Free chapter · Read without an account
Episode 2
______Wani sanyayyen murmushi Mami tayi tana mai shafa bayan AZEEZ ta ce "welcome my dear"
Alhaji Aminu ne ya ce " mu je ko" yayi gaba tare suka jero har mota, AZEEZ ya buɗe back sit suka shiga ya zaga ya hau driving sit ya ja suka nufi gida.
Mami ta ce " nagaji sosai Alhaji"
AZEEZ ne ya ce "ya jikin naki me doctor Ali Khan ɗin ya ce?" Mami ta ce "kai barni na samu resting ya su Munir?" AZEEZ ya juya ya ci gaba da tuƙi ya yi shiru bai ƙara tankawa ba.
Alhaji yayi murmushi ya ce "miskila kafi mahaukaci ban haushi, dan bata sanar da kai abinda doctor ya faɗa ba, shine ba ka amsa mata ya yaranta suke ba?" AZEEZ ya yi yaƙe ya ce " no daddy they are fine"
Mami ta taɓe baki ta ce " kasan abinda ya sa ya ce haka kawai ya faɗa ne dan ya riga kowa sani ya hau yi min ƙa'ida kamar shi ne Ali Khan ɗin"
Alhaji Aminu ya ce" hmmm lokaci dai ba Spain zai tafi ba, kamar yau ne zai dawo a matsayin hypertensive and cardiologist doctor ko my son"
"In sha Allahu Daddy" da haka suka isa gida, gate Man ya wangale tangameman gate ɗin ya na ta washe baki "barka da isowa Alhaji sannunku da zuwa Hajiya"
Motar ya bi da gudu bayan ya rufe gate ɗin, AZEEZ ne ya fara buɗewa ya fito miƙa yayi ya na faɗin "kai driving is not essay mtsww"
Daddy da Mami suka fito su Munir da Siyama ne suka fito a guje ganin Mami ta dawo, sati biyun da bata nan duk sun shiga damuwa.
Faɗawa jikinta sukayi suna murna, gaba ɗaya ta rungume su cikin fara'a.Ma'aikatan gidan sun fito suna ta faman barka da isowa, Mami ko kallonsu ba tayi ba, suka shige ciki, Rashida mai aiki ce ta ɗauko trolley ɗin da ke booth ta shigar da ita.
Yaƙe kawai suke dan sun san masifaffiya ta dawo, abu kaɗan zata hau su da zagi da cin mutunci ta tsani talakawa ganinsu take wulaƙantattu.
Siyama wacce take bin AZEEZ shekara biyar tsakaninsu yanzu tana 18yrs sai Munnir 15yrs sai auta Maryam (pretty) 10yrs ita ce sa'ar AZIZAN BABA.
Mami ta nufi ɗakinta dan watsa ruwa ta huta hakama Daddy, Pretty da Munir suka ci gaba da t.v game ɗinsu a parlour suna jiran fitowar iyayen nasu dan jin ya jikin Mami, duk da pretty ta ce bata ga rashin lafiyan da take ba, amma kullum sai a ce wai bata da lafiya.
AZEEZ da ya shige ɗakinsa rage kayan jikinsa yayi ya janyo system ɗinsa ya hau kallon bf ɗin da ya zame masa masifa da bala'i duk wani sabon fita ya sanshi.
Da kansa ya ke biyawa kansa buƙata tun yana s.s1 suke wannan aikin da abokansa Bilal da Mubasshar, a yanzu Bilal ya zama cikakken ɗan luwaɗi bama a ƙasar yake da zama ba, ya na Turkish.
Bilal kuwa har neman mata yakeyi duk kansu 23yrs only, AZEEZ ne kawai yake gansar da kansa ta wannan hanyar. babu wanda ya san abinda yake aikatawa sai ALLAH, sai Bilal abokinsa.
Sai da ya ɓata kusan 45mnt sannan ya shiga wanka, sallah yayi sai kuma ya ji kunyar abinda ya ke aikatawa, kuma hakan ba shi zai hana shi ƙara yi ba a duk sanda ya so.
A dinning suka haɗu kowa ya na lunch, AZEEZ ya ja stool ya zauna ya na haɗe rai wai shi first born.
Daddy ne ya ce" idan kun gama ku same ni a sitting room" ya tashi ya wuce, da Okay suka amsa.
AZEEZ ya ce "mami wai me doctor Ali ya ce tun kuna can nake tambaya pls tall me"
Mami ta ce " babu abinda ya ce sai samun lafiya da nake kuma ya ce yanzu zan iya cin maggi sosai kai har gishirin ma da potassium and magnesium ma na warke tas" Tunda ta fara zayyano kayan nan yasan ba haka ba ne, dan ko lafiyayyen mutum ba'aso ya cika cinsu da yawa, murmushi yayi ya ce "shi doctor ɗin ne ya sanar da hakan ko Mami?" ɓata rai Mami ta yi ta ce" a'a nayi ƙarya kai da fa lafiyata ƙalau sanadin haihuwar ka na haɗu da lalurar nan, mai makon kafi kowa tausayamin sai son bin diddigina to bansani bamtsw mai kafiyan tsiya tswww" ta ƙarasa da harara ta miƙe ta bi Daddy, Siyama da Mannir da pretty su ka tashi dan zuwa kiran Daddy, AZEEZ da yaji ba daɗi abinda Mami tayi masa, shiru yayi ya na mai tunanin meyasa kullum zuciyarsa ba nishaɗi da walwala, daga tambaya Mami ta yi fushi da shi.
Bin su yayi dan yasan shi kaɗai ake jira, ya na shiga sitting room ɗin ya koma kusa da Mami ya zauna ya na mai kalar tausayi, ganin yanda ya yi yasa Mami kama kunnensa ta ce " smile-smile" murmushi yayi ya na mai jin ƙaunar Mami na bin jini da ɓargonsa.
Daddy ya ce "ku dai kuka sani" dariya sukayi gaba ɗaya.
Sai da kowa ya nutsu Daddy ya ce "Alhamdulillah mamanku kullum ƙara lafiya ta ke kamar yanda likita ya sanar da mu, a yanzu haka ya ce "ta kula da abincinta kun san dai cin vegetables da fruits ya na matuƙar taimakawa masu hawan jini, sannan kamar yanda kuka sani haramun ne cin gishiri a gidan nan da duk wani abu dangin kanwa indai ba umarnin likita ba ne ko?" duk suka ɗaga kai, Mami ta sha kunu tana jiran yakai aya.
Daddy ya ɗora da faɗar su kula da lafiyar mahaifiyarsa, sai da ya gama Mami ta ce " kai da ƴaƴanka duk kun ɗauki maganar Ali Khan tamkar wahayi, to ni dai ba zan iya ci gaba da cin abu babu taste sosai ba,saboda Allah maggin ma ace ga limit ɗin da za'a samin a abinci kamar wata ƴar yaye" kowa ƙunshe dariyarsa yake sanin Mami ba ta son ayi mata iyaka da komai na rayuwa.
AZEEZ Ya ce " munji kuma zamu kiyaye dokokin likita daman muna kula sosai Daddy, yanzu ya jinin nata ya yi normal?"
Daddy ya ce "Alhamdulillah bai hau sosai ba, dan kafin mu dawo ma yayi normal sai dai ance ta daina yawan tunani"
"me yake damunki Mami" duk ka ƴaƴan suka tambayeta kamar haɗin baki, cikin so da ƙauna na uwa da ƴaƴanta ta ce "ba ni da wata damuwa sai guda ɗaya.......
MAZOJI
Layin ɗiban ruwa ake a famfan da ke ƙofar gidan Maigari, yara da ƴanmata wasu sanye da kayan saƙu wasu riga da zani haɗin gambiza.
AZIZAN BABA da ta ɗauko tulunta dan ɗebo ruwa ta bawa shukarta ta zogale da ta da sa a gidan, ba wai dan amfanin gida ba a'a wannan shuka tafi mata komai mahimmanci a gidan.
Ba ta tsaya ko ina ba sai bakin famfan ta ture bokitin Barira ta tara nata, Barira da aka kusa aurar da ita dan budurwace shekararta goma sha biyar, ta ɗauki tulun AZIZA ta buga shi da ƙasa ya fashe, ta hau zagin AZIZA, " dan uwarki ba ki da kunya ko, ni sa'arki ce da zaki janye min ruwa ki tara wannan ruɓaɓɓan tulun naki...Kamar zakanya AZIZA ya ɗane wuyan Barira ta kafa mata haƙori , ihu Barira ta sa jin uban cizo a bayanta, nan da nan aka hau ƙoƙarin raba su, AZIZA na dukan Barira Barira na dukan AZIZA ya kushi ta koma yi ta na cizonta a duk inda bakinta ya kai, sosai Barira take kuka.
"kai subhanallahi ku kubari mana" wani babban Mutum ya taso daga ƙofar gidan Maigari ya fara rabasu ana jan AZIZA ta janyo rigar Barira sai ga riga ta biyo hannun AZIZA tsindir ta yi wa Barira, yara suka hau ihu suna dariya, Hannatu ce ta yi saurin cire mayafinta ta sanyawa Barira wacce ta durƙushe ta na ta kukan abinda AZIZA ƙanwar bayanta tayi mata.
"Na rantse da kwarankwatsa bazan yarda ba, wallahi sai an biyani tulu na alkur'an ba zan yarda ba" masifa take ta na ta ƙoƙarin ƙwacewa daga hannun Malam Kallamu.
Gaban Maigari ya direta babu wanda bai ga abinda ya faruba, aikuwa Maigari ya daka mata tsawa, sai anan AZIZA ta sa kuka.
"ke meyasa ba ki son zaman lafiya iyi, ƴar tatsitsiya da ke sai bala'i sa'arki ce iye to baza a biyaki tulunba"
"idan an isa Allah ya tsine min tulun tun na auren Innata ne kuma ta kashe shi, a ce ba za'a biya ba, alkur'an duk inda na ganta sai na kasheta da ruwan duwatsu"kuka ta ke amma bakin bai mutu ba.
Malam Isa da ya san halinta ne ya fara rarrashinta ya ce " to kiyi shiru za'a biya ki kinji, bari kukan haka nan, meya haɗa ku?" AZIZA ta ce " shukata ce take son ruwa zata sha, jiya ban bata ba har ta kusa mutuwa, shine nayi sauri dan na ɗebo na zuba mata, ta fasamin tulu na" ta ci gaba da kuka.
Mai gari ya ce a shiga gida a ɗauko tulu a bata, wani Yarone ya tafi da gudu ya shiga gidan Maigari, tare da wani saurayi suka fito, tulun yaron ya kawo, Maigari ya kira saurayin da bai fi irin 20yrs ɗin nan ba ya ce"Amir ɗebo ruwa a tulun nan ka kawo min" Amir ya amsa ya nufi famfo, da sauri aka janye ya cika tulu ya kai.
Lantana kuwa sai gidan da yake kallon famfan ta shiga aka ara mata riga ta sa,sai kukan anganta take, ga Fulani da kunya.
Kasa fitowa tayi ta zauna a gidan ƙawayenta sai zugata suke akan ta ci uban AZIZA idan suka haɗu.
A guje Yara suka je gidan BABA, suna haki suka hau ba da labari, Baba da yake gyangyaɗi ya ji abinda yara suke faɗi, a ruɗe ya fito ya na dogara dandarsa ya ce "wace shegiyar ce ta taɓa AZIZAN BABA muje yau sai na ga ƴar gidan Uban waye a garin nan" da ƙar ya ke iya saurin buguzun-buguzun kawai yake da babbar riga.
Inna Gaji ma mayafi ta zara ta bi bayansu dan ganin wana irin duka akayiwa shalele, a kira ƴan sanda, sai faɗa take tana tafiya kamar zata daki babu, AZIZA na hango BABA ta tashi a guje ta nufe shi ta na zuwa gabansa ta zube ta hau burgima da rawar bori, faɗi take wallahi ba za ta yarda ba, ita ba sabon tulu take so ba.
BABA ya gigice ya na faɗin, wace ƴar jakar Ubance iye? Maigari da kowa ya ke girmama BABA dan yafi su tsufa aka shiga ba shi haƙuri ana ya nutsu ayi masa bayani.
Lantana da ƙawayenta suka fito, yara su ka hau yi mata dariya, suna faɗin "anganta anganta hahhh" a guje Lantana ta ruga tana kuka sosai.
Inna Gaji ce ta ƙaraso ta na ɗago AZIZA ta fara duba jikinta ko anyi mata rauni, ayi wacce za'ayi...........
Zinariya ce✍🏻