Free chapter · Read without an account

42

by Hauwa A Usman · DAMA TA

*DAMATA* 




   

         *NA*




*BATUL ADAM JATTKO*



*Gargadi*

*Banyarda ajuyamin lbr ta kowane irin sigaba saida izini dan lbr DAMATA ba kirkirarriyar lbr bane lbr ne dayafaru da gaske sai abinda aka dan kara dan kawatar da lbr banso fadamuku lbrn Gaskiya neba sai danaga wani matsala yana neman kunnuwa dan haka akiyaye tabashi danni banyi shima saida izinin maishi kuma yanzu fara DAMATA zuwa yanzu inajin (4months)* 

*Bisssalam*


*42*



A binyi shine kiyar da muyin adua Allah ya bai yanata dan munemi yafiyar ta."


"Shid kadena min maganan yariyar nan dan ni bana son kodajin sunanta,

Kuma da kake cewa zasu nemi yafiyar ta kamanta batada tunani bata masan memuka mata ba....

"kedakata inde wannan abinda yafaru dake bai zame miki izina ba baza kitabayin nadama ba,

To albishirin ki ni yanzu kowa yasan ni mijin Fatima ne bai yananta kawai nake jira na zauna da kayana duk da bata da tunanin inason ta kuma zan gyara kuskurena yarane de kamar yanda kika fada kin tsira dasu dan bana son asirina yatonu akaran kaina ma,

Kuma kina da hakki na shayarwa da reno da kikayiwa yaran dan anbar miki bawani abubane Allah zai bata wani tunda ita tana da lfy keko baza ki taba iya haifuwa ba."


Har yagama tana jinsa kalaman suna kona mata rai amma bata da karfi da lafiyan da zatayi wani yunkurin dan haka tarabu dashi dan tasan abune da bazai taba yuwuwaba ta zauna da kishiya 


Dr Muktar zaune gaman Maman Fandau yagama mata bayani koma tunda ga kan yanda Nabil ya yaudari Fandau da yanda duk abubuwan suka kasance bai boye mata komai ba 

Mama wani irin gumine yake raso jikinta na murnan yarta tana cikin koshin lfy da kuma mamakin abinda Nabil yayi yanzu dama maganan da yafada karyane yanzu yan biyun 

Nan jikokin tane Fujjirat jikartace

" Mutari hadani da Fandau din a waya mugaisa."


"Dr yace Mama kiyin Hakuri komai yakusa zuwa karshe badan yanayin jikin Hadim bada yanzu angama da komai,

Nide fatana kar kowa yasani har sai yafada da bakin sa dan nasan halinsa."


"bawanda zaiji Insha ALLAH Muktar Allah yamaka albarka ban tabajin labarin da yafaranta min kamar wanan ba ko budewan idona banji haka ba ni Aisa ina da jikoki 4 daga Nabil haryanzu banji son ya saragu araina ba saide makaruwa dan tun farko baisan yata bace da yasani kuma sunriga sunzama taya, 

Bazai iya rabuwa da itaba shine yakulla wanan karyar dan yasamu daman zamada ita."


Dr yace"gaskiya kam kodaga yanda yayi jinya adalilinta dakuma yanda yake nemanta yayi nisa sosai akanta."


Hakade suka gama tattaunawa har yafi 

Mama cikin al ajabin duniya da mamakin yanda wai suka yaudari Malam Dauda har yadaura musu aure 


Bayan sati 4 Hadim tawarke sosai dan harta danfara takawa da sanda take takawa dan de tagamu da kwararen asbiti ne da sosai anyarda da ingancin aikinsu har an sallameta sunzo gida 


*Nabil da Fandau* sunyi nisa sosai a chat dinda sukeyi wani lokacima shiyake tabota dan yana jin dadin yanda take tsaramasa kalamai daku ma kwantar masa da hankali akan Fatiman sa dan yazu tagane itace Fatima dan tamasa tambaya cikin dabara kuma yagama ta tayi mugun jin tausayi sa dan ba abinda yaboye mata na karyan da yayi wa Iyayen duk ba gaskiya yafada ba taji dadi 

Yanzu ma da kansa ya tabota ganin tana online 


 _slm bakiye bacci bane dawa kike fira haka kode nasamu kanine_


Tana cikin bawa Akkaram nono taji message ya shigo tasan Nabil ne dan wayan nasane nashi kadai jawoshi tayi ta bude tana murmushi har ta gama karantawa ta maida masa da Ripley 

_Ameen kaima ina nema maka yardan Allah yakake ya Fuj da kuma me jiki?_


_Ameen Fuj gata tayi bacci mejiki tana dakin ta ba kinki zuwa dubata ba."_


_Ayyya Abu Fuj naji tsorone kaga matar ka tanada kishi kartamin abinda tayiwa Fatin ka_


_Hhhhhhh baza tamiki ba aike bance ina sonki ba Fatina kodan nace inason tane taji kishinta_


_hakane fa aheni akatsa nake to Allah yabarka da Fatin ka_


_Ameen nagode sister kin iya adua da gaske kinkusa aure_


_nade kusa samun mijin amma bance nasamuba_



Yace _ok_


Tace _dadi na dakai kajerce magana bakason magana me tsawo nikuma gashi yau voice naka nake sonji duk da bayau nafara jiba ba_


Bayi mamaki ba datace ba yau tafara jin muryar saba dan yasan ana fira dashi akafafen labaru dariya yayi afili yace maki gama koshin wahala ba


Audio Yayi cikin zakeken muryarshi yace "muryata kawai kike bukata kenan to gashinan ai muryata tanada araha wanda bai kaiki bama yaji akyuta balle keda kike farantamin kike tayani aduan samun *Fatina*."

Yana dariya yake maganan cikin kayatarwa  


Ai Fandau jitayi kamar ta shide dan jindadi tana sauraron muryar sa tana wani lumshe ido saida ta saurara yafi so 10

 Sannan tarubta masa Ripley 


_kasan wani abu?_

_"a a_

_Allah yayiwa muryar ka wani baiwa ko kasan dahaka?_


Yamayar mata kamar haka 


_nasani dan naji abakin mafi zakin murya acikin duk kan muryoyin duniya dan Fatima ta dabance muryar ta daban ne kullum sai muryar yamin gizo_


_bayan ita bawan taba gaya baka kenan sa ita_


_nasha ji bazan iya lissa famiki wanda suka ce ba kamar yanda bazan iya irga gashin kainaba amma inason nuna miki nata yafi kwanta min_


_Gaskiya kana fifita wanan Fatin fa zaka sa nadawo yar aunty Hadim fa_


_dako zaki rage girman ki a idona_


_Ummm saina kega kamar kafison Fatin ne wai wakafi so cikin su?_

 Yace _Uumm kinsha min wanan tambayar ina baki amsa to dukka inason su dan dukkan su matanane kuma yan uwanane amma ya isa dan bacci nakeji_

 Tayi saurin mayar masa 


_please amma meyasa nekake nuna rashin damuwa agareni kamata yayi kaji muryana nima kamar yanda naji naka_


Sarai yaga message dinta amma yasauka bai bata amsaba 


Dariya tayi tace bawan Allah kenan 


Hakan ma saida tayi recording dinta tura masa


 "shikenan dama inason nace maka nayi mafarkin kaga *Fannndo*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol