Free chapter · Read without an account
Chapter 20
*ZANEN ZABUWA*
©️ *Nana Haleema*
*Book 1*
*Page 20*
Kallon gadon da yake kwance take yi abinda ta jima bata ji ya motsa a zuciyar ta ba taji yana motsi a lokacin hakan ya tabbatar mata da yayan tane. A hankali take take takawa hawaye na zuba a idon ta ga jikin ta na rawa kamar mazari kamar wacce take jin sanyi haka jikin ta yake rawa.
A hankali ta k'arasa inda yake tana kallon sa tun daga k'afar sa har fuskar sa da saka rufe rabin ta da oxygen ga bandage an d'auke goshin sa dashi, bakin tane yake rawa tana so tayi magana amma ta kasa sai nuna shi da take yi tana kuka kamar ranta zai fita dan numfashin ta har wani fizgewa daga jikin ta yake yi.
Mahaukaciyar ramar da taga yayi ga bak'i da yayi shine ya sake tayar mata da hankali ta kasa nutsuwa hawaye yak'i tsayuwa daga idon ta, nuna shi take da hannu tana so tayi magana amma ta kasa sai yi take kamar tana shaquwa tana nuna shi tare da girgiza kanta.
A lokacin su Umma da Abba da Gwaggo suka shigo sai Nura a bayan su, da gudu ta k'araso inda su Umma suke tana nuna shi da yatsa tana shaquwa ga jikin ta na rawa hawaye na zuba, Rik'e ta Umma tayi amma ina idanun ta run rufe ruf bata gani sai numfashi ta da yake k'okarin barin jikin ta.
Ganin hakan ya saka Mufeedah saurin fita ta kira likita amma kafin suzo har Jannat ta suma. Rik'e ta nurses sukayi aka fita da ita daga d'akin aka kwantar da ita a d'akin kusa dashi aka shiga bata nata taimakon.
Gwaggo ma kuka take yi sosai ganin yadda Imran ya koma kamar an saka sirinji an zuk'e shi haka Umma ma kawai kallon sa suke suna zubar da hawaye. Shi kansa Abba dakewa kawai yake amma ramar da Imran yayi tayi bala'in tayar masa da hankali nesa ba kusa ba.
Dr Ansar ne ya lek'o d'akin ya gansu jugum-jugum babu wanda yake magana sai kallon Imran da suke yi yace, "Ko zaku iya fitowa sabida kar a tashe shi." Babu musu dukkan su suka fito aka zauna a kujerun da suke k'ofar d'akin.
Abba ne yayi k'arfin halin kallon Mufeedah da fuskar ta tayi wani irin ja kana ganin ta kaga wacce taci kuka ta k'oshi yace, "kece kika yiwa Jannat waya kika sanar da ita?." D'aga kai tayi ta mayar da hawayen ta tace, "Eh nice, nima naje gidan gonar Daddy ne a d'azun sai na ganshi a wajan idon sa a rufe gashi babu kowa shine muka tawo nan."
"Alhamdulillah alakulli halin, Allah yayi miki albarka Mufeedah, mun gode Allah ya saka miki da alkhairi." Gwaggo ta fad'a tana kallon ta tana cigaba da goge hawaye. Murmushi tayi kawai bata ce komai ba Abba ma yace, "Allah ya saka da alkhairi badan ke ba da yanzu bamu san hannun da ya fad'a ba, su kuma wanda suka aikata masa haka Allah bi masa hakkin sa ya saka masa abinda sukayi masa."
"Amin Abba." Ta amsa tana hawaye sosai.
Umma dai ta kasa magana sai goge kwallah da take tayi, Nura ne yace, "me suka ce yana damun sa?." Sai da ta goge idon ta sannan tace, "Akwai ulser, malaria, jinin sa kuma ya hau."
"Subahanallahi, ya Allah ya sakawa Imran duk wad'an da suka yi masa haka Allah ya bi masa hakkin sa."
Wayar tace tayi k'ara ta kallah taga sunan Mummy ba tare da tunanin komai ba ta d'auka, fad'a sosai Mummy take yi a cikin wayar Mufeedah ta dafe kanta domin itafa ta manta abinda ya kaita gidan gonar ma bata yi shi ba.
Mik'ewa tayi ta koma gefe sannan tace, "Kiyi hak'uri naje gidan gonar da niyar d'auko sak'on sai naga Imran d'ina a wajan yana cikin bad condition shine hankali na ya bar jiki na na d'auko shi yanzu haka muna Diamond hospital." Shiru ta kumayi alamun tana sauraron abinda Mummy take ce mata kafin tace, "ban sani ba wallahi Mummy nidai kawai na ganshi ne ko iya magana baya yi shiyasa hankali na ya bar jiki na na manta da abinda naje yi, yanzu ma y'an gidan su suka zo Jannat d'in Yaya Muhsin ma da ta ganshi suma tayi."
Shiru tayi tana jin mai Mummy take cewa kafin ta kashe wayar ta koma ta zauna.
Dr Ansar ne yazo wajan ya kalle su yace, "Kar ku damu babu komai firgita tayi ne shine hakan ya saka ta ta suma amma da ta farfad'o shikenan." Godiya sukayi Mufeedah ta zauna.
Kusan mintina ashirin sai ga Muhsin ya iso wajan Mufeedah na ganin sa ta isa inda yake ta fad'a jikin sa tana kuka sosai, d'an d'ago ta yayi daga jikin sa ganin sirikan sa suma kallon sa yace, "shikenan ya isa ki daina kuka Allah zai bashi lafiya kinji?." D'aga kai tayi cikin kuka ya rik'e hannun ta suka k'arasa inda su Abba suke.
Har k'asa ya duk'a ya gaishe su kafin yace, "ya mai jiki?".
"Da sauk'i." Abba ya amsa yana kallon sa dan bai san wacece Mufeedah a wajan sa ba.
"Allah ya bashi lafiya." Ya sake fad'a suka amsa da amin.
Ganin kallon da Abba yake masa ya saka shi yace, "ni ai Yayan Mufeedah ne uwa d'aya uba daya muke ita kad'ai ce k'anwa ta." Abba ya fad'ad'a murmushin sa yace, "kai masha Allah ga kama nan kuna yi." Murmushi yayi kawai amma zuciyar sa na wajan Jannat dan tunda Mummy tace masa ta suma ya kasa nutsuwa sai da ya fito.
"Jannat d'in tana wannan d'akin." Umma ta fad'a tana nuna masa d'akin da ta lura abinda yake so kenan. Ai kuwa bai jira komai ba ya mik'e ya shiga d'akin da take.
Bai jima sosai a ciki ba ya fito dan bata farka ba har lokacin ya shiga wanda Imran yake kwance shima bai jima sosai ba ya fito ya dawo inda ake zaune suka zauna.
Kusan awa d'aya suna zaune a lokacin har su Anty Surayya sun iso asibitin ana zaune ana zaman jiran tsammani. A lokacin Jannat ta fito daga d'akin da aka kwantar da ita tana dafe kai kamar zata fad'i Anty Surayya tayi saurin taro ta tana fad'in, "Sannu Jannat, meya fito dake?." Kallon su Gwaggo take yi kafin tace, "mafarki nayi ko? Ba Yaya na na gani ba."
Gwaggo ta kalle ta tace, "ba mafarki kika yi ba Jannat Yayan ki kika gani." Lumshe ido tayi ta bud'e ta d'an kwace daga rik'on da Anty tayi mata tana takawa a hankali ta shiga d'akin ba wanda ya hana ta. Tun daga nesa take k'are masa kallo, kayan jikin sa sunyi bala'in yin daud'a har mannewa suke yi a jikin sa ga ramar da yayi ta fitar hankali ya koma kamar bashi ba, idon ta ta kai fuskar sa taga gashi ya taru sosai a kansa da kuma fuskar sa ya koma kamar wani mahaukaci mara gata.
Kasa jurewa tayi ta fara kuka ta k'arasa inda yake ta zauna kusa dashi tana kallon fuskar sa, numfashin sa da yake sauka a hankali take kallo ta zabga uban tagumi tana kallon sa tana share kwallah.
Tun ana saka ran farkawar Imran har aka cire domin dukkan su wuni sirr sukayi a asibitin har Muhsin dan shima ya kasa tafiya ganin yadda Jannat take kuka hankalin ta ya tashi over shinr ya hana shi nutsuwar da zai asibitin, sallah ce kawai take tashin su daga wajan dan abinci ma sai Yaya Binta ce ta tawo dashi daga gidan ta aka ci amma kowa baya so ya motsa gani suke kamar zasu kuma neman sa su rasa ne.
Cikin Jannat da Mufeedah an rasa wanda yafi wani damuwa akan halin da Imran yake ciki domin dukkan su babu wacce ta iya kai lomar abinci bakin ta sai kallo da ido kawai.
Bayan sallar i'sha Anty Surayya ta Mufeedah da Muhsin basa wajan sunje sallah ta kalli Abba tace, "Abba ya za'ayi da zaman asibitin nan ne? Private ne yanzu iya zaman nan da yayi Allah kad'ai yasan kud'in da aka ci balle kwana." Abba yayi shiru kafin yace, "babu damuwa Surayya ya zauna bazai gagara ba ai" Abba ya fad'a dan sosai ya samu kud'i a hannun sa na gudunmawar bikin Jannat.
Abba ya sake cewa, "ya kamata duk ku koma gida dare yayi ku barni a nan ni zan zauna dashi." Nura ya kalli Abba yace, "Abba da kaje ka huta kaima ni zan kwana dashi babu wani abun."
"A'a Nura yau ka kashe harkokin kasuwar ka gwara kaje ka huta Allah ya kaimu goben."
Jannat da take zaune tace, "Abba nima zan kwana." Dai-dai lokacin da Muhsin ya dawo wajan Abba yace, "A'a Jannat ki tafi gida gobe in Allah ya kaimu sai ki dawo." Jannat ta fashe da kuka ganin haka Umma ta rik'o ta tace, "Daina kuka Jannat gobe in Allah ya kaimu sai mu dawo gabad'aya."
"Umma gani nake kamar in na tashi zan dawo ace baya nan." Ta fad'a tana kuka sosai tana kallon Umma.
"Babu abinda zai faru Abban ki yana tare dashi" Umma ta fad'a cikin sigar rarrashi tana kallon ta tare da share mata hawaye.
Mufeedah ce ta k'araso wajan Abba ya kalle ta da kulawa yace, "Mufeedah kema kije gida ki huta a barwa gobe in Allah ya kaimu, Allah ya albarka." Duka badan sun so ba suka fito daga asibitin aka bar Abba a ciki.
Nura ya hau machine d'in sa ya tafi Mufeedah ta d'auki Umma da Gwaggo a motar ta su Yaya Binta kuma ko wacce tayi gidan ta.
Ita kuwa Jannat tana can tana kuka har suka tafi bata sani ba taji an kira sunan ta cikin sanyin murya ya saka ta juya suka had'a ido da Muhsin maimakon ta daina kukan sai ta cigaba, k'arasowa wajan yayi yace, "Haba Jaana ki daina wannan kukan mana kema fa ba lafiya ce dake ba, daman ba fatan mu Allah ya bayyana shi ba kuma gashi an ganshi ai godiya zamu yiwa Allah ba kuka zaki dinga yi ba."
Goge idon ta tayi bata ce komai ba ya rik'e hannun ta yace, "Muje na kaiki gida ki huta duk sun tafi an barki." Ba musu tabi bayan sa ya bud'e mata mota ta shiga shima ya shiga yaja motar.
Had'a kai tayi da guiwa ta kuma fashewa da sabon kuka wanda hakan ya jashi dole ya faka motar yana kallon ta kafin yace, "Jaana kin san bana son wannan kukan naki ko? So kike nima nayi kukan ne?." D'aga kai tayi ta kalle shi cikin kuka tace, "Kaga yadda Yaya na ya koma? Ya rame fa yayi bak'i kamar bashi ba, fuskar sa duka gashi haka kansa, Yaya na mai tsafta amma kaga kayan jikin sa yadda sukayi bak'i kuwa? Allah ne kad'ai yasan irin wahalar da wanda suka sace shi suka bashi, Ya Allah na rok'e ka duk wanda ya aikatawa Yaya na wannan aikin ka saka masa ka bi masa hakkin sa kasa shima ya d'and'ana zafi da rad'ad'in rashin sa da mukayi muma."
Cikin kuka take maganar wanda dole mai sauraren ta yaji tausayin ta domin kana ganin ta zaka san daga zuciyar ta maganar take fitowa. Runtse ido yayi jin addu'ar da take yi ya kamo hannun ta yace, "Jaanaaa kiyi hak'uri ki daina kuka kiyi masa addu'ar samun lafiya, su kuma wanda suka sace su d'in kiyi musu addu'ar shiriya."
A wani fusace ta kalle shi tace, "Addu'ar shiriya? Ni Jannat nice zan wa wanda suka sace Yaya na addu'ar shiriya? Ai in bance Allah ya tsine musu albarka ba bazan ce Allah ya shirye su ba, kuma in sha Allah sai sun girbi abinda suka shuka da izinin Allah." Idon ta yake kallo har ta kai k'arshe sannan yace, "Shikenan naji nidai buri na ki daina wannan kukan Jaana ko kin manta ke amarya ce ne?."
Idon ta ta share sannan tace, "ni ba amarya bace yanzu in kaga na zama amarya to tabbas Yaya na yaji sauk'i, dole ma a d'aga bikin nan dan baza'a yi biki na Yaya na yana asibiti ba." Girgiza kai yayi domin yasan abinda bazai tab'a yuwa bane a wajan sa yace, "Shikenan yadda kika ce amma ki fara share idon ki." Ba musu ta share idon ta ya kunna motar suka cigaba da tafiya yana sake kwantar mata da hankali har suka isa gida.
Bata wani tsaya sunyi sallama ba dan ba'a hankalin ta take ba ta fita zuwa gida ya bita da kallo yana murmushi kafin yace, "kome zai faru nasan mahaifin ki bazai tab'a d'aga wannan d'aurin auren ba sai dai in a fasa duk wani events da aka shirya, in ma aka d'aga d'aurin auren buri na bai cika bama kenan, ai yadda yake kwance a asibitin nan da ya farfad'o nake so ya sake komawa ciwon zuciya kuma ma." Ya k'arasa fad'a yana jan motar sa ya bar unguwar.
A daren zan iya cewa dukkan mutanen gidan bacci b'arawo ne kawai ya sace su shima kuma da burin gari ya waye a koma a ga halin da Imran yake ciki.
Tunda akayi asuba basu koma ba Jannat tana zaune kawai dan bata jin k'arfin jikin ta gashi Umma ta hana ta fita da tuni tayi nisa a hanyar zuwa asibitin hakan ya saka ta kawai tayi gefe kamar marainiya. Gwaggo ce ta had'a abinci wanda za'a tafi dashi can Umma kuma da kanta ta shiga d'akin Imran aka d'auko masa kayan sawa koda zai farka sai ya canja.
K'arfe shida da wani abun Nura yazo musu da mai adaidaita sahu suka shiga suka wuce shima kuma yabi bayan su a machine. Adaidaita sahun su yana tsayawa Motar Mufeedah ta tsaya ta fito daga motar tana gyara hijjabin jikin ta.
Juyawa tayi sai suka had'a ido da Umma tayi murmushi ta k'araso ta tsuguna har k'asa suka gaisa da Umma da Gwaggo sannan ta mik'e suka gaisa da Nura da Jannat suka shiga ciki gabad'aya.
A hankali suka shiga d'akin Abba yana zaune akan sallaya yana azkar ko wacce ta samu waje ta zaune ana kallon Imran yadda suka barshi jiya haka yake sai ruwa da ya k'are aka kuma saka masa wani, Kusa dashi Jannat taje ta zauna kamar jiya tana kallon fuskar sa idon ta ya ciko da hawaye.
Abba ya shafa addu'ar kafin ya juyo ya kalle su yace, "Ku kuwa da sassafiya haka kuka fito sai kace yak'i?." Murmushi kawai dukkan su sukayi kafin a gaisa su tambaye shi mai jiki yace, "gashi nan dai har yanzu bai motsa ba, likitan yace zai jima yana bacci daman tunda ya jima bai samu bacci ba dan a jiyan ma sau biyu ana canja masa kwanciya yanzu ma fitar su kenan an canja masa."
Jinjina kai kowa yayi a cikin su ana kallon sa kowa yayi shiru babu mai magana a cikin su kafin Abba ya kalli Mufeedah da take goge kwallah yace, "Mufeedah ya iyayen naki, Suna nan lafiya?." Kallon sa tayi tace, "Lafiya lau Abba, anjima kad'an zasu zo suma."
D'akin ya sake komawa shiru babu mai magana sai da gari yayi haske sosai sannan Abba yaje gida ya dawo.
Yadda akayi zaman jiya haka yau ma ta kasance har dare babu labarin farfad'owar Imran sai y'an dubiya da suke ta zuwa ciki har da Mummyn su Mufeedah. Haka jiya haka yau ma suka koma aka bar Abba asibitin kowa yana fatan Allah yasa in sun dawo gobe ya farfad'o.
Washe gari da misalin k'arfe goma na safe suna zaune dukkan su har da su Yaya Binta Jannat kuwa tana wajan zaman da ta yiwa kanta wato kusa dashi. A hankali Imran ya fara motsawa yana k'okarin bud'e idon sa.
Jannat da ta gyara zama tana sake ware idon ta a kansa, a hankali taga ya bud'e idon sa kafin taga yayi saurin mayarwa ya rufe, Ganin hakan ya saka tace, "Abba Yaya na ya farka, wallahi ya farka yanzu ya bud'e idon sa ya kulle." Ta fad'a a gigice tana tsalle tana kallon sa.
Da sauri Nura ya fita ya kira likita sai gasu da Dr Ansar ya k'araso inda yake ya cire oxygen d'in hancin sa ganin numfashin nasa ya dawo dai-dai kafin yace, "Sannu Imran." Bai motsa ba bai kuma yi magana ba hakan ya saka Dr ya sake cewa, "ba lallai sai kayi magana ba in kana jina ka motsa kanka ko k'afar ka."
Sai kuwa aka ga ya motsa yatsun k'afar sa wanda farce yayi musu yawa a jiki Dr yace, "Alhamdulillah, zaka iya bud'e idon ka? In zaka iya kayi shiru in baza ka iya ba ka motsa k'afar ka." Sai kuwa ya motsa k'afar tasa Dr ya kuma cewa, "idon nayi maka zafi in ka kalli haske ko? Kana jin kamar ana soka maka allurai a cikin sa haka ne?." Nan ma ya motsa k'afar sa alamun eh.
Dr ya juyo ya kalle su yace, "kar ku damu da rashin maganar sa zata bud'e nan da anjima kad'an musamman ma in aka bashi abu mai zafi yasha, sannan maganar gaskiya dole sai an bincika lafiyar idon sa munga abinda ya sami idon nasa."
"Me ya samu idon Yaya na?." Ta fad'a muryar ta na rawa sosai. Dr ya kalle ta yace, "Sai mun duba mun gani sannan zamu san abinda yake damun sa, yanzu abinda za'ayi za'a taimaka masa ya tashi a samu yayi wanka da ruwa mai zafi sannan a bashi ruwan tea mai d'an yaji yasha bayan kamar minti goma da shan tea d'in nasa sai a bashi abinci, inda dama a yanke masa faratun hannun sa dana k'afar sa, mu kuma zuwa anjima zamu zo a bincika abinda ya samu idon sa." Yana gama fad'ar hakan ya fita.
Zubewa Jannat tayi akan Kujera ta fashe da kuka mai sauti Umma tayi saurin rik'o ta tana aikin rarrashin ta, Nura ne ya k'arasa inda yake ya d'ago kafad'un sa aka samu ya mik'e zaune dak'yar yana yatsine fuska kana gani yadda yake yi kasan yana jin wani abu wai shi azaba, hannun sa ya mik'a inda yake jiyo kukan Jannat d'in ganin hakan ya saka Anty Surayya ta kalle shi tace, "Jannat kake wa magana?."
Kansa da yayi masa nauyi ya d'an daga kad'an sabida ciwon da yake kan nasa ai da sauri ta mik'e ta k'arasa inda yake ta saka hannun ta a cikin nasa, rik'ewa yayi kafin ya sake ta ya fara k'okarin mik'ewa tsaye, dukka mutanen d'akin fita sukayi dan a bar shi ya shirya sosai aka bar su da Nura.
Da taimakon Nura ya mik'e dak'yar suka fara tafiya band'akin yana dafa bango har aka k'arasa Nura ya had'a masa ruwa mai zafi aka d'auki sabon brush a band'akin aka matsa man wanke baki a jiki aka bashi.
Da kansa yayi wankan ya kuma wanke bakin sa duk da idon sa a rufe yake, tun a band'akin Nura ya taimaka masa ya saka kayan da ake dakon su kullum sannan ya fito a hankali Nura na rik'e dashi.
Yana zama suka dawo aka bashi shayin da akace yasha ya fara kurb'a a hankali ruwan na sauka a cikin sa a wahalce, d'akin yayi shiru babu mai magana kowa hankalin sa yana kan Imran har ya shanye tea d'in ya jingina da gadon yana sauke numfashi.
Bayan mintinan da likita ya fad'a aka bashi dankali soyayye ba laifi ya d'an ci kad'an kafin ya ajjiye dan sosai yaje jin wani irin zafi in abincin ya sauka a cikin sa.
Bayan gama cin abincin nasa Nura ya samo reza sabuwa ya yanke masa faratun sa kamar yadda suka ce, y'an mintina kad'an aka kwashe likitoci har uku suka shigo, d'aya daga cikin likitocin ya kalli Nura da yake tsaye yace, "Dan Allah kulle mana ko wacce kafa da kasan haske zai shigo d'akin nan sannan ka kashe duka fitilun d'akin." Ba musu Nura yayi abinda akace d'akin yayi duhu sosai babu abinda ake gani.
Likitan ya kalli Imran yace, "bud'e idon ka yanzu mu gani." A hankali Imran ya fara bud'e idon sa har ya ware su tass a d'akin yana kallon likitan duk da ba ganin sa yake ba. Likitan yace, "yana yi maka zafi idon?." D'aga kai yayi alamun eh kafin ya sake cewa, "kana jin wani abu kamar tsakuwa a ciki?." Nan ma ya d'aga kai alamun eh yana ji.
Girgiza kai likitan yayi kafin yace, "kar ka rufe idon fa, d'an bud'e labulen can." Ya fad'a yana kallon Nura, ba musu ya d'age haske ya shigo d'akin Imran yayi saurin janye idon sa yana k'okarin rufewa amma bai rufe d'in ba, da hannu likitan ya sake yiwa Nura alamun ya sake bud'e wani, sake bud'ewa Nura yayi haske ya sake yawaita a d'akin.
Kamar kiftawar ido haka Imran yayi saurin kulle idon sa yana kare idon da hannun sa sabida ji yayi kamar an watsa masa wuta mai zafin gaske a ciki ga suka da yake masa kamar allura.
Likitan ya sauke ajiyar zuciya ya kalli sauran likitocin a hankali yace, "idon sa ya samu matsala." Karaf a kunen Jannat.