Free chapter · Read without an account
10
by Hauwa A Usman · RASHIN SANI…
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''
🔟
Da sauri ya fito daga office d'insa,
har yana tuntub'e, akan step ya tsaya yana hanga yarinyar da zai samu ya aika kiran su Sanah,
daga can nesa ya hango wata yarinyar tana k'ok'arin shiga Hostel get,
da k'arfi ya d'aga murya yace " hey,
yarinyar ta juyo a d'an tsorace,
ganin Sir Moli tsaye yasa jikinta d'aukar kerrrrma,
da sauri ta k'araso ta tsuguna a gabansa,
gaidashi take amma bai iya amsawa ba,
saboda yadda zuciyarsa ta gama jagulewa,
yace " ke ajinki nawa?
Jikinta na tsuma tace " JSS2,
yace " kin san Sanah Hamraz?
Ya tambaye ta idanshi na kanta,
cikin kerrrmar jiki tace " eh,
mamaki ne ya kama shi sosai jin ta santa,
kamar zai share sai kuma yace " ya akayi kika san su,
bayan ba class mate d'inki bane?
Jikinta na rawa tace " kowa ai ya san su a makarantar nan,
" saboda me?
Ya kuma tambayar ta a tak'aice,
yana yi mata tambayar ne dan yana san samun k'arin hujjar cin uban Sanah,
"tun ranar da suka daki Aunty Era suka zama popular's,
"Ok, maza jeki kira min su yanzu,
yayi maganar yana komawa cikin office d'insa,
da sauri yarinyar ta mik'e jiki na rawa tayi hanyar hostel,
a zaune ta iske su suna hira da Halan,
yarinyar tayi sallama, kana ta kalli su Sanah tace " Sir Moli na kiranku,
k'irjinta ta dafe had'i da zaro idanuwa waje,
tace " mu kuma?
Yarinyar tace " eh ku yace,
Halan ta kalli yarinyar tace " waya ce ku kira masa?
"Sanah Hamraz ta bata amsa,
ido Sanah ta kuma zarowa tace " na shiga uku me kuma nayi masa?
Ta tambayi yarinyar, tace " ban sani ba, ya dai ce kawai na kira masa ku,
Halan tace " ya kika ga yanayinsa?
Yarinyar tace " ban kula da fuskarsa ba dan kai na duk'e yake har ya gama yi man magana,
Yarinyar ta fad'i haka ne saboda gudun abinda zai je ya dawo,
dan tasan halin Sir Moli sarai,
Halan tagai dubanta ga Khulud ,
da jikinta ya fara rawa tun jin kiran da Sir Moli yake yi musu,
tace " me kuma kuka kuma yi masa?
A tsorace Khulud tace " wacce ni, mai kai ba gashi,
ai sai dai ki tambayi Oga,
Halan ta kalli Sanah tace " yau kuma mai kika tarowa kanki?
Kamar zatayi kuka tace " wallahi Aunty Halan tunda muka dawo ban sashi a ido na ba,
balle nayi masa wani laifin,
idon Halan na kanta tace " kin tabbatar?
Kai Sanah ta gyad'a mata, cikin sanyin jiki suka mik'e had'i da zarar hijabansu,
Halan tace " Allah dai yasa alkhairi ne,
Sanah tace " kayya Aunty Halan kema kin san a kira mutumin nan babu alkhairi,
Halan tayi murmushi, tace " ku irink'a maimaita " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
ku kuma d'auke numfashinku,
ku karanta, Qulhuwallahu Ahad,
sannan ku maido da numfashinku ku karanta Nasi da Falak'i,
da لا ØÙˆÙ„ ولا قوه الا بالله العلي العظيم,
har ku isa gare shi, in sha Allah duk girman laifin da kuka yi masa Allah zai d'ora ku a kansa,
cikin sanyin murya Khulud tace " to Aunty Halan mun gode,
kamar zata fasa ihu Sanah tace " wai ni meye dalilin kiran dayake mana?
Halan tace " o! o! ni da nake nan tare daku ina zan sani?
" Idan kinje can sai ki tambaye shi,
ko idanki ya gane miki,
batare dasun kuma cewa komai ba suka fita,
addu'o'in da Halan ta gaya musu suke ta maimaktawa,
Moli nacan zaune kamar zai fashe saboda tsananin zugin da zuciyarsa keyi masa,
minta d'aya minti biyu sai da duba agogo had'i da jan tsoki,
kishingid'a yayi ya rufe idanta,
yana sauraren yadda zuciya ke azalzalarsa gami da bugawa da sauri,
a k'ofar office d'in suka ci burgi,
kowa yana kallan kowa still they're praying,
Sanah tace " kiyi sallama,
Khulud tace " inyi sallama kamar yaya?
Tayi maganar cikin rad'a gudun kar ya ji,
Sanah tace " amma dai kin san idan ni nayi bazai amsa ba ko?
"Sanin kanki ne shanya mu zayyi,
batare datace komai ba ta matsa kusa da k'ofar tayi sallama,
batare daya amsa sallamar ba yace " in,
a tak'aice, Sanah ta tab'e baki had'i da cewa " sai kace karifi ayi maka sallama kak'i amsawa,
mstwwwwww taja tsoki can k'asan ranta,
durk'usawa sukayi a gabansa,
Khulud tace " Sir ina wuni?
Batare daya bud'e ido ba yace " Alhamdulalillah,
Oga Sanah ko kwata-kwata bata da niyyar gaidashi,
Khulud ta d'an tab'a ta da hannunta tace " ki gaida shi,
baki ta turo ta kau da kanta gefe,
hakan ya tabbatarwa Khulud bata gaida shi,
sun kai 7 minutes batare daya,
motsa ba balle ya bud'e idansa ko yayi musu magana,
Sanah na k'ok'arin yin magana taga ya mik'a hannunsa ya d'auko voice recorder,
yayi playing, still idansa na rufe,
suna fara saurara Sanah tayi baya zata fad'i tana daga tsugunnan,
dab'assss ta zauna a k'asa jiki ba kwari,
tun kafin su gama sauraran voice d'in suka fara gurzar kuka,
kamar ransu zai fita, while duk ilahirin jikin su na kerrrrma,
da tsuma yake, tsoro da firgici ya gama kama su, dan sun san babu mai kwatar su yau a hannun Sir Moli sai Allah,
har record d'in ya k'are Moli bai motsa ba,
yana yadda yake, idanshi rufe,
yana daga hakan yace " that's good,
"hmmmmmm yace yana sauke ajiyar zuciya,
"ashe ni k'aramin d'an iska ne kice babbar?
Yayi maganar still his eyes closed,
"shege d'an iska mai girman kan tsiya, miskilin banza,
ya maimaita under his breath,
"please ina san nasan girman kai da muskilnaci, iskanci da ja'iranci, kwartancin danayi Malama Sanah?
"Ina san sani kiyi man bayani in briefly,
yayi maganar still bai bud'e idan shi ba,
batayi magana ba sai sautin kukan su dake tashi,
"ashe ni munafuki ne, kuma shege, marar aikin yi sai kwanciya?
Ya kuma tambayarta,
mai lab'ewa a uncompleted building,
yana kurb'e-kurb'e da zuk'e-zuk'e ko?
" Mugu azzalumi still ko?
"wallahi idan har kina san na kyale ki sai kin yi man bayanin wad'annan halayen da kika danganta ni dasu,
bayan na tabbatar bani da alak'a da ko d'aya daga cikin su,
ina saurarenki yi min bayanin,
kwartanci, iskanci, ja'iranci, muskilnaci, munafurci, girman kai da zaluncin nadayi miki,
kafin mu zo kan shege, shaye-shaye, zuk'e-zuk'e da kurb'e-kurb'e,
shiru duk suka yi, babu abinda suke yi sai kuka,
jin shiru yasa shi bud'e idansa a hasale ya zabura ya daka musu gigitacciyar tsawa,
" ke dan kan uwarku bada ku nake ba?
Idonsu duk suka d'ago suka kalle shi,
cikin matsanancin tashin hankali da tsoro,
suna had'a ido da yaran yaji tausayin su ya saukar mishi a rai,
musamman dayaga yadda suke kukan mutuwa,
ji yayi zuciyarsa da ransa sunyi masa sanyi,
duk wannan zafi da k'unar ran dayake ji sun gushe,
sai ma matsanancin tausayin su daya mamaye ruhi da gangar jikinsa,
ajiyar zuciya ya sauke yace " shut up!,
duk sukayi shiru saboda tsoro,
ido ya k'ura musu na tsayin lokaci kafin yace "ku tashi kuje,
cike da mamaki suka d'ago suna kallansa,
yace " badaku nake ba?
Da hanzari suka mik'e jiki na rawa zasu fita har sun kai bakin k'ofar fita yace " don't be a greedy girls,
you know greedy pupils will pay for their sins,
jiki na rawa suka amsa da " to!,
bai k'ara bi ta kansu ba ya koma ya kwanta,
yana mamakin abinda yaji yanzu,
ya kuma kasa koda yi musu kallan banza.
_K'ARFI DA TASIRIN ADDU'A KENAN, DUK MAI YINTA BAI TAB'EWA KO WULAK'ANTA,_ _MUSAMMAN DAGA BAKIN YARAN DA BASU BALAGA BA, SABODA ALLAH YACE " DAN YARA K'ANANA DA DABBOBI AKE YI MANA RUWAN SAMA,_
_SANNAN ADDU'AR YARA BATA DA HIJABI GA UBANGIJI, SHIYASA WASU SUKE TARA YARA SUNA YI MUSU ADDU'A_
A bakin hotel get suka iske Halan tana jiransu,
suna ganinta suka fad'a jikinta suna sakin kuka,
a kid'ime ta d'ago su tace " lafiya,
dukan ku yayi?
Kai suka gyad'a mata a tare, tace " me kuka yi masa?
Cikin kuka Khulud ta zayyane mata duk abinda ya faru tun daga farko har k'arshe,
ajiyar zuciya ta sauke jin bai dake su ba,
ta mayar dasu jikinta ta rungume,
Sir Moli sai juyi yake cikin dare ya kasa bacci,
babu abinda yake tunani sai irin words d'in da Sanah ta jefe shi da su,
shi abinda yafi d'aure mishi kai k'arfin halin yarinyar da dakewar zuciyarta,
murmushi yayi lokacin daya tuno,
wai irin su ne masu lab'ewa a uncompleted building suna kurb'e-kurb'e,
da zuk'e-zuk'e, murmushi ya kuma yi had'i da girgiza kansa.
A week later Ziyad ya dawo visiting,
Sir Moli ya tarar akan staff zaune,
Ziyad ya mik'a masa hannu suka gaisa suna yiwa juna murmushi,
a nutse Moli ya tambayi Ziyad wad'anda ya zo gani,
Ziyad yace " Sanah Hamraz da Khulud Rawan,
& Halan
murmushi Sir Moli yayi yace " Bother su ne?
Ziyad yace " same Mom & Dad,
ka san su ko?
Cewar Ziyad,
"sosai, Moli ya bashi amsa yana murmushi,
Ziyad yace " ah Sanah ana tab'a halin anan ma kenan?
Ya fad'a yana murmushi, Moli ya zuba mishi ido,
"hmmm wato haka take kenan har a gida, shegiya 'yar iska,
ya fad'a cikin ranshi,
Ziyad yace " nasan dama za'a rina ai dama mai hali baya tab'a fasa halinsa,
murmushi Moli kawai yayi batare dayace komai ba,
head girl ya aika ta kira su,
shi kuma ya shige cikin staff yana mamakin nutsuwa da kamalar Ziyad.
Da gudu Sanah da Khulud suka k'araso, suka fad'a jikinsa,
a nutse Halan ta k'araso, tana murmushi,
sai da ya gama magana da wasa dasu Khulud kana yace " maza ku d'auki kayan kukai hostel,
kuma idan kun tafi karku dawo,
sai da aka sha daru da Sanah kana ta tafi tana kuka,
shima sai da yace mata idan bata daina rigima ba bai k'ara zuwa,
kana ta tafi,
bayan sun tafi ya karkata gaba d'aya hankalinsa ga Halan,
har k'asa ta duk'a ta gaidashi,
ya amsa cike da fara'a da tsantsar farin cikin tarbiyyarta,
a hankali ya kira sunanta " Halan!,
cikin nutsuwa ta amsa "na'am,
yace " zan tambaye amma please ki sanar da ni gaskiya,
tace " in sha Allah,
sai da ya nisa kafin yace " anyi miki miji?
Kanta ta duk'ar kanta k'asa kana tace "a'a,
yace " kina da wanda kike so?
Ta kuma cewa "a'a,
da k'arfi ya sauke ajiyar zuciya,
"Alhamdulillah yace,
kana yaci gaba " magana ta gaskiya Halan,
tunda na d'ora ido na kanki naji kin kwanta min,
na kuma samu nutsuwa dake,
abinda yasa ban zurfafa sosai ba,
sai dan gudun ko kina da wanda kike so,
ko wanda zaki aura, kuma nasan nema cikin nema haramun ne,
magana ta gaskiya ina sanki ya fad'a kan shi tsaye,
tunda ya fara magana ta duk'ar da kanta k'asa bata d'ago ba,
har ya dasa aya, shiru yayi had'i da kafe ta da idonsa dan ganin reaction d'inta,
ganin tana murmushi ne yasa shi fahimtar ya samu karb'uwa,
hira yayi ta zuba mata, ita sai dai ta bishi da eh ko a'a,
kud'i ya bata amma tak'i karb'a,
babu yadda bayyi ba, dole ya hak'ura.
A kwana a tashi ba wuya wajen Allah,
kamar yaune su Sanah suka dawo hutun first term gashi yanzu har sun kusa gama second term exam,
while Ziyad ya zo a term d'in waje 10 tyms,
sosai soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin Halan da Ziyad,
har maganar takai ga iyaye, an tsaida magana akan data gama secondary school za'ayi bikin su,
ranar hutu Sanah da Khulud da Halan sun sha kuka sosai,
kasancewar zasu bar Halan a makaranta,
zaman vocation,
koda suka koma gida hutu Mamu d'orawa tayi daga inda ta tsaya wajen koyar dasu girki da sauran abubuwa,
ranar da hutu ya k'are sosai Sanah tayi ta mak'alewa Aarib,
sai da kyar aka raba su, tana risgar kuka,
washe Monday first week na third term,
akayi assembly kamar yadda aka saba,
kowacce students ta kama hanyar class d'in su,
class d'in su Sanah yayi shiru dan basu da yawa wad'anda suka dawo,
dukkan su sunyi shiru cike da tsantsar kewar gida,
ganin haka yasa Sanah tashi ta cire hijab d'inta taci d'an mara dashi a k'ugunta,
ta hau saman seat ta fara kid'a,
abinka da wad'anda ke cikin kewa,
ga kuma k'uruciya na damunsu,
ai ko suka zage suka shiga tik'ar rawa da wak'a, while Sanah naci gaba da kid'an tana rawa daga zaune saman seat,
Khulud na zaune bata ko motsa ba, tana ta dariya,
Sir Moli na SS2 yana teaching,
yaji kid'a na tashi, his face with surprise,
saboda yaune first time daya soma jin maka makamancin haka a school d'in,
a hankali tako ya biyo inda yake jin sautin na tashi,
jin sautin na fitowa daga JSS side,
yasa mamkinsa k'aruwa sosai,
bai tsinke ba sai da ya ganshi a k'ofar JSS1 class,
a hankali ya shiga, ganin Sanah ta tara yara tana yi musu kid'a da wak'a,
yasa shi tsayawa cike da tsantsar mamaki yana kallan ikon Allah,
a ransa kuma yana mamakin wannan wacce irin yarinya ce?
Sosai kid'a da wak'a ya d'auki zafi,
kwata-kwata hankakin su Sanah bai kai gare shi ba,
ya kai a k'alla wajen 15 minutes a tsaye yana kallan yadda Sanah ke zazzaga fitsara,
while Khulud na zaune a nutse tana bin su da kallo tana murmushi,
juyowar da Sanah zata yi idanta ya sauka akan Sir Moli dake tsaye hard'e da hannuwasa a k'irji,
cikin wani irin mugun zafin nama ta yunk'ura da niyyar guduwa,
yayi wuf ya rik'e ta, sai lokacin hankakin sauran ya kai ga Sir Moli,
kowacce ta koma seat d'inta ta zaune a matuk'ar tsorace jikinsu sai kerrrrma yake,
ajin yayi tsit,
tsawa ya daka musu " ku dan kan uwarku tun da kuka zo makarantar nan kun tab'a ganin anyi kid'a?
Duk suka ce " a'a,
" wa yasa ku kid'a da rawa yanzu dan ubanku?
Jikinsu na kerrrrma suka ce SANAH HAMRAZ,
"Idan tace ku shiga wuta zaku shiga?
"A'a,
" wallahi daga yau kuka kuma yi mana kid'a school sai naci kan uwarku,
yayi maganar while yana rik'e da Sanah gam a hannunsa,
tuni Sanah ta soma kuka, jikinta sai kerrrrma yake,
gaba d'aya tsoro ya gama cika mata ciki,
ji take kamar ta saki fitsari,
Khulud na zaune inda take cikin matsanancin tashin hankali da matsananciyar fargaba,
kuka kawai take dan tasan yau Sanah ta shiga ukku,
a fisace ya fita da Sanah, Khulud tayi saurin mik'ewa tabi bayan su,
jin taku a bayansa yashi juyowa,
tsayawa yayi cak ya zubawa Khulud ido,
" ke koma, yayi commanding nata,
shiru tayi tana kuka batare data motsa ba,
ya daka mata tsawa "ke dan uw.....
kasa k'arasawa gazin ta yayi, idansa ya runtse da k'arfi, kana ya bud'e yace " ki koma,
cikin kuka Khulud tace " please Sir kayi hak'uri, tare mukayi laifin ni da ita,
ba ita kad'ai ce tayi ba,
Sanah tayi saurin cewa " no Sir banda ita, ni kad'ai ce nayi laifin,
kafewa Khulud tayi akan harda ita,
while itama Sanah ta kafe banda ita,
kallan Khulud yayi yace " this is the last time da zance ki koma class,
Sanah tace " my Ulud idan baki san nayi fushi dake to ki koma,
tsawa ya daka mata "ke dan ubanki ubanwa yasa bakin ki,
shegiya 'yar iska fitsararriya,
yayi maganar yana matse hannunta dake cikin nashi,
kamar zai karyata,
tsananin azaba ne yasa Sanah sakin gigitaccen kuka,,
tana tsallen wuya,
cigaba da tafiya Sir Moli yayi rik'e da Sanah a hannunshi,
Khulud ta tsaya a inda suka barta tana kuka,
dan yadda taga idanshi, da yadda yake jan Sanah kamar zai b'alla ta,
yana tafiya a zafafe kamar mahaukaci tasan yau sai buzun Sanahrta..................... .
Don't forget to vote , follow and comments
MOMYN ZARAH