Free chapter · Read without an account

Episode 15

by Rahinat Hussein (R.Hussain) · AZIZAN BABA





_______________Daddy!Daddy!!! jiki na ƙaiƙayi yake yi, wayyo Allah na" ya cire riga yana ta mutsu-mutsu, Daddy da ke kusa da shi ya ce "subhanallahi me ne a cikin rigar" Mannir da Siyama suka hau matsawa ganin yanda yake zabura yana tashi, soshe-soshe yake kamar mahaukaci sabon kamu.

"Mudan yi parking mu gani" Daddy ya faɗa yana mai riƙe Abdul-azeez gani yanda yake soshe- soshe gami da zabura.


A ɗari ya fito daga cikin motar yana sosa jikinsa, wandon ya ke ƙoƙarin cire, yana tsalle yana ihu gami da rawar asosa-asosa, gaba ɗaya su Munnir suka sa kuka.Ya cire wandon dagaa shi sai boxer.



"Shikenan yaya ya haukaci Daddy wallahi sun haukata shi" Siyama ya faɗa tana kuka, Daddy da yasan abu ɗaya zai sa Abdul-azee haka shi ne karara, Mudan ya ce " Alhaji anya ba cikin karara ya shiga ba?"duk suna kan Abdul-azeez ganin neman shiga cikin daji yake, ana riƙo shi.



Gaba ɗaya ya soshe jikinsa ko ina ya kakkarce, ƙaiƙayin ba sauƙi sai ƙaruwa da yake yi.


Gaba ɗaya ya fita hayyacinsa hawaye da ihu gami da tsalle yake yi kawai, yana faɗin "ƙaiƴayi asosa min asosa min wayyo Allah na" gaba ɗayansu sai sosa mata akeyi ana yi masa sannu ganin da gaske karara ne.



Sun fi minti arba'in suna fama kafin Abdul-azeez ya samu damar jin sassauci a jikinsa, duk jiki yayi burɗin-burɗin kamar wanda yayi borin jini, fuska a kumbure saboda tsabar susa, duk ta tashi idanunsa sunyi jajir,jikinsa duk ƙasa saboda burgimar da ya dinga yi a ƙasa.



Sannu suke ta yi masa, pretty ta ɗauko ruwa a mota ta kawo masa, ya karɓa ya shanye ya na wahalallan numfashi.


"A'ina ka samo karara?"Daddy ya tambaya ganin yanda yakoma fututu kamar wanda yayi shirin wasan tashe.

Abdul-azeez ya ce" ban je ko ina ba, in banda cikin gida" 

Tinani ya yi take ya ce" Daddy ka ce karara sunan abun ko, kuma dole a gona ake samu ko?" Daddy ya ce" tabbas"

Aikuwa wallahi wannan yarinyar ce ta sakama min lokacin da ta riƙe ni" Daddy ya yi shiru yana nazari ya ce"tashi mu tafi tsaiwar mu nan risky ne" haka suja hau mota,Mudan yana Allah ya kiyaye gaba.



Abdul-azeez da ya ke ji tamkar yayi tsuntsuwa ya koma Mazoji, babu abinda yake illa cizon yatsa da huci.

Ganin kowa yayi shiru, Abdul-azeez yana ta ƙara susa, pretty ta ce"Daddy AZIZAN BABA ce ta saka masa, dan ina ganin hannunta da leda lokacin da ta riƙe yaya ta na ce wa ya ce mata haukaciya" Daddy ya ce" a'a Baba ba ita ba ce, maybe a hanya ya samo bai saniba" 

Abdul-azeez ya ce "ba wata hanya wallahi Daddy ko kaffara babu ita ce kuma sai ta san ni ta zalunta"Siyama ta ce" ina ma ba mu tawo ba wallahi sai na zaneta daman ni yarinyar kwata-kwata batayi min ba" Daddy ya ce "kar na ƙara jin kun ƙara tayarda maganar nan" duk sukayi shiru.


Har suka isa Kano cikin unguwar Tudun yola, Abdul-azeez bai daina susa ba. 

Mommy da tasan suna hanya, ta shirya musu lafiyayyun dishes.


Ta na jin sun shigo ta cika da murna, sai yanzu hankalinta ya kwanta, ta window ta ke kallonsu Daddy ne ya fara fitowa yana hamdala sai Munnir da yake driving sit sai kuma su Siyama.



Abdul-azee ne ya fito gabanta ne ya faɗi ganinsa kamar an to no daga rami, "innalillahi'wa'inna'ilaihirrajiun me ya same shi haka" da sauri ta fita ta sauka ƙasa hankali a tashe.


Ma'aikata na yi musu barka da zuwa, "Meyasa me Abdul-azeez haka na shiga uku" sai ta hau kuka.

Pretty ta ce" a hanya ne ya shafo karara"Mami ta ce "shi ne ya mai da shi haka?" Daddy ya wuce dan ya gaji liƙis, sallah kawai yake so yayi, part ɗinsa ya wuce.



Anan Abdul-azeez ya samu damar magana, Mami wannan yarinyar ce ta samin karara bansaniba"

Momi ta ce" wha!  i didn't undersand, who?" taɓe baki Munnir yayi ya wuce dan yunwa yake ji, nan Siyama ta hau kora mata bayani da yanda Abdul-azeez ya kusa haukacewa.



Wutar tsana da ƙiyayar AZIZA na ƙara ruruwa a zukatan Mami da Abdul-azeez, Mami ta ce" yaushe aka haifi yarinyar da har ta iya zuwa ta taɓa ɗana, wana irin sakin fuska ta samu da har ta samu nasarar sa maka karara!" ta faɗa da tsawa.


Siyama ta wuce hakama pretty, ganin yanda Mami ta hau sosai Abdul-azeez ya ce" tunda na shiga garin wallahi banji nayi dariya sau ɗaya a cikinsa, bazan taɓa bari ba, muddin ta na cikin ahalinmu ni ne ƙaddararta sai na sa ta tsani kanta,da kanta sai na mai da ita mujiya (owl) a idanun kowa" yana alwashi ya na shafa jikinsa inda ya ji burɗin har yanzu yana nan.


Sai lokacin Mami ta ji sassauci a ranta, ta ce" wuce kayi wanka ka huta, ni zan san abun yi"


Ta shi yayi ya wuce, wanka ya shiga yana shiga cikin ruwan yaji mugun zafi, kamar ruwan barkono dan jikinsa yayi jajir dan susa da burgima a ƙasa, cikin dauriya yayi wanka ya duba fuskarsa a mirro, tana nan a kunbure idanunsa sunyi jajir, sun shige lungu, alwala yayi ya ɗaura towel ya fito, goge jikinsa yayi ya  shafa Nevia da wasu different perfumes ya sa milk jallabiyya ya, gyara gashinsa, sallar azahar yayi ya kwanta don tunani abinda zai yi wa AZIZAN BABA.



Daddy na shiga ɗakinsa ya yi sallah,sannan ya ɗauki wayarsa dan kiran BABA ya sanar da shi sun sauka lafiya, duk yanda ya so samun BABA bai samu ba dole ya haƙura kafin anjima ko za'a da ce.




Shiru-shiru Mami ba ta biyo bayansa ba, kwana biyu baya nan, amma ta shigo tayi masa sannu da zuwa ta taimaka masa yayi wanka abun ya gagara,ji yayi ransa ya ɓaci, dakewa yayi ya fita dan zuwa yin lunch, su pretty da Siyama da Munnir duk suna cin abincinsu, ba Mami ba Abdul-azeez, ganin Daddy ya zauna pretty ta ce "Sannu daddy" ba tare da ya ce komai ba ya ce "je ki kira min yayanku" da sauri ta miƙe ta nufi ɗakin Abdul-azeez.


Handle ɗin ta kama zata murɗa, ta tuna kashedin da yayi musu, gaba ɗayansu, "kar wanda ya je min ɗaki ba tare da ya nemi permission ba, sai kunjira na ba da izini, duk wanda ya shigo ba tare da sanina ba, sai ransa ya ɓaci.


Knocking tayi tana sallama, "yaya Daddy is calling you" Abdul-azeez da yake kwance ya amsa ta okay i'm coming, get out of my side" Da sauri ta bar wajen, ta koma tana faɗin gashinan zuwa, fitowa yayi ya nufi dianing ɗin yana zama daddy ya ce "ya jikin naka"Abdu-Azeez ya ce"yayi sauƙi", okay Siyama zuba mishi abincin" plate ta ɗauko ta buɗe fried rice ne da cowslow sai chicken pepper, ta zuba masa, ta janyo ɗayan flak ɗin zata zuba masa   farfeson kayanciki, ya ɗaga hannu, ya ce " bar shi" ya ja ya fara ci,




 A zuciye Mami ta nufi ɗaki, abun yayi matuƙar ɓata mata rai, zagaye ta farayi a hannu a goye a bayanta, ta na tunanin yanda zata raba Daddy da ƴan'uwansa.


Wayarta ta ɗauko ta fara neman layin Hajja Fatu, gantalliyar na can yawon kai hajarta gidajen ma'aurata,ta zage sai yaba kayan take, kinsan Allah Hajiya Amina idan kika yi amfani da wannan hmmm ke da kishiya sai dai kiji a maƙota ba dai gidan nan ba"


Matar ta washe baki cikin jindaɗi, ta ce"ai na shaida kayanki ƙarshe ne ƙawata hahhhh" suna dariya ta ji ringing ɗin wayarta, bag ta zuge ta ɗauko tana amsawa ganin Hajiya Hadiza ce.


"Kina ina Hajja Fatu?" Mami ta faɗa cikin fusata,Hajja Fatu ta ce"lafiya na ji ki haka?" ke dai ki sanar da ni dan bazan iya bari, ƴaƴana su zama juji a dangin miji ba" Hajja Fatu ta ce" kai ni na zaci ma wani abun ne ashe akan dai waɗan nan halittun ne, me yafaru?"


Mami ta kwashe gaba ɗaya abinda ya faru a ƙauye ta sanar mata, Hajja ta jinjinakai ta ce" yanzu ace abun har ƙananan yara suna da damar da za suyi wa babban ɗa, ai ko pretty bai kamata a ce ana taɓa ta ba bare Abdul-azeez, gaskiya Hajiya Hadiza bazan ɓoye miki ba,kinyi sake sosai"

Mami ta ce" shiyasa na kira ki gobe da safe zamuje gurin malamin nan" 

Hajja Fatu ta ce" Allah ya kaimu, aikuwa kin taimaki kanki"


Mami ta kashe waya ta na neman layin Hajiyarsu.

Hajja Fatu ta mai da waya, ta na faɗin " wallahi matan auren nan suna ba ni mamaki, ni akwai shegun da suka isa su juyani, ba danginsa ba har mijin nawa hmmm ba dan ruwa ya daki babban zakara ba da hmmm Allah dai ya sauwaƙe"

Hajiya Amina ta ce" kai Hajja Fatu ya dai kamata ki samu ki ƙara aure, ai sai haƙuri mazajen nan namu" Hajja Fatu ta ce" ke raba ni da auren nan, aure har huɗu amma ba wani canji nagaji da yinsa"

Hajiya Amina ta ce" ki dai yi tunani" ta sai magungunan da take so, Hajja Fatu ta ɗau kayanta tayi gaba.



Zulai mai aikin gidan ta ce "kai amma Hajiya ba ta da tunani, kina da irin wannan magungunan kuma kike yawo ba aure, meyasa ba ki zauna ba tunda kina da hana kishiya da na riƙe mijin, meyasa ba ki riƙe mijin ba, mtsww rashin hankali kawai" ta ci gaba da goge-gogenta.



Mami ta kira Hajiyarsu, su Hisham su na gidan ana ta hira da ke juma'a ce daga masallaci duk gida suke yowa.


Ganin kiran Hadiza Hajiya ta amsa "Assalamu alaikum"daga can Mami ta rushe da kuka ta ce" yanzu saboda Allah abinda Aminu yake yi daidaine Hajiya?"Hajiya Ruƙayya ta ce" subhanallahi na faɗa miki shi zaman aure gaba ɗayansa haƙuri ne, sun dawo ne ko kuwa?"

Nan Mami ta zayyano ƙarya da gaskiya ta faɗa ta na kuka da faɗin ba'a ƙaunar ƴaƴanta, abun har ya kai ga har yara ma, suna neman rayuwar ahalinta.


Hajiya ta ce" nasan mutanen mu na ƙauye,wallahi Hadiza akwai abinda yayi wa yarinyar hakanan ba za ta yi masa haka ba, ki nutsu ki san abinda kike, ki sa su ƙaunaci ƴan uwansu,ina faɗa miki wannan hali ba na ƙwarai ba ne, ki yi ta haƙuri kinji ko" 


Zuciyar Mami kamar ta fashe,kuka kawai take kamar wata yarinya ta kashe wayar ta na faɗin "yanzu ace uwata ba za ta ƙwatarmin ƴan ci ba,ba magana mai daɗi sai dai a wajen ƙawaye zan ji sanyi saboda Allah " ta share hawayenta ta na fatan gobe tayi, sai ta farraƙa Daddy da kowa nasa,babu wanda zai ƙara yi wa komai ,daga su sai su.


Fushi take sosai da Daddy har dare bata je inda yake ba, haƙura yayi ya nufi ɗakinta ganin duk yaran kowa ya na ɗakinsa gajiya ta sa su baccin wuri.


Handle ɗin ɗakin ya murɗa ya shiga, kamar yanda ya santa da fushi ta na zaune bakin bed ɗinta ta zabga tagumi, murmushi Daddy yayi saboda ya san hali tun ƙuruciya fushi ne da ita, jin an shigo ta ɗaga kai ganin Daddy ne ya sa ta kauda kai dan ko ganinsa bata son yi, duk wani planing ya rusa mata shi.


"Haba my baby wannan fushin fa duk na mene uhm?" ya faɗa cikin sigar soyayya, ƙara ɗauke kai tayi, zama yayi kusa da ita ya ce..........



MAZOJI 



Hahhhh wo ni, wo ni AZIZAN BABA kowa ya ci ladan kuduri dole sai yayi masa aski ɗal,ta ɗane baki, Inna Gaji ta ce "ke da wa kuma, kinga AZIZA ki daina tsokana" 

Ta kuma kwashewa da dariya ta ce"a gabanku wannan jan ƙosan ya ce min mahaukaciya ba ku ce komai ba, shi ne zan nuna masa kalar nawa haukan nasan kafin ya je Kano zai gane waye mahaukaci tsakaninmu"

Inna Gaji da BABA da suka dawo daga rakiya BABA ya ce " ba dai ya tafi ba ai sai kiyi haƙuri, kuma kinsan ba mu san ya faɗi haka ba, ki bar ni da shi ni nan na ishe shi"


AZIZA ta ce "ai na daɗe da ramawa ta je ta ɗauko ledar da sa mu karara ta ce "gonar Mato na je na samo wannan na sa masa, zai san ba'a taɓa AZIZAN BABA akwana lafiya" 

Cikin faɗuwar gaba BABA ya ce "me ne a ledar?" 

"Karara ne BABA hahhh" ta kwashe da dariya ta na rawa da juyi.


"la'ilaha'illahu ke AZIZA ba ki da hankali kararan kika sa masa?" BABA ya faɗa ya na nufarta, ba ta re ta ankara ba ta ji ya kai mata duka a baya, ya na faɗin"kinsan irin jikinsa kuwa, ki kayi masa wannan abu" 

Cak ta tsaya cikin mamakin dukan da BABA da kansa ya kai mata, sai kuma ta zube ta hau ihu da kururuwa " wayyo ALLAH na shikenan na rasa mai ƙaunata wayyo uwata wayyo ubana, meyasa ku ka tafi ku ka barni shikenan ba ni da sauran gata" wannan kalaman ba ƙaramin tayarwa da su Baba Tabawa da BABA hankali yayi ba, sai jikinsa ya hau rawa, ya na faɗin "yi haƙurin AZIZAN BABA, tsautsayi ne ba da niyya nayi ba" Baba Tabawa ta fara cicciɓota ta na bata haƙuri, Inna Gaji ce ta ce" ai tun farko Malam laifinka ne a ce ba za'a tsawatarwa yarinya ba, ai icce tun yana ɗanye ake tanƙwara shi" ai kuwa sai BABA ya hau Inna da faɗi, " Aishatu na fuskanci daman ba ki ƙaunar maraya, ke ce daman kika sa na bugeta, alkur'an ke ce ki ka tunzara ni har na daki AZIZA" Inna ta ce" ni Malam? BABA ya ce"kwarai ma kuwa waye bai san kaidin ki ba, so kike ki ji tsakanina da AZIZA kuma ta Allah ba dai ta ki ba" AZIZA dai ihu take ba hawaye Baba Tabawa sai alƙawarirrika take yi mata akan indai tayi shiru, zan siyo miki sabon kaya, zan je da ke unguwa, zan sakewa ƴaƴanki ɗinkuna kowanne kala goma zanyi masa, za ki ci alkakaki da nakiya, to tashi maza kar ki ɓata kayanki, ai laifin Yayan ne akan wana dalili zai ce miki mahaukaciya, kansa yayi wa ai ta shi ƴar albarka" sai ga AZIZA ta yi shiru, BABA kuwa ya dinga sirfawa Inna faɗan ba gaira ba dalili akan Inna ce ta sa ya bigi AZIZA, Baba Tabawa abun ya ba ta dariya dan kowa yasan babu ruwan Inna.


Wannan dariya da Baba Tabawa tayi, shi ya fusata Inna, to munafuka wallahi Tabawa ki kiyayeni, ko ina ruwanki naga ai ni da Mijina da jikata ne ko, in banda kini bibi meye naki a ciki?" Baba Tabawa dai ta na ta dariya gami da ɗaga AZIZA ta ce muje in baki ki siyo alkakin kin ji" BABA ya washe baki ya ga yanda Inna ta ke ta maganganu BABA Tabawa ta yi mata banza.

BABA ya ce "oh ni Mahamuda wai ke ba za ki girma ba haba Aisha wannan wana irin hali ne" AZIZAN BABA ta ƙi kula BABA da Inna ta bi Tabawa ta bata ɗari biyu da kwano ta ce"je ki ki siyo abunki" 


Inna ta shige ɗaki dan shirun nan da Tabawa tayi mata, ya fi komai ƙona mata rai, BABA ya samu ya tashi ya shiga ɗakinsa ya na adana kuɗaɗen da Aminu ya ba shi, dan cefane da sauran abubuwan buƙata.


Kwanon wayarsa ya buɗe ya duba ya kara a kunne wai ko Aminu ya kira bai ji ba, dan kwana kin baya da aka kira baya ɗakin, lokacin da Aminu ya kira ba ya kusa, sai ya zata ko ana jin sautin a can ƙasa ne, jin baiji komai ba ya ajiye.

 AZIZAN BABA na fita a hanya ta haɗu da Lantana tana raba alawar aurenta, tun daga nesa take tayi mata dariya ta na tuno faɗansu.

Lantana ta ɗauke kanta, saboda tsakanin da mahaifinta yayi musu,Lawisa ƙawartarta ce ta ce "wannan yarinyar kamar fa mu take wa dariya" Lantana ta ce " rabu da ita, kar ki kulata"

AZIZAN BABA ta ce"wooo anga wa ta anga wa ta anga wata ba riga hahhh" kafin ka ce me AZIZA ta tara yara ana ta yi wa Lantana dariya,kuka ta sa tana mai rugawa gidansu.


Lawisa ta nufi AZIZA a zuciye ta ɗauketa da mari, a gigice AZIZA ta juya ganin gansamemiyar budurwa ce, ta dafe kunci ta na "kai,kai,kai, kika mare ni?" cikin hassala Lawisa ta ce "an mareki dan......Kafin ta ƙarasa ta ji an janyo ƙafarta sai ga ta tim a ƙasa" yeeeeh!!!!" yara suja hau ihu, AZIZA ta fusge mayafin Lawisa ta yar ta bi ta da cizo ko ta ita, da ya kushi, Lawisa na kai mata duka AZIZA na cizonta, azaba ta sa Lawisa fashewa da kuka, ga yara ana ta ihu, kwanon da zata siyo Alkaki ta janyo ta buga wa Lawisa a goshi, ta ta shi a guje ta yi gidansu..........



Zinariya ce✍🏻

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.