Free chapter · Read without an account

67

by Hauwa A Usman · RASHIN SANI…

_*RASHIN SANI.......*_





*HAUWA A USMAN*

    _JIDDARH_




'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''




6⃣7⃣




" Ni ne Doctor d'in da kuka kawowa Khulud lokacin data samu injury a Roni,

tun a lokacin na nuna miki so da k'auna ta gare ki,

na kuma nuna sha'awar aurenki dan ke irin macen danake so ce,

amma sai kika rik'e hannu na a lokacin zan shiga emergency room,

kikace nayi miki alk'awarin zan taimaki Khulud,

nayi miki alk'awarin zan ceci rayuwarta,

zan kuma kula da ita, sannan zan bata kulawa,

kin tuna ni yanzu.....!?


Ya fad'a hawaye na zubo mishi,

tun a lokacin nasan Khulud bazata tab'a haihuwa ba, saboda haka ne na hanata zuwa hospital bayan munyi aure,

saboda kar'a sanar da ita bazata tab'a haihuwa ba,

haka duk asibitin da muke zuwa nike sawa a juya result d'in saboda Khulud,

dana fuskanci tana cikin damuwa da kokwanto shiyasa na yarda muka fita k'asar waje aka fad'a mata,

bayan kun rabu dani haka na rink'a bibiyar rayuwarku,

saboda ku na mayar da Zohal da Wajnah makarantar ku,

ranar da kuka gama secondary school muka had'u daku,

a ranar zuwa nayi na sanar miki ina sanki,

amma lokacin kin san meya hana ni fad'a miki.....!?


"Saboda a lokacin kinyi maganar data tuna min alk'awarin dana d'aukar miki,

bayan nan na cigaba da bibiyarki in baki manta ba mun kuma had'uwa har na watsa miki ruwa,

da ranar da kika mare ni, kin san meyasa na auri Khulud.....!?


Gaba d'aya jugum-jugum sukayi suna binshi da ido,

" na aure ta ne saboda cika miki alk'awarin ki,

na auri Khulud ne saboda kince baki da abinda kike so kamar Khulud,

na auri Khulud ne saboda ke da bakinki kika fad'a min duk mai sanki yaso Khulud,

kin ce min kina rok'on Allah duk abu mai dajara idan zai baki ya bawa Khulud,

kince min kin fi son Khulud ta kasance cikin farin ciki fiye da ke kanki,

amma wallahi ko sau d'aya ban tab'a son Khulud ba,

idan muna sex in har ina san nayi releasing sai na ayyana dake nake yi bada ita ba,

duk sanda na kalli Khulud fuskarki nake gani akan tata ba tata ba,

a lokacin danake yi miki wad'annan abubuwan ba wai ina yi ne dan cin mutunci ko na rabaku da Khulud ba,

ina yi ne danna nisanta ki daga gare ni,

dan duk sanda na ganki wallahi ina mantawa da ni kaina waye,

zan iya samun loosing control nayi wani abun wanda zai iya haifar da matsala a tsakanin ku,

ina yi miki hakan ne danki nisance ni, dan matuk'ar kina rab'ata komai yana iya faruwa,

ina ni santa kai na ne daga gareki gudun haifarwa da ahalinku matsala,

ba wai ina yi ne dan ina k'inki ba,

maganar Aryan kuma ki tuna sau hud'u fa Sanah ina ganin macen dana fi so a wani yasa yi na da wani daban, 

ya zanji dad'i fisabilillahi,

bayan ina mutuwar sanki wallahi a kanki zan iya bada rayuwata,

dan haka dole nayi kishinki dole naji ba dad'i duk sanda nayi gamo daku,

amma ki kwatanta abun akan kanki kiji ya zajiki idan kika ga Aryan da wata a kuma yadda nake samunku.....!?


K'uri Sanah tayiwa Hanash da ido cike da tsantsar tausayawa,

kwata-kwata tama rasa wanne tunani zatayi ta rasa mema zatayi,

yayinda Khulud ke tsaye tamkar mutum mutumi,

" wallahi ke nake so Sanah ke kad'ai ce macen dana so nake kuma so,

amma danayi hak'uri Allah yaga sadaukarwar danayi akanki,

sai ya sanya kika aure ni kika kuma haihu dani......!

bamu san me Allah ya b'oye a tsakanin mu amma kije kiyi tunani,

ya k'arasa maganar had'i da barin parlor'n,

zaman dirshen Sanah tayi a k'asa gami da sanya mahaukacin kuka hannunta duka biyu aka,

yayinda Khulud ke tsaye hawaye na gangaro mata,

" yanzu dama Hanash bani yake so ba......!?


"Asalima bai tab'a so na ba, albarcin Sanah naci......!?


" Duk irin tsagwaron soyayyar danake yi mishi da wacce na nuna mishi ashe ban tab'a burge shi ba.....!?


"Akan shi naci amanar Sanah akanshi nawa Sanah mugun butulci,

akanshi idanuwa na suka rufe ruf ya zama na bana ji bana gani,

dama duk abanza nake a gurinshi.....!?


" Duk mahaukaci kuma azababba kishin danake yi akanshi ashe banza nake......!?


"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,

wannan kad'ai ya ishe ni izza a gaba,

amma duk da haka Hanash ya cika cikekken d'an halak daya iya pretending true love,

bayan kwata-kwata babu son a zuciyarshi,

kuma wacce yake yi dominta ma bata sani ba,

Khulud dake tsaye hawaye na zubo mata tayi maganar a bayyane,

sai da Sanah tayi kukanta mai isarta kana ta mik'e ta koma part d'in ta,

ta zube saman bed tana sauke ajiyar zuciya,

tana tuno abubuwan da suka faru a baya,

" ashe dama Hanash shine wannan likitan...!?


" Ashe Hanash so na yake yi, ya dad'e yana mahaukacin so na amma ban sani ba......!?


"Lalle shima yayi namijin k'ok'ari ya cancanci a jinjina mishi,

na kuma tausaya mishi sosai ,

Hanash ko bedroom d'inshi ya koma ya shiga ya kulle yayi ta rusa kuka wiwi ya rasa me gare shi wanda zai sanya Sanah tsanarshi,

ya rasa abinda yayi mata da take yi mishi wanna muguwar k'iyayyar,

Khulud ma na can tana ta fama rusgar kuka kamar ranta zai fita.


Bayan kwana biyu


Duk yadda Sanah tayi iya k'ok'arin ta kanta manta da Aryan koyaya ta samawa Hanash guri a zuciyarta abun ya gagara,

dan kwata-kwata bata jin ko d'igon sanshi a ranta,

sai tausayinshi kawai datake ji da mutuncinshi da take gani,

amma fa babu batun so ko soyayya,

kwanciyarta ta gyara tana tunanin ta yadda zata iya tunkararshi,

tace ya sake ta, a fili tace " but I can't do without Aryan,

he's my heart, my soul and my happiness,

my life without him is like nothing ina sanshi sosai ina mutuwar son Aryan,

rabuwa dashi tamkar rabuwa da rayuwata ne,

a hankali ta tashi zaune gami da gyara zaninta ta d'aga kanta sama,

tana tunani ta jima haka kafin ta sauke kauta k'asa tana kallan tiles had'i da sauke ajiyar zuciya,

tace " he's my everything I really love Aryan more & more most,

cikin sanyin jiki ta mik'e ta nufi bedroom d'inshi,

a hankali ta tura k'ofar bakinta d'auke da sallama,

dakyar ya iya amsa mata cikin rawar murya,

kanta k'asa ta shiga ta tsaya daga gefenshi d'an nesa dashi,

cikin mutuwar jiki ya tashi zaune saman bed,

idonshi kanta yace " wani abun kike buk'ata.....!?


Kanta k'asa hawaye na zubo mata tana wasa da yatsun hannunta,

ta d'aga ta kalleshi, ganin yadda yayi muguwar rama yasata fashewa da kuka,

dan ita tafi kowa sanin bala'in so,

ko wani ta gani can daban cikin wahalar so dole ta tausaya mishi,

balle wanda ita yake so.....!

muryarshi na rawa yace " lafiya wani abun ke damunki.....!?


Cikin matsanancin kuka tace " kayi hak'uri.....!

I'm so sorry Hanash but I cant........!

" what.....!?


Yace idanshi kanta,

cikin kukan tace " I'm sorry but I love him,

I really love him so much I can't do without him,

please let me go......! nasan kaima kana so na, 

dan naga hakan cikin kwayar idonka,

nayi-nayi na taushi zuciyata na bata hak'uri na kuma rarrasheta,

ta jure rashin Aryan Moli ta hak'ura da k'addarar da Allah ya d'ora mana,

amma na kasa Hanash nayi-nayi na cusawa zuciya ta sanka amma hakan yak'i,

please Hanash divorce me please,

a hankali ya mik'e ya isa gareta ya sanya hannunshi ya tallafo kanta,

ya d'ora goshinshi saman nata goshin,

yana kuka wiwi while itama tana kuka,

dukkansu babu wanda ya iya furta koda kalma d'aya sai kuka da suke yi,

" I'm so sorry Hanash....! wallahi mutuwa zanyi idan bana tare dashi,

cikin kuka yace " ni ma idan bana tare dake mutuwa zanyi,

kamar yadda kike jin son Aryan nima ina jin naki fiye da haka,

please don't leave me.....! idan kika barni mutuwa zanyi nima,

goshinshi saman nata tace " please ka tausayawa rayuwarmu ni da Aryan,

rungume ta yayi yana kukan sosai yace " I can't......! I cant Sanah,

" please make my heart happy & peace please Hanash,

cikin nutsuwa ya sake ta had'i da takawa yabar wajen ya juya mata baya,

yace " kije.....!

cikin kuka tace " please......!

" please leave........!

ya fad'a cikin sanyin murya, a hankali ta juya ta fita nufi bedroom d'inta da gudu ta fad'a saman bed,

tana fita ya durk'ushe k'asa yana rusa kuka tuburan muraran.


Khulud ko tafi kowa shiga tsantsar tashin hankali da damuwa jin Hanash yace bai tab'a santa ba,

sosai itama ta rame ta k'ek'ashi sauk'inta d'aya yaranta,

idan ta kalle su tana samun sauk'i da sassauci cikin ranta da zuciyarta,

wani lokacin ma harta ji ta mance damuwarta, dan Allah ya sanyawa Khulud matsanancin so da k'aunar yaran,

Allah ya jarrabe ta da sansu dan duk damuwa da bak'in cikin da take ciki,

da zarar ta kalle su ko suna kusa da ita take mantawa,

mutane da dama suna tsananin mamaki da al'ajabin son da Khulud ke yiwa su Hajeer,Zotal da Sultan,

duk inda mai karatu ke tsammani son da Khulud ke yi musu ya wuce nan.


Sanah durk'ushe gaban Mimmee tana ta kuka tana rok'onta akan ta sanya Hanash ya sake ta,

a hankali ta d'aga kanta ta kalli Sanah tana sauke ajiyar zuciya,

kamar zatayi magana sai kuma tayi shiru ta kalli Khulud tace " Hanash yana gidan nan kuwa....!?


" Gaskiya ban sani, amma bari naje na dubo,

" yauwa jeki duba min, idan yana nan kice yazo daga nan,

" to tace tana fita, bata jima ba suka dawo tare,

kallo d'aya Mimmee tayiwa Hanash ta kauda kanta saboda bazata iya jure kallanshi,

cikin mayuwacin hali irin haka ba,

cike da tsantsar tausayawa ta kuma kallanshi ta kalli Sanah,

take taji kwalla ta taru a idonta, bak'i ace sun dai-dai ta sunyi mazansu ba,

a k'asa Hanash ya zauna batare dayace komai ba,

cikin k'arfin hali Mimmee tace " Hanash kasan meke faruwa ko....!?


Kuka ya sanya wiwi harda majini, tamkar ana zare ranshi,

wanda su kansu Khulud da Sanah sunyi mamaki,

yace " dan girman Allah Mimmee karkiyi min wannan maganar,

karki ce na sake ta, wallahi idan na sake ta mutuwa zanyi,

yanzu haka ma ina gaf da rasa rayuwata,

komai nawa ya lalace komai nawa ya tsaya cak Mimmee akanta,

wallahi idan aka raba ni da ita mutuwa zanyi,

please karki yi min haka Mimmee, itace rayuwata rabuwa da ita tamkar tsinkewar numfashi na ne,

cikin kuka a matuk'ar fusace ya juya ya kalli Khulud yace,

" kin cuce ni Khulud kin lalata min rayuwata da komai nawa,

dan sai da na riga na gama fidda rai da mallakar Sanah,

ban tab'a zato ko tsammanin zan same ta ba, balle har na aure ta,

saboda nasan babu yadda za'ayi na had'u na aura,

na gama sadaukarwa akanta, na cire rai na, na d'auki k'addara, na fawwalawa Allah,

amma sai gashi saboda tsabar san zuciya irin taki kika aura min ita,

kika shigo da ita cikin rayuwata da duniyata,

kika lalata min farin ciki na kika wargaza min komai,

kin cuce ni Khulud, kin cuce ni, ya fad'a cikin matsanancin kuka,

" amma ba ni kika cuta ba kanki kika cuta, ki sani shi sharri d'an aike ni,

 duk nisan da zayyi sai ya dawowa mai shi,

daga ni har Sanah da Aryan kin cutar damu da rayuwar mu,

kinyi wasa da zuciyoyin mu, kin gara mu kamar ball,

to ki sani, wallahi.......! wallahi......! wallahi.......! tallahi......! billahil azim.....! na rantse miki da girman Allah muddin aka raba ni Sanah,

ke ma sai na rabu dake, muddin aka saka ni dole na saki Sanah kema sai na sake ki,

sai na azabtar da zuciyarki kamar yadda kika azabtar da tamu mu uku, 

sai na gara zuciyarki nayi wasa da ita kamar yadda kikayi da tamu mu uku,

sai na sanya ki kuka kamar yadda kika sanya mu kuka mu duka......!

dan haka kima shirya dan baki ci bulus da lalai ba, bakici banza ba,

wallahi ko zan mutu koda shine kad'ai abinda zanyi sai na rama mana.


"Wallahi mutuwar aure na da Sanah tamakar mutuwar aure na dake,

rabuwa ta da Sanah kamar rabuwata ne dake ne dan haka kima shirya,

yadda muka azabtu ke ma sai kin d'and'ana kinji idan da dad'i,

inyaso su su rayu cikin farin ciki ni dake mu rayu cikin k'unci, da rashin masoyin tare,

dan bazan wahaltu ni d'aya ba, 

kuma dama komai nake yi miki dan Allah da ita nake yi miki,

albarkacinta kike ci, tunda haka ne kowa ya kama gabanshi,

muguwa azzaluma kawai, ina zama na lami lafiya kina motsa min soyayyata,

kika tuna min jiya, kika tsokano zuciyata kika faman min shekararran ciwon dake cikinta,

kin cuce mu, kuma kema kin cuci kanki dan bamu kad'ai ne zamu san zafin so da k'unar rabuwa da masoyi ba........!

" ya isa haka Hanash, a gaba na kake irin wannan maganganun.....!?


"Wallahi bana cikin hayyacina Mimmee, gaba d'aya na gama zaucewa na fita hayyaci na,

kad'an ya rage a kad'amin gangi a saka ni turu,

na haukace Mimmee, wallahi na haukace ban san me nake yi ba,

a zauce nake, kwakwalwata bata aiki kwata-kwata komai ya tsaya min cak,

mutuwa zanyi, jiki na yana bani ni ba mai tsayin rai bane,

yayi maganar tamkar mahaukaci,

idonsu Mimmee ta faka ta share hawayenta,

tana k'ok'arin yin magana Jaddah tace " meke faruwa naganku haka jugum-jugum.....!?


Ta fad'a tana gyara d'aurin zaninta,

shiru Mimmee tayi tama rasa ta ina zata fara,

kallansu Jaddah tayi tace " lafiya meke faruwa kuke kuka ku dukanku......!?


Babu wanda ya kula ta saboda yadda kowanne cikinsu yake matsanancin kuka wiwi,

" ku tashi ku bamu waje, Jaddah tace danta fahimci abinda ke faruwa,

ba musu suka mik'e kowannensu cike da tsantsar bak'in ciki,

kowa ya nufi bedroom ya fad'a kan bed yana kuka, Khulud ta jawo Hajeer, Sultan da Zotal ta rungume su tsam,

tana kuka tace " zan iya d'aukar da komai, zan iya jure komai amma banda rabuwa daku.


A fannin Sir Aryan Moli har yanzu bai san wainar da ake toyawa ba,

shi baima san Sanah ta haihu ba, balle yasan abinda aka ciki,

sanye yake cikin d'anyen yadi fari k'al wanda kallo d'aya zakayi mishi ka hango tsadar dake gareshi,

duk da baya cikin walwala da farin ciki amma fuskarshi akwai annurin haske,

sannu a hankali yake tura basket d'in yana d'aukar expensive perfumes,

wata yarinya ya gani wacce bazata wuce shekara 24yrs ba,

ta k'ura mishi ido, bata ko blinking,

d'an kallanta shima yayi yaga kamar ya santa,

amma ya rasa tuna inda ya santa,

murmushi ya sakar dan tuni ya daina wulak'anci a rayuwarshi,

itama murmushi tayi tace " sannu ina wuni.....!?


" Lafiya lau, am....! kamar na sanki ko......!?


"Eh.....! ka sanni I'm your old students....!,

" yauwa ko nace, but a ina please....!?


"Roni....! ta bashi amsa tana murmushi,

baka gane ni ba ko.....!?


Sai da yaji gabanshi ya fad'i dan gani yayi kamar Seeyah,

" eh....! gaskiya kin d'an kwanta min,

yayi maganar cikin dakewa, 

tana murmushi har lokacin tace " SEEYAH.....! ce, 

ai ji yayi kamar yayi ihuuuu ya rasa inda zai saka ranshi,

murmushin shi ya fad'ad'a yace " ayya Seeyah, kece dama.....!?


" Dama nayi miki kallan sani....!, ya kike ya rayuwa.....!?


"Lafiya lau, Alhamdulillah, takawa yayi har gabanta yana jin fad'uwar gaba,

amma ya dake ya isa gareta yace " please forgive me,

I knew I was made mistake but a time d'in akwai k'uruciya da yarinta dake damuna ni ma,

murmushi tayi tace " lah...! ba damuwa komai ya wuce, ni ma ina da laifi a time d'in,

dan nayi tsaurin ido, kuma in banda Allah yasa kai nagari ne,

da kana iya yin amfani da wannan damar ka lalata ni ka cuci rayuwata,

na yafe maka Allah ya yafe mana baki d'aya,

& nagode sosai dan hakan yana faruwa a makarantu da dama bad relationship between students & teachers,

saboda mu mata muna da raunin zuciya, wasun mu bama iya b'oye feeling,

so hakan yakan jawo a lalata mu a cuci rayuwarmu, dan a time d'in ina 14yrs kaga me na sani,

namiji yana iya yi min wayau, dan haka nima ina da laifi da har na bari hakan ta faru,

ji yayi tamkar an sauke mishi Zuma rock akanshi da k'irjinshi,

take annurin fuskarshi ya fad'ad'a,

yace " nagode sosai, kinyi aure ne.....!?


"Hummm dakyar Abba na ya barni na gama secondary school,

dan an bashi labarin abinda ya faru a Roni, 

dan haka ya tsorata sosai ina gama secondary school ko sati banyi gida ba,

yayi min aure da cousin brother na,

yarana uku mata biyu namiji d'aya, ta fad'a tana nuna mishi mijinta da yaranta,

" masha Allah, Ubangiji ya raya su,

ya albarci zuru'a, " Amin ya Rabbi,

Sir kai ma kayi aure.....!?


Batare daya sani ba, yace " eh.....!,

" kai amma nayi maka murna,

Sanah ka aura ko....!?


Ido ya zaro yace " ya akayi kika sani....!?


Tana dariya tace " karka manta a lokacin fa I'm in love,

so duk wasu love sigh na sansu,

kuma nasha ganinka kana d'aukar pictures d'inta,

dariya yayi yace " ikon Allah, sai da ta had'a shi da mijinta suka gaisa kana sukayi sallama,

haka nan yake jinshi cikin farin ciki da annushuwa,

yana cikin driven wayarshi ta soma ringing sharewa yayi yak'i yin picking,

jin an k'ara kira ya sashi kallan wayar,

ganin sunan K'ALBI....! dan har lokacin bai canja sunan ba,

jikinshi na kerrrrma yayi picking,

cikin rawar murya Hanash yace " kana ina please.....!?


Yadda Aryan yaji muryar Hanash yasa gabanshi mahaukacin fad'uwa,

cikin tashin hankali yace " lafiya Hanash badai wani abu ne ya faru ba.....!?


Ya fad'a muryarshi na cracking,

" Alhamdulillah, but please kana ina.....!?


"Gani ina fitowa daga shoprite ina hanyar gida na,

" please ina san ganinka, ina zanzo na ganka.....!?


"Kai yanzu kana ina....!?


" Ina gida, "ok to karka damu gani nan zuwa,

dropping wayar sukayi, kana Sir Moli ya k'arawa motar wuta,

dan zatonshi ko Sanah ta samu matsala wajen haihuwa,

a harabar gidan ya iske Hanash yana sintiri yana kai kawo sanye da jallabiya,

yana ganin Sir Moli ya shigo ya nufi motar da sauri jikinshi yana kerrrrma,

cikin fargaba Sir Moli ya fito while gabanshi yana fad'uwa,

batare da b'ata lokaci ba Hanash ya zube gaban Sir Moli bisa gwiwoyinshi,

had'i da sanya kuka wiwi, da k'arfi Sir Moli ya runtse idanuwanshi,

gami dayin baya taga-taga zai fad'i,

badan motarshi data kotareshi ba da babu abinda zai hana shi fad'uwa,

shima durk'ushewa k'asa yayi, yayi kneeling down,

gami da d'aga murya ya kwarara rikitaccen ihuuun kuka,

wanda gaba d'aya gidan sai da ya amsa, da gudu Jaddah, Mimmee Wajnah da Zohal,

Khulud da yaranta duka sukayi yo waje,

Sanah dake kwance tana jin ihuun gabanta yayi masifaffiyar fad'uwa,

dan ko motsin takun k'afar Sir Moli da fitar numfashinshi da bugun zuciyarshi taji zata iya ganewa,

jikinta na tsuma tajiyo waje da gudu itama,

gaba d'ayansu sukayi turus a harabar gidan, gami da zuba musu ido,

 hakan yasa Hanash tsaida kukanshi cak,

ya zubawa Sir Moli ido cike da tsantsar mamaki,

tari Sir Moli ya soma yi sosai numfashin shi yana yin sama-sama,

hannunshi dafe da k'irjinshi, a hankali jini ya soma d'iga ta hancin Sir Moli,

while yana cigaba da tarin, dakyar Sir Moli yace " please karka ce min Sanah ta mutu,

wallahi kana fad'a min anan take zuciya ta zata buga na mutu,

" a'a ba mutuwa tayi ba, alfarma zan nema a wajenka please,

ka dubi girman Allah ka dubi girman Allah Aryan ka bar min Sanah,

wallahi nima ina mahaukacin santa akanta ina iyayin komai, idan aka raba ni da ita nima mutuwa zanyi,

kwata-kwata tak'i yarda dani, tak'i ta amshe ni a matsayin mijinta na sunna,

nasan duk duniya babu wanda zai iya saita zaman auran mu sai kai Aryan,

babu wanda zai cewa Sanah ta zauna dani,

ta yarda ta amince ta zauna da ni sai kai,

ka dubi girman Allah please Aryan,

Hanash ya k'arasa maganar cikin kuka yana durk'ushe gaban Sir Moli,

ya rik'e k'afafuwanshi gam kamar his life depend on it

a haukace Sanah ta sanya kuka gigitaccen kuka had'i da nufarshi tana girgiza mishi kanta,

ko d'an kwalli bata dashi, tace " no Aryan....! please karka bar mishi ni, 

ni taka ce kai kad'ai, dan kai aka halicce ni, bani da wani miji a duniya bayan kai,

danayi rayuwa da wani d'a namiji ba kai ba, na gwammaci mutuwa ta,

cikin kuka Hanash ya kuma k'ank'ame k'afar Aryan kana ya shiga bashi labarin abinda ya faru,

tun farkon had'uwarsu da Sanah, har zuwa ranar, shi kanshi Sir Moli ya girgiza da jin labarin,

kana Aryan ya cigaba " please kodan yaran mu 'yan biyu ta haifa yanzu ma,

yaran mu uku biyu maza d'aya mace, 

yayi maganar yana mik'ewa jikinshi na rawa ya amshi su Hajeer da Zohal daga hannun Khulud ya mik'awa Sir Moli,

kana ya dawo ya kama hannun Sultan ya kaishi gaban Sir Moli ya sashi yayi kneeling down,

ya kalli Sultan yace " bag him to leave our happiness with us,

kasancewar Sultan yana da masifaffan yawo yasa ya karkata kanshi gefe had'i da cewa " please Uncle.....!

ido Sir Moli ya runtse da k'arfi dan tunda yake bai tab'a zaton zai tsinci kanshi cikin wannan mummunan k'addarar ba,

wai yaushi ne rik'e da 'ya'yan Sanah da Hanash har da 'yan biyu,

Allah kenan mai yin yadda yaso, wato wad'annan yaran sune suka raba su,

muna tamu Allah na tashi ta Allah kuma itace dai-dai,

ko a mafarki aka fad'a mishi akwai rabon haihuwa da aure tsakanin Sanah da Hanash bai yarda.


Balle ace mishi harda 'yan biyu, iko sai Allah, yaran ya kalla yaga babu ruwansu suna ta faman wasa da hannunsu,

kallanshi ya mayar kan Sultan dake durk'ushe har lokacin,

yaga tsantsar kamarshi da Sanah kamar an tsaga kara,

amma 'yan biyun kamarsu d'aya da Hanash,

idonshi ya kuma runtsewa da k'arfi zafafan hawaye suna zubo mishi,

take yaji wata irin tsantsar so da k'aunar yaran ta shigeshi kwata-kwata bai ji wani abu kansu ba,

sai ma sansu dayake ji yana ratsa shi,

take yaji tsantsar tausayin yaran ya kama shi,

a hankali ya kama hannun Sultan ya mik'ar dashi tsaye,

ganin abinda Sir Moli yake shirin yi,

yasa Sanah soma girgiza kanta tana cewa " no....! no....! Aryan, a'a karkayi min haka,

ka tuna alk'awarirrikan da mukayiwa junanmu,

wallahi nafi sanka sau dubu akan yaran nan, nafi san na rayu da kai fiye dasu,

na fi san kasancewa ta dakai da samun farin ciki d'orarre akan su,

kayi min alk'awarin zaka bani farin ciki marar iyaka, kayi min alk'awarin zaka sanya rayuwata haske zaka yalwatamun duniya ta,

amma meyasa kake k'ok'arin bari na.....!?


"Why Aryan.....!?


Ganin bai da niyyar yin magana illa hawaye dake ta faman sintirin zubo mishi,

yasa ta mayar da kallanta ga Hanash tace " meyasa ka kasance mutum mai san kanshi Hanash.....!?


"Meyasa ka gwammaci k'untatawa zuciyar mu mu biyu akan taka kai kad'ai......!?


" Kamar yadda kake ji a ranka game da ni,

ni ina jin fiye da haka akanshi,

haka zalika yana jin fiye da hakan shima,

had'a hannayenta biyu tayi waje d'aya ta durk'usa gaban Hanash tana kuka tace " dan Allah ka barmu muma mu rayu cikin farin ciki da salama a rayuwarmu,

ka barmu muma muji dad'in duniya, da soyayyar da muke yiwa junanmu,

ka barmu mu cika buri kan mu mu mayar da mafarkan mu gaskiya please Hanash,

cikin matsanancin kuka Hanash yace " bazan iya ba Sanah, wallahi ko za'a kashe ni ban tab'a iya sakin ki,

ina sanki nima, dan Allah ko ba dan ni ba kodan yaran mu,

cikin masifa tace " yaran me....!?


"Ni basu gaba na, Aryan ne kad'ai a gaba na, 

cikin rawar murya Aryan yace " no Sanah na barwa Hanash ke ki zauna da yaran mu........!

bata gama jin abinda zai fad'a ba, ta zube k'asa wanwar a sume,

SANAH.....! Sir Moli ya kira sunanta a razane, jikinshi na kerrrrma,

ya aje su Hajeer ya nufe ta, Hanash na k'ok'arin d'agata Sir Moli ya ture shi,

zubewa yayi a gabanta had'i da d'ago yana jijjigata,

yana wani irin kukan mutuwa a haukace,

tarin ne ya kuma sark'eshi sosai a karo na biyu while jini na zuba daga bakinshi,

idanuwanshi na lumshewa a hankali a hankali,

while yana cigaba da jijjigata yana kiran sunanta,

gaba d'ayansu kowa tsaye yayi yana kallan irin wannan makauniyar soyayyar wacce ko turawa, indiyawa da larabawa albarka,

abu kamar a film, take Mimmee ta soma kuka, Jaddah da Khulud ma kukan suke yi wiwi,

sai lokacin Mimmee ta fahimci ashe ba kishi ne da Khulud Sanah bata san had'awa ba,

wato Hanash ne bata so, b'oye mata tayi saboda alkunya,

shi kanshi Hanash ya tsinke da al'amarin Sanah & Aryan, dan tsaye yayi cak ya kasa motsawa daga inda yake,

yayinda ya zuba musu ido, shi kanshi yanzu ya sadak'ar da tsantsa kuma zallar soyayyar dake tsakanin Aryan da Sanah,

daga Rabbi take, wannan itace soyayyar gaskiya ita ce true love never end,

soyayyar gaskiya itace wacce ake mutuwa tare a rayu tare, a raba farin ciki tare a raba bak'in ciki tare,

ayi kuka tare ayi dariya tare, shi kanshi ya tsinke da al'amarin nasu, yasan duk wanda yayi gigi da gangancin raba soyayya da masoya irin wad'annan,

dole zaiga ba dai-dai ba, dole sai shima Allah jarrabe shi, sai yanzu ya tabbatar da Aryan Moli yafi shi so da k'aunar Sanah,

sai yanzu yasan shike k'aryar yana santa, amma Sir Moli shine wanda yake hak'ik'anin santa,

a fili yace " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ya Allah ka yafe min amma ban iya sakin Sanah,

yayi maganar idanshi na kansu,

jikin Khulud na rawa ta shek'a musu ruwan data d'auko,

a tare suka sauke ajiyar zuciya, gami da bud'e idonsu,

Hanash na k'ok'arin yin magana Mimmee ta taka gabanshi,

ta kifa mishi gigitattun kyawawa lafiyayyun marika,

tace " wallahi ka bani kunya Hanash,

ashe dama kwata-kwata babu d'igon tausayi ko imani a ranka......!?


Zayyi magana Mimmee tayi saurin dakatar dashi ta hanyar d'aga mishi hannu tace " na baka umarnin KA SAKI SANAH YANZU YANZU UMARNI NA BAKA BA ALFARMA NAKE NEMA DAGA GAREKA BA,

wallahi idan baka sake ta yanzu ba, ni yanzu zan TSINE MAKA..................!






MOMYN ZARAH    'YARBAIWA

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol