Free chapter · Read without an account

Chapter three (3)

by Amatallah M Al'amin CHANNEL · HAKURI NA YAKARE

💦💦💦 *HAK'URI NA YA K'ARE*😭💦💦💦



 writting by 


*MARYAM BINT ABDURRAZAK SALIS (Oum Mashkur)* 


Marubiciyar👇

*suhailat* free book

*ba a san maci tuwo ba...* sai miya ta k'are paid book 300👌

 *rud'in shed'an* had'in gwiwa/ usman ango free book


And now👇

*HAK'URI NA YA K'ARE*

    Gajeren labari free book



*ABIN LURA*👇

*Labarin ya faru a gaske hakazalika wacce abin ya faru a kanta tana buk'atar kulawar ku wajen bata shawarwari sannan tana cikin cikin dukkan groups d'ina na book idan kuka bata shawara zaku samu lada.*


*TSOKCI*

*An canza suna da kuma garuruwan da abin ya faru saboda tsaro🤷‍♀️*



*🌍MANAZARTA*

*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*

***

______________________________*True life storie*

 




Labarin kaso 97% gaskiya ne ubangiji ya bamu ikon amfani da abinda labarin ya k'unsa.


  

Ina godiya ga Allah mad'aukakin sarki da ya bani ikon rubuta wannan gajeran labari, wanda labari ne na gsky ina ptn zamu amfana da abinda muka karanta.🙏



15&16


Mijin sameera keke napep yake ja, kasancewar Sana'a ce me matuk'ar rufin asiri yana yi mata duk abinda take buk'ata, hakan kuma ya tsone wa mahaifiyar sa ido, ba gida d'aya suke ba amma kullum sai inna taje gidan don taga abinda yake faruwa a gidan.




A wannan lokacin ne kuma k'anwa ta ilham zata zana jarabawar clapaing babanmu yace na tanbayi mujahid idan ya amince zai biya min sai mu zana jarabawar tare da ilham, lokacin da nayi wa mujahid maganar ya amince, cike da murna ta naje gida na fad'a aikuwa baba ya biya min akayi min komai lokacin jarabawar kawai muke jira.




Yaro na muhssen ya k'ara girma da wayo yanzu yana cikin shekara ta 4 kenan k'aninsa hanif kuwa yana shekara d'aya da rabi, ban yaye shi ba, ameera tana zaluntar muhssen duk abinda yayi mata ko yaya ne sai ta make shi,idan na nuna rashin jin dad'i na sai goggo tace zan raba musu zuminchi ita kuma a lokacin shekarun ta 10 rayuwa da ameera itama sai a hankali sai dai ita bata yi min sata amma fa akwai lafiyar had'a munafurci, tasha had'a ni da goggo akan abinda bai kai ya kawo ba, nafi jin dad'i idan muhssen ya tafi gidan mu kasancewar ya iya zuwa tuntuni hankali na yafi kwanciya da hakan, shi kansa yafi sakewa a can don sai ya wuni zirr wata ranar ma sai ya kai dare sai an tura ameera taje ta d'auko shi, wata rana da taje zata taho dashi ya nuna baya son ya tafi babu yanda maman mu bata yi akan ta barshi ba amma yarinyar nan ta murje idanun ta tak'i barin shi, da suka fita ma kwad'e shi tayi tana jansa a k'asa shi kuma yana kwance a k'asan sai kuka yake tsalawa, ilham ta lek'o tayi mata magana amma ko a jikinta ta cigaba da jansa a k'asan, ran ilham yayi matuk'ar 6aci ta koma zata d'auko hijabi ta fito don tayi niyyar sai ta mare ta, kafin ilham ta fito har sun sha kwana.



Lokacin da suka je gida yayi busu-busu da k'asa yana ta kuka ban tanbaye shi dalilin kukan sa ba don nasan mafi yawanci idan taje d'auko shi sai ta dake shi, haka nayi masa wanka na canza masa kaya, goggo taje unguwa ranar duk muna cikin d'aki na dasu ameera, sai ga ilham k'anwata da ta shigo ba taga goggo ta wuce d'aki na, ganin ameera a d'akin yasa ta kalle ta cikin fad'a tare da cewa."Ameera wlh duk ranar da kika k'ara zuwa d'aukar muhssen kk ja shi a k'asa sai na dake ki don d'azu ma naso in kwad'a miki mari, tsabar fitsara babu yanda ba ayi dake akan kibar shi za'a kawo shi ba amma kika k'i bayan kin dake shi kuma shine kika dinga jansa a k'asa yanzu da kinji masa ciwo fa?"



Ita dai ameera shiru tayi ko k'ala bata ce ba, nasan kuma don tasan goggo bata nan ne, da tana nan bazata yi shiru ba sai tayi mata rashin kunya, ni kuwa nasan halin ameera abinda bai kai ya kawo ba ma ta iya had'a maka sharri balle anyi mata fad'a, na kalli ilham kafin nace."Kinga ilham babu ruwanki d'an uwanta ne duk abinda tayi masa tsakanin su ne."



"Nasan d'an uwanta ne aunty zuhra sai dai ni bazan bari ta zalunce shi a gaba na in k'yale ta ba, duk abinda zata yi masa tayi amma ba a gaba na ba don ni ba irin ki bace."


Ilham ta fad'a ranta a 6ace, ni dai ganin zata kula min matsala nace tayi min shiru saida taga raina ya 6aci kafin na samu ta bar zancen muka cigaba da hirar mu, har lokacin kuma ameera tana zaune bata k'ara magana ba har ilham ta tafi, bata dad'e da tafiya ba goggo tayi sallama ameera wacce take kwance tana jin sallamar ta fita da sauri, cikin tsananin mamaki na bita da kallo don a tunani na ma tayi bacci, kafin na gama mamakin na jiyo ta ta fashe da wani irin kuka me tada hankali, hankalin goggo yayi matuk'ar tashi ta fara tanbayar abinda nayi mata, wai yarinyar nan bud'an bakin ta sai cewa tayi mun had'u dani da ilham mun zage ta ilham kuma ta dake ta, aikuwa a take na jiyo goggo ta fara sababi har da cewa ."Sai Allah ya saka mata azzalumai ma ciya amana, indai akan muhssen ne ku k'arata dashi babu ruwan ameera dashi. " ranar kam na k'ara tabbatar da makirci irin na ameera, dukda naji babu dad'i amma fad'an na goggo bai dame ni sosai ba idan da sabo yakamata na saba, tunda ga wannan lokacin ameera ta daina zuwa gidan mu d'auko muhssen a cewar goggo bazata k'ara zuwa gidan namu ba ma.




Baba be san abinda yake faruwa ba saida wata rana yace ameera taje ta d'auko muhssen dare yayi goggo tace."Ai bata zuwa gidan. " baba ya kalle ta da mamaki kafin yace. "Saboda me?"


Nan goggo ta fad'a masa dalilin su wai ilham ce take dukanta don kawai ta daki muhseen, bai ce komai ya fita daga gidan ashe wai gidan mu ya tafi akan yana son ganin baban mu, lokacin bai dawo ba hakan tasa bai samu ganin sa ba, bayan ya dawo aka sanar masa sai gashi yazo da kansa, ciki baban ya shigo dasu aka shinfid'a musu tabarma, bayan y'an gaishe-gaishe baban su mujahid ya dube shi sannan yace. "Malam abinda yasa nake son ganin ka shine wata matsala ce ta fara kunno wa nake son mu taru muyi maganin ta, nasan dai kana da labarin abinda yake faruwa tsakanin zahra'u da habibu." Cikin rashin fahimta baba yace."Gaskiya ni bansan abinda yake faruwa ba Allah yasa dai lafiya?"



Shiru ya d'an yi kafin yace. "Akwai abinda ya had'a su Wanda takai yanzu kusan shekarar su 5 basa magana da juna." 



Baba yace. "Ikon Allah shi yasa ashe ranar da muka had'u da habib naga yana min wani kallon banza, to amma menene ya had'a su?"


Shiru baban nasu yayi kafin yace. "Gaskiya dai babu Wanda yasan abinda ya had'a su, kuma abinda ma yasa na kira ka shine ameera d'iyar y'ar waje na ce suka samu matsala da ilham k'anwar zuhra har ta kai ga naji ance wai ita ameeran ta daina zuwa gidan saboda ilham d'in na dukanta sannan kaga bai kamata ace abubuwa irin haka suna faruwa a tsakanin mu ba tunda an riga da an zama d'aya."




Baban mu yana da hak'uri sai dai idan ransa ya 6aci bai iya magana ba yana iya fad'a maka me ciwo, a ganinsa wannan matsalar duk laifin baban su mujahid ne tunda har suka iya bari yara suka d'auki tsawon shekaru 5 suna gaba ba tare da an d'auki wani mataki ba, ya riga yasan halin y'ay'an sa yasan abinda zamu iya da Wanda bazamu iya ba don haka ya kalli baban nasu kafin yace."Maganar gaskiya Mlm wannan duk laifin ku ne ka duba kaga tsawon shekarun da aka kwashe ana gaba tsakanin yaron ka da matar yayansa kuma kuka zura idanu ba tare da kun d'auki wani mataki ba, sannan yarinyar nan nasani bazata tsokane shi ba amma duk anbi an k'wazzabe ta, wlh ban ta6a sanin abinda yake faruwa tsakanin zahra'u da habibu ba, koda yake yakamata ace na fuskanci wani abun tun ranar da yayi min wannan Kallon banzan saboda yana jin haushin d'iya ta ya had'a dani, to ni yanzu babu abinda zance akan wannan al'amarin sai dai ince kayi k'ok'arin gyara gidan ka, nima zanyi wa ilham magana babu ruwanta da yarinyar, amma gaskiya ka tsawatar masa akan cutar da ita da yake, ashe shi yasa yarinyar kullum take cikin rama."





Ba wai baba da yake zaune a gabansa ba hatta mu da muke cikin d'aki saida muka yi mamakin yanda babana yake maganar, baban su mujahid yace."amma Mlm bai kamata ka goyi bayan yarinya ba alhalin ba a ji abinda ya had'a su ba." Murmushi baba yayi sannan yace. "Babu damuwa a kira su da ita dashi sai mu gano Wanda yake da laifi."



Zuciya ta ta hau lugude lokacin da naji ana kira na, mik'ewa nayi jiki a salu6e na sanya hijabi na na fita na tsugunna a gabansu kaina yana k'asa, babu irin kiran da baban su mujahid baiyi wa habib ba amma yayi mirsisi yak'i zuwa har zuwa yayi ya lallashe shi akan yazo ayi maganar yak'i zuwa, haka dole ya hak'ura ya dawo jiki a sanyaye cike da kunya babu shakkah a lokacin na k'ara jin tsanar habib a raina fiye da ko yaushe, mutumin da bai san darajar iyayen sa ba, kuma babu jahilci sai dai rashin aiki da ilimi mutumin da ya haddace al'qurani me girma sai dai ina yawan fad'a iliminsa bashi da amfani.




Baban su mujahid ne ya dube ni kafin yace. "Zahra'u me kika yiwa habib ne tsakanin ki da allah kin san dai a baya ba haka kuke ba."



Murya ta na rawa kamar zanyi kuka saboda fargaban abinda zai faru bayan baba na ya tafi na sani goggo tana jin duk abinda yake faruwa don a saitin window d'in ta muke zaune, saida nayi namijin k'ok'ari kafin nace."wlh baba ni dai a iyakacin sani na banyi masa komai ba nasan dai tun farkon cikin muhseen da nk zubar da yawu muka fara samun matsala dashi amma bayan haka ban san komai ba sai dai a tanbaye shi. "



"Shikenan tashi kije." Baban nasu ya fad'a kafin ya dubi babana yace."Yaro ne shi me k'yank'yamin tsiya haka Allah yayi shi amma zan ja masa kunne."



Ido cikin ido baba yace. "Mlm kenan itace fa tun yana d'anye ake lank'wasa shi, a iya k'in zuwan da yayi ya nuna min baka isa dashi ba kuma k'in zuwan sa ya tabbatar mana da laifin sa ne kuma dama na fad'a maka zahra bazata tsokane shi ba, dama dai ilham ce ta fita zafi nasan zata iya tsokanar sa, don haka kayi k'ok'ari ka gyara gidan ka."



Yana gama fad'in haka ya mik'a masa hannu suka yi musabaha ya sanya takalmin sa yai tafiyar sa.....



*masoya hak'uri na ya k'are ina ptn hak'urin ku be k'are ba😂 sakamakon jin shiru kwana biyu saboda matsalar rashin wuta, bana samun ishashshen cajin da zanyi typing, sannan ina k'ara baku hak'uri kasancewar akwai tafiya da ta kama ni zuwa niger ranar Tuesday in sha allah, zan dakata da yin posting sai na dawo amma idan na samu dama zan k'ara yin koda 2 pages ne kafin na tafi ina ptn zaku sanya mu cikin addu'oin ku allah ya kaimu lafiya ya dawo damu lpy,ngd sosai da bibiyar hak'uri na ya k'are 🙏🙏 *




Oum Mashkur

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol