Free chapter · Read without an account

20

by Hauwa A Usman · RABO AJALI..

_*RABO AJALI...!*_


*HAUWA A USMAN*

_JIDDARH_


'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''


LITTATTAFAINA MASU ZUWA

SAKI RESHE...!

WATA SHARI'AR...!

DUK NISAN DARE...!

NISAN KWANA...!

NADIYA...!

ABU A HUDU...!

DA KAMAR WUYA...!

SAKI NA DAFE...!


2⃣0⃣



Da sauri Umairah tace " eh sosai ma, karatu sai kin zab'i wanda zakiyi,

Neelah na haki tace " zani...! zan biki birni ki saka ni a makaranta, 

dai-dai lokacin Abpa da Dada suka k'araso wajen, Neelah ta cigaba da cewa,

" ina san nayi karatu sosai, ina san na nunawa mutane masu k'amari da ji dakai,

had'i da shiga hurumin Ubangiji suna yiwa Allah shishshigi cewar babu wanda ya san gaibu sai Allah,

haka babu wanda ya isa yasan me gobe zata haifar sai Allah, ina san na tabbatar masa zan amfani kai na da rayuwata in sha Allah,

tayi maganar cikin zafin rai da bushewar zuciya,

kai da ganin yadda take maganar da yadda ta kafe idonta akan Umairah bata ko k'iftawa zai tabbatarwa mutum zuciyarta ta zama k'ek'ashewa,

kallan jama'ar da suka taho tare Umairah tayi had'i da had'iyar yawo kut,

saboda yadda Neelah ke magana ya tabbatar mata tabbas akwai wani abu dake cin zuciyar yarinyar,

cikin mamaki da tsoro Abpa yace " me...!?


"Neelah kin san me kike fad'a kuwa....!?


Batare data kalleshi ba tace " eh Abpa'am nasan abinda nake fad'a cewa nayi ina san tafiya neman ilimi

ina san nima nayi alfahari dakai na, kuma kuyi alfaharin haihuwata da kuma kasancewata 'yarku,

jikin Dada na kerrrrma ta k'arasa inda Neelah ke tsaye ta rik'e hannunta tana k'ok'arin janta,

kafewa Neelah tayi tak'i motsi, cike da jin kunya Dada ta d'ago kanta ta kalli jama'ar k'auyansu,

da sukayi cincirundo suna kallansu, d'an murmushin yak'e Dada tayi tana rik'o Neelah,

muryarta k'asa-k'asa tace " mu tafi bukkar mu, a hankali Neelah ta zame jikinta daga na Dada ta nufi Abpanta,

wanda ke tsaya yana kallanta, idonta kanshi tana zubar da hawayen bak'in ciki,

tace " dan Allah Abpa'am karka ce a'a, dan Allah karka hana ni tafiya neman ilimi,

yasha fad'a min bazan tab'a morar rayuwa ta ba, yasha ce min bazan tab'a amfanar rayuwa ta ba,

yasha ce min haka zan k'are cikin wahala da tsantsar bak'in cikin rayuwa,

dan Allah Abpa'am karka bari maganarshi ta zama gaskiya,

ko kana so maganar shi ta zama gaskiya.....!?


"Kana san na rayuwa cikin k'unci da bak'in cikin rayuwa....!?


" Kana san na zama marar amfani ta yadda bazan iya amfana da morar rayuwa ta ba balle har wani ya amfana daga gare ni.....!?


" Abpa'am kana san na zama marar amfani da mamora na k'are rayuwa ta cikin k'unci da takaicinshi.....!?


"Ko kana san maganganun shi su zama ajali na, bak'in shi ya zama sanadiyyar mutuwata bayan ga dama ta samu Allah ya kawo hanya mafi sauk'i da zan mayar da maganganun shi tamkar almara ....!?


Abpa'am muddin na cigaba da zama anan maganganunshi zasu zama gaskiya,

zayyi galaba akaina, dan nasan wallahi Allah bak'in ciki ne zayyi ajali na,

shiru Abpa yayi idonshi kanta, yana sauraran maganganunta

" sau d'aya tak a rayuwata Abpa ta na rok'e ka alfarmar yadda zanyi da rayuwata,

sau d'aya tak ina rok'okanka dan girma Allah Abpa ka barni nabi zab'in zuciya da rai na,

ka bari na bar wannan k'auyan da kowa ke kyamata kowa yake raba 'ya'yanshi dani suke hana su wasa dani, har suke neman camfani,

na zama tamkar mujiya, ku kanku sanadi na kun sha yin kukan bak'in ciki,

saboda ni kuka daina shiga taro, Abpa'am saboda da ni har sallah a masallaci dai na fita kayi,

k'asa-k'asa 'yan k'auyan suka fara maganganu suna cewa " oh! ji rashin kunya k'iri-k'iri wajen yarinyar nan dan Allah....!,

Saude tace " yo yarinyar data san dad'in namiji dama meye bazata yi ba,

wani yace " hummm ai kad'an ya gani ma, badai san abin duniya ne yasa ubanta ya bada aurenta ga wanda bai sani ba, ai idonta ya riga ya gama bud'ewa tarr bata da wata sauran kunya yanzu,

ido Abpa ya runtse da k'arfi yana jin zafin maganganun mutanen,

" dan Allah Abpa'am karka bari maganganunsu suyi tasiri a kanka da zuciyarka,

karka bari maganarsu ta rinjayi ranka, dan Allah kada ka kula da abinda zasu ce ko abinda suke fad'a,

babu abinda basu riga da sun fad'a ba, babu wata magana mai zafi ko bak'ar magana wacce ta rage basu jefe mu da ita ba,

babu wani abu da zasuyi ko su fad'a yanzu wanda zayyi mana zafi, balle har mu kula dashi,

sosai zuciyar Umairah da jama'ar da suka zo tare ta karye, cikin matsanancin tausayawa,

Umaira ta bud'e baki da niyyar yin magana, Abpa yayi saurin dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu,

fuskarshi a had'e murtuk yadda kasan bai tab'a yin dariya ba,

ganin haka yasa Neelah durk'ushewa k'asa had'i da fasa matsanancin kuka,

ta zube a gabanshi tare da kifa kanta saman k'afafunshi,

ta rik'e shi gam da duka hannayenta tana rusgar kuka da iya k'arfinta,

tana cewa " shikenan yayi nasara akaina, ya ci galaba akaina, tabbas muganganunshi gaskiya ne,

dayace bazan tab'a amfanar rayuwa ta ba, balle na amfani wani, 

yayi gaskiya dayace a haka zan k'are cikin wahala da tsantsar bak'in ciki tare da k'unci,

yayi gaskiya dayace bazan tab'a ci gaba a rayuwa ta ba, yayi gaskiya daya ce rayuwa ta bata da amfani, 

yayi gaskiya dayace....! kukan datake yi ne ya sark'eta ta kasa k'arasa maganar ta,

sosai ta cigaba da kuka tana cewa " mutuwa zanyi, wallahi Abpa'am Dada'am mutuwa zanyi,

rayuwa ta bamai tsayi bace, haka Allah ya tsara bazanyi tsayin rai ba,

ajali na a kusa yake, ta k'arasa maganar tana zamewa gefe,

Abpa ya kafeta da ido kwalla na gangarowa daga idonshi, dan sosai maganganun Neelah suka karya mishi zuciya,

while Dada na tsaye gefe batace komai ba, cikin karaya Neelah ta cigaba da cewa,

" dan Allah Abpa'am karka karya min kwarin gwiwa ta, karka bari gaba d'aya buri da mafarkaina su tafi a banza,

dan Allah Abpa'am ka cika min buri na, sau d'aya tak a iya tsayin rayuwa ta na tab'a rok'arka abu, dan Allah karka k'i yi min Abpa,

sau d'aya na tab'a nuna maka abinda raina ke so da zab'in rai na, a baya zab'inka nakasance ina bi, kuma zan kasance mai bin zab'inka har izuwa k'arshen rayuwata,

nayi maka alk'awarin duk abinda kace nayi shi zanyi, duk abinda kace na bari zan bari, 

duk abinda ka zab'arwa rayuwa ta shi zanyi, dan nasan bazaka tab'a cutar dani ba,

a hankali Abpa ya sauke ajiyar zuciya, gami da sanya hannu ya goge hawayen dake gangarowa saman kuncinshi,

kana ya d'ago Neelah suka fuskanci juna yace " kin tabbatar duk abinda nace kiyi shi zakiyi....!?


Da sauri ta d'aga mishi kanta, tana shashshekar kuka tace " ko karatun nan da nake mutuwar so kace na bari wallahi na hak'ura dashi har a tashi duniya,

kanta ya shafa yana murmushi yace " muje gida to, da sauri ta kalleshi suka had'a ido, kana ta kalli su Umairah dake tsaye, ta kuma kalli motarsu, 

ido ta lumshe da k'arfi hawaye na zubowa kan kuncinta, ta d'an d'auki lokaci a haka kana ta bud'e idonta, ta goge hawayenta 

had'i da kallan Abpa cike da karaya tace " muje....!,

yayi mata murmushi, itama ta mayar mishi da martanin murmushin,

suka wuce Dada ta bi bayansu, da k'arfi Umaira ta d'aga murya, tace " yanzu bazaka barta ba fisabilillahi duk irin biyayya da maganganun da yarinyar nan tayi maka...!?


Tayi maganar cikin rawar murya saboda tausayawa Neelah duk da bata san taimkamaiman abinda ya same ba,

cak Abpa ya tsaye had'i da juyowa ya kalli Umairah fuskarshi a had'e murtuk yadda kasan bai tab'a yin dariya ba,

a hankali Umairah tace " kayi hak'uri idan maganar dana fad'a tayi maka zafi, amma ya kamata ka duba lamarin yarinyar nan,

murmushi Abpa yayi kana yace " ba dole sai taje gida ta shirya ba, ko haka zata biki babu kaya.....!?


Baki Umairah ta bud'e cikin jin dad'i tana murmushi ta kasa furta koda kalma d'aya,

mahaukacin tsalle Neelah tayi tare da rungume Abpa tana kuka had'i dayin dariya duk a lokaci d'aya,

tana cewa " nagode Abpa'am, nagode nagode nagode sosai Abpa'am, murmushi yayi yana rik'e hannunta yace " muje ki shirya kar dare yayi muku a hanya,

" to..! Neelah tace tana saurin wucewa gaba, Dada dake gefe ta goge hawayenta tana murmushi tabi bayan su,

juyowa Abpa yayi ya kalli Umairah da jama'ar ta yace " muje mana akwai maganar da zamu yi daku ai,

tun kan Abpa ya gama rufe bakinshi Umairah tabi bayansu, jama'arta suka rufa musu baya,

bayan sun k'arasa bukkarsu Abpa ya kalli Dada yace " ku shiga bukkarta ki taya ta shirya kayanta,

Dada ta amsa da " to!, yayiwa su Umairah iso har cikin bukkarshi, ya zaunar dasu kana ya fita, 

bai dad'e ba ya dawo d'auke da kwaryar damammiyar fura da nono mai rai da lafiya da gashashshen nama,

ya aje gabansu yace " Bismillah, kana ya fito ya kawo musu ruwa, ya kuma fita, bai jima ba ya dawo, ya tarar sun cinye tas dan sunji dad'in abincin sosai, gefe ya koma ya zauna,

yana zama Dada da Neelah suka shigo, suma suka zauna,

kowa yayi shiru tsit ana sauraran Abpa, d'an gyaran murya yayi kana ya soma magana,

" baiwar Allah ya sunanki....!?


Yayi maganar hankalinshi kan Umairah, fuskarta d'auke da fara'a tace " Umairah,

" a wanne gari kike da zama...!?


"Ni 'yar garin kano ce, amma ina aure a garin Abuja, d'an shiru Abpa yayi kana yace " to! kin san dai yanzu zamani da duniya sun lalace,

ta yadda har baka iya tantance tsakanin mutumin banza dana kirki,

kwata-kwata amana da halacci sunyi k'aranci a wannan zamanin,

sai kayiwa mutum rana yayi maka dare, ko kaga mutum a rana ka jawo shi inuwa yayi k'ok'arin hankad'a ka cikin ranar,

wad'annan dalilan sune suka sanya zumunci, taimakon da tausayi sukayi rauni,

kowa yake ta kanshi daga shi sai 'ya'yanshi, haka ma mutune masu k'aramin k'arfi suke tsoran taimakawar wani, 

saboda yanzu mafi yawancin mutane basa yin abu dan Allah, nasan shiyasa kowa ya hana 'ya'yanshi a garin nan,

duk da nima Allah ya sani banyi niyyar barin Neelah ta tafi ba,

amma danaga tana so, kuma naga bakiyi kama da mutanan banza ba,

kallo d'aya nayi miki naji hankali na ya kwanta dake, na kuma samu nutsuwa, 

naji zan iya dank'a miki amanar tilon 'yata, saboda bakiyi kamata da maci amana ba,

bakiyi kama da wacce zata iya cutar da mutane ba, dan kamalarki ta nuna hakan,

na kuma tabbatar da bazaki cutar min da Neelah ta ba,

ya k'arasa maganar cikin sanyi da rawar murya idonshi kan Umairah yana karantar yanayinta,

murmushi Umarah tayi cikin tabbaci da yak'ini tace " mu ba haka muke ba,

kuma in sha Allah bazaka tab'a samunmu da cutar maka da 'ya ba,

zamu rik'e ta tamkar 'yar cikin mu, zaza mu bata ingantacciyar tarbiyya da kulawa mai kyau,

a fili Abpa ya sauke ajiyar zuciya tare da kiran sunan Umairah a hankali,

" Umairah, "na'am ta amsa, Abpa ya cigaba " ni Mus'ab na dank'a miki amanar tilon 'ya ta Neelah,

Allah da mala'iku da wad'annan mutanen su zama shaida a tsakanin mu,

na dank'a amanar Neelah a hannunki, ki d'auke ta tamkar 'yarki ta cikinki wacce kika durk'usa kika haifa da kanki,

wacce ta tsaga jikinki ta fito, wacce ta kwanta a cikin ki, ko k'anwarki da kuke uwa d'aya uba d'aya,

ki kula da ita kamar yadda zaki kula da kanki, ki bata ingantacciyar tarbiyya kamar yadda zaki bawa 'yar cikinki,

kiji tsoran Allah akan komai ki tuna fahimmancin alk'awari da amana,

duk abinda tayi ba dai-dai ba ki tsawarta mata, ki rink'a nuna mata dai-dai da wanda ba dai-dai ba, 

kiyi min alk'awari zakiyi duk abinda nace, sannan kiyi min alk'awarin ke da kanku zaku rik'e ta, a hannunku zata zauna, dan Allah dan na k'ara samun nutsuwa da kwanciyar hankali,

dan bani da kowa a duniya daya wuce Neelah da mahaifiyarta,

Neelah ita kad'ai ce 'yata dana ke gani, cikin sanyin jiki Umairah ta had'iyi yawu tare da fitar da numfashi, 

tare da jinjina kai tace " nayi maka alk'awarin zan rik'e Neelah hannu biyu kamar 'yar ciki na ko k'anwata,

nayi maka alk'awarin zan kula da ita, zan bata kulawa, zan zame mata uwa mahaifiya,

zan zame mata abokiyar shawara har iyakar rayuwar ta, idan kuma hankalinka bai kwanta ba kana iya bin mu ka gano inda muke zaune,

murmushi Abpa yayi kana yace " a'a ba sai na biku ba, kallanshi ya mayar ga Neelah yace,

" kiji tsoran Allah a dukkan lamauranki, ki rik'e Umairah uwa mahaifiya sannan kuma yayarki,

kada ki sake ki sab'a umarninta, ki zauna da ita da tsarkakekkiyar zuciya, bisa gaskiya da amana, kada ki sake ki ci amanarta ko kiyi mata butulci,

idan kika sake kiga ci amanarta ko kika butulce mata bani babu ke duniya da lahira,

da sauri Umairah ta d'ago ta kalli Abpa taga tsakanin shi da Allah yayi maganar,

ya d'ora da cewa " saboda gaba d'aya mutanen duniya duk kusan hali da d'abi'un mu d'aya ne,

ayi mana alkhairi mu saka da sharri, a jawo mu jiki ayi mana komai na rayuwa daga k'arshe muyi butulci, 

cikin kuka Neelah tace " in sha Allah Abpa'am bazaka tab'a samu na da laifin butulci ko cin amana da ha'inci ba,

" kuje Allah yayi muku albarka, ya tsare ki da tsarewarshi, ya kare ki daga dukkanin sharrin abin k'i,

Ubangiji ya had'a ki da dukkan alkhairi da nasarar rayuwa ya musanya miki da sharrin dake cikin tafiyar nan zuwa alkhairi,

Allah ya baku hak'urin jure zama da junanku, duk aka amsa da amin, ya kalli Umairah yace " to sai ayi ta hak'uri zama da yaro sai hak'uri,

" bakomai, cewar Umaira, Abpa ya kalli Dada yace " kina da abinda zaki ce....!?


"A'a ka gama fad'ar komai, sai dai nace Allah ya tsare, ya kaisu lafiya, har bakin mota Abpa da Dada suka raka su Umairah, Neelah, na kuka, Dada da Abpa na hawayen rabuwa da ita,

hakanne ya tabbatarwa da Umairah akwai soyayya da shak'uwa mai k'arfi tsakanin Neelah da iyayenta,

yayinda da tausayinsu ya kama Umairah sosai, har suka bar k'auyen Sunkhanni, Abpa da Neelah suna d'agawa juna hannu.


Har suka k'arasa masaukinsu a cikin garin Taraba Neelah nata aikin kukan rabuwa da iyayenta,

sosai Umairah ta rink'a rarrashin Neelah tare da kwad'aita mata karatun,

har dai ta samu tayi shiru, cikin rarrashi Umairah ta sanya Neelah tayi wanka ta sake kaya kana tayi sallah,

ko da dare yayi tare suka kwanta akan bed dan harga Allah Umairah tana da sauk'in kai da sanyin hali,

kwata-kwata bata da k'amar mutane ko jin kyankyaminsu, ba ruwanta da wulak'anci,

ita kowa nata ne, kodan ita 'yar talawa ce oho, a hankali Umairah ta shafa kan Neelah cike da tsantsar tausaya mata,

deep down tana jin mugun so da k'aunar Neelah na shiga ranta da zuciyarta,

dan tunda taga Neelah taji tana santa tsakani da Allah, while ita Neelah babu abinda take saukewa cikin baccinta sai ajiyar zuciya da shashshekar kuka,

da sassafe Umairah da Neelah suka shirya driver ya d'auke su yakaisu airport,

batare da b'ata lokaci ba aka yankar musu ticket d'in Abuja,

k'arfe sha biyu na rana suka dira garin Abuja, direct gidanta ta wuce, 

tun daga airport Neelah ta saki baki cike da k'auyenci tana ta kalle-kalle,

bata gama tsinkewa ba sai da taga a irin mahaukacin gidan da driver yayi parking,

cike da gajiya Umairah ta fito ganin Neelah bata da niyyar fitowa yasata cewa " fito mun zo gidan,

ido Neelah ta zaro cike da matsanancin tsoro da tashin hankali had'i da k'auyenci tace " nan gida ne....!?


Kallanta Umairah tayi tana murmushi tace " uhmmm, ido waje Neelah tace " anan zamu zauna....!?


"Eh mana, cewar Umairah, cikin tsoro Neelah tace " kin tabbata nan ba gidan yankan kai bane....!?


Sosai maganar ta bawa Umairah dariya, ta rink'a dariya ,

marairaice fuska Neelah tayi tana k'ok'arin yin kuka tace " Abpa'am amana ta ya baki dan Allah kada ku yanka ni,

ganin yadda tsoro ya kama Neelah sosai yasa Umairah daina dariyar tace " babu abinda zanyi miki, dan kin zama k'anwata,

fito mu tafi, Umairah ta fad'a tana mik'awa Neelah hannu, yawo Neelah ta had'iye cike da tsoro gami da d'ora hannunta saman na Umairah,

ta fito, hannunta Umairah taja suka shiga cikin gidan, suna shiga Naufal yana fitowa daga shi sai 3 quarter da rigar red tag,

fuskarshi d'auke da fara'a yana dariya, yayi hugging Umairah yana cewa " I really misses you so much my heartbeat,

hugging d'inshi itama tayi tana dariya tace " I missed you too dear,

tsananin tsoro, tashin hankali da zallar fargaba ne yasa Neelah sandarewa a tsaye,

dakyar ta soma jan k'afarta tana yin baya had'i da girgiza kanta ,

cikin k'ank'anin lokaci hawaye ya soma ambaliya kan kuncinta,

nuna Naufan ta shiga yi da hannunta cikin rawar baki tace " kai ne bak'on birni.....!?


Tayi maganar tamkar zararriya, idonta cikin na Naufal tace " tsakani na dakai Allah ya isa ban yafe maka har abada, ka cuce ni ka cuci rayuwa ta,

ta fad'a tana nuna shi, tana gama fad'ar maganar ta juya ta fice da gudu...............!







MOMYN ZARAH    'YARBAIWA

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol