Free chapter 路 Read without an account

SHAFI NA 22

by Fatima Zara Alhassan 路 ZUMUNTA KO MUGUNTA

ZUMUNTA KO MUGUNTA??馃摎






            NA 





FATIMA ZARA ALHASSAN 


          (拼ar mutan Argungu馃挅)







INA MI茦A 茒UNBIN GODIYA TA GA MASOYA NA, SABO DA JAJIRCEWAR SU, WAJEN BIBIYAR LITTAFAI NA, ALLAH YA SAKA MU KU DA ALKHAIRI馃槝





INA MAI 茦ARA BA KU HA茦URI, AKAN RASHIN JI NA, DA BA KU YI BA KWANA 2馃憦





INA GODIYA GA ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, DA YA BA NI IKON CI GABA DA RUBUTA WANNAN LITTAFI BI SA IYAWAR SA. ALLAH YA SA IN KAMMALA CIKIN AMINCI!



4/2/2023



SHAFI NA 22




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM



***


Wannan shi ne mafarin zaman malam Ba茩o a gidan malam Kabiru....


**


Kammalawar cin abincin su ke da wuya, malam kabiru ya shiga cikin gida da kwanukan abincin da su ka cinye...



Inna Murja ce ke ta kai kawo wajen gyara tsakar gidan ta. Macece mai tsafta 茩warai d gaske.



Da sallama 蓷auke a bakin su, su ka shigo cikin gida, malam kabiru ya nufi wajen wanke-waken su, don ya ajiye kwanikan abinci, ya bar malam Ba茩o su na gaisawa da Inna Murja.


Bayan ya aje kwanikan


Ya mi茩a ma ta keson (Tabarma) ya na magana " Har mun kammala, yanzu za mu wuce"


"To malam Allah ya tsare ya kai ku lafiya,ya kuma ba ku ikon aiki sosai, sannan ku dawo cikin amincin sa"



Murmushi malam kabiru ya yi, ya na mai 茩ara 茩aunar matar sa, duk shekarun da su ka yi tare, bai sa murja ta gaji da kula da shi ba.Ba bu ranar da zai fita ba tare da ta jero mishi addu'o'i ba. kullum ya kalli matar shi, sai ya ce" da ace murja ta samu ilmin zamani, yadda ta samu na addini, tabbas da za ta ri茩e mu茩amai kala-kala.



Tun 蓷azu malam Ba茩o ke kallon su ya na murmushi, ya na kuma mamakin cewa, dama akwai irin wannan soyayyar a 茩auye? A tunanin shi, wayayyu ka 蓷ai ke soyayya? ( kun fa ji, tunanin malam Ba茩o馃槄?)



Da fa kafa蓷un sa, malam Ba茩o ya yi. Firgigit ya dawo hayyacin sa, ya na cewa 


"Amin amin Murjanatu na"



Ai malam Ba茩o mai zai yi inba dariya ba...



Shi ma malam kabiru, kunya ya ji, ganin dariyar da Abokin na sa ke yi mi shi.



Sannan ya ce "zo mu tafi, dariyar ta isa haka nan, a rage dariyan,lokacin yin ta na nan zuwa"



Tsit ka ke ji, malam Ba茩o ya bar dariyar, ya zubawa malam kabiru idanuwan sa, wa蓷an da su ka rine, da alama kukan zuci, ya ke yi...



"me ya sa, ko yaushe malam kabiru ke cewa ya adana dariyar sa, lokacin yin ta na nan zuwa? shi kan sa ya san cewa, idan ya ce ya na da sauran farin ciki, to ya yaudari kansa. 



Amma har gobe, ya na 茩ara godiya ga Allah da ya ka蓷o shi, cikin rayuwar malam kabiru. 


Sabo da mutum ne mai barkwanci, da son jama'a, uwa uba ya na da ibada sosai...



Ganin irin kallon da ya ke jefo mi shi, ya sa malam kabiru jan hannun shi, su ka fita...




Zaune su ke su uku a office 蓷in Barrister Aminu Bello 蓷an tsoho, babban lawyer a fannin shari'a, kuma ya yi 茩aurin suna sosai a najeria, wajen iya sharia



Sarki Fu'ad ne, zaune da shiga irin ta Aneesa, ba za ka ta蓳a cewa ba Aneesa ba ce.San nan ya koro wa Barrister Aminu duk bayanan sa, kasan cewar, yau kwana goma shaa biyar kenan, da aka bu蓷e kes(case) 蓷in mutuwar iyayen Aneesa, magana har ta kai katu.



kuma katu ta ba da damar su 蓷auki lawyer.



Tun last week sarki fu'ad ya zo wajen Barrister Aminu, (Aneesa) su ka tattauna akan wa蓷anda ta ke zargin su ne su ka kashe mata iyaye...



"Malama Aneesa, me ya sa ki ke zargin su?



"Sabo da a gaba na, abun ya faru"



"ko a gaban ki, abun ya faru, idan ba shaida, to ina mai tabbatar miki aikin banza ne. 茩wararrun hujjoji, su ne cin nasara a kotu. 


Sabo da haka, dole mu dage wajen bincike, ba zamu sakarwa 拼an sanda komai ba, kuma in sha Allah zan saka ido akan su kawu."



"Toh shikenan Barrister, nagode, sai na ji ka,Jazakallahu khairan"



"Amin-amin Aneesa, duk yadda muka yi da 拼an sanda zan kira ki"



Su kawu ba su san cewa Aneesa ta yi magana da al茩ali ba.



Cikin sauri Barrister Aminu, ya shigo cikin office 蓷in, ya na cewa:


"Dan Allah ku yi ha茩uri na sa ka ku jira, wlh wani uzuri ne, ya tsayar dani"



"Ba damuwa Barrister, take your time"


Cewar Aneesa(sarki fu'ad)



Su kawu sai hararar barister su ke, 茩asa-茩asa, sarai ya gan su, su na hararar shi.



Gyaran murya Barister ya yi, ya na mai kallon su kawu, don ba zai iya ha蓷a ido da Aneesa ba, sabo da 蓷an banzan kwarjinine da ita sosai, san nan ya ce



" Abun da ya sa na ce muku mu ha蓷u, sabo da in sanar mu ku cewa, za ayi zaman kotu ranar litinin mai zuwa in sha Allah,kamar yadda al茩ali ya sanar da mu, 


shi ya sa na ce, ba ri inji ta bakin ku, me ake ciki game da shaidu? sabo da shaidun da mu ke dauke da shi yanzu ba zai isa ba, dole sai mun kawo wasu."



"Barrister na ji kana maganar shaidu? duka-duka yaushe aka fara binciken, da har za a samu shaidu? cewar kawu Bala"



Murmushi Barrister ya yi, " A tunani na za ku yi farin ciki kuma ku 茩ara ba ni 茩warin guiwa?"




"mun yi farin ciki, amma ka fa蓷a ma na, wane shaidu ne ka ke cewa ba zai isa a gabatar da shi a katu ba? Cewa kawu Tukur...



Murmushi Barrister ya yi, ta re da gyara zaman shi, "ku yi ha茩uri akan rashin fa蓷a mu ku da ban yi ba, tuntuni. Akwai wasu 拼an fashi biyu da aka kama, da laifin kisan kai, bayan binciken da rundunar 拼an sanda su ka yi, an gano cewa wa蓷an nan 蓳arayin su na 蓷aya daga cikin mutanan da su ka je gidan Alh. Mai Noma, su ka kashe shi ta re da mai 蓷akin sa.


Amma kuma sun shaida ma na ba su, su ka yi halbi ba, da sa hannun wasu mutane...


Amma kar ku damu, wannan shaidun ya nu na min cewa akwai babbar nasara a cikin wannan shari'ar."




Mutuwar zaune su kawu su ka yi,sai uban zufan da ke karyo mu su...



"Mu na godiya Barrister, kuma in sha Allah, nima zan yi 茩o茩ari na ga na samo na wa shaidun, sabo da aiki mutum 蓷aya ya raina" Cewar Aneesa (Sarki Fu'ad).




" kar ka damu Barrister dole mu ma mu tashi tsaye don ganin an hukunta wa蓷an da su ka kashe ma na 蓷an uwan mu," cikin kuka kawu Tukur ke wannan maganar...




A gajiye ta shigo cikin 蓷akin, ta yar da jakarta a kan gadon ta, san nan ta mai da kallon ta 蓳angare 蓷aya inda roomate 蓷in ta ke kwance ta na bacci.



Dundu ta na蓷a ma ta a bayan ta, ai ba bu arziki Feenat ta tashi a firgice ta na kwa蓳e fuskar ta.



"Dama wallahi nasan ke ce, saboda mugunta mutum na bacci za ki zo ki tashe ni!?"



"Cikin taikaci ta ke kallon 茩awar ta ta, "idan har ba ki son muguntar, to ki tabbatar da kin gama aikin ki kafin ki yi bacci, idan kuma ba haka ba wlh ko gobe sai na yi mi ki dundun da ya fi wannan ciwo. Ke ki ka raba mana duty, in yi gyaran 蓷aki da safe ki yi na rana, amma sabo da zaman ki lazy ko tsinke ba ki 蓷auke ba? Ta re da 蓷aukar filo ta 茩ara ma kawa feenat.



Feenat asalin ta 拼ar jahar kano ce, ta na cikin 蓷aliban da kwankwaso ya ba wa scholarship, wannan kenan



Rigimar su ba ta wuce Aneesa ta gyara wuri, feenat kuma ta 蓳ata wajen.



Ita ma 蓷auko na ta tayi ta na ramawa, kafin ka ce kwabo duk sun ya mutse 蓷akin...



茦wan茩wasa 茩wafar da aka yi ne ya hana su ciki gaba. Bu蓷e 茩ofar ke da wuya ta  san ya ihu sabo da murnar ganin wadda ba ta yi tunani ba.



Rungume juna su kayi, su na farin cikin ganin junan su...



"Murmushi Sarauniya ta yi, ta na mai cewa: Auta Aneesa wurin zaman ma sai na ro茩a? tare da murmushi akan fuskar ta"



"Dariya Aneesa ke yi, "tsabar murnar ganin ki ne ya sa ka ni rashin ganin  ba a zaune mu ke ba"




Bayan sun zauna feenat ta gaishe da sarauniya san nan ta fita



" Sarauniya tun da ki ka kawo ni, ba ki sa ke zuwa ba, kuma kin san ban da kowa sai ke, ta re da fashe wa da kuka!"



"Auta Aneesa ba dai rigima ba, toh ke in ban da abunki, don mi na ba ki 茩aho? kuma kin san na fa蓷a mi ki ,cewa duk ranar da ki ka yi kewata, da zarar kin busa shi, za ki je duk inda ki ke son zuwa.


Amma duk da haka ki yi wa maman ki uzuri kin ji?"



"Cikin jin kunya Aneesa ta ce " na yi mi ki uzuri mamata, ni ma dan Allah ki yi ha茩uri , wlh na manta da 茩ahon sam"




Murmushi sarauniya ta yi " Ba ki yi min komi ba Aneesa, da fatar ba bu wata matsala dai ko? kuma ki na karatu da kyau?"



Cikin jin kunya Aneesa ta ce, " ina karatu sosai sarauniya.Yanzu haka mun fara rubuta Test, shigowa ta kenan...



Sallamar feenat ne ya katse Aneesa


Ta na 蓷auke da table water a hannun ta,


"mama ga ruwa" cewar feenat



Murmushi sarauniya ta yi ,san nan ta shafa kan feenat ta ce, " Allah ya yi mi ki albarka feenat"



"Sarauniya me ya sa yaya Fu'ad be biyo ki ba?"




"Kar ki damu Auta, yayan ki aiki ya yi mishi yawa, amma da zarar ya kammala aiyukan shi, zai kawo miki ziyara in sha Allah."



"Allah sarki yaya fu'ad! Allah ya ba shi sa'a. Sarauniya ba ri in dafa ma na abinci"



"Auta ki na nufin kullum sai kin yi girki?! To miye amfanin 茩ahon da na ba ki? ma za tashi 蓷auko min 茩ahon in ga ni."



Cikin sauri Aneesa ta 蓷auko shi, ta ba sarauniya, sai 茩yalli ya ke yi kamar zinari



茦ahon sarauniya ta kai ga bakin ta, ta busa shi cikin 茩warewa, nan ta ke abinci iri-iri su ka bayyana a gaban su...



Cike da mamaki Aneesa ta ce, "yanzu ina da wannan abun na tsaya 蓳atawa kaina lokaci?"



Murmushi sarauniya ta yi, san nan ta ce "Ai sabo da ba ki 蓷auke shi da mahimmanci ba ne, shi ya sa ba ki kwantar da hankalin ki wajen koyon aiki da shi ba. Amma duk abun da ki ka sawa ranki, da zarar kin busa shi shikenan."




Haka dai su ka kwashe a wanni su na fira,daga baya sarauniya ta yi ma ta sallama san nan ta tafi...





Sai yamma su malam kabiru su ka dawo daga gona, ko wannan su ya gaji.



Bayan magrib malam kabiru ya zo kiran malam bako ya zo su ci abinci. Sai dai me ze  gani a bakin 茩ofar? Tashin hankali...!!!




瞥ar mutan Argungu























Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol