Free chapter · Read without an account
A DUNIYAR MU
by Khadija Umar · A duniyar mu
A DUNIYAR MU
Page 1&2
Bismillahir'rahmanir'raheem
Wata macece wacce ba zata wuce shekara ashirin ba cikin wani ma daidaicin gida daidai na talaka mai rufin a siri,
shara take da sauri da sauri wani wajan yana sharuwa wani wajan kuma ana wuce shi, tana gamawa ya yadda tsintsiyar ta nufi ɗakin ta,
tana shiga ta fito sanye da hijab da ƴar post a hannun ta ta fice daga gidan tasa mukulli ta rufe,
tafiya kaɗan tayi ta iso ƙofar gida mai ƙaramin get ƙofar a buɗe take don haka ta shiga
da sallama,
wasu mata ne a cikin gidan ko wacce ta cire hijab wata ma vest ce ajikin ta wata kuma kayan bacci, shewa aka saka lokacin da ta shigo wata daga cikin su wacce da alamun ita ce matar gidan tace "" a'a kaga amare yau ango bai fita da wuri bane ko?
sheƙewa ragowar matan gidan sukayi da dariya suna tafawa, bata ce komai ba ta nemi waje ta zauna tana cire hijab ta buɗe post ɗin hannun ta ta ciro' agwaluma ta fara sha,
ƙura mata ido sukayi kamar zasu cinye ta,
"'Shukrah me zan gani haka ? kardai kice har kinyi ciki? cewar wata mata wacce duk ita kaɗaice mai kaya complete a cikin su tana yauƙi tace ""chaɓ lallai kinshiga layin ƴan jagwal ""bangane jagwal ba cikin shine jagwal?,
naga haihuwa abun nema ce kuma bakiga yanda yake farin ciki ba kamar ya goya ni,
"""hehehe cewar matar tana gyara zama ta ce ""ai dole ya nun miki farin cikin sa tinda an ɗakko hanyar da zai ƙara aure
furzar da ƙwallon a gwalumar tayi zuciyar ta na bugawa tace "" haba maman Nabila ya daga yin aure zaki fara yi min zancen kishiya? gaskiya banji daɗi ba,
""nasan ba zakiji daɗi ba amma dole saina faɗa miki idan banda ƙuruciya irin taki da rashin wayewa daga yin aure wata biyar har kin bari ya banka miki ciki? to wllh tin wuri kisan abinyi don kina haihuwa kinzama mama zaki lalace shi kuma ya auro wata su cigaba da chilling kina ji kina gani kinzama uwar ƴaƴa,
haba kalleki fa black beauty ga diri amma ace tin yanzu har zaki fara tarwa kanki tension,
ki dube ni ki gani shekara ta shida da aure ƴata ɗaya saida na shekara biyar ma sannan na bari na haihu kuma nasan ke shaida ce yanda miji na yake ji da ni saboda har yanzu kallon budurwa yake min,
amma da na tara yara fa? da yanzu ina da kishiya
""To yanzu ni ya zanyi? Shukrah ta tambaya tana bada attension ɗin ta ga Maman Nabila,
saida ta ɗan yamutsa fuska sannan tace "" a zubar da shi kawai,
""what? kina nufin inje a zubar da cikin daga nan na mutu ko?
kujera Maman Nabila taja ta zauna sannan ta ce "' ku ke nan da ake raina muku hankali amma ni waye ya isa ya raina min wayo?
waye ma yace miki ana mutuwa? da ana mutuwa da ban mutu ba,
A tare mutanen gidan suka haɗa baki wajan cewa kina nufin kin taɓa zubarwa ? ""hmm zubarwa ai ɗaya kenan guda uku na zubar kafin na bar cikin Nabila, amma ya kuka ganni jiki na fess ƴata fess miji na yana ji da ni duk abinda nake so shi yake yi kunga ai naci gari,
Shukrah wacce hamkalin ta ya ke kan Maman Nabila ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya tace ""to yanzu yaushe zamuje? kuma a'ina ake zubarwa ?
"" bakida matsala da wannan kedai ki tanadi dubu biyu kawai,
cike da zaƙuwa Shukrah tace"" ina da su kawai yaushe zaa je?
" ko gobe ma idan kinshirya cewar Maman Nabila tana saɓa ƴarta a baya ""na shirya Allah ya kaimu goben da ayi mn kishiya ai gara na zubar, taɓ ai wllh bazan taɓa bari wata ƴa mace ta shigo min gida ba,
Shewa suka saka gidan gaba ɗaya jin ƙarar mota tayi parking a ƙofar gida wata mata ce ƴar kimanin shekara talatin ta shigo tana yauƙi,
oyoyo hajiya ta cewar matar gidan tana ɗakko dadduma ta shinfiɗa sannan ta ɗakko kukerar roba ta zauna,
Buɗe kanta matar tayi sai ga wani ƙamshi yana tashi daga gashin kanta,
magana kowacce take son yi mata amma yanda take amsawa cikin izza yasa suke shakkarta,
Kitsu matar gidan ta shiga yi mata suna ɗan hira sama sama ta ce ""uhm niko hajiya ta wannan gayu haka gashi kuɗn kitson ki ma daban ne wai menene sirrin, jin ta tambaya yasa ragowar matan suka haɗa baki wajan faɗin
""gaskiya ne
Maryam da tun shigowar matar ta rafka tagumi tana kallon ta ta ce""
Haba ke kuwa duk sanda Kika zo kitso sai kin tafi kin barmu da zancen ki ga gayu ga kuɗi duk da mun san ba wani mai kuɗi kike aure ba amma kinga saboda ƙwaƙwƙwarar sana'ar ki gashi yaran ki ma basa zuwa makarantar gwamnati ki taimaka ki faɗa mana sirrin mana ko muma mun samu mu farfaɗo,
Hmm kamar yanda kika faɗa sana'a ta mai ƙwari ce don a rana zaki iya samun dubh ɗari biyu har sama,
gaba ɗaya suka gigice da jin wannan maƙudan kuɗaɗe ba tare da sanin ta hanyar da kuɗin ke zuwa ba,
murmushi matar tayi tace "" sunana Samira a da amma yanzu ana cemin hajiya Samee saboda ina da ƴaƴan banki,
saidai amma nasan ba zaku iya ba musamman ke wannan ta faɗa tana nun Shukrah wacce gaba ɗaya hankalin ta baya wajan sannan ta ɗora da cewa naga ke kadai ce bakiyi magana ba ,
Murmushin yaƙe Shukrah tayi ta ce ""gaskiya ni yanzu banida sha'awar wani busness idan ba naga nayi maganin matsala ta ba,
so ina ga ko zuwa gaba ne sai in fara,
Kafin Shukrah ta rufe baki Maryam da Maman Nabila da Aisha wato matar gidan (mai kitso) suka tari numfashin ta da cewa ""
Mufa hajiya Samee ko wane irin busness ne zamuyi a wannan duniyar wakeyi dakai ba kada ƴan canji ko zancen da akeyi a unguwar nan ana cewa muna yawo muna haɗuwa gidan Aisha me kitso wllh da muna da kuɗi sai girmamawa tsakanin mu da mutane,
"
"Kunyiwa kanku dabara cewar hajiya Samme tare da zaro wani kati a jakar ta ta miƙa musu ta ce" ga kati na gobe da jibi bana nan zanje abuja so ranar litinin kuzo gida ku same ni,
waro ido sukayi jin ta ambaci abuja suna kaɗa kai a ransu suna jin suma sun kusa arziƙi.
-------------------------
Tafkeken gida ne wanda tsayawa bada labarin haɗuwar gidan ɓata lokaci ne
wasu ƙatti ne majiya ƙarfi su uku suke gadin gida,
parking space ne iya ganin mai gani ga motoci nan kamar a company,
gefe guda wata tumface wacce aka zagaye ta da gilas ba komai bane a ciki ba face helcopter guda biyu,
sai wata doguwar rela daga gefe wanda shine main house ɗin ,
ina kunna kai ciki wani ni'imtaccen ƙamshi ne ya daki hanci na da kuma ƙayatuwar palon da suka haɗu suka burgeni,
kujeru set uku ne a palon amma space ɗin dake palon zai iya cin wasu uku akan kujera wani mutumi ne ɗan kimanin shekara hamsin amma yana da jiki ba laifi,
a gefe wasu yara ne su huɗu suna sauraren sa da alama maganar da suke tattaunawa tana da muhimmanci,
Kabir, Kamis, Kamal Hidaya ina so ku faɗamin inda zakuje ku zauna kafin a gama zaɓe saboda yau pilot zai dawo gobe zaku bar ƙasar nan,
Dady Indi'a zani
cewar Kabir yana karkaɗa ƙafa washe baki Dadyn yayi yace ""uhm hindu ga rawa ga waƙa saura ku.
Nifa Dady ina ganin babu wanda ya cancan ta ya yi fighting wajen ganin kaci zaɓe bayan mu tinda mune ƴaƴan ka idan kaci zaɓe ƙaruwar mu ce tinda kuɗin namune
""wata razananniyar tsawa Dady ya dakawa Kamis ya ce ""ba zaiyiwu ba kunfi ƙarfin kuyi fighting akan naci zaɓe na tara kuɗin da ko jikokin ku ba zasuyi talauci ba don haka ko a media ba za'a ji muryar ƴaƴa na ba bare kuma wajan ɗaukar makami.""
Sorry Daddy to zanje Uk Kamis ya faɗa yana ƙunƙuni
""ok that is good idea,
hey auta kefa? cike da shagwaɓa wacce aka kira da auta tace ""
Dady nima india zani washe fararen haƙoran sa yayi yace good girl that is my baby iam froud of you "" thank you my Daddy i really love you,
mai da kallonsa yayi ga Kamal wanda gaba ɗaya hankalin sa yana kan system ɗinsa yana operating ya ce " To babban yaya kaifa?
"" Hmm excellency kenan kaima kasan babu inda Kamal zaije shida yake shirin zama soja
cewar wata
matashiyar mata wacce zata kai shekara arba'in amma hutu da jindaɗi yasa ba tayi kama da shekarun ba ,
Mai da kallon sa ga Kamal yayi yace "" da gaske ne abunda nake ji?
Da gaske ne Dady zan yi hidima wa ƙasa ta zan binciko duk wani wanda ke da hannu cikin durƙushewar tattalin arziƙin ƙasa ta kuma zan hukunta shi ko waye yana kaiwa nan ya ɗauku computer n sa yayi hanyar part ɗin sa,
da kallo Dady yabi Kamal yana sauke numfashi tare da goge gumin da ya karyo masa.
-------------------------
Kalle ni don Allah ga fari ga kyau ga kyakykyawar halitta Allah yayi min amm wai ni za'a liƙawa mai tuƙa napep
Allah ya kiyaye nafi ƙarfin sa wllh cewar wata matashiyar budurwa wacce ba zata wuce shekara sha takwas ba riƙe da mudubi a hannun ta na kallon irin halittar da Allah yayi mata,
wata mata ce ta fito daga banɗaki da buta a hannun ta daga ganin yanda suka tsananin kama zaka gane mahaifiyar ta ce ta kalle ta cikin ta kaici tace ""yanzu Jamila ni zaki kunya ta ? ni zaki wulaƙan ta? menene laifin Nura? bayan duk akan lalurar ki komai nasa ya ƙare,
ai da ba haka yake ba sai da ya saida filin da yake ginawa da adaidai ta sahun sa guda biyu akayi miki aiki sannan don rashin kunya yanzu kice kinfi ƙarfinsa?
""dama fa can talakane umma
ke ma yanzu kince saida ya saida kayan sa akamn aiki kinga kenan bashida kuɗi a ƙasa,
kan ta matar tayi zata kaima ta duka ta taka wani ɗan ƙaramin dutse zata faɗi da gudu wata yarinya ƴar kimanin shekara goma sha shida wacce kana gani zaka san ita ƴar matar ce don har tafi waccan kyau ta yaho ya tiƙe matar tana cewa
""sannu Umma ki dena damuwa da halin aunty Jamila ki barta duniya ce,
"" ke kuma wllh ki kuji randa haƙƙin yaya Nura zai kama ki butulu kawai,
a fusa ce wacce aka kira da Jamila tayi kan yarinyar tana cewa ""sa'ar koce ni wllh zan tattaka ki inga mai tsaya miki,
nizan tsaya mata cewar umma tana kallon Jamila da mamakim canjin halin ta cikin ƙanƙanin lokaci ta ce
""yanzu Jamila ba zaki riƙe maraicin ki ba? sai kin jawomin zagi ko? shike nan kiyi duk yanda kika ga dama ta faɗa tana jan hannun yarinyar tare da cewa muje Jasmin karta taɓa ki ""to Umma na Jasmin ta ce tana kwantar da kanta a kafaɗar Umman....
Maman Sharifa ce
Comment