayinta akan Sadauki sannan ta umurceta da kada ta b'oye mata komi dake ranta, amma taki yin motsin kirki sai shafar yatsun ƙafarta takeyi. Murmushi Mami tayi tare da umurtanta da ta tashi taje ta karya tunda tak'i yin magana.


"Ina Azumi."


Ta ambata a hankali kuma cike da shagwaba'a.


"Masha Allah, ai namanta yau Alhamis, to Allah ya karb'a ya bada lada."


"Amin."


Shiru ya sake ratsa wurin zuwa can Mami ta kalleta a natse ta gano da maganar da take son furtawa, kiran sunarta tayi "Muneerah."


"Na'am Mamina."


"Sanarmin da zancen dake ruhinki kada kiji komi, nayi miki alkawari kome ye shi ina tare da ke sannan ki haɗa da bani amsar tambayar da nayi miki, shin kina son Babana ko takuraki yayi?"


Tafi mintoci biyar bata ce komi ba har sai da Mami ta dafa kanta cikin cewa "Sarauta gadonsa kikayi ba haye ba d'iyata, idan baki zamo mai nazari kafin bada amsa ba tabbas baki cika d'iya ga Sarki Abdul Hakim ba."


Dagowa tayi tana murje ido cikin turo baki ta ce "Mami kiran sunar Abbanmu tsirara fa kikayi."


"To Abban su Doctor Neerah, shi kenan na lullub'e?"


Dariya ne ya kufce mata domin bata taɓa jin Mami ta kirata da sunar irin haka ba.


"Tubarkallah, masha Allah, Allah Alhamdulillah da ya azurtani da d'iya mai kyau koda kuwa kuka takeyi."


Kafad'ar Mami ta kife fuskanta tana cigaba da dariyan mara sauti.


"Tashi mugama magana domin yau yau ake da zama na musamman akan zaɓinku daga nan sai a tsaida lokacin biki."


"Mami nifa ba zan ƙaryata yaya Yarima ba kawai duk abinda ya sanar da ke hakan ne, dama shi ne abinda zan faɗa miki tun d'azun nake jin nauyi."


Tana gama ambata ta mik'e da sauri ta fice domin gujewa tambayoyin Mami wanda amsasu zasu bata kunya matuk'a. Bayanta Mami tabi da kallo baki buɗe sai kuma ta tsare gira tamkar an aiko mata da sakon mutuwa.


"Da sake bazan yarda da wannan gangancin ba na aurawa Babana jinin k'anwata ya ƙarasa kunyatani cikin dangi."


"Mamina kada kiyimin haka, tunda dai kinji gaskiya to ki kai maganar ga Abba tare da sanya mana albarka."


Tsirawa k'ofar shigowa falon tayi ido ba kiftawa har Sadauki ya iso gabanta ya zauna tare da riƙe ƙafarta muryansa cike da rauni ya ce "Natuba Mamina, bazan sake aikata zunubin da ya gabata ba, zan zauna da Muneerah har ƙarshen rayuwata domin ita ce sirrina, tasan waye Aliyu sama da ku mahaifana sannan bazan taɓa baki kunya ba nayi miki wannan alkawarin, dan Allah ki yarda da Babanki Mamina."


"Babana wannan daɗin bakin naka bai karɓu ba dan haka tashi ka bani wuri domin bazan taɓa amincewa da wannan auren ba dan kafi kowa sanin wacece Nana Safiyya gareni, ni ce na saki Nono ta kama to ba zan amince da wannan lamarin ba."


"Please Mamina am begin you, kada ki rabani da Muneerah domin ita ce zaɓin ruhina."


"Babana idan ka sake ambatar kalma ɗaya tak a wurin nan sai ranka yafi dare duhu, oya! Maza ka b'ace min da gani "


Maimakon ya tashi sai kawai ya kife fuskanshi a ƙafarta, tana jiyo saukan d'umin ruwa wanda hakan ya tabbatar mata da kuka ya keyi amma hakan baisa ta janye daga dokin nak'in data hau ba saima janye ƙafarta da tayi ta mik'e ta shige bedroom d'inta ta kulle k'ofa. Dafe goshinsa yayi cikin jin kansa na sarawa yanayin da baya so na son kawo mashi ziyara, a hankali ya mik'e ya shige dakin Lailah inda ya sami Neerah daren jiya, ya zauna a saman Cushing tare da d'an zamewa ya kwnta ya d'aga kansa sama ya tsirawa ceilling ido, abin mamaki sai ya ji barci na ziyartansa amma idonsa yaƙi kullewa. Fitinannen k'amshinta ya jiyo yasa ya sake ware idonu na kallon fuskanta da ya bayyana a saman fankan da ke juyawa, hannu ya daga ya nunata cikin cewa "Har a sashin mahaifiyata sai kinzo kin tozartani?"


D'age masa gira tayi cikin jifarsa da shu'umin murmushi sai kuma ta bayyana zaune gefenshi, ƙafa yasa ya hankad'ata sakamakon tuno makarkin da yayi jiya tamkar a irin haka abin ya soma kafin ta rikid'e masa zuwa sifar Neerah, ya haik'e mata ba d'igon imani. 


K'irjinsa ne ya harba tuno baya, a mugun fusace ya mik'e ya nunata da yatsa cikin amo mai amsa kuwa ya ce "Kina taɓani na rantse sai na kasheki!"


"Ka taɓa ganin inda Aljani ya mutu?"


"Za a fara akanki, azzaliman banza kawai,mara addini!!."


Ya kai ƙarshen maganar cikin buɗe murya bai ko tunanin Mami zata iya jiyo shi.


"Kai ka koyamin zalincin ya kai Yarima Aliyu Sadauki takwarar mafarin Mungaye Malam Aliyu Malle kuma takwarar Baffan mahaifiyar shi Fulanin Sarki Abdul Hakim."


"Ya isheni haka nan ya ke banziya!."


"To nayi shiru amma in kamanta zauna in tuna maka zalincin da ka aikata wanda ya janyoni bibiyan farin cikinka."


Kafin yayi yunkurin magana ta turashi zaune ta hanyar hura masa iskan bakinta ya lumshe ido ya bude cikin jin mutuwar jiki, ta nuna bango da yatsa sai ga gidansa na dajin Tekun Kabobo ya bayyana, ya ware idonu ta gyaɗa masa kai cikin cewa "Ka tuna zalincin da kayi a wannan gidan?"


Bai amsaba illa kallon gidan dakeyi cikin wani yanayi mai wuyar fassaruwa.


"Nayi alkawarin sai ka ambatawa Masarauta aika-aikan da kayi da bakinka a gaban dubban Jama'a kuma a yau ɗin nan saboda aikina na daf da zuwa ƙarshe."


Lumshe ido yayi yarda lamarin ya kasance ya soma dawo masa a idanu tiryan-tiryan, kafin kwabo yaji tamkar gashi a bakin Tekun Kabobo da mafarin lamarin ya soma, wani iziyar ruwa ya zashi zuwa cikin Tekun duk yarda ya so kufcewa halaka ya kasa sai ya hango Neerah a tsakiyar Tekun na d'ago masa hannu ya zabura da ƙarfi, Mami ta zabga salati sai ya kalleta a razane, idanunsa sun sanja kala zuwa jajur, cigaba da karanto addu'a tayi tana tofa mashi ya ritse ido na jiyo amsa kuwwan ihunta, da hanzari ya toshe kunnuwanshi, Mami ta sake zabga salati, muryanta na rawa take cewa "Kada kayimin haka Babana indai akan aurenku da Muneerah ce kake son haukacewa walalhi na amince, Allah ya tsare afkuwan abinda nake tsoro, ya baku zaman lafiya da zuri'a masu albarka."


Komawa kwance yayi najiyo dariyarta a daf da kunninsa kana daga bisani tace "Na tayaka yaƙin samun cikar burinka na auren masoyiyarka saura samuwar nawa wanda ya ke nak'asu ne ga ci gabanka domin Birnin Mungaye baza su amshi azzalimi matsayin jagoransu ba, na tafi kada mamanka ta ƙarasa konani da gatan addinku wanda kake da sani akansa amma na haka su amfane ka."


Yanajin iskan tafiyarta ya juyo ya tsirawa Mami ido sai a lokacin yaga a she harda Abba, da Neerah a d'akin, bai lura ba sai yanzu. Runtse ido yayi tare da tura hannayensa a cikin sumarshi. Jan hannun Mami mai martaba yayi suka fice batare da Sadauki ya sani ba saboda ya amincewa kansa Sadauki na tare da shafan Junnu.


"Yaya Yarima."


Kollonta yayi ta sakar masa murmushi tare da matsowar ta zauna a hannun kujeran da ya ke kwance ta soma bashi labarin abinda ya faru cikin natsuwa.


"Ina fitowa daga falon Mami na hango zaka shigo sai na b'oye sai da ka shige sai na samu kaina da biyo bayanka, na jiyo duk yarda kukayi da Mami shi ne na biyo bayanka domin sake samun tabbacin kalaminka na cewa ni ɗin sirrinka ce sai na samu kana ta magana kai kaɗai, sam na kasa fahimtar abinda kake faɗa ga daishi da yaren da nasani kake maganar amma harshenta yana sark'ewa ta yarda maganar bai fitan da za'a fahimta, ganin kamar baka hayyacinka shi ne na kira Mami, tana zuwa ta soma tofa maka addu'a ganin abin na son fin ƙarfinta sai ta kira Abba inda yana shigowa ka dawo hayyacinka lamarin kamar shafan Aljannu."


'Innalillahi wa inna ilaihin raji'un.'


Ya ambata cikin rashi yana maijin harbawan halittarshi da ƙarfi wanda ya haddasa masa zabura tare da kai hannu gabanshi cikin dibara gudun kada Neerah ta gani saidai ita sam bata lura da sanjinsa ba, saima tambaya da ta jefo masa.


"Yaya Yarima wasu kalan mafarkai kakeyi? In da hali ka sanar da ni irin wanda kayi jiya tunda na zama sirrinka kuma zan cigaba da kasancewa sirrinka na har abada."


Kallonta yakeyi cikin jin wani kalan sha'awa na taso masa na daban da yarda ya saba shiga, sam bai fahimtar zantukan da takeyi.


Jin bai amsa ba sai ta kalleshi, mik'ewa tsaye tayi jikinta na rawa dan a take ta tuno mafarkinta na jiya mai wuyar sha'ani, ware idanu tayi a kansa tare da tsirawa inda hannayensa suke ido, ya cire hannun cikin dibara, suka tsirawa juna ido ba k'iftatawa, a take Neerah ta gano halin da yake ciki wanda a irinsa ta ganshi a barcinta na daren jiya, sai dai tuno abinda ya faru tsakaninsu yasa ta nemi barin wurin saidai ta makaro dan a zafafe ya damki dantsen hannunta ya jefata a k'irjinsa ya matse, yana sauke numfashi da sauri da sauri tare da jin harbawan halittarshi cikin salon da bai taɓa samun kansa ciki ba, sai ya sami kansa da ware ƙafa ya matse guk'unta gam.


"Innalillahi wa inna ilaihin raji'un, na mutu Mamina, dan Allah Yaya Yarima karufamin Asiri."


Abinda Neerah ta iya furtawa kenan cikin ƙaramar murya saboda tana gudan kada tayi ihu su Abba su dawo su gansu a haka Sadauki ya kunyata lamarin da zai iya kawo nak'asu ga samun damar mallakan junarsu a matsayin ma'aurata tare da hawa karagar mulkin Birnin Mungaye. 


Jikinta ne ya soma rawa cikin jin shiga matakin da bata san ta inda ya afku ba wato feeling da take cikawa su Lailah bakin bata cikin mata masu motsawar sha'awa, duk in suka nutsa cikin hiransu na 'yamma, inda zasuyi ta tsokanar da cewa bata cika mace ba ne shi yasa.


Juyatan da Sadauki yayi zuwa ƙasan shi cikin fita hayyaci yasa ta dawo ɗan tunanin da ta afka, sai dai ta makaro wurin kwatar kanta domin ya saka mata ƙarfi yana kaimata summba a zafafe a duk inda bakinsa ya sauka.


*Alhamdulillah.*


This is the end of free pages.🤩


Affuwan idan na b'atawa masu jiran shi a kyauta, hakan ya faru ne saboda wahalar da rubutu ke da shi gami da kashe lokacin ayyuka.


Pay 300 only to 0468069082, Haruna Safiyya GTbank. Send the evidence via ***.


*Yanzu labari ya soma.*


*Ga dai Sadauki da Dr. Neerah, shin ko ya zasu ƙare? Wani Zalinci Sadauki ya aikata da ya zamo kalubale a rayuwarshi? Wacce Aljana ce wannan? Shin burinta na wulakanta Sadauki a cikin fadar birnin Mungaye na samuwa kuwa? Waye Sarkin Mungaye cikin Sadauki, Hud, Sardauna da ɗan dogarai Salis? Burin Mamma da Umma na samuwa kuwa? Sannan ga Tsibiri can na shirin kamawa da wuta. Wa zai kawo masu ɗauki? Shin ta ina Gimbiya Lina zata soma? Burinta na hayewa karagar mulkin Hatsabibin Tsibiri tare da kawo canjin mulkin Aldalci na cika kuwa? Shin itama Lima na samun damar mulkan Tsibirin? Me ye sirrin da Lina take b'oyewa? Shin ta yaya Hadimi Tsidau ke kub'uta? Waye Sadauki Gauɗu da dalilin mallakawa Gimbiya Lina sirrukanshi na tsafi? Shin Ifritu Baushe na yin nasarar ɗauke Mah tare da mallakan Gimbiya Lina kuwa? Buda na samun cikar burinsa na auran Lina da hawa kan mulkin? Ya Abun zai ƙare? Shin na mallakan tulun ruwan albarka da Zoben sihiri kuwa?*


Waɗannan dama wasu bayanen duk suna tafe cikin cigaban labarin HATSABIBIN TSIBIBI( labari mai ɗauke da sashi biyu) A cikin farashi mai sauk'i #300 kacal. A turo ta asusun banki kamar haka 0468069082 Haruna Safiyya GTbank, sai a turo shaidan biya ta wannan layin wayar: ***.


Thank you so much my fans. I said kada ku bani kunya dai.😊


Momyn Haske ne🥰


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol