Free chapter · Read without an account

43

by Hauwa A Usman · DAMA TA

*DAMATA*


           *NA*  


  *BATUL ADAM JOTTAKO*



        *43*


*Editing AYSHA ALIYU GARKUWA*





      




*Hadim* duk suna zaune a genaral parlour su Nabil Ummi Maman Hadim,

 saiga driver yashigo da Fujjirat dan gidan Dr ta wuni sauk'eta da drv yayi ta arce dagudu tayi wajen Nabil tana cewa.

" Abuu." cikin gwarancita ware hannun sa yayi yace "Oyoyo Mamana."

sannan ya d'an kalli drive yace.

 "Kako kyauta dan yanzu nake shirin zuwa d'auko ta."

 baturen murmushi yayi yafice 


Cikin kulawa da k'auna Nabil ya shafa kan Fuj tare da cewa.

"Wow waya miki wanan gyaran? yayi kyu sosai."

Cikin gwaran cinta tace.

 " *Aunty kirki* ."


Maman Hadim tace.

 "Kaji harda wani cewa yayi kyu,

 wannan bak'ar wani kyu gareta bak'a sai sadaka."

 Hadim tace.

"Mama ai Fuj ba bak'a bace."


"Eh mejin tsoronta zaice ba bak'a bace,

 wankan tarwad'a ce,

 niko bana tsoron ta kinga dole bak'a zance mata."

Hadim tace.

 "Kalan chocolate cefa Mama tafi fari kyu yanzu su ake yayi."

Aiko Nabil dad'i har ransa dan Fandau dinsa yatuno kai ya jinjina

Yace.

 "sosai Maa sunfi shiga rai da ratsa zuciya."


Hadim sai asannan tagane ta kwafsa daure fuska tayi tace.

"Fuj zonan wai ni Nabil wacece Aunty kirki nanne a gidan Dr? 

Kullum taje ta dawo sai tayi tamin zancenta."


ido ya lumshe tare da cewa.

 "Bansan taba sunanta kawai nakeji awajen yaran gidan da Fuj."


Amma wani abune yafado masa Aunty kirki ko itace matar Dr kai ba ita bace ita da take kulle adaki tunuwa da wanan yatuno masa Akkaram d'an gidan Dr tunda yaga d'an so d'aya bai k'ara kanin saba,

 Dan yaje gidan Habiban tace,

 anfita da yaron gayana son doctor yazo su d'auki mataki d'aya amma Dr ya makale a 9ja.!


Ummi ma dariya tayi tace.

 "kai Ya Fatime kina kushe min cuwuna fa to ki dubi mace har mace kice sai sadaka,

 to kwantar da hankalin ki batayi ta tsohon naku."


Duk aka sa dariya banda Nabil da yake duniyar tunani.


Fuj tasa hannun a aljuhunta tafito dawani paper ta mik'awa Hadim 

Tace.

"Aunty kirki sweet." 

Karb'a Hadim tayi ta bud'e sweet d'inne ko a ciki an nad'e,

amma takar dar da rubutun cikin yafi daukan hankalin ta dan kullum idan tadawo da sweet d'in aciki amma da acikin pepper kuma duk rubutun irin daya ne tana karantawa amma bata daukan abin da muhin mance sai yau da taga ansa sunanta wai *mum Fujjirat*


Ga aminda aka rubuto kuma ba banbanci da na kullum 


'''Rance ba kyuta bane..! sadaka yana da ranar fansa..!

 Dutse ba abincin gara bane..!

 wani baya amsa sunan wani..!

 ajiya maganin wataran..! ~Aunty kirki~''' ..!


Hada hausar tayi amma bata fashici komai ba dama kullum hakane zata karanta amma bata fahimta,

 amma yau da tasa mum Fuj tasan ita akayiwa massage din kenan gabanta ne taji yafad'i to wacece Aunty kirki?.

 Ita dai Fuj karban sweet dinta tayi tana sha.


 Itako Hadim sai ta sauk'ata ta dauki sandar ta tana dingisawa ta haura saman, 

Wayan Habiban ta kira tana dauka tace.


"Wacece Aunty kirki?."


Habiba tace.


"Ranar ma kinmin wanan tabbayar nace miki bakuwace yar uwar Abban Nol ce.!"


"Kibani ita."


"Ok tana sama bari in kirata,

 ai tana da kirki tana son FUJJN ki."


"Ok kiratan."


Habiba ta kashe wayan tukun ta kira Fandau ta mata bayane yadda sukayi sanna takira Hadim tace.

 "To gata."

Fandau ta karbi wayan bayan tayi salama tace.

"Mum Fuj ya Fuj ta sauka lafiya?."

Wani irin faduwan gaba Hadim taji danjin muryan wada bata kaunan ji arayuwar ta amma tasan ba ita bace muryane kawai yazo d'aya 

da haka tace.

 "Eh tazo muna godiya fa da kulawan ki akan 'yarmu,

 amma wani abu da kike rubutawa bana ganewa,

 shine yau nace baride na tambayeki me fassaran sa??."


"Au wai 

RANCE BA KAUTA BA NE..!

 SADAKA AKWAI RANAN FANSA..!

 DUTSE BA RABON GARA BANE..!." 

WANI BAYA AMSA SUNAN WANI..!."

Hadim tace.

 "eh."  

"Ok kinsan yaran Aro ALLAH yabamu ba dukuba ko,

 abin da ba duka aka baka ba kinga rancene ba naka bane nasiha namiki dakuma tunatarwa yara rancene."

 "tace hakane fa to nagode dawanan tunatarwar ina fatan wataran zaki kawo mana ziyara ko?."


Wani irin bahagon murmushi mai d'an sauti Fandau tare da cewa.

"ai Aunty zuwa gidan yafi K'arfin ziyara karki damu wataran ana mugun tare."


Hadim tace.

 "gaskiya kinci sunanki Aunty kirki kinada kirki,

 to bawa Auntyn naki ko."


Fandau tana dariya ta mik'awa Habiba wayan 

Habiba tace.


"to ya k'afar? 


"Alhamdulilah da sauk'i."


daga nan suka dan taba hira dan ita Hadim bata kawo akanta wani Fandau tana kusa ba kawai tana son jinne me Aunty kirki take nufine kawai. 


Nabil ne zaune a d'an wani runfa na shan iska acikin gidanshi kiran Maman Fandau yashigo woyar sacikin murmushi ya d'auka Yace.

"Allah ya taimaki HAJIYA Mama."

 Tace.

"Ameen tareda d'ana ba."


"Mama ya gida?


"kowa lafiya amma sai rashin Fandau bawani labari ne?."


Abin yabawa Nabil mamaki dan shi bata tab'a tuntub'ar sa akan Fatima ba koda shine yamata zancen haka take cewa yayi hakuri insha ALLAH za aganta yadena damun kansa,

 sai gashi yau da kanta take tambaya,

 karfa taga gazawarsa shiko ba irin neman da bai yiwa yariyar nanba cikin rawan murya da kamar zai yi kuka yace.

 "Wllh Mama ana cikin bincike fa,

 amma har yanzu bawani labari,

 mama idan bansamu Fandau ba rayuwa bazata zo dai-dai ba yanzu nakoma bakin aikin na amma nakasa shiga filli ko sau d'aya Mama,

 amma nasa ayi istahara man agani nide na sha sawa anamin anacewa tana hannun mekyu da kaina ma nayi amma danagan ta a mafarki sai tajuyamin baya."


Cikin kuka yakarasa maganan 


Mama taji tausayinsa duk da tasan karyar da yayi.

 "Haba mesunan malam kazama namiji mana ka kuma sake kokarin nemanta dan tunkafin kagaya mana matar kace kamin alkawarin kawota da hannun ka."


Yace.

"nayi Mama amma gashinan nakasa cikawa Mama duk tunanina yakare akanta narasa yazanyi har wajen 'yan duba saida na Ayyana zuwa sai kuma naji tsoron,

 *Hukuncin Allah."*

book din Aysha Ali Garkuwa kenan mai fitowa


Mama tace. "Subahanallahi kul kai da kasa addu'a kana da Allah meyakai ka sakin reshe ka kama ganye."


 haka takoma lallashinsa saida yadan sauk'o 

Tace.

"ina Fuj?."

Yace.

"Sunfita dasu jidda da su Gana."

"kasuwa sukaje?."


"eh harda Iya da Inna ZAINABU suna da yawa sunzo

Duba Hadim ne."


"kai dana sani da nabisu nazo ai dubata nima."


"Ba damuwa Mama akwai yan zuwan jibi zansa Grema yakarbo passport dinki ayi visa dake."

"nagode d'ana." 

A haka 

Sukayi sallama 


Yau har su Maman Fandau sun sauka Hadim ta tarbi Maman cikin fara adan ita arayuwan bata da matsala dakowa sai kishiya bata sonjin wanan kalman ko ga watane ba itaba.


Shiko Nabil sai yau yabud'e sakon Fatima menaci kamar yanda yasaka mata 

Yana dariya ya bude a

Audo saida ya gama karan ta sakonnin ta duk na korafine akan kwana 2 yashare ta sai ida tace.

_amma banso mukayi irin wanan rabuwan ba dan na d'aukeda amatsayin d'an uwa dalilin haka na nemi muga juna kafin nabar kasan amma kayi burus dani inason inmaka albishi da maganan da nagaya maka na nakusa samun masoyi ya tabbata dan nasamu *mijin raina* shaharare kamarka wanda da maka dama ni burina na auri wanda ya shahara a ball dan tun ina yariyar inke da wanan raayin burina yaci ka nasamu mijin raina kaima ina maka fadan samun Fandau dinka_


_nasan kasan mesonnawa dan makusan cinka ne_

_*BILAL MAINA KANGE BG* nayi murna da zama matar abokin kaga muna tare *FATIMA MUHAMMAD GARGAR*_

*Bissalam*.


Sai pic din Bilal da yagama budewa ya baiyana afili yafurto nima ban soki ba me BilAL zaiyin dake ta haka kika bullo kuma yariya dariya yayi sosai yace amma da nake pic din kika turo da yafi dan naga yanda kike amma fa sunan Gargar yabugeshi dama yar meduguri ce kuma gargar anguwan Zannah ne.


 kunan audio nata yayi saime jin muryar da arayuwansa bazai taba banta meshiba ya fara dukan dodon kunnen sa

 kamar agabansa take maganan.

*SHIKENAN DAMA INASON NACE MAKA NAYI MAFARKIN KAGA _FANNNDO CE_*.


Meyasa tun ranan bansaya naji ba nace ina bacci ashe me irin muryan Fateena ce dan tundaga ranan bai wani sake bude message nata ba

 saiya sake dubawa *FATIMA MUHAMMAD GARGAR*

full name nata ya akayi sunan ma yazo dayan da Fatima sa gaban sane yaji yasake faduwa yace to wacece yasan de ba Fandau bace dan Fandau batada lafiya kuma me zai kawota London! amma daya duba Last seen 

Wajen 1week kenan rabonta da online yariyar da kullum sai yaganta on ya kunna 

Voice yaji so ba adadi muyar natane de ba wai gizon ne ba kawai sai ya yanke hukuncin yayi call nata har yayi dialing amma aka ce masa anrufe layin gaba daya cikin haushi yasake shiga cikin sakon nin nata yaci karo ko da sokon da take cewa.

 _To YASHIDDAS yaune tashinmu fa dan ma nasan zakaje bikin mudan yazame maka dole_ 

Afili yace.

" Towai ko da gaskene?." da sauri yagirgiza kai yace.

" Sam bade BilAL dinaba bayanda za'ayi ya shirya aure batareda ya gayamin ba."

 amma shi yanzu duk bawanan ba yafison yaji muryar wanan wanda take masa gizo da Fandau 


Yana cikin haka wayansa ya fara ringing yana dubawa BilAL ne ya dauka yana cewa.     "Kamar ko kasan kaine araina dan yanzu nake shirin

 kiranka."

BilAL yace.

"Sai kuma gani ba toya akayi?."

Dariya Nabil yayi yace. 

"kimanin 3 months kenan muna chat da wata yarinya har tace galabata mukayi dan sabo da ita to dan tamin tayin kanta nace a a, yanzu kuma naci karo da sakonta wai dama shaharata a wasan ball take so yanzu tasamu wani shima shaharare ne burin ta yacika kawai saigashi ta toromin pic dinka dan ita wawuyace."


Dariya BilAL yayi yace. "Me abin wawanta kan aciki ai wanda Fatima tayiwa tayin kanta yaki amsa shine wawa domin *DAMACE* babba sosai tazo masa yasake yarinya yar sarauta yar babban gida bata inda bata kai macce ba,

 burin kowane namiji na karbeta nikam dan gudun kar *DAMATA* ta kubcemin,

 yanzu haka ma ina airport din London zan tafi neman auren ta ahe dasai dai kaji na angwace."


"Wai dama da gaskene ?to wacece ita tacemin sunanta Fatima Muhammad garga,

 kai kuma gashi kacemin Yar sarauta ce yar wane gidane kaina yadaure? ."


BilAL yace, 

"yes da gaskene naji tausayin tane dan tafadan min tarihinta kakaf kusan irin abin da Hadim tayiwa matarka,

 aka mata saide ita ba aci nasaran sa mata alluran ba,

 kuma ita nata zalincin ma yayi yawa wai fa auren sukayi dan ta haifu su dauka sumata sakin wulakanci kuma har ta haifun yanzu haka yaranta ukku suna wajen su amma tafita da cikin nabiyu amma acewar ta wai nima nasan mijin nata masai dai dan tanason cusa masa haushi bazata gayamin ba sai bayan munyi aure, 

Da auren gaggawa naso muyi da ita saboda nina daukawa kaina lefin nina yaudareta na aureta gudun kar abata wani wada Iyayen suka zaba mata nikuma inason ta shine muka gugu na aureta, 

dan tacemin 

kishiyoyin Mamar ta zasu mata gorin taje karuwanci amma dayake ta na tsorace da abin da wancen mugun ya mata shine tace ita sai anje gaban iyayen tukun ."



Cikin firgice Nabil da yaji kamar ya dankare awajen kode Fateen sace 

Dasauri da rawan baki yace.

 "tagaya ma ya zaman ta kewansu ta kasance? tagayama ya yanayin yaran nata yake mata ko maza? 


"Eh tagayamin da farko macce ta haifa na 2 kuma twins duk maza 

Yana yin zaman su kuma labarin da tsawo idan kanason ji ka sameni a airport din dan bayanzu zamu tashiba."

 ai Nabil baima gama sauraron BilAL ba yakashe wayan jikin sa yagama bashi Fateema sace kawai da sauri yashiga gidan.


 amma me yatarar ana wani danjan da Inna ZAINABU idan maku manta ba a koi photon Fandau adakinta na itada Bagana da Mama kuma na taba cemuku Fandau da takeson koyan rubutu tarishin rayuwan ta take rubutawa to pic din yana cikin wannan life story nata ta turashi kasan bed sai yau yasmin ta fito dashi tana gama karantawa ta cikin kuka tace.

" Wllh awannan karon idan ba ayarda dani ba zanfasa kowa yaji." kunsan Yasmin lawyer ce mekare hakkin dan ADAM dan haka tana da mugum tausayi gakuma ta jima tana tara bayanan dan bata yarda da yanayin Hadim ba su Jidda ko dasu aka karanta Inna ZAINABU da Maman Fandau duk suna dakin sai da akayiwa Inna filla filla ta tusiye maman Fandau akan ta fada mata gaskiya aiko Mama ta fadi iya abinda Nabil ya fada musu dai ita bata so hakan ba ta fison taga Nabil yacire taurin kai yafadi komai da kansa kuma ko min daren dadewa tasan gaskiya zaiyi halinsa.


 

Dasauri Inna ZAINABU ta sauko har tana hardewa ta haye saman Hadim da dama Mamar ta da Ummi sun sata a sakiya ta fadi gaskiya dan dama agaban Ashuwa kanwar Hadim abin yafaru dan haka ita tazo da gudu da gaya musu shine fa gidan yasake cakud'ewa Inna tana ganin Nabil tace.

" Zonan babban munafiki itan idan shegiyar muguwa bata fad'i gaskiya ba ai kai baka isa kak'i amsamin ba."

 daganan tabasa bayani komai yace.

 "Hakane amma batun yara natane ba gaskiya bane,

"K'arya take yaran Hadim ne."


"Kunci uwar da kaida uwar Hadim din munafuki matar taka mai kugun mazanne zata ta hafi yara har ukku,

 Dama Dr Hafeez yace min bata taba haifuwa ba kuma tana da matsala,

 bazagin da banyiwa yaron nan ba har maita na daura musu har uwar Hajja meram saida naje nayiwa cin mutumci kuma nace idan Halima bata haifu lafiya ba to dasa hannun dan ta sai nayi shari a dasu yanzu haka ina cuku cukun makashi kotu,

 wannan abin ya bullu gaskiya tayi halinta ashe kune abin jefawa kotun wannan wane irin masifa ne ALLAH kakawo mu karshe zamani da mutum zai iya jin abinda yafi karfin jinsa wanan wane irin masifane?." 


Shiko Nabil bama fahim tar ta yake ba hankalin sa yana wajen BilAL ga ihun da ake masa yarasa ma meyazo d'auka cikin dan haka kawai yace "kuhada kayanku kusameni a airport."


"au ni ban isa kagayamin ba sai munje gaban uban ka za kama fadi gaskiya ai dama yasmin tace min a haifu wan fari ranan da Hadim tace ta haifu tagan ta tana sallah da sauran bayanai dan de nak'i yarda ne ashe kune mak'aryatan ko duk jikina kunne ne bazan yarda dakuba."


Shide ficewa yayi bai tsaya ba."


Zaune suke wani kebeben daki na musamman acikin airport din 

"Yanzu kana nufin har ka yanke shawaran aure batare da sani naba kenan?."


"Shiddams kenan ai ance *ASIRIN CIKI SAI HANJI* kuma kai ba auren ma kayi har kazauna da matar tayi ciki batare daka gayamin ba,

 nima kuma surprise din ka nasoyin dande kazomin da batunne da bakaji ba amma yanzu ai andena yarda da kowa yaro kayarda da kanka kawai."


Nabil yace.

 "Kai kasani niyanzu bani tarihin nata tukun."


Dariya BilAL yayi yakwashe komai yagaya masa...

Ai tun kafin yakarasa jin lbrin ya zube k'asa yanayiwa ALLAH sujjadar godiya yad'ago yana cewa Alhamdulilah Rambana."


Bilal yayi murmushi irin na nuna ana tayasa murnan nan

 Yace.

 "ai nasan dole duk wani masoyina ya tayani murna sai ma kaganta wllh nasan har kyutan kujerun Makkah sai kayi thanks kum....!"

Nabil yace.

 "Wane kai wllh itace Fandau d'ina ita nake nema." 

BilAL kamar da gaske Afirgice yace. "what!?"


"Wllh itace nima bansan yanda akayi ta samu lafiya da kuma zuwa London ba."


BilAL yace.

 "To kadawo hankalin ka dan ita taka bata tab'a haifuwa ba niko wanan ta haifu yanzu ma cikin da tafita dashi yananan tana goyon d'an,

 in maso kake na barmaka ita dan kai tafara cewa tana so to wllh baka isaba,

 nariga nakamu da sonta kariga kasaki daman ka niko bazan yarda nasaki *DAMATA* ba dan sau d'aya take zuwa arayuwa kuma inajin son....!"

Ai kafin yakarasa fada Nabil ya wankeshi da wani irin marin da yajawo hankalin Security's d'in BilAL dana Nabil suka shigo da gudu amma ganin abokai mafi kusa wanda basu isa su shiga tsakani suba yasa sukayi curku-curku shiko Nabil duk yagigice mari kawai yake zubawa Bilal ya cukumo wuyan rigansa shiko BilAL tsayawa kawai yayi yana kallon ikon Allah wai yau shi ake mari bai taba sanin mezafin mari ba sai yau sai da yagama iya marin sa yagaji har fuskan BilAL ta kumbura yayi jajir abin kida fari ga hutu sakin sa yayi kuma yadurkusa agaban BilAL din yana rokon sa yagaya masa inda matarsa take da gaske cikinta bai zube ba.

shima BilAL dur kusawa yayi yace.

 "Haba Babana me yayi zafi ka hukunta danka haka kaga yanda kamin akan mace,

 lallai na yarda mata masifane kalli yadda kamin." 

yaja hannun Nabil ya d'aura kan fuskansa shiko Nabil hanunsa yajanye yace.

"Ba maganan wasa bane seriously ina matata? 

Kai kanka sheda ne yanda nasha wahala akanta gayamin inda matata take?."

Bilal yazaro wayansa yace.

 "Ni kaga tawa banajin tana kama dataka."


Dasauri Nabil ya d'ago jajayen idon sa ya zubasu kan pic din Fandau da tayi wani mugun kyu wanda bayan kyanda tayi saida akayi editing duk yanda aka canzata idan yaganta bazai kasa gane taba yafara magana 

"kagani ko Wllh itace ina take?."

Ya Allah yasake daga hannu yana godiya ga Allah 


Daure fuka BilAL yayi.

 "To idan itace me hujjan ka kokana da huja bazan barmaka ita ba ai koda itace wllh baka isa na hakura da itaba azabure Nabil ya tashi yana tunkaran BilAL yana cewa.

"Matata cefa da aurena akanta ko atarihin kaji kalman saki a ciki da kake abbaton kana sonta zakayi mugun nadama idan bakinka yakara furta wani kalma akan matata."

a hatsale 

Bilal yace.

 "Kai kaine zakayi nadama idan kak'ara cewa kasan Fateema dan tawace ka.....!


ai BilAL bai karasa ba sabo da wani irin shaka da Nabil yayiwa makoko ransa........!



*To mabiya DAMATA yakukaga page gaba zai kasance dan kunsan dole agurfana gaban ZANNAH MODU abinda kuka dad'e kuna nema anza wajen fa ga Inna danja natafe ya Hadim zata dauki bai yanan FANDAU*

*dan Fandau tace mata rance ba kyuta bane* ...!


*karku manta fa tsakanin abokan biyu akwai rigima NABIL yayiwa BILAL rashin kirki bayan uban BilAL shine yayiwa Nabil gata ko ya manta ne


*


*B JATTKO*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol