Free chapter · Read without an account
Chapter 7
CIWON 'YA MACE
By
Fadila Lamido
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
Page 13-14
Saidai ta na daf da isa gurin ta ga motar ta tashi dan haka ta tsaya cak a daidai lokacin da ta jiyo Yaya Bashir yana kiranta. Juyowa ta yi cikin da sauri ta ke kokarin isa gurin tare da cewa acikin zuciyarta "Kodai dama idona ne ya nuna mani kamar ya kira ni." Da irin wannan tunanin ta ta koma cikin Mamy batare da tabar waiwayen bayantaba, har yanzun ta na mamakin zuwan Poul wannan gurin.
Hotona suka kara yi bayan sun gama suka wuce gida, suna isa gidan ma samunsa su ka yi cike da jama'a, Aunty Saratu ce ke kula da bakin, gaba daya dangin cike suke da farin ciki tare da sha'awan Nur tare da ganin kazonta, ga uwa uba nutsuwa da hankalin dake gareta.
Shima Abba sosai ya yi farin ciki saidai a kasan zuciyarshi ya na da wani tunani akan Nur; ganin inda kwana biyu yanayinta yake kokarin canzawa daga kyawawan dabi'u zuwa munana.
Ita ko Mamy a yau kallon tsananin kauna ta ke ma Nur; duk da cewa ta canza amman tasan wane ne sular canzawan na ta.
Washegari Nur ta tashi da tsananin gajiya lokacin da ta isa dakin Aunty Saratu zama ta yi cikin nuna gajiya. Kallonta aunty Saratu ta yi sannan ta yi murmushi tare da cewa "Ai zuwana uku kina bacci"
"Da kin tashe ni Aunty, ina tashi naji kamar an kwashe min 'ya'yan hanjina." Mikewa Aunty ta yi tare da fadin "Duk sabo da yunwar? Ai sai ki yi maza ki je ki karya ni na azama zaki makaranta ne"
"A'a saida yamma zani" Nur ta fada tare da gyara zamanta. Adaidai wannan lokacin Abdallah ya shigo dakin, sai dai ganin Nur yasa ya dan yi jimmm kadan, sannan ya shigo ya zauna tare da fadin, "Aunty ina son na yi magana da ke" Kallon Abdallah Aunty ta yi sannan ta mike ta isa kujeran da Abdallah ya zauna ta zauna gefen sa tare da cewa "Ina jin ka" Juyowa yayi ya kalli Nur ya ce "Baza ki bamu wuri ba ?" Kallon shi Nur ta yi sannan ta mike ta na kokarin fita taji ya ce, Kina kallona ne da wasu dakwa-dakwan idon ki kamar na mage, kallon aunty Saratu ya yi sannan ya nuna Nur tare da fadin "Wai dan Allah aunty kuna ganin abin da nake gani kuwa?" Jin haka yasa Nur ta tsaya cak, itama Aunty Saratu cike da mamaki ta ce me ye shi? "Jibeta fa kamar sanda daka kalleta babu abin da kake gani sai dai katon hanci da wasu manyan abubuwa da suke jan ta" Kirjinsa ya nuna da hannu dan haka Aunty ta yi murmushi kadan tare da cewa, "Nur ki je abinki" Wucewa ta yi a hankali tanajin lokacin da Aunty ta ce "Abdallah kenan, baka da dama"
"Wallahi Aunty da ka kalleta su kawai kake gani abun ko tsari babu, ko ta ina yariyar nan bata da hali, a baya tausayinta nake ji, yanzun ko dana kalleta saina rasa da wacce dambar zan kwatanta ta sabo da muninta da nake gani." Runtse ido Nur ta yi sannan ta wuce, sosai ta yi dana sanin sauraron kalamansa, cike da damuwa ta koma dakinta, a cikin zuciyarta ta ce, "Wato sabo da tsabar muni na ya rasa dambar da zai hadani da ita, hawaye ne suka zobo mata tasa hannu ta share sannan ta mike ta isa gaban madubi, kallon kanta take acikin madubin tare da rike hancinta sannan tace afili, "Mene ne wasu abubuwa da suke janna? Zan so nasan meye shi wannan abin dake jana" Kiran da taji Aunty Saratu na mata ya sata share hawayen sannan ta nufi dakin.
Wayar Abdallah ta miko mata tare da fadin, "Abdallah ne ya manta awayar shi, gashi ana ta kiran shi, ki kai mashi ya na gidan su Auwal."
Amsa ta yi sannan ta fice a dakin, dakinta ta koma ta sanyo babban Hijjabi, sannan ta daura nikabi ta rufe fuskarta, fitowa da ga cikin dakin ta yi tare da kallon wayar, wannan ne karo na farko da ta fara ma wayarsa kallon kurulla, tsintan kanta ta yi da danna wayar yayin da wani kyakyawan hoton budurwar yariya ya bayyana, sosai kyan yariyar ya dauke hankali Nur; har ma ta fara tunanin inama ace takai ta kyau, wani abin da ya kara bata mamaki wayar a bude take, cikin sauri ta shiga danna wayar, cika ta yi da mamaki lokacin da ta ga mutanen da yai waya da su daren jiya, duk sunayen mata ne har su tara, Kuma ko wacce ya dauki tsayon lokacin yayin da yai waya da ita, gurin adana hoton cikin wayar ta nufa, ta fara dubawa, nan ta fara cin karo da hotonanshi dare da taurarin finafinen Hausa mata da maza, tun da ta bude bakinbta ta kasa rufewa sabo da tsabar mamaki, tunani ta shiga yi shi kuma me ye ya hadashi da Yan fim din Hausa ko shima ya na fitowa ne aciki ko kuma Fim din yake son ya fara, gefen videos ta gani ta na kokarin shiga gurin taje motsin tafiya dan haka tai sauri ta maida wayar cikin hijjabinta tare da fitowa daga cikin falon. Mamy ta gani ta na fitowa daga dakinta bayan sun gaisa Mamy ta ce, "Ke zani in tado ashe kin tashi ma."
"Na tashi Mamy, zan kaiwa Yaya Abdallah wayarsa gidan su Yaya Auwal" Ajiyan zuciya Mamy ta yi tare da cewa, "To yi maza ki dawo" Juyawa Nur ta yi ta fice da sauri take tafiya domin yunwa ke kwakular cikinta.
Tafe take tana sake-sake cikin zuciyarta akan wayar da ta ga yayi cikin dare, kenan baya bacci koma ya na yi to bana kirki bane, sannan ganin shi cikin yan fim yasa ta fara tunanin domin dama batasan aikinsa ba tasan dai ya na zuwa Office amman bata San me ya ke acan ba, wata zuciyar ce ta ce kila dai yana zuwa gurin yan matanshi ko abokanshi amman Abba nasan bazai barshi yayi wasan Hausa ba.
Tsakanin gidan su dana su Auwal babu nisa, dan haka nan danan ta isa, ta na tura get din gidan ta hangi takalman maza da yawa a bakin kofar wannan ya tabbatar mata da suna da yawa acikin dakin.
Bakin kofar ta tsaya ta rangada sallama cikin zazzakar muryanta, da ga cikin dakin ta ji an amsa ganin babu wadda ya fito Kuma babu motsin tafiya ya sata sake yin Sallama yayin da aka sake amsawa daga ciki tare da cewa shigo mana.
Yamutsa murya Nur ta yi sannan ta tura kofar tare da shiga cikin dakin, suman tsaye ta yi ganin Sumayya zaune Yaya Abdallah ya daura kansa akan cinyanta, idon shi rufe yayin da Sumayya ke wasa da kasunbarsa, kasa cire idonta ta yi a kansu, ta na mamakin wannan lamarin bakinta sake. Ita ko Sumayya tun da suka hada ido da Nur tai saurin cire hannunta a jikinshi tare da rasa abin yi.
Da ga bayanta ta ji ance, "Abdallah ga kanwarka." Da saurinshi ya bude idonsa tare da waigowa ya kalli Nur sannan ya fara kokarin tashi zaune yana me cije lebenshi na kasa, bayan ya tashi zaune ma saida ya damki sumarshi sannan ya ce, "da ga ina? Me ya faru?" Kawar da kai Nur ta yi sannan ta fito da hannunta da ga cikin hijjabin ta mika mishi wayar tare da cewa "Inji Aunty" Hannu ya mika ya amsa dan haka Nur ta juya da nufin ficewa a dakin, sai a wannan lokacin ta kula da wasu matan dake gefe su biyu tare da Auwal da wasu abokan nasu guda biyu. Cikin sanyin jiki sosai ta fice a falon a daidai lokacin da Abdallah ke cewa, "Inazuwa karki wuce, ki jira ni anan kinji" A harabar gidan ta tsaya nesa da dakin kadan, fitowan Sumayya ta gani dan haka ta bita da kallo, babu abin da ke daure mata kai kamar wannan al'amarin, wannan lamarin shine mafarin gigicewarta domin kuwa Sumayya tana da aure da yaranta biyu, "ina ta baro mijinta ta taho nan gurin? Anan ta kwana? Ko kuwa da safe tazo? Mijinta baya gari ne? Ko kuma yana garin amman ta tsallakeshi ta fito ta na dakunnan gemon katon kawai? Yaranta fa? Shiryasu ta yi suka tafi makaranta ko kuwa?" Nur ke tambayan kanta, ganin babu me bata waddan nan amsoshin ya sa ta sakin ajiyan zuciya tare da dauke idonta akan get din gidan.
Adaidai wannan lokacin Yaya Abdallah ya fito har ya kawo inda take bata motsa ba, cikin daure fuska ya ce, "Mu je" Gabanshi ta shiga ta fara ta fiya da sauri, ganin haka Abdallah yai saurin cewa "Ke tsaya" Nan take ta tsaya tare da kallon shi, kawar da kanshi yayi tare da cewa, "Me kike son nasiya miki?" Kawar da kai ta yi sannan ta ce, "Babu komai" Yawo ya hadiye sannan ya ce, "A'a mu je na siya miki wani abu mana" Shiru ta mai har suka isa kofar gidan, cikin bada Umarni ya ce, "Tsaya a nan na dauko mota mu je ki zabi abin da ranki keso ko nawa ne zan biya" Turo bakinta ta yi gaba tare da cewa "Yunwa nake ji bari naje naci abinci tukuna"
"Ki tsayani nace ko" Abdallah ya sake fada cikin yar tsayawa.
Dole ta tsaya, domin ba yadda ta iya dashi, cikin gidan ya shiga ya fito da mota duk tana tsaya kawai tana binshi da kallo, "Shiga" Abdallah ya fada cikin bada Umarni, wannan karon ma shiga ta yi batare da tace komaiba,. sannan ya daga waya ya kira Mamy ya sanar mata da in da za su sannan ya sauke wayar yana satan kallon Nur.
Koda suka isa dankareren kantin da kanshi ya zabar mata kayan shafa da turaroka, sannan ya ce, idan akwai abin da take so ta dauka. Kallon shi kawai ta yi ta kauda kai bayan sun fito a gurin suka dauki hanyar komawa, ganin sun kusa gida ya waigo ya kalli Nur tare da fadin "Na miki siyayya bakice min kin gode ba? Can kasa-kasa Nur ta ce, "Na gode" Murmushi ya yi kadan sannan ya ce, "Ko ke fa? Kanshi ya shafa sannan ya ce "Nasan kiga Sumayya ko?" Kai Nur ta da ga alamar eh, Abdallah ne ya cigaba da cewa "Ta yiwa su Mama kara ne tazo duba jikin Auwal, kinsan ya kwana biyu babu lafiya" Sanyi jikin Nur ya kara; daker ta iya da ga kanta ta kalleshi. Ganin haka Abdallah ya yi ajiyan zuciya sannan ya ce, "Amma dai duk da haka karki fada ma Mamy, kinsan har yanzu ba dadinta nake ji ba, tun akan wancen batun da aka gaya miki karya ki ka hau kai kika zauna, ki ka kasa yiwa yi min adalci alhali hakan ba gaskiya ba ne, kuma kinfi kowa sanin ba halina bane, dan haka ina rokon ki dan Allah kada ki gayawa kowa.
Ta gefen ido Nur ta sata kallon shi sannan ta ce, "To" Numfashi Abdallah ya fesar sannan ya ce "Kin min alkawari?" Wannan karon kai Nur ta daga a dai-dai lokacin da suka shiga gida, kokarin Bude motar ta fara Abdallah yayi saurin cewa, "Nur nasan halinki ke din kina da sirri, kuma bakyacin amana" Wannan karon ma dai Kai Nur ta daga sannan ta fice acikin motar.
Lokacin da Nur ta shiga gida kallon mamaki Mamy ta yi mata, ganin ta rike da ledoji ga kuma Abdallah da ke binta abaya. Wani shashin na zuciyarta ne ya tuna mata baya kadan, dan haka ta kawar da tunanin komai. Abdallah ko bebar falon ba Saida ya ga Nur ta gama cin abinci ta kwashe ledojin siyayyar da yai mata ta shige dakinta.
Washegari ta kama Moday dan haka Nur da wuri ta wuce makaranta.
***
"Abdallah wai yau lafiya kuwa? Yanayin ka kamar mara lafiya" Mikewa yayi tare da fadin, "Bacci ne be isheni ba Mamy Sam ban rutsa ba" Da kallo Mamy ta bi shi sannan tace, "Kuma kace lafiya lau kake?" Yana Shirin barin dakin ya ce, "Eh banajin ciwo sam." Bayan ya fito kofar gida wani ajiyan zuciya ya sauke sannan ya ce afili, Tun da har ta fita bata gayaba nasha in sha Allah, hannunshi ya mika ya shafa suman shi sannan ya sake cewa dole tabar gidan nan, akullum kara tsanarta nake yi ta takura ni da yawa" Saman motarshi ya zauna tare da neman hanyar dazai yi maganin matsalar da take Shirin fin karfinshi
****
Nur da Helen akan hanyar su ta dawowa daga makaranta, da kafa suke tafiya yayin da Nur ke cewa "Helen ki dago kafa mana, yau naga kina nafiya ne lakakai-lakakai.
"Wlh yunwa nake ji Nur, kwana na uku basa wani kwakwaran abinci a cikina ba" Da sauri Nur ta kalleta tace "Sai me to?" Cikin halin ko in kula ta ce, "Ya ce bashi da kudi me gidan, kudin dake hannun Mamma kuma duk sun kare" Lumshe ido Nur ta yi sannan ta ce "Matar shi fa?" Hmm suna yin abincin su suci..." Tun kafin ta rufe baki Nur tace, "Wannan ba daidai ba ne, shiwai bejin tsoron Allah ne, kato dashi ya na yiwa Maman shi horon yunwa? Na ga baya jin tsoro ko shakkar mama, shiyasa ada bana yadda idan akace itace mahaifiyarshi, ya kamata asamu wani yayi mai wa'azi.wai ku baku da wani Malami ne da zai nuna mishi mahimcin iyaye?"
"Hmmm, Mamma ta hakura da zama tare dashi, ta ce kudin mota kawai take nema mu koma Kauyen su, Nur kila karatu na zai tsaya kwanan nan"
Sosai maganar ta doki zuciyar Nur cike da tausayawa tace "Karki yi wasa da karatunki, gara kuci gaba da hakuri, ko Kuma ku dawo gidanmu ku zauna idan har kun gaji da zama anan"
"Mamma ta gaji Nur, kullum ta na kuka bata baccin kirki, idan ya ga tabar kusa dashi za'a iya samun saukinshi"
"Ni dai karku tafi Helen, yanzun kizo muje gidanmu kici abinci kafin kije gida"
"Da sauri Helen ta kalli Nur ta ce, bazan iya zuwa ba bayan nasan mama bataci ba, bama ta da lafiya tun shekaran jiya"
Adaidai lokacin da suka kawo kofar gidan su Helen din Nur ta ce "Mu je to idan kika ce saiki kamai Mama nata"
Jin haka yasa Helen tabi Nur sai dai Koda sukaje bata tsaya ci ba zuba mata a ka yi ta tafi dashi.
Bayan tafiyan Helen ne Nur ta bawa su Mamy labari halin da su Helen suke ciki, sosai suka tausaya ma su, saidai mama na tsoron taimakonsu saboda Poul ba kirki gareshiba
***
Washegari misalin karfe 04:12pm Abdallah ne zaune a gaban Abba, tun da Abba ya kirashi a waya ya zufa taki tsayawa har yanzun da yake zaune a gaban Abba, zallar bacin rai da damuwa kawai ya ke hanga a fuskar Abba, dan haka hankalin shi ya tashi sosai, kosawa yayi yaji dalilin kiran, sai dai Abba yaki kallonsa sai aikin Bude takardu yake kuma fuskarshi babu wasa ko kadan acikinta, rabon da yaga fuskar Abba haka har ya manta saidai wata zuciyar na ce mishi kila zato ne kawai yake yi, yayin da wata zuciyar ke tuna masa da matsayin Nur a gurin Abba, Sunanshi da yaji Abba ya kira shi ya katse mishi tunanin azabure ya dago ya kalleshi..