Free chapter 路 Read without an account
Episode 19-20
馃尲馃尲馃尲ZUBAR HAWAYE NA馃尲馃尲馃尲
STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU 馃挒馃挒馃挒
ELEGANT ONLINE WRITER'S 馃摎
*FREE PAGE*
馃摎馃摎PAID BOOK馃摎馃摎
PAGE 9
_________________________Basu Suka tashi barci ba sai karfe 12 dai-dai Anty lauratu ne tafara tashi,da Addu'an barci a bakin ta Wanda ta koya a wurin Nasreen,Bata fi minti 5 da tashi ba Nasreen ma ta tashi da Addu'a a bakin ta,Mika tayi tana salati,gaishe da Antyn ta tayi sannan ta dau Dan karamin hijabin ta ta fita waje,rijiya ta nufa ta ja ruwa sannan ta shiga bayi,tana shiga daki ta dau tsintsiya ta share dakin ta gyra shi,Anty lauratu ko kwanoni ta wanke,haka suka raba aikin,in Nasreen na shara ita zatayi wanke wanke in ko Anty lauratu ne tayi shara tor Nasreen ne da wanke wanke.Haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda a yanzu Nasreen ta cigaba da talla,in anyi girki da su akeyi,sai da aka Kai ruwa Rana sossai kafin Anty lauratu ta yarda Nasreen ta cigaba da talla,yau tun karfe 4:00am suka tashi inda Anty lauratu ne ta daura ruwan da za'ayi girki da shi,ita ko Nasreen tana sharan daki bayan ta gama tayi wanke wanke,ta gyra tsakar gida,wurin karfe 8:26 Suka gama komai da komai,wanka Nasreen ta shiga bayan ta fito tasa wani Kaya Mai dan kyau da wani Dan mayafi Karami,tayi bala'in kyau,Anty lauratu ne tace unun emmata kinyi kyau sossai fahhh! murmushi sossai Nasreen tayi har dimple dinta da wushiryar ta suka fito,hannu tasa tana kulle fuskan ta da shi, murmushi Anty lauratu tayi tace zoki wuce lokaci na tafiya,cire hannun ta tayi a fuska ta wani sunnar da Kai kasa,fita sukayi waje Anty lauratu tace karki manta kiyi Addu'a kinji,"da insha Allah Nasreen ta amsa mata" daukan tiren tallan tayi ta nufi zauren gidan Anty lauratu na boye da ita,daga mata hannu tayi tana mata Addu'a,ba ita ta bar wurin ba har sai da Nasreen ta bace ma ganin ta,cikin gida ta koma Bata tsaya a tsakar gida ba daki ta shiga,kan gado ta hau ta Dan kwanta tana Mai kewan Nasreen.
Arif ne zaune a office sai dudduba files yake,Kira ne ya shigo wayan shi,Yana jin tsautin ya gane Mai kira,aje biron dake hannun shi yayi ya jingina da kujera,kujeran na juyi da shi,amsa Kiran yayi Yana gaishe da dady,amsawa daddy yayi da kulawa,bayan sun gama gaisawa daddy yace ka shirya zuwa karfe 11 zakuje meeting a Barnawa,"da toh daddy ya amsa" tsaukar da wayan yayi ya ajiye shi saman table sannan ya Kara kwantawa da kyau akan kujera,tunanin Angel ne ya fado Mai a Rai,yarin ya Yar karama daya kamata ace tana makaranta Amman take tallah,Mai yasa take tallah,tuna kayan da ya ganta da shi ajiki ranan ne yasa shi girgiza kai, sannan yace da alarmun wannan family nasan taimako,haka ya dinga tunani har ya shafe tsawon lokaci bai sani ba,kararrawar da aka danna a kofan office dinshi ne ya dawo dashi daga dogon tunanin daya lula,gyra zaman shi yayi sannan ya bada izinin shiga, sallama yayi sannan ya shiga da sallama,gaishe da boss din shi yayi da ladabi, sannan ya Mika mishi file din hannun shi Yana mishi bayani,alamu ya mishi akan ya ajiye sannan ya nufi hanyyan fita a office din,ajiyan zuciya Mai nauyi ya tsauke sannan ya rike kan shi da hannu biyu yace" what have come over me,I don't know that little girl but am so worried about her,ohhhh!Allah help me,ya karasa Yana kulle idan shi",ya fi minti 15 a haka kafin ya Kara sauke wani ajiyan zuciya Yana duba agogon dake manne a office din shi yaga 11 tsaura minti 30,tsaukar da kanshi kasa yayi Yana duba files din da aka shigo mishi dashi,11 tsaura minti 10 ya gama bincika files Mai bukatan signing Kuma yayi,tashi yayi ya dau rigan shi daya hanga saman kujeran da yake zaune,dauka yayi yasa sannan ya dau laptop din shi yasa a jaka,daukan jakan yayi ya hanga a bayan shi,wayoyin shi ya dauka ya rike a hannu hadi da makullin motan shi,sannan ya nufi hanyyan fita a office din shi,Kiran daddy ne ya shigo wayan shi dai-dai ya gama kulle office din shi,daukan Kiran yayi da sallama a bakin shi,"toh kawai naji yace sannan yasa wayan a aljihun shi" wani lifta ya hau Wanda zai sada shi da office din daddy,sallama yayi a bakin office din daddy,bayan daddy ya amsa ya bashi izinin shiga,shiga yayi fuskan shi dauke da murmushi,nuna mishi kujera daddy yayi ya zauna,bayani yamai akan abin da za'a tattauna a meeting,bai fi minti 15 ba ya fito a office din daddy,tsauka kasa yayi harabar company inda driver da body guard k jiran shi,wani daga cikin sune ya matso da tsauri ya amshi jakan hannun shi Yana gaishe shi da ladabi,bude Mai kofan mota akayi yasa Kai ya shiga,zagayawa driver Mai suna mudi yayi ya zauna a driver seat,kunna mota yayi sannan yayi reverse ya nufi kofan company inda an riga da an wangale makeken gate din,motoci biyu ne Suka fito daga company,daya Wanda Arif k ciki dayan Kuma na guards.tafiya suke cikin natsuwa,sunyi tafiya Mai tsawo kusan minti 15 kafin sukayi kicibis da goslow,Wanda ya hadu a sakamakon lalacewa da wani tipa yayi a tsakiyan titi,tun da a ka bar company Arif ya dau wayan shi Yana lasawa baiko daga Kai ba har sai da aka Kai wurin goslow din,"Daga Kai yayi Dan yaga Mai ya tsayar dasu,daga Kai yayi yaga I dama Nan wurin ba'a raba shi da goslow,juyawa Naga yafara Yi alamun akwai Wanda yake nema,chan Naga yatsayar da kanshi a wuri daya Yana kallo, umurni Yaba ma driver daya bude Mai kofa",yallabai Ina zaka, "tsawa ya daka Mai da har sai da ya firgita driver", ba ma shi kadai ba harda Wanda k zaune a kujeran Mai zaman banza,bude Mai kofan yayi batare da ya Kara tan baya ba,wa inda k dayan motan ne Suka fito,daga mutsu hannu yayi,iko suna ganin haka Suka tsaya dan sun gane abin da yake nufi.
wasu emmata dake zaune a motan dake opposite na guards,daya daga cikin su tace wow! feenah wannan guy din ya hadu,dagowa feenah tayi dan taga guy din da kawar ta k kodawa,iko tana daga Kai tagan shi,sai da nunfashin ta ya kusa daukewa,Kara waro Ido tayi tana kallan Shi, a zuciyar ta tace "irin wannan namijin take burin aure,ya Allah ka mallakamim shi a matsayin miji",meenat dake kusa da feenah sai magana take mata Amman Bata jiba duk hankalin ta ya dauku,sai data daka mata duka a cinya kafin ta dawo hayyacin ta,turbune fusaka feenah tayi tace Mai haka meenah kinsan banasan duka kohhh! Tohh! Ina ta Miki magana kin min shiru shiyasa na mareki,Ni dai barni tukun,dariya meenah tayi tana tafa hannu,tace shegiya kin fola daga ganin guy, murmushi feenah tayi tace k dai Kika sani,duba inda tagan shi dazu tayi Amman babu shi waige tafara Yi Amman babu alamun shi,fita tayi a motan tana waige waige chan ta hango shi a gurin en kwauye,zaro Ido tayi alamun mamaki,sai wani yatsina take kaman taga Kashi,takawa ta Fara Yi a hankali har ta nufi inda yake tsaye ya na raba fada,tana kaiwa ta tsaya daga Dan gefen shi,"ji tayi Nasreen na bayani tana kuka cikin siririn muryan ta Mai dadin ji,duk da yarinya ce karama Amman ko wata baba bazata gwada mata zakin muryar ba,"tunda ta Fara magana yake kallon ta most expecially Dan karamin bakin ta",tana kaiwa aya ya tsauke ajiyan zuciya a boye, tanbayar dayar ma yayi,daga jin yanayin bayanin ta ya gane Bata da gaskiya,"sai kawai ya share ta yace nawa ne kudin ki gaba daya,ya fada Yana kallon Nasreen"shiru tayi na sakwan biyu sanna tace duka na dubu biyu ne, nasiyar da na dubu data dari biyu tsaura na dari takwas,hannu yasa a aljihun shi ya dibi kudi da baimasan nawa bane ya mika mata kin amsa tayi ta langwabe Kai kaman Yar baby,Shima kallon ta yake,da yaga dai taki amsa shine ya bude baki yace Angel ki amsa,dago zarazaran idanuwan ta da hawaye ya jika tayi ta zubasu a kan shi,bude bakin ta tayi a hankali tace sunana Nasreen ba "igel" ba, "murmushi yayi jin yanda ta Kira sunan,ki amsa na Baki kyauta kinji Nasreeen, yakira sunan da wani salo" shiru tayi tana tunani,toh yanzu in ta amsa mai zata ce ma Anty lauratu, wazata ce ya Bata,in mama ta gani wani fassara zatayi mata,girgiza Kai tayi alaman a'a bataso,yabata dai-dai kudin ta kawai,feenah dake tsaye a bayan su tun zuwan ta ne ta Ciro dari takwas a jakan ta ta mika ma Nasreen,hannu kawai Suka gani a tsakiyan su,dagowa duk sukayi suka ga wata kyakyawan budurwa da bazata wuce shekara 21 ba,Nasreen ba tayi tsaurin amsan kudin ba har sai da feenah ta umurce ta,hannu biyu tasa ta amsa sannan tace nagode Yar uwar duncle,ita duk a tunanin ta kanwar shice,Dan ganin hasken fatan su yazo daya,Arif ko kallon feenah yake Dan shikam bai San ta ba,ita Kuma feenah sai wani yauki take ta zata ta Dan samu shiga,juyawa Nasreen tayi ta Fara hada kayan ta,Kiran sunan ta yayi tayi tsaurin dagowa,yace Angel inasan sanin gidan ku,zaro Ido Nasreen tayi,tace unnnunnnn........ duncle ban iya nunama gidan mu,nadai gode da kulawa,juyawa tayi ta Fara tafiya har ta nace ma ganin shi,juyawa Shima yayi da niyyan komawa wurin motan shi,muryar yarin Yar Nan yaji tana Mai magana alamun ya Bata minti biyu,tsayawa kawai yayi ba tare daya juyo ba,Dan shiru fina tayi kafin tace in bazaka damu ba kaban number ka sai muyi waya,Dan shiru yayi na sakwan biyu kafin ya karanto mata number, Yana gamawa ya bar wurin,motan shi ya koma Yana shiga ya jingina da kujera Yana tunanin abin da yasa Nasreen taki amsan kudin shi,ya lura duk tsauran mutanen wurin sun so ace sune za'ayi ma kyautan kudi,ya lura yarinyar nada tarbiya abin duniya bai dame taba haka yayi ta tunani har goslow ya washe, ba shi ya Kai wurin ba sai karfe 12:10, direct hall din da aka kama ya nufa ya shiga da sallama,duk aka amsa Mai,Wanda ba musulmi ba kuma yace welcome......................
BY GIMBIYA AYSHU 馃挒馃挒馃挒