Free chapter ยท Read without an account

39

by Hauwa A Usman ยท Kโ€™ADDARA TAH

'''K'ADDARA TAH!!!'''


    ๐ŸŒน

   ๐ŸŒน๐ŸŒน

  ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

  ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

 ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน



      ~NAH~



*HAUWA A USMAN*

     _(JIDDARH)_




*๐ŸŒˆKAINUWA WRITERS ASSOCIATIONโœ๐Ÿป*

     _(DASHEN ALLAH)_




_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ฦ™ai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da K'assai_


*EDITING BY MOMYN ZARAH*


39


Wani mahaukacin ihu Aisha tayi, tayi kansa tana kuka " please karka mutu idan ka mutu Aunty na bazata iya jure rashin ka ba, itama mutuwa zatayi, ganin baiko motsa ba illa dafarar dake zuba a bakin sa, yasa yin waje tana ihu, " Abba please ku taimake wallahi mutuwa zaiyi idan ya mutu Aunty ma mutuwa zatayi, ko kallan ta Abba baiyi ba, sai Baba ne yace " subhanallah ya juya direct doctor office ya nufa, da gudu nurses suka d'auke a gadon marasa lafiya sai Emergency. 




Da kyar Aisha ta bar asibitin sai da Abba ya b'ata mata sannan suna shiga gida Fauziyyah ta jiyo kukan Aisha da gudu ta fito, tana tambayar ta lafiya, cikin kuka Aisha ta fad'a jikin ta, murya na rawa tace " Aunty Fa'iz ya mutu..... Wani irin ihu ta saka wanda kusan duk unguwar kowa yaji, kanta ba d'an kwali tayi waje da gudu tana ihu kamar zararriya, duk ta fita haiyacinta Abba da Baba, Mama, Umma ido kawai suk bita dashi duk sun kasa magana shiko Sadik mutuwar tsaye yayi, saboda tsabar rud'ewa,dakyar yake iya jan numfashi, gaba d'aya duniyar tayi masa nauyi, kansa sai juywa yake, bibbiyu yake gannin komai, baya jin komai a kunnuwsa sai shuuuuuuuu.




Kafad'ar Sadik Aisha ta kama ta shiga girgiza shi tana kuka" please yaya ka taimaka Aunty fa ta fita kar tayi wani wajen takai 3mnts tana yi masa magana amma bai ma san tana yi ba, sai data girgiza shi karfi ta sakar masa kuka sannan ya dawo haiyacinsa, cikin firgice yake kallon Aisha yana jin abinda take fada yana kuma tuno abunda ya faru, Aiko da gudu ya fita ya bi bayan ta, dakyar ya gano ta a titi tana ta shara gudu kamar mahaukaciya bata san inda kanta yake ba, batasan inda take nufa ba, saura kiris mutu tabi ta kanta cikin zafin nama Sadik ya rik'o ta ta fada jikinsa, suka zube a k'asa, k'uuuuuuu mai motar ya taka birki, a hankali ya mik'e rik'e da hannunta yayi gida da ita, itako binshi kawai take dan kwata-kwata bata cikin haiyacinta. 




Yana shiga gida rik'e da hannunta bai tsaya ko ina ba sai da d'akinta a bakin gado ya zaunar da ita, ya mik'e ya d'auko mata ruwa ya bata tasha ta sauke ajiyar zuciyar, kusa da ita ya zauna ya jawo ta jikinsa ya rungume ya kwantar da kanta a kan kirjinsa, kawai shima sai ya fara kuka, dan sai yanzu ya tabbatarwa kansa san masu wani yake, sai yanzu yasan kwata-kwata Fauziyyah bata sanshi, gangan jikinta kawai ke tare dashi ruhinta yana ga Fa'iz, sai ya tausayawa kansa, a hankali ta d'ago kai ta kalle shi, cikin sanyin murya tace" yaya kuka kake? 



Murmushin k'arfin hali ya k'ak'aro, ya girgiza mata kai alamar a'a, kanta ta k'ara mayarwa cikin k'irjinsa ta kwantar tace " yanzu yaya shike nan Fa'iz ya mutu tayi magana kamar ana fisgarta daga bakin ta, shiru yayi dan bai san amsar da zai bata ba, dan shi kanshi bashi da tambaci akan rayuwar Fa'iz ko mutuwar sa, kanta ya shiga shafa mata yana d'an bubbuga mata bayan ta, a haka har wani wahalallan barci yayi gaba da ita badan ta so ba, yana ganin tayi barcin ya mik'e ya kwantar da ita a hankali ya fita. 





Yadda yabar kowa haka ya same su, illa Umma data tafi gida sai Mama data shiga d'aki, anan ya iske Abba da Baba sai Aisha dake ta faman kuka, a tsaye, kai ya sunkuyar zai fita, a hankali Abba ya kira sunanta, tsayawa yayi cak, dan shi kwata-kwata bai so hakan ba so yayi a kyale shi kawai ya tafi yayi jinyar zuciyar sa, da kyar ya amsa Abba yace" kayi hak'uri Sadik nasan kana da mutuk'ar hak'uri kuma kana mugun san Fauziyyah in sha Allah Fauziyyah bata da wani miji dana wuce kai koda bayan rainane, na baka amanarta, ka kula da ita, karka kula da duk wannan abubuwan dake faruwa, ni ne dai mahaifin Fauziyyah kuma na baka ita duniya da lahira idan Fauziyyah ta auri wani namiji bakai ban yafe mata ba, sai dai idan kaine kace ka fasa aurenta ko baka santa, cikin sanyin jiki yace " nagode Abba, ya fita shima Baba jiki ba kwari ya fita yayi gida, koda Sadik ya shiga gida d'akinsa ya wuce ya fad'a katifarsa ya saki kuka mai ban tausayi.




Jikin Mama a sanyaye ta zauna kusa da Abba, shima cikin mutuwar jiki ta d'ago kai ya kalle ta yace " Maman yara ya akayi ne? shiru ta d'anyi sai tayi ajiyar zuciya tace" Abba ni kuma sai nake kamar muyi tunani kar muyi gaggawa kar muyi abinda zai dame mu, "kamar me fa? cewar Abba, " ina ganin kamar idan akayi auren Fauziyyah da Sadik a halin da ake ciki akwai matsala, kar muyi abinda zai zo ya damemu daga baya, kaga mune masu 'ya mace duk abinda zai faru mune a k'asa, kuma mutanen nan sunyi mana halaccin da ko d'an uwan mu bai mana ba, kar mu had'a auren Fauziyyah da Sadik azo asamu matsala zumunci yazo ya lalace tunda ni da kai da shi kanshi Sadik da kowa ya tabbatar da Fauziyyah bata san Sadik, Fa'iz take so, kada azo ayi aure a rink'a samun matsaloli har komai ya lalace. 




Kuma ni ina ganin yanzu Fa'iz ya shiryu, duk inda ake neman mutumin kirki yakai, ya zama malami makaranci kuma kowa shaida ne akan irin mugun son da yake yiwa Fauziyyah, ji fa mawuyacin halin daya shiga akan 'yar mu, mu tausaya masa mana, mu duba yadda ya koma, duk a kanta yace bashi da kowa sai mu sai Fauziyyah yace ita ce kowa da komai nasa, ni dai a gaskiya ina ganin gwara a bashi a barsa ya k'arasa b'arnar da yayi, ba sai mun tonawa kanmu asiri ba, hakan ma kad'ai na iya haifar da matsala, rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali a zaman takewar auren su, kasan fa budurci mahimmin abu ne mafi girma arayuwar mace da aurenta, amma dai yadda ka gani ni dai shawara ce tawa, duk maganar da Mama keyi Abba ya k'ura mata ido baya ko k'iftawa, ita ko tak'i fasawa harda saida takai aya, shiru duk sukayi sai Mama ce tace " Abban yara ko baka ji nane, murmushin su na manya yayi yace " duk naji, amma indai ni ne mahaifin Fauziyyah to bata da wani miji sai Sadik,Shiko Fa'iz abinda yayi ne a rayuwar sa yake girbar abinsa, ai dama ita duniya ta gaji haka, kamar yadda Fa'iz yake tak'amar yana san Fauziyyah haka Sadik yake santa shima, haka ma ya fad'a masa a gaban mu (duk yadda kake ji akanta nima ina jin fiye da haka) ki duba halin daya shiga yanzu duk ya fita haiyacinsa, kuma ma ai da kunya na kalli idon Malam Bala nace masa na fasa bawa d'ansa auren 'yata Fauziyyah, dan dai ku mata baku da hankali da kara akan 'ya'yan ku, ai mu muna dashi, wallahi koda mutuwa zatayi idan ta aure saita aure shi sai dai ta mutu,wallahi Allah koda shi da kansa Sadik din ne yace ya fasa bai isa ba, Mama zata k'ara yin magana Abba ya d'aga mata hannu ya dakatar da ita yace " ya isa na riga na gama yanke hukunci. 




Shiru Mama tayi bata kuma magana ba, ta mike ta fita tabar mai dakin ya bita da kallo a ransa yana mamakin irin sankai na mata a kan yaran su, saboda san da iyaye mata suke yiwa yaran su zasu iya rufe ido suyi komai, Mama na fita d'akin Fauziyyah ta wuce bacci ta iske ta tanayi sai ajiyar zuciya take yi, murmushi Mama tayi tace " Allah yayi miki mganin matsalarki da damuwarki, Ubangiji yayi miki zabin alkhairi ta shafa kanta ta fita. 




 Fa'iza zaune a Landon a wani park tana bura sigarinta kanta cike da attachment, ga barce zak'o-zak'o idan ka ganta sai ka rantse bata tab'a sanin wani abu Musulunci ba, balle kace mata Hausa/Fulani da ka ganta kasan cikekkiyar karuwa ce, 'yar bariki, marar kunya, wani inyamuri sanye da kanan kaya akwai sark'ar + da ganin sa kaga katan arne, marar imani, ya nufo inda su Fa'iza ke zaune kallon Gans dinta tayi tace " ku bar wajen ga Joy nan kuma kun san akwai babban dill, babu wanda yace kala kuwa ya mik'e yabar wajen, Joy ya k'araso ya zauna tana murmushi yace " Dear how are you? Cikin murmushi tace " fyn, n u? " am not Ok, kallon tambaya tayi masa cikin sigar bariki tace " why dear, " yesterday u make me angry, tace " am so sorry dear, am very busy yesterday, but today I will make u happy to night, " are you sure? "Yes of course, just get ready 4 me 2Night, dariya yayi ya mik'e yace" ok let me get ready since now, itama dariya tayi. 




Joy katan arne ne, d'an Nigeria ne a Landon suka had'u sunje siyayya ita da Gans dinta, tun daga ranar suka k'ulla alak'ar banza, ita bata san waye shi ba, harka kawai sukeyi, kamar yadda akwai wani mugun abu a ranta game dashi,shima haka akwai wani mugun abu daya ke shirya musu, dan sun dad'e suna shirya masa plan da target dan su damfare shi, sai Allah ya tsallakar dashi, basu san karrrr yake kallan su ba, da bakaramin shege bane duk wani takun su kallan su kawai yake, yazo mata a matsayin kwata-kwata bai san inane Nigeria ba, balle yasan yaren Hausa, nan ko, ko Ubanta bazai fad'wa joy Hausa ba, tana jin Hausa sosai fiye da tunanin mai tunanin, dan babu wata kalma dazaka fad'a da Hausa bai sai san ma'anar ta ba, kallan su kawai yake, kowaye zaiyi wining oho. 




Emergency room 



*Alhamdulillah*




*MOMYN ZARAH*




*PLS KUYI HAK'URI DA WANNAN*




HAPPY SALLAH 2 ALL MUSLIM 




BYE

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol