Free chapter · Read without an account
7
_*RABO AJALI...!*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''
_Follow me on Instagram:- hauwa_a_usman_jiddarh_
7⃣
A kid'ime President ya mik'e tsaye had'i da zubawa Neesah ido,
batare daya iya furta ko da kalma d'aya ba,
cikin rashin fahimta Nana tace " what....!?
"Ban gane ba wai kina nufin aurenshi zaki yi....!?
" Yes Nana....!, ko da wata matsalar ne....!?
Muryar President a d'age yace " halan kin manta nan da next 10 days d'aurin aure ki ko....!?
Baki Neesah ta turo tana k'ok'arin yin kuka tace " I know! but I love him Dad...!,
a fusace President yace " baki da hankali Neesah, so kike ki mayar dani mutumin banza....!?
"Kin san harkar siyasa yanzu hakan yana iya jawo matsala,
ko ya haifarwa da jam'iyya matsala da fitina, tun farko inda kin san baki sanshi da baki bari an saka biki har ya zo gab da gab ba,
sai da aka gama buga kati aka raba invitation card sannan kice baki sanshi....!?
Kuka Neesah ta kuma sakawa had'i da diddira k'afa tace " wallahi ni dai Neehal nake so,
kuma shi zan aura babu wanda ya isa yayi min auren dole,
tana gama fad'ar haka ta shige bedroom d'inta had'i da banko k'ofa,
President zayyi magana Neesah ta fito tace " karka manta da batun kawo min mahifinta da ita kanta,
sannan ina san ganin Neehal dan zanyi singing a contract d'in nan,
dan haka ina san ganin su gaba d'aya gobe, sannan ka kira siriki na Alhaji Bilal Lagosa ka bashi hak'uri,
kace mishi karya damu babu komai,
President zayyi magana Neesah tace " no...! Dad just call him now,
tayi maganar da k'arfi tamkar tana magana da yaronta kamar yadda yaran turawa keyi,
bisa mamaki na sai naga President ya zaro wayarshi cikin Aljihu yayi dialing number Alhaji Bilal Lagosa,
instead of yayi mata fad'a koya nuna mata batayi dai-dai ba,
wayar Alhaji Bilal Lagosa ta soma ringing dai-dai lokacin yana tsaye gaban Neehal da Nauman yana zazzaga musu ruwan bala'i,
kasancewar shi mai matuk'ar zafi da fad'a dan baya wasa,
kamar bazai d'aga wayar ba, sai kuma yakai duba ga wayar dake aje gefe,
ganin sunan President yasa shi saurin mik'a hannu ya d'auka tare dayin picking ya kara a kunnenshi,
Neesah na tsaye a gefen President ta tsura mishi ido hannunta sark'e gaban k'irjinta,
bayan sun gama gaisawa ne President yace " I'm very sorry da maganar dana fad'a maka d'azu,
Neesah ta sanar dani ba laifinshi bane, so dan Allah karka d'aga hankalinka komai yana nan kamar yadda yake,
sannan gobe zan saka hannu a kwangilar, sai kazo ka amsa,
da sauri Neesah tace " no...! bashi ba ya turo Neehal d'in dai, I want see him,
idan kaga yadda Neesah ke bawa President oder yana bi saika rantse ita ce ta haife ba shi ya haife taba,
saboda tsakanin k'aunar da yake yi mata yasa yake yi mata biyayya wacce ita ce ya kamata tayi mishi,
da sauri Alhaji Bilal Lagosa yace " Alhamdulillah nagode sosai mai girma President,
goben in sha Allah zanzo da kai na,
" no...! ka aiko Neehal d'in gida sayya karb'a a hannun Neesah,
tunda su suka fara sai a barsu su k'ara abinsu gwara ma su fara koya tun yanzu tunda ba'asan me Allah zayyi gaba ba,
" haka me kam, Alhaji Bilal Lagosa ya fad'a yana murmushi irin na manya.
Bayan su Alhaji Bilal Lagosa sunyi sallama,
Neesah ta kalli President tace " call her useless father,
ba musu President yayi dialing number Alhaji Ubayyu,
bugu d'aya shima yayi picking cike da girmamawa ya gaida President,
ba wani dogon bayani President yace " gobe kazo villa house kai da 'yarka,
sai da ya d'an suruna tamkar yana gaban President yace " wacce daga cikin yaran nawa...!?
A dak'ile President yace " surukar Alhaji Bilal Lagosa, ya fad'a had'i da dropping wayar,
cike da tsantsar farin ciki Neesah ta rungume President had'i dayi mishi kiss,
tace " thank you...! thank you so much Dad, yana murmushi ya shafa kanta yace " kinyi farin ciki yanzu....!?
"Sosai Dad, " good Soul babu abinda nafi so a rayuwata ta duniya kamar na ganki cikin farin ciki,
" I love you, Neesah tace, kana ta kalli Nana dake tsaye tana kallansu,
cike da so da k'auna da kuma zallar farin ciki, tace " I love you Nana,
kanta Nana ta shafa tana murmushi tace " I love you too,
bayan Alhaji Bilal Lagosa ya aje wayar kana ya kalli su Neehal yace " Allah ya taimake ka,
komai yayi settling, gobe ka shirya da yamma kaje ka karb'o takardun contract d'in,
sannan inkaje ka maimaita abinda kuka yi kunji,
kansu k'asa sukayi godiya kana suka fita,
suna fita waje Nauman ya tuntsure da dariya sosai,
Neehal ya kalle shi a k'ufule yace " kai kuma uban me kake yiwa dariya....!?
Nauman bayyi magana ba ya cigaba da yin dariyarshi har da rik'e ciki,
sarai Neehal ya gane abinda Nauman yake yiwa dariya marin da Dady yayiwa Najwah ne yayi mishi dad'i,
tsoki ya ja yana kallan Nauman yace " kai...! wai me kake yiwa dariya ne, ko kaga abin dariya a jiki na.....!?
Nauman bayyi magana ba, ganin Nauman bashi da niyyar yin magana yasa shi jan uban tsoki,
had'i da shigewa cikin mota ya tayar, Nauman yana dariyar yace " bari na zaka yi nan....!?
Neehal bayyi mishi magana ba yaja motar yabar harabar gidan,
dan tuni Najwah ta dad'e gida tun korar da Dady yayi mata bata tsaya ba tayi gida direct,
Alhaji Bilal Lagosa yayi murmushi dan yana bayansu yace " kyale shi Nauman rarrashi zai tafi yayi sakarai lusari kawai,
da sauri Nauman ya juya jin muryar Dady, Dady yace " ka amshi key hannun driver sai ka d'auki duk matar da tayi maka ka tafi gida,
sosai Nauman yayiwa Dady godiya dan wannan ce mota ta biyar da ya bashi,
" ba nace karka sake yi min godiya kan duk abinda na baka ba....!?
Hak'uri ya bawa Dady kana ya shiga d'aya daga cikin jibga-jibgan motocin dake harajar gidan ya tafi gida,
Neehal na danna kai cikin parlor ya fara jiyo sautin kukan Najwah,
da sauri jikinshi na kerrrrma ya k'arasa shiga ya isa gareta ya durk'usa gabanta,
yana k'ok'arin yin magana wayarta ta soma ringing,
tana kukan ta kalli wayar taga sunan Abbanta, kallan Neehal tayi tana kuka tace " Dady ya fad'awa Abban mu abinda ya faru ko....!?
"No..! gaskiya bana tunanin haka kema kin san Dady bazai tab'a yin haka ba,
wayar na gaf da tsinkewa Neehal ya d'aga had'i da sanya wayar a hand free,
bayan sun gaisa Abban Najwah yace " ka cewa Najwah ta shirya gobe zamu je villa house President na nemanmu,
yayi maganar so calm dan tunda shugaban k'asa ya kira shi gabanshi ya shiga fad'uwa yana dukan uku-uku sosai,
yana tunanin abinda yasa President ke nemanshi shi da Najwah,
amma bai kawo komai ranshi game da Najwah ba dan bai tab'a tunanin zata iya aikata aikin da har President zai nemeta ba,
jin abinda Abban Najwah yace yasa gaba d'aya k'irjinsu bugawa da k'arfin tsiya,
jin sunyi shiru yasa shi cewa " hello...!, ko baku jina ne...!?
Neehal ne yayi k'arfin halin cewa " muna jinka Abba,
Abban yace " lafiya kuwa...!, kodai kun san meke faruwa....!?
Shiru suka k'ara yi gaba d'ayansu wanda ya tabbatarwa Abban tabbas sun san meke faruwa,
kuma akwai wani abu k'asa, dan haka yace " ku fad'a min koma meye dan nasan ta yadda zan b'ullowa al'amarin tun wuri,
bakin Neehal na rawa ya sanarwa da mahaifin Najwah abinda ta aikata,
" innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
dama baki da hankali Najwah baki san me kike yi ba....!?
Yayi maganar kamar zai faso ta cikin wayar yazo ga Najwah,
a tsorace Najwah ta shige cikin Neehal had'i da k'ara sautin kukanta,
da k'arfin mahaifin nata yace " rufe min baki munafuka muntuniyar banza,
wallahi ki sani duk abinda ya faru gobe kanki zai k'are shegiya,
kafin suyi magana yayi dropping wayar, cikin matsanancin kuka mai cin rai da zuciya,
had'i sa karya zuciya, gangar da ruhin ma'abocin sauraro Najwah tace " wallahi Allah ban san abin zai kai haka ba,
ido na ne ya rufe ruf gaba d'aya, na kasa controlling kai na,
but I'm very sorry na haifar maka da matsololi da dama, na jawa sanadiyyar fushin iyayen mu akan mu,
dan Allah ka yafe min kar abin yayi min yawa please my heartbeat,
take santa, k'aunarta da tsananin begenta da yake yi sukayi tasiri wajen karyar mishi da zuciya,
tsakanin tausayinta ya lullub'e shi, har bai san sanda kwalla ta cika mishi ido ba,
cike da zallar shauk'in so Neehal ya rungume Najwah tsam a jikinshi,
yana sauke ajiyar zuciya gami da shafa kanta yace " bakomai my Happiness komai ya wuce,
ki daina damun kanki kina kuka kar kiyi ciwon kai kinji, bana san wani abu ya sameki dan idan wani abu ya same ki,
bazan tab'a yafewa kai na ba, so please ki kwantar da hankalinki mijinki yana tare dake koyaushe,
a ko'ina a kowanne lokaci, cikin kowanne irin yanayi na rayuwa،
yayi maganar cikin rawar murya, deep down yana jin kamar yayi hauka saboda k'unar da zuciyarshi keyi mishi,
maimakon yaji zafin Najwah sai take yaji zafin Neesah da tsantsar tsana da k'iyayyarta sunyiwa zuciyarshi k'awanya,
in banda umarnin Dady ne zuwanshi gobe da babu wani abu da zai k'ara had'a shi da Neesah ko'a lahira,
jikinshi ta k'ara shigewa tana k'ank'ame shi sosai tace " am sorry dear nayi maka alk'awarin ban k'arayin kwatankwacin abinda nayi,
nayi maka alk'awarin zan canja, zan daina duk abinda nake yi,
zan daina bak'in kishi zan rink'a controlling kishi na,
zan zame maka mace ta gari matar rufin asiri,
cikin jin dad'i Neehal ya shafa kan Najwah yana murmushi yace " thank you so much,
an I promise to be with you for ever an ever, I will be by your side always, an i will make you happy, happier woman in the whole earth,
zan zama naki ke kad'ai zan kuma dawwama a naki har abada,
nayi miki alk'awarin bazan tab'a yi miki kishiya kona k'ara aure ba,
kamar yadda kike ke kad'ai a zuciyar Neehal haka zaki kasance ke kad'ai a zuciyar shi har abada,
kiss ta shiga manna mishi ta ko'ina shima yana mayar mata da martani.
Washe gari a villa house, Neesah zaune makeover tana tsantsara mata kwalliya ta garari,
jikinta sanke da doguwar rigar material irin ready mate d'innan,
wacce Indian, da turawa ke sawa idan zasu fita party,
rigar kalar dark purple mara hannu da k'ok'on bra a gabanta,
tun daga k'asan rigar har zuwa cinya a tsage yake, santala-santalan cinyoyinta waje, farare tasss dasu, ta saka takalmi high hill mai shegen tsayi,
kashin ganta yasha gyara sosai idan ka ganta sai ka rantse bata tab'a sanin musulunci ba,
balle yaran Hausa/Fulani, jikinta sai fidda sihirtaccen k'amshi yake na mutuwa,
duk kamun kan d'a namiji idan yaga Neesah sai wani abu ya tsarga mishi.
Cikin isa da tak'ama Neesah ta taka zuwa parlor inda Neehal ke zaune,
yana zaman jiranta, jikinshi sanye da d'anyar shadda Gezza,
d'inkin sosai yabi da shaddar yayi kyau sosai, k'uruciyarshi ta k'ara bayyana,
Neesah ta k'arasa gareshi fuskarta d'auke da shu'umin murmushi,
mai d'auke hankalin ma'abota kallan fuskarta, yana ganinta ya mik'e tsaye,
fuskarshi babu annuri sosai , tana isa ta rungume shi had'i dayi mishi kiss,
kamar yadda tayi jiya kana ta zauna kusa dashi had'i da mik'a mishi files d'in,
tace " an gama komai, saura kuma fara aiki,
"Okey, kawai Neehal yace ya soma k'ok'arin mik'ewa,
mayar dashi ta yi zaunar had'i da hawa kan cinyarshi tace " ya naga kana sauri haka 'yan samari ina zuwa....!?
Fuskarshi babu walwala sosai, yace " am busy,
" har akwai busy dayafi wannan....!?
Shiru yayi baice mata komai ba, tace " idan wani abun ke damunka ka fad'a ba damuwa,
tayi maganar tana rik'e da kumatunshi, tunani yayi kamar na 10 seconds wanda ya sashi yin murmushi,
had'i da rik'e k'ugunta ya gyara mata zama sosai kan cinyarshi,
cike da yaudara Neehal ya kalli cikin kwayar idanta da narkakkun idanuwanshi,
yace " please ina san ki yafewa Najwah,
ki yafe mata Allah yana san mutane masu yafiya, masu saurin manta sharri suyi rik'o da alkhairi,
please karki yiwa mahifinta komai, karki ci masa mutunci saboda abinda 'yarshi tayi miki,
kar laifin Najwah ya shafi mahifinta ki tuna ko Allah baya kama wani da laifin wani,
please forgive her for my sake Neesah,
ajiyar zuciya Neesah ta sauke kana tace " zan yafe mata zan kuma janye kiran da nayiwa mahaifinta bisa sharad'i d'aya,
idan ka yarda....!?
Neehal ya kalle ta cike da mamaki yace " wanne iri sharad'i kuma....!?
Tayi murmushi tana shafa fuskarshi tace " marry me...!,
" what....!?
Neehal yace cikin kid'ima da rud'u, " yes mana ko ban kai ka aure ni bane....!?
"No...! No...! Neesah, I can't...! bazan iyaba,
yayi maganar duk ilahirin jikinshi na tsuma,
" Okey ba damuwa Neesah tace tana mik'ewa had'i da tab'a baki,
da sauri Neehal ya rik'e ta ya shiga rarrashinta yana bata baki,
har ta sauko tace " tou na yarda na yanje maganar aure amma bisa wani sharad'in,
da sauri yace " fad'i muji,
" ka fara yi min alk'awarin zaka yarda dashi,
shiru Neehal yayi na tsayin lokaci kana yace " okey ba damuwa,
Neesah tace " yau saura kwana tara biki na, ina san ka kasance saurayi na na kwana tara,
kafin aure na, idan har cikin kwanaki taran nan baka ji kana so na ba,
bazan matsa maka ba, zan auri Nabeel saurayi na wanda zan fara,
amma bisa sharad'in kayi alk'awari tsakanin ka da girman Allah,
zaka fad'i gaskiyar abinda ke cikin zuciyarka,
shu'umin murmushi mai cike da fassarori da dama Neehal yayi,
cike da izza, tak'ama da zallar yarda da kanshi yace " ba damuwa na yarda na amince,
daga nan suka shiga hira sosai kana Neehal yasa Neesah ta kira President a gabanshi ta fad'a mishi ta fasa san ganin Ubayyu,
sosai hakan yayiwa President dad'i dan shima ba'a son ranshi bane,
dan dai dole ne bashi da yadda zayyi yasa shi amsa mata,
daga villa house Neehal wajen Nauman ya wuce danya bashi labarin haukan Neesah na soyayyar kwana tara,
a parlor'n Mama ya iske Nauman yana cin abinci, kasancewar shima yanzu hankalinshi a kwance yake yasa shi zama yaci sosai,
bayan sun gama cin abincin suka fito harabar gidan suka zauna saman mota,
Neehal yace " kai wai kasan me....!?
"Ai dama tunda na ganka yanzu na san akwai labari bani nasha,
Neehal yana dariya yace " Neesah bata da hankali ina ga fa, kana ya shiga bashi labarin abinda ya faru tsakanin shi da nisa, yana dariya,
ido Nauman ya k'ura mishi har ya dasa aya kana Nauman ya sauke ajiyar zuciya gami da cewa,
" baka tunanin zaka iya fad'awa tarkonta....!?
Cak Neehal ya tsayar da dariyarshi kana ya kalli Nauman yace " what do you mean....!?
"Kana tunanin ni Neehal Bilal Lagosa zan fad'a soyayya da Neesah...!?
Cikin mamaki Nauman yace " me kake nufi da kai Neehal ko itama kana ganin kafi k'arfin ka so ta...!?
"Wallahi sosai ma kuwa, kamar ni Neehal ne zan so wannan abar mai kama da 'yar tsana,
mai zubin Babyn roba, kai baka tab'a ganinta ba ne...!?
Cikin al'ajabi da tsantsar mamaki Nauman yace " sosai ma,
ina following d'inta ma a Instagram da Twitter, yanzu wannan d'ince kake cewa kafi k'arfinta Neehal...!?
"Shin baka k'are mata kallo bane...!?
" Sosai ma kuwa ni da har zama kan cinya ta tayi, Allah babu abinda zanyi da wannan abar,
Allah ya kyauta ni Neehal Bilal Lagosa nayi dating da wannan wai dan hauka har da maganar aure,
turrrr wuce nan na wuce da saninta da tunanin ta wallahi,
idon Nauman ya k'urawa Neehal ya kafe shi da ido cike da zallar mamaki,
yace " yarinyar data fika wayewa, ilimi, bud'ewar ido,
yarinyar da tayi karatu a America, tayi huld'ar da kusan gaba d'aya jinsin duniya,
yarinyar da take da madarar kyau, Allah ya zanata ya bata halitta mai kyau,
Neehal me kafi yarinyar nan ko me matarka Najwah takai ta balle ta fita.....!?
Cike da izza da tak'ama gami da self confidence yace " wallahi na wuce auren Neesah nesa ba kusa ba, jikinta ko wanne tom & jerry ya gama gani,
yayi maganar in arrogant,
" ka wuce me, dame kafi k'arfin ta....!?
"Kaga idan kana santa go ahead ni zanyi maka jagora ma,
ido kawai Nauman ya k'urawa Neehal yama rasa me zaice mishi,
deep down yana tunanin hali da d'abi'un shi, idan yace yafi k'arfin Umaima da Umaina but how zaice yafi k'arfin Neesah ta ina ta yaya.....!?
Duk abinda yake tak'ama dashi itama tana tak'ama dashi,
kyau, kud'i, ilimi, gata, nasaba, da kuma alfarma wasu daga ciki ma ta fishi,
shi dai yasan babu abinda Najwah takai Neesah balle ta fita,
idon Nauman kan Neehal yace " WACCE IRIN MACE KAKE SO....!?
Cikin rashin fahimta yace " kamar ya, bayan Najwah har akwai wata mace da zan kuma buk'ata ne....!?
" Hummm kana bani mamaki Neehal idan kace Umaina da Umaima yara ne,
Neesah ai ba yarinyar bace, tunda zatayi sa'arka,
idan kace Umaina da Umaima 'yan k'auye ne basu waye ba, ai Neesah ba 'yar k'auyen bace,
duk inda mace takai Neesah ta kai, haka ma Umaina da Umaima suna da halitta mai kyau,
amma dukka kushe su,
ANYA NEEHAL KASAN SO....!?
"KASAN ZAFIN SO DA RAD'AD'IN SOYAYYA KUWA....!?
"KASAN ME AKE KIRA DA KALMAR SO, KA TAB'A D'AN D'ANAR ZAFI, K'UNA DA D'ACIN SO....!?
KASAN TRUE LOVE KASAN SOYAYYAR GASKIYA....!?
" An ya Neehal ba gigin yarinta da k'uruciya ke d'ibarka ba....!?
"Neehal anya baka da ZAB'IN RANKA, baka da tsarin zuben macen da kake so a can k'asan ranka.....!?
" Neehal na fara tunanin giyar k'uruciya ke d'ibanka amma har yanzu baka san so ba,
baka san me ake kira da so ba, tabbas akwai wani abu bunne cikin zuciyarka,
akwai abinda Allah kad'ai yasan meye shi a zuciyarka wanda ko kai da kanka baka san meye shi ba,
baka san meye a cikin zuciyarka ba, baka san meye binne a gefen zuciyarka ba,
kai kanka baka san waye kai ba, baka san meye b'oye cikin k'ark'ashin zuciyarka ba,
baka san meye so ba, baka san wa kake ainahin so ba, baka san ainahin meke cikin zuciyarka ba,
tabbas na tabbatar akwai wani abu gefen zuciyarka,
akwai abinda Allah kad'ai yasan dashi cikin zuciyarka kaima baka sanshi ba.
Tsoki Neehal yaja yace " kaji shirmen banza kai ban ce maka baka san meye so ba sai kai ne zaka ce ban san meye ba,
kai da baka da aure baka da budurwa kayya kamata a tambaya meye so,
amma ni tuni na wuce wajen Neehal yayi maganar yana dariya,
" hummmm Neehal kenan kana da ji da kanka, kana da tak'ama da kanka had'i da cika baki,
wallahi ka kiyayi rayuwa da illar so, ka kikayi mace, ina yi maka addu'ar kar Allah ya jarrabe ka da mahaukacin makahon so...!
kiran sallar da aka kwala ne ya hana su cigaba da maganar, lokaci d'aya suka kalli agogon hannunsu,
kana suka sauka daga saman motar suka shiga part d'in Nauman suka d'aura auwala suka nufi masallaci,
bayan sun idar da sallah Neehal yayi gida, a hanyar gida ya tsaya yayi take away,
kana ya nufi gida, tun daga harabar gidan Neehal ya fara ganin fasassun glasses zube k'asa,
ganin haka yasa shi tsayawa cak yana kallan broken glasses d'in kana ya kalli part d'in Najwah,
da sauri ya shiga part d'in ya iske Najwah zaune zaman dirshen a tsakiyar parlor'n,
wayar ta gabanta ta zubawa wayar ido tana kollo,
a hankali yabi parlor'n da kallo ganin duk wani abu ma glass dake parlor'n a fashe yake,
gaba d'aya parlor'n an fasa komai an tarwatsa komai, komai a hargitse yake,
hannun Najwah yana zubar da jini ta yayyanke sosai, gashin kanta buzu-buzu kamar tab'abb'iya,
ta d'aga pure red eyes d'inta ta kalli Neehal dake tsaye kamar an dasa shi ya kasa koda furta kalma d'aya,
a hankali ya ajiye ledar dake hannunshi ya k'arasa ga Najwah had'i da mik'a hannu da niyyar ya tab'a ta,
cikin k'araji ta yarfar da hannunshi gefe tana huci,
" lafiya meke faruwa dake .....!?
Yayi maganar kamar mai koyan magana danya tabbatar ba lafiya ba, deep down gabanshi na muguwar fad'uwa,
jikinshi na rawa kamar mazari,
batare da tayi magana ba ta mik'a mishi wayarta, hannunshi ma rawa ya amsa video ya gani wanda yasa gabanshi fad'uwa,
hannunshi na rawa yayi playing, zaune ya ganshi a sofa a villa house Neesah na zaune saman cinyar shi,
suna kallan kwayar idon juna, da alama kwararre masanin computer sosai,
yayi editing video domin daga inda Neesa tace " bisa sharad'in zaka aure ne, sai inda Neehal yace " eh na amince, na yarda, wato wajen dayace mata ya yarda da batun soyayyar kwana tara,
aka had'a da inda Neesah tace zaka aura ne sai abin yayi tamkar lokaci d'aya akayi maganar,
while Neesah na zaune saman cinyarshi hannunshi rik'e da k'ugunta,
wata irin razananniya fad'uwa gaban Neehal yayi, k'irjinshi ya buga da k'arfi, ya d'ago kanshi ya kalli Najwah dake rik'e da sharb'eb'iyar wuk'a idanta kanshi,
tana gurnani kamar zakanya ko bujumin sa,
a fili Neehal yace " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un dan yasan babu irin bayanin da zai gamsar da Najwah,
wuk'ar hannunta ta d'aga tana kallan Neehal kana ta nufi shi a haukace................!
Don't forget to vote,follow and comments
MOMYN ZARAH 'YARBAIWA