Free chapter · Read without an account
Page 7&8
*⚜️NIDA UWAR MIJINA⚜️*
_By_
*'Yar mutan kankia ❣️*
*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
***
_It's 500 via account number 0777512438 jamila Abubakar Bello access bank, shidar biya via ***_
🆓🅿️0️⃣7️⃣▶️0️⃣8️⃣
Washe gari bayan sun gama breakfast suka tafi wajen aiki, daga wajen aikin kuma Usman ya wuce wajen Maryam, soyayya suke sosai shi da Maryam bayan ya nuna mata irin son da yake mata tace daman ita a shirye take dan haka ya turo iyayenshi, bayan sun gama gaisawa ya wuto kaduna, da yake shima Usman a Abuja yake aiki, shine v.managed din C. B. N, ita Maryama anan take aiki, nan suka hadu.
Bayan ya dawo daga wajen aiki, gidan Baba Bala ya wuce, dan Baba Bala shine yayan Babansu, kuma yanzun shine ya zamai masu uba, dan komai zasu yi suna zuwa suna neman shawararshi a matsayin shi na mahaifinsu.
Bayan ya gama gaisawa dasu, suka zauna nan yake gaya mashi ance ya turo iyayen shi, su nemamai aure.
Kallonshi sosai Alhaji Bala yayi sosai sannan yace."Usman wannan shine auren ka na shidda kenan, kuma duk nine nan nike zuwa nema maka auren nan, to bari kaji nagaji da zuwa nema maka aure daga wannan shine neman auren da zaniyi maka na karshe, idan ma wasu aljana ce ta aureka, ka bari na fara nema maka magani sannan naje na nemo maka auren yar'mutane."
Tunda ya fara maganar kan Usman yake duke a kasa, shima yana mamakin yanda yake biye ma Momynshi tana sashi sakin duk matan da ya aure, amman daman ya aiyanama kanshi ba zai biye ma Momynshi ba ya saki Maryam ba, dan yana sonta sosai, cewa yayi."ayi hakuri Baba in sha hakan ba zata sake faruwa ba." cikin fada Alhaji Bala yace..."Tama sake mutunmin banza kawai, angaya maku shi aure wasa ne? Yanzun yaran zamanin nan baku dauki aure bakin komai ba, da an daura maku mata kuke sakin su, shiyasa yanzun zawarawa suke son sufi yan matan yawa ma, idan laifi mace tayi maka ka kaita wajen manya su yi mata fad'a mana, amman kawai dan hauka irin na yaran yanzun daga laifi sai saki, laifin da bai kai laifi ba sai kaji an saki mace, to kulelekulelenka wallahi Usmanu, ba zuba maka ido zanyi ba kana sakin mata ba, idan ita Saudatun ta sama ka ido toni ba zan samaka ba, dan haka tashi ka ban waje ka turo man address din gidan su yarinyar gobe in sha Allah zani tafi."
Godiya yayi sosai sannan yace tura mashi take ta whatsapp ya wuce gida.
"Zainaba tunda kun sasanta da Kamal bani san aita wannan doguwar soyayyar dan haka idan yazo yau kice mashi ya turo magabatanshi muyi magana, asa baikon bikin nan naku."
"To Dady shikenan insha Allah zani gaya mashi idan yazo, amman Dad wallahi ban gaji da ganinku ba."tafada cikin shagwaba ita a dole bata gaji da ganin iyayen nata ba, kallon ta Alhaji Masa'ud yake yana murmushi, dan ko shi ji yake kamar karya yayi ma Zainaba aure dan yanzun amman ya zaiye aure dai dole ne ta yi shi ko ba yanzun idan lokaci yayi sai tayi, kuma kwanciyar hankalinshi shine ya kaudata yayi mata auren, dan darajar ya'mace gidan mijinta, ce mata yayi."gidanku Zainaba, ai aure dole ne, kuma ai darajar ya'mace gidan mijinta dan haka nidai abunda zan gaya maki idan kinyi aure, to sai anyi hakuri, dan hakuri shine gishirin zaman duniya Allah yayi maku albarka ku dukanku."
"Amin Dad, zan gaya mashi, insha Allah."
"Yauwa yarinyar kirki tashi ki daura abinci dare ma, dan na lura Dadynki so yake yau ya saman ke kuka."
Murmushi kawai tayi ta tashi ta shiga kitchen ta fara aikin gabanta, kallon Alhaji Hajiya tayi sannan tace."wallahi Zainaba tausayi take bani da, da yanda zanyi da wallahi bata yin wani aure, amman ya zanyi dole ne shi aure, ashe haka uwa take ji idan lokacin rabuwa da yarinta yayi, zata kai ta gidan wani."!?
Kallonta yayi sanna yace."haka akeji mana Hajiya, ai ba yanda ko wace uwa za'ace ta aurer da yarinyarta bata ji ba dadi ba, hakuri akeyi, sannna sai aba zuciya itama hakuri."
"Hakane kuma Alhaji, Allah dai ya basu zaman lafiya, yakuma tabbatar masu da alkhari."
"Amin ya Allah, ai jiya Annas shida Muhamud suke kai kayan auren Auta suma."
"Hakane, wai Auta da aure, ni abun dariya ma yake bani."
"To ai lokacin shi shima yayi, amman Annas yace ma nan gidan zai zauna shida matar ko."!?
"Wallahi banji dadi ace lokaci guda sun kwashe subar man gida ni daya, kai dai Alhaji ba zama kake yi ba sosai, daman Zainaba ce take ebeman kewa itama auren zatayi, ba gwara ya zauna nan ba, inajin motsinsu a kusa dani ba."!?
"Eh hakane, amman ni bansan zama da uwarmiji fa, kinsan ku Mata da yan tsugune tsugune Hajiya."
Murmushi tayi sannan tace."haba Alhaji ai da akayi cases na uwarmiji amman banda yanzun, kuma ni ina ruwana da sha'aninsu, ni kawai zaman ne bansan yi ji daya ba, kaji dalili."
"Shikenan Allah ya tabbatar da alkhari, ai rana daya za'ayi bikin nasu da Zainaba in sha Allah."
"Allah yasa."haka suka gama maganarsu lokacin Zainaba ta gama yin abincin daren ta shiga dan shiryawa dan tasan Kamal yana hanya.
Bayan ya gama abunda yake yasa drive dinshi, ya kaishi airport ya zo gida, motarshi ya hau ya dauki hanyar zuwa wajen sahibar tashi, yana zuwa direct shiga yayi ya samu waje yayi parking din motarshi sannan ya kirata yace ta fito gashi nan ya iso, daman tunda ya shigo take hangenshi ta sama,ƙara gyra fuskarta tayi sannan tasa hijab dinta tace ma Anani Kamal yazo ita ta tafi, kitchen ta fara shiga ta hado mashi drinks da ruwa, sannan taje,zaunawa tayi tace."sannu da zuwa sahiba."
Kallonta yake yana murmushi dan kallonta kawai yana sashi farin ciki, balle tayi magana, cewa yayi. "Yauwa masoyiyata fatan na samu ki cikin koshin lafiya."!?
"Lafiya lau Alhmdulh, ya gida ya Momy dasu Husna."!?
"Duk suna lafiya lau, suna ma gaidaki."
Murmushi kawai tayi, sannan ta sauko ta zuba mashi drinks din yasha bayan ta gama sha tace mashi."Dady yace ka turo iyayen ka, suyi magana asa baikon bikin mu."
Wani irin farin ciki ne ya lublubeshi, dan bai san sanda ya furta."Alhmdulillh, Allah na gode maka."
Cigaba da kallonta yayi sannan yace."masoyiyata da gaske ne ko kuma mafarki nike."
Kulle fuskarta tayi da tafe hannunta sannan tace. "Da gaske ne ba mafarki kake ba, nice nan gabanka nike gaya maka Dadyna yace ka turo iyayen ka gobe."
tashi yayi yace mata."zafi zafi kan buga karfe masoyiyata, ni zan tafi yanzun naje na gaya ma magabata na, dan yau ji nike kamar ance an daura auren ma."
Ita dai Smile kawai take bugawa dan Zainaba ba daga baya wajen iya murmushi, raka shi tayi bakin mota sai da taga tafiyarshi sannan ta koma cikin gida ta gaya ma Anani yanda sukayi dashi.
Daga gidan su Zainaba gidan Sadiq kawai ya wuce, bayan sun gama gaisawa yace mashi."Abokina Zainaba tace man Dadynta yace na tura iyaye suyi magana asa baikon bikinmu, wata shawara kake da ita kuma."!?
"Alhmdulillh ai Kamal komai yazo cikin sauki, yanzun ka tashi kaje gida karda Momy taga baka dawo da wuri ba ku samu matsala, gobe da safe sai kaje ka gaya ma Baba Bala, sai yaje ya nema maka auren ta."
"Hakane, amman Sadiq nayi ma Momy adalci kuwa idan taji kawai ansa man biki ba tare da ta sani ba."!?... Shiru Sadiq yayi yana kallonta tabbas yasan irin son da kamal yake ma Momy bai san bacin rainta ko kadan, amman idan ba ta haka aka bi ba taua zai samu Zainaba din da yake so, idan har aka cigaba da biye ma Momy to tabbas Kamal zai mutune baiyi aure ba, murmushi ya danyi yana cewa... "Wannan shine adalcin Kamal, da kaje ka ja mata abun magana, ai gwara kayi auren kasan ma rabonka ne yazo kusa shiyasa, idan kuma Momy ta matsa tace zata hanaka wallahi rabo yana iya kasheta kaga gwanma taji kawai ansa bikin nasan ko zatayi maka fada, amman kuma dole tayi hakuri."
"Maganarka gaskiya ce Sadiq, ni na tafi, komai kenan sai kajini."
"To angon Zainaba bada kanka asare kaje gida kace ya faɗi."
Dariya kawai yayi ya tafi gida dan yaga lokacin dawowarshi yana son kure mashi, baida lokacin tsayawa ba Sadiq ansa.
Bayan ya koma gida wanka ya fara yi sannan yaje apartment din Momy, abinci suka ci sannan suka wuce massalaci, bayan sun dawo wajen Momy suka koma sukayi firar dare, dan duk daren duniya tare suke fira da Momy sai 11 suke zuwa su kwanta.
Bayan sun koma apartment dinsu waya ya kira Zainaba suka sha wayar su sannan suka kwanta.
Bayan sun gama breakfast ya ce ma Momy ya tafi wajen aiki, daga nan ko bai wuce ko ina ba sai gidan Alhaji Bala.
Yako yi sa'a ya tadda shi a gida bai kai da fita ba, bayan sun gaisa da matarshi ya shiga dakin Baban nashi, zaune ya tadda shi yana karanta newspapper, bayan ya gaidashi ya fara yi mashi bayanin abun da ya kawo shi."Baba daman zuwa nayi na gaya maka inda nike neman aure ance na tura iyaye na, amman maganar gaskiya Momy bata san ina neman auren ba."
Kallonshi Alhaji Bala yayi yana cewa...."Subuhanillahi, Kamalu, ya akayi zaka fara maganar aure amman baka gaya ma Momynka ba."!?
Sosa kai ya fara yi sannan ya dukar dakanshi kasa ya fara ce mashi."Baba na lura Momy bata san taga munyi mata maganar aure, da zaran munyi mata maganar aure zatace bamu isa aure ba, sama da shekara goma kenan, ina nuna ma Momy aure nike so, amman sai tace ita ban isa aure ba, idan nayi aure Yanzun to matar da na aure wayau zatayi man ta kwashe man kudi ta gudu, ko kuma tayi man wayau ta dunga anshe man kudi, haka sukayi da Yaya Usman, da ya matsa mata sai ta barshi yayi auren amman a gabana take sa yana sakin duk matar da ya aure tace mashi ai tayi mata rashin kunya, ni kuma wallahi aure nike so shiyasa na yanke shawarar ban gaya mata dan ko na gaya ma ta ba saurara zatayi ba balle ta anshi uzirina shiyasa nace sai dai taji ansa man baikon biki, amman mudun taji zanyi aure wallahi sai ta hana, kaji dalili na Baba."
Zuface ta wanke Alhaji Bala da kuma tarin mamakin Momy, tabbas bari yayi kama da mutun, shiyasa duk sakin da Usman yake ma matanshi bai taba jin tayi complain ba, aikuwa idan har maganar Kamal gaskiya ce to tayi na karshe dan zai nuna mata karfin ikon uba kan yaranshi, kallon Kamal yayi yace...."Ita Saudatun take wannan aika aikar Kamalu."!? Duk da har kasan zuciyarshi baiji dadin tonama mahaifiyarshi asiri ba a wajen yayan babanshi, amman ba yanda ya iya dan baida choice da ya wuce wannan dan ya tabbata Baba bala ne kawai zaiyi masu maganin matsalar Momy shida Usman a hankali yace..."Eh itace Baba."
Girgiza kai kawai Alhaji Bala yayi ya cigaba da cewa..."Allah ya yi maka albarka, yanzun gaya man gidan da ita yarinyar take, daman yau zani abuja maganar auren yayanka, kai kuma wani gari take ita yarinyar."!?
"Nan kaduna, a unguwarmu, sai dai ba layinmu daya ba, Alhaji Masa'ud speaker din governor to diyarshi ce."
"Masha Allah, ai tare mukayi secondary school dashi Baban nata, Abu yazo da sauki ma, sannan dan Allah Kamalu idan akayi auren nan karka biye ma Momynka kayi na dan'uwanka kaji."?
"Eh Baba insha Allah."
"Yauwa Allah yayi maka albarka, kace masu gobe insha Allah zani zo, yau dai Abuja zani zuwa anjima insha Allah."
"To Baba, Allah ya kaimu na barka lafiya."
Bayan tafiyar Kamal ya kira Zainaba yake shada mata gobe iyayen nashi zasu zo, ta gaya ma Dady, dan yau bai samun damar shigowa da marece, bayan sun gama waya ya tafiyarshi wajen aiki, ranshi tas.....
*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500
*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500
*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀****
*Muje Zuwa.... 🖤*
*Yar'mutan kankia ce❣️*
Share domin Allah