Free chapter · Read without an account
Chapter 27
CIWON 'YA MACE
BY
Fadila Lamido
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
Page 50
Zamewa Aunty Bilkisu tayi daga kan gadon zuwa kasa, tare da fashewa da kuka, saida tayi kuka ma'ishi sannan tace, "Nur bantaba soyayya da wani namiji ba sai shi, ni nama kaina cikin? Shine saurayina na farko kuma shi na aura, acikin kwana shidda da mukayi a tare be kusance ni ba tabbas, amman akwai wani srirri tsakanina dashi" Cikin rashin fahimta Nur tace "Har yanzu baki bani amsa ba Aunty" Hawaye ne suka zobowa Bilkisu alokacin da take cewa "A zahiri bashi bane babanta, amman a badili bata da uban da ya wuce shi." Mikewa Nur ta yi tare da cewa, "Yaya Abdallah yasan da hakan?"
"Hmmm, be sani ba kamar yadda ya nuna"
To mai yasa kikayi shiru tun abaya Aunty?
"Nur! Nayi shirune sabo da bani da hujja da kuma yanayin yadda ya bijiro da maganar ya fini gaskiya, babu wadda zai fahimce ni"
Shiru Nur ta yi tsawon lokaci zuwa can tace, "Tunanin ki kenan babu wadda zai fahimceki amma akwai, Aunty na shirya taimaka miki ki fita daga cikin wannan zargin"
"A'a, Karki fara Nur, zaki tayarmin da fininane kawai na samu abin ya fara kwanciya, bazaki iya ba Nur, kinyi kankanta, iyayenshine kawai zasu iya tursashishi, saidai su dinma babu hanyar da zasu fahimce ni."
"Aunty idan anyi shiru zancen ya kwanta mai zakicewa yariyar nan alokacin da ta bukaci son ganin Ubanta? Ni dai ki bani hadinkai kawai."
"A'a Nur, ki bari kawai, Kinga akwai zumunci a tsakanin ku, wannan maganar tana iya lalata muku zumunci, kuma daga karshe baza'a fahimce ki ba, nagode Nur bazaki iya ba."
"Zan iya Aunty, bazan yi maganar nan da kowa a gida ba, na yi wayau yanzu ba yadda kike tunani bane, karar shi zaki yi a kotu, ni kuma zan tattara hujjoji in tsaya miki, abun mai sauki ne indai kin bani hadin kai, dole zai amsa yariyar nan." Shiru Bilkisu tayi tare da cewa "Su Mamy ma ai bazasu yarda ba Nur, da sunji zaki shiga maganar komai na iya faruwa."
"Babu ma wadda zai sani Aunty, shi ya Abdallah takardan kawai za'a kai mishi sai in yaje koto" Nutsuwa ne ya fara shigar Bilkisu, domin bata tabayim irin wannan tunanin ba, ajiyan zuciya Bilkisu taitayi, yayin da take karajin nutsuwa na shiganta, saidai tana ta tunanin zumuncin Nur da Abdallah karya samu tankarda, dan haka Nur ta nuna mata ko ba itaba akwai kawayenta da zasu iya taimakawa, jin haka Bilkisu ta gamsu, har suka yanke karahen watan za'a shigar da karan kotu. Wannan ranar cike da farin ciki Nur ta koma gida, haka ma Bilkisu wani irin nishadi taji yana shigarta domin kuwa idan har akwai yadda za'ayi kowa ya gane ita ba yar isa bace zarafi kowa farin ciki da hakan. Nur kuwa aharabar gidan ta samu Abdallah da Yaya Bashir zaune, sun shinfida babban darduma, wucesu tayi bayan tawa Yaya Bashir sannu, daker ya amsa tare da hararan bayanta, Abdallah ne ya kalli Bashir yace "Wai Bashir mai ya hadaka da yariyar nan ne wai? Abin mamaki yake bani, yadda kake mata yanzun"
"Hmmm, Abdallah na kule sosai da ita, kaima ai kaban haushi shiyasa ban gaya maka ba, tun kafin abin yayi nisa na kawo maka zancen kaki saurarona, har ankai matakin da yanzun Nur ta tage wai wannan Poul din zata aura"
Wanni irin kallon Abdallah yayi wa Bashir tare da cewa "Da gaske ko wasa?"
"Wanni irin wasa kuma, dan Allah waike duk gurmin da akayi agidan baka sani ba?"
"To ni inama nake zuwa gidan, ko nazo ma ni aba'amin maganarta, yanzu ita da gaske take zata aura wadda ba musulmiba?"
"Ai ya musulunta, tun shekara 6 baya, kuma wallahi sabo da ita ya musulunta, sun dade tare wannan abun Yana Kona min rai, yama raina mutane, abin ma da yake kara kuna min rai, wai Abba cewa yayi idan ta dage bashi ita zaiyi, dan bazai mata auren dole ba, narasa mai yasa Abba ke lallabata, duk abin da take so shi yake mata, wai yasa a mishi bincike akan halayyar yaron a yanzun tunda shi take so"
"Wanni irin kallo Abdallah yayiwa Bashir, tare da cewa, "Aiko bazata aure shiba, ka bari zanyi maganin abin, ai naga ta girma yanzu, har wani kwambu takewa mutane, ni tama wuce da ajina ko kallona bata yi bare da kaisheni, ni banso Abba ya barta ta yi karatunbama, amman zanyi maganinta idan bata gaidani dan Allah ba zata gaidani dan dole" Mikewa Bashir yayi cike da haushi yana cewa "Narasa wanni iri so Abba yakewa yariyar nan, sam baya son bacin ranta, nasan tun da yace haka babu wadda ya isa ya hanashi yayi mata abin da ranta yake so cikin mu.
Bayan Bashir Abdallah yabi da kallo, har ya fice acikin gida, sai fada yake kasa-kasa, da alama sosai abin yake sosa ranshi, mikewa Abdallah yayi shima ya nufi cikin gidan, adakin Mamy ya samu Nur zaune kusa da Mamyn, sallamar da yayi Mamy ta amsa itako Nur dagowa ta yi ta kalle kofar ganin Abdallah ne ta kauda idonta tare da mikewa tsaye ta dauki wayarta da kwanon cincin din dake gabanta ta fice batare data kalli Inda yake ba, Binta da kallo Abdallah yayi har ta jawo kofar sannan ya kalli Mamy alokacin da take cewa Bashir fa?
"Ajiyan zuciya yayi tare da cewa ya wuce ai, amma kila zai dawo anjima"
"Be min sallama ba, naso na ganshi kafin ya wuce"
"Lafiya?" Abdallah ya fada bayan ya tsare Mamy da ido"
"A'a be shafekaba maganar Nur ne, kuma aikai ba shiga lamarinta keke ba" Mikewa Abdallah yayi tare da cewa "Kai Mamy, wai be shafeni ba" Juyawa yayi yana kokarin fita adakin tare da cigaba da cewa "Shikenan dai" Bin bayanshi ta yi da kallo har ya fice sannan ta tabe baki tare da cewa "Aure dai ya gagari Abdallah idan ma wani abin yake har yanzun Allah ya shiryeshi ya dawo dashi kan haya kan madaidaiciya. Lokacin da Abdallah ya fito Nur na zaune afalo, can gefe ta juyar da kanta, shiko ta gefen idon sa yake kallonta har ya fice afalon. Adaren ranar Bilkisu ta kira Nur a waya bayan ta mata bangajiya tace, Nur hankalina yana ta kara nutsuwa akan maganar shigar da karan Abdallah, sai dai ina tunanin karya rofe ido ya min rashin mutuncin da yayi min abaya.
"Hmmm, Aunty Bilki shari'a sabanin hankali ce, nasan halin Yaya Abdallah fiye da yunwar cikina, idan baki mantaba bama shiri ni dashi, nasanshi farin sani makirine, nasan ta yadda zan bollo mishi"
Amman Nur sai nake ganin idan na sakaki agaba amatsayin wadda zata karenj a kotu rikicin ku da Abdallah zai kara gaba kuma ban miki karaba"
"Kara? Har kike maganar kara Bilkisu ai wannan abin kamar taimakonshi ne za'ayi idan ya yaga laifina nasan daga karshe iyayenmu zasu fahimta, yanzun da baya magana dani din kare ki nayi, ai ki cire wannan tunanin, kisa a zuciyarki cewa baki sannan alakarmu dashi ba, ni Kuma na miki alkawarin in sha Allah Abdallah saiya karbi Ummi, Ina da tarin hojjojin da zaisa Alkali yabawa Abdallah Ummi amman sai da hadin kanki, wai to mai ya hana Abdallah ya kusanceki tsayon kwana shidan?"
Wallahi Nur haka kawai bayan ya gama wasa Dani yace wai mukulla.
Lumshe Ido Nur tayi, ganin hakarta ta fara cimma ruwa, cikin dibara Bilkisu zata fada mata yadda akayi Abdallah yayi mata wayau, afili kuwa cewa ta yi, "Ai tun barko naso da aka tambayi ki ya kusanceki kice eh kawai, tunda ya kwana dake adaki daya akuma kan shinfida daya kuma saida kika cika wata goma da auransa kika haihu dan haka aure ya bashi, matsalar kawai ke da kika ce be kusanceki, to amman nasan yanzun zaki fada min komai ai"
"Ai ni Nur yanzun mafita kawai nake nema abin yaki ci yaki cinyewa"
"To kije ki shirgar da karanshi koto da zaran an kawo mishi sammaci zanzo muyi magana"
Sallama sukayi bayan Bilkisu tawa Nur godiya.
Bayan sun gama waya falo ta fito ta zauna cike da tausayin Bilkisu a yammacin ranar gaba dayan su suna falon Mamy Aunty sai Nur, hira suke sama-sama sukaji sallamar Mamma, cikin sauri Nur ta juya ta kalleta sannan tai saurin rufe idonta kamar mai bacci, dan a yanzun yar kunya suke shiyasa sai su jima basu hadu da Zainab da ita ba domin yanzun ba shiga cikin gidan take ba, hakama Zainab bata zuwa tunda ta gaya mata abin da Yaya Bashir yace akanta , su Mamy ne suka amsa sallamar bayan ta shigo suka nuna mata wurin zama, Ganin haka Nur ta tashi zaune tare da gaida Mamma cike da jin nauyinta, itako Mamma cike da nuna kauna ta amsa, mikewa Nur ta yi ta nufa daki alokacin ta taji Mamma na cewa "Mammy wurin ki nazo" dan haka ta kasa shigewa dakin ta makale jikin bango, muryan Mamy taji tana cewa "To gani Mamman Zainab" Cikin nutsuwa Mamma tace "Mammy Nur na zo akan maganar Nur da Aliyu na, naji cewa yanzu kunsan suna son junansu, dan Aliyu ya gaya min abin da ke faruwa, Aliyu na son Nur sosai, ta dalilinta rayuwarshi ta canza, ta dalilinta yana kula dani da kanwarshi, Kuma har gobe kullum hallayyarshi dada gyaruwa take, na fahimci a yanzun da rayuwar Nur yake koyi, Duk irin tsaron da ya kula ana bawa Nur a gida irinshi yake bawa Zainab, duk abin da ya kula inaso kafin ma in fada yana mini, tunda Aliyu ya musulunta bansake zubar da hawayen damuwarshi ba, domin kullum nunawa yake yafi jiya kirki, a yanzun nasan samun shi nasan rashinshi, haka kuma dazaran ya shiga damuwa gabana yake kawo damuwarshi, bazan boye muku ba Ina jin dadin wannan yanayin da muke ciki, Kuma na tabbatar da cewa Nur ce ta kawo haske acikin rayuwarmu, ya jima da rabuwa da matarshi yanzu ko sunanta baya son a ambata, Mamyn Nur, Dan Allah ku taimakeni bana son ya rasata, sun dade tare, sun saba da juna, tunda yaji abin da Babanta yace ya shiga damuwa walwalarshi ta ragu, zamowa Mamma ta yi kasa ta Isa gaban Mamma ta rike kafarta tare da cewa, "Dan Allah ki taimakeni kuyi hakuri karku nuna kyama a garemu"
Yadda Mamy taji ta rukurkume kafarta yasata dafa kafadar Mamma tare da cewa tashi Mamman Zainab, ai matar mutum kabarinsa ce, duk yadda wani yaki ta da Aliyu, idan Allah ya nufa matarsa ce babu wadda ya Isa ya hana, haka Kuma duk iri son da danginta sukewa Aliyu idan Allah ya nufa ba mijinta bane ko ranar auren ne baza a daurashi ba, abin da nake son ki gane shine, wani baya taba auren matar wani, tun da naji wannan labarin addu'a nake idan Alheri ne Allah ya tabbatar, idan Kuma babu alheri Allah ya canza musu da mafi Alheri, shi kanshi Abbata gabanta ne ya tsaurara abin, amman a bayan idonta addu'a yake Allah ya zaba abin da yafi alheri" Nur dake labe ajiyan zuciya tayi tare da murmushi, acikin zuciyarta take cewa "Ai nasan Abba bazai matsa min ba, kuma nasan idan na dage Aliyu nake so zai aura minshi, domin shine ma alheri, saboda shi nake so, Kuma na dage da addu'ar Allah yasa ya zamo mijina" Muryan Aunty ta jiyo tana cewa "Mamman Zainab ki kwantar da hankalin ki, kema ki nemi zabin Allah, amman ko kadan ba yadda kike tunani bane" Mikewa Mamma ta yi sannan tai godiya, tana kokarin fita Mamy tace "Kuma idan Abbanta ya dawo zan sanar dashi zuwanki dan ya kara daukan abin da mahimcin" Sosai Mamma taji Dadi ta fita tana godiya bayan Mamy da Aunty sun Dan taka mata. Daki Nur ta koma cike da farin ciki, tshinta kanta ta yi dayin dariya ita kadai a dakin. Adaren ranar taji Baffah yazo, Mamy da Aunty falon Abba suka tafi, Dan haka ta fito falo ta zauna, tun tana jinta cikin nishadi har ta fara gajiya da zama, domin gani ta yi har goma ta buga batare da sun dawo ba, mikewa ta yi da Nufin wucewa daki taga su Mamy sun shigo, Aunty ce ta dubeta tace "Ina zaki? Bacci nake ji, zanje in kwanta" Nur ta fada tana kokarin famintan fuskarsu, Mamy ce tace "Ki yi sauri ga Baffanku can kije ku gaisa" Aunty ce tace "Anya kuwa taje?" Ji tayi Mamy tace "Gara taje tun da Abban su ya yanke magana bazaice komaiba Kuma" Ganin sunyi shiru Nur ta juya ta fita, hangosu ta yi a harabar gidan suna kokarin fita shida Bashir, dan haka ta daga daga Murya tace "Baffah!" Waigowa yayi ya kalleta, sannan ya juya yaci gaba da tafiya, Bashir ma Waigowa yayi ya Dan kalleta sannan ya bode motar ya shiga, shima Baffah cikin motar ya shiga ya zauna, Adaidai lokacin da Nur ta tsaya bakin get din tace "Baffah Ina wuni" Daker ya iya Bude baki yace "Lafiya lau" kafin ta sake cewa wani abu taga Yaya Bashir ya ja motar sun wuce, da sanyin jiki ta koma cikin gida, tana kokarin shiga falon taji su Mamy na cewa "Ai dole aji ra'ayin Ummynta, ba a yanke hukunci ba" Jin haka yasa tana shigowa ta masu sammala ta shige dakinta cike da damuwa, bayan ta gama tunanin yadda Abba ya amsa gaisuwarta, ta koma tunanin Ummy da taji su Aunty na maganar za'a nemi shawaranta, tsaki taja fali, tare da cewa "Wai dama haka ake shiga damuwa lokacin aure? Kowa sai an nemi shawaranshi? Yanzu nasan ana tambayan Ummy sai ta yi shawara da yaranta, duk su gama zugeta tunda ba sona suke ba" wayarta ta jawo ta Kira Ummy, cikin yanayi irin na wadda ya fara bacci tace, "Nur lafiya bakiyi Bacci ba har yanzun?"Eh Ummy, cikin nutsuwa ta fara bawa Ummy labarin Aliyu daga karshe tace "Ummy idan an tambaye ki kice kin yarda karkiyi shawara dasu Yaya Jamal" Jimmm Ummy ta yi bayan tsawon wani lokaci tace "Ke ce ma zaki gaya min abin da ya dace in yi?" Kina hauka ne Nur tubabben zaki aura sabo da idonki ya rufe ko?" Can kasan makoshi Nur tace "Ummy mun dade tare, dan Allah karkice komai, yadda tai maganar Kamar ta ce wayyo Allah yasa Ummy cewa "To ni gaskiya Nur idan zan gaya miki kiji banaso, maganar iyayenki Kuma idan sunkirani bazance komaiba tunda ubanki na raye, duk abin da ya yanke shikenan, amman ke ina son ki canza tunani" "Ummy shi nake so, shakaranmu shidda tare, dan Allah ki mana addu'a kawai, kuma karki bari su Yaya Jamil su sani" Sabo da kin dauke su makiyanki ko? "A'a Ummy, ba haka bane, ni kiyi hakuri dan Allah"
Can kasan makoshi Ummy tace "Shikenan, naji, Saida safe, kashe wayar ta yi batare da ta bari Nur ta yi magana ba, dan haka Nur ta kalli wayar ta yi murmushi kadan. Washari Misalin karfe bakwai na safe, Abdallah ne yayi sallama falon Baffah, Baffah da Bashir ya samu aciki, dan haka ya Isa daf da Bashir ya zauna, tare da gaida Baffah, bayan Baffah ya amsa ya bawa Bashir hannu suka gaisa, Baffah ne yace "Jiya da daddare ai na dauka zanzo in sameka anan?" Murmushi Abdallah yayi, tare da cewa, "Na dan jira ai Baffah da naga shiru na wuce nace da safe na dawo" Baffah ne yace "Toh hakan ma babu lalifi, Ina can gidan nakune ai, Babanku ne ya kirani, Jinjina kai Abdallah yayi alokacin da Bashir ke bin Baffah da Abdallah da kallo, ganin haka Baffah ya kalli Bashir yace, "Jiya lokacin munacen gidan Abdallah ya kirani awaya gashi yazo wurina bana gida." Murmushi Bashir yayi sannan ya kalli Abdallah dake kokarin saka wayarshi a aljihun gaban rigarshi, a daidai lokacin da Baffah ke cewa "Abdallah to ya wajen kasuwancin ku?"
"Alhamdulillah Baffah"
"Ma sha Allah, Baffah ya fada yayin da ya sake cewa to lafiya dai ko keke nemana?" Wannan karon sunkuyar da kai Abdallah yayi tare da shafo keyarshi yace, "Lafiya lau Baffah, dama akan maganar Nur ne" Cike da Mamaki Bashir yabi Abdallah da kallo, kosawa yayi yaji wata dibarar zai billo dashi domin hana auran Nur da Aliyu, gani yayi Abdallah nata fama shafa keya, har Saida Baffah ya sake cewa "Inajin ka Abdallah?" Kanshi akasa ya ce, "Baffah dama ina santa ne, abani auranta"
Wanni irin kallo Bashir yawa Abdallah yayin da Baffah ke cewa "Ikon Allah, kai kanka ko kuwa abokinka ka ke nemanmawa?"
Batare da ya dago kansaba yace "A'a, ni ne Abba."Shiru Baffah yayi yana kallon Abdallah da har yanzu kanshi na kasa, haka shima Bashir har yanzun ya kasa cire idonshi akan Abdallah, mamaki yasashi rasa a inda yake, daker ya iya juyar da kanshi ya kalli Baffah dake dannan waya fuskarshi daure, kosawa yayi yaga mai Baffah ke shirin yi Kuma, bayan ya gama dannawa a kunnensa ya daura tare da cewa "Barka da safiya" Shiru yayi zuwa can yace "Abdallah ne yazo yanxun ya sameni akan cewa yana son Nur, zai aureta" Shiru Baffa yayi sannan yace "Nace nabashi" saurare ya tsaya yi daga cikin wayar sannan ya cigaba da cewa, " 'Yarkace amman ai danane yake so, a'a dakata mana, ni ban maka katsalandanba, yariyar yar kace ni kuma na sanar maka d'ana naso, nasan baza'ka iya ce min a'a ba, ko ka tsallake ni kabawa dan wasu" Shiru Baffah ya sake yi zuwa can yace "Ba biye mata za'ayi ba ai" sauke wayar yayi sannan ya kalli Abdallah dake sukuye dakai har yanzun yace, "Shikenan ka je karka damu" Godiya Abdallah yayiwa Baffah, sannan ya mike ya fita, Bashir kuwa bin Abdallah yayi da kallo har ya fice, Daker ya iya mikewa yabi bayanshi, acikin motar ya samu Abdallah jiki a sanyaye, cikin kureshi da Ido yace "Abdallah lafiyarka kalau kuwa?"
"Hmmmm, Mai ka gani Bashir?"
"Nasan tsakanin ka da Nur ba shiri kuke ba, kasha cemin ba ruwanka da ita, amman kaje kana cewa Baffah kana sonta zaka aureta, wai kana nufin bayan ka kore Aliyu zaka dawo kace wasa kake ne?"
"Hmmmm, Ba wannan maganar Bashir, da gaske nake zan aureta.
Kallon cikin Ido Bashir ya sake yiwa Abdallah tare da cewa "Ta yaya zaman ku zai yiyu ahaka alhalin ba son juna kuke ba?"
"Ni ina sonta Abdallah, kuma itama nasan nan badadewaba zata soni."
"Tab lallai, dan Allah Abdallah karka lalata mana zumunci."
"Bashir ka kwantar da hankalinka, tunda nace ina sonta Ina sonta ne. Ban damu da tasoni a yanzun ba, da zaran an daura auren anyi me wuyar, sati daya yayi yawa zata saki jikinta, in dai nine, kuma da bakinta zakaji tana yabon halina, cikin awanni zan iya canza tunaninta, domin ni kamar wahainiya haka nake, a duk lokacin da naso ina canza launi."
"Kafada Abdallah ya daga, tare da cewa shikenan Allah ya tabbatar da alheri" Motar ya bude ya fita yayin da Abdallah ke cewa "Bazakaje can gidan ba" batare da Abdallah ya juyoba yace "A'a" Motar ya tada yabar wajen, shiko Bashir dakinshi ya koma ya zauna, duk yadda ya so ya samu nutsuwa ya rasata, ganinsa yayi yanata zarga-zarga bashi zaune bashi tsaye, zuwa can yasa hannun sa ya shafi kumatusa ruwa yaji, dan haka ya kalli Hannun tare da cewa "Hawaye?, Mai yasa zanyi hawaye dan d'an uwana yace yana son Nur, Mai yasa lokacin da naga an amince mata da Auren Aliyu banyi hawaye ba?" Tsaki yaja afili, sannan yaci gaba da cewa "Ashe ni ma dai wawane, wani tsaki ya sake ja, sannan yayi murmushi ya nufi bayin dake cikin dakinshi ya wanko fuskarshi.
*******
Ku tayani Jin wani al'amari mai ban mamaki, Wai Abdallah ne yaje wajen Baffah su wai yana son Nur zai aureta"
Tukunyar dake hannun Nur ce ta subece ta fadi, Karan fafuwarta yasa su Mamy waigawa gaba daya, "Abbane yace waye yayi Bari?" Cikin sauri Mamy tace "Nur ce"
"Au tana gidan ne? Agogon dake daure a hannunshi ya kalla tare da cewa "Bata wuce makaranta ba?" Cike da damuwa Mamy ta Isa bakin kitchen din kokarin shiga take taga an turo kofar, hannu tasa ta tura amman ko motsi kofar bataiba, hakan ya tabbatar mata da kulle kofar ta yi, Aunty dake bin bayan Mamy ne ta ce "Taji abin da Abban su ke fada ne fah" Shiko Abba kofar ya fara bugawa tare da cewa "Nur to mene ne na rofe kofar kuma? Ki fito mana kiji."
Nur kuwa komawa ta yi ta jingina da jikin bango bayan abincin ya bare a kasa, Ahankali ta zame ta zauna akasa, tare da kai hannunta duk biyun ta daura a ka, saidai babu ko digon hawaye a fuskarta, bakinta ta motsa tace "Na shiga uku na lalace, wannce irin masiface? Ya Allah na rokeka karka kaddaro min auran Yaya Abdallah, mugu ne, azzalumi macuci, wadda besan darajan mace ba" Kasa ta karayi da murya tace "Mazanicine ya Rabbi karka hadani aure dashi, Fasikine masharraci, idan akwai sunan da yafi na zalinci muni Yaya Abdallah ya cancanshi" Murya Mamy taji cikin rawa sosai tana cewa, "Nur daga Jin ana magana sai ki rufe kanki aciki, kina haukane? Ki bude ki fito ai ba dole ba" Shura kafa Nur ta fara kamar mai shirin yin birgima, kasa-kasa taci gaba da cewa, Mamy bazan iya kallon idan ku keda Abba ince bason Abdallah ba, idan kuma bance banson Abdallah ba, yaya zanyi da Aliyu, ina tsananin sonshi, shine irin namijin da nake son aure, yaya rayuwar shi zata kasance bayan ya rasa ni" Sai wannan lokacin hawaye ya zobo mata, yayin da taci gaba da cewa "Zaice naci amanarshi bayan Kuma ni shi nake so, zaice na yaudareshi tsawon shekara shidda, wallahi bazan iya rayuwa batare da Aliyu ba, ina tsananin tausayin shi, Kuma Yaya Abdallah wurin Baffah yaje" haura kafa ta sake yi tare da cewa "Idan ma wurin Abba ya tsaya ya zanyi ince bana son d'ansu? Bayan sune suka raineni har nazama cikakkiyar mutum, na shiga uku, zai yi wuya in tsallake auren Abdallah, ni gaskiya bazan aureshi ba, saidai idan mace tana auren maza biyu" a daidai wannan lokacin wayar Nur da ta fadi akasa tai kara, kallon wayar ta yi tare da rarrafawa ta isa gabanta ta dauka, ganin sunan Bilkisu yasa gaban Nur faduwa tare da tuna alkawarin su, cike da jarumta ta dauka, muryan Bilkisu taci cike da zaki tana cewa "Nur na je na shigar da kara har an taho kawo mishi takardan sammacin" Kasa cewa komai Nur tayi domin gudun karsu Mamy dake bakin kofar su jiyota.
Abba kuwa tuni hankalinshi ya tashi domin ko motsin Nur din basaji, dan haka yanzun da yaji wayarta tayi kara ya cigaba da kiran sunanta cikin tsayawa tare da bata Umarni ta bude kofar....
Alhamdulillah anan nakawa karshen Littafi na daya free ne, Littafi na biyu za'a daurashi ne akan manhajar Arewabooks, ku biyoni domin jin yadda zata kasance acikin Littafin na biyun kuma na karshe da yardan Allah, yanzu za'a fara wasan, wannan labarin salonshi daban ne, wadda baya anfani da Arewabooks yayi kokari ya sauke ayi Following dina @fadilalamido ko ta link din da ke kasa.
WhatsApp no: ***
https://arewabooks.com/book?id=63ea17c2c189e841487b66f2