Free chapter ยท Read without an account
KUSKUREN BAYA page 2
๐๐๐๐๐๐
KUSKUREN BAYA
๐๐๐๐
๐๐๐๐๐๐
WRITING BY
*BAGUDO& MIMI'S QUEEN*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
***
๐ ฟ๏ธ02
A firgice ta juyo Ibrahim ta gani tsaye a bayanta yana sakar mata murmushi, ta yatsina face d'inta tana kauda kanta gefe ,tsaye yayi yana kallonta gabansa na wani irin fad'uwa, musamman daya tuna shine dalilin accident din da tayi.
Cike da sanyin jiki ya k'ara matsowa daf da ita ya rage tsawonsa har tana iya jin karar bugun zuciyarsa da hucin numfashinsa a gefenta, runtse idannunta tayi ta juyo zata mishi magana karaf idanunsu ya tsarke cikin juna har saida hancinsu ya da'n gogi juna.
Tsura ma juna idanu sukai kafin daga baya tayi ko'karin da'uke kanta shima yaso yin hakan sai dai ya kasa aiwatarwa, sake juyo daita yayi akayi rashin saa hancinsu ya goge juna kanta ya bugi goshinsa . "Ouch!". Ta furta a hankali cikin Jin zafi ta kai hannunta kan bandage din dake zagaye a kanta.
"So...sor...sorry!". Ya fada a rikice , ta tsura masa Ido tare da lumshe masa Ido tana radadi , idannunsa ya runtse Shima kamar ciwon a kanshi yake , ware idannunta tayi a hankali tana kallon yadda duk yabi ya rud'e yake bata hakuri a natse ta samu guri ta zauna tuni Shima gwiwowinsa suka mazauni a gabanta Yana kallonta kmr ranar ya fara ganinta .
"I.B!". Ta Kira sunansa cikin sassanyar muryarta kamar yadda ta saba kiransa, lokaci guda ya d'ago rinannun idannunsa ya zuba mata Yana kallonta itama shi take kallo cike da tsananin tausayawa."Tan I am really really sorry for causing you so much troubles on your special day". Ya fada yana kallonta cike da kulawa da nuna lallai yana nufin abunda yake furta mata har cikin ransa.
Lumshe idannunta tayi ta bud'e a hankali " Hey is not your fault kawai haka Allah ya tsara karka yi blaming d'in kanka akan accident din Dana samu ". Ta fad'a tare da kauda kanta gefe dan ko kada'n batason ganin irin wannan yanayin nasa , dan yana karya mata zuciya .
"ni ne naja komai Kinga dole nayi blamed kains akan abinda ya faru idan ban kira ba a wannan lokacin ba this wouldn't have happened to you , nayi diverting attention di'nki I am very so......"."Oh my god I.B!"ta sake fada cike da bacin rai idannunta a rufe.
"I am s...".
"I know you are Kuma nayi accepting kaima kayi hakuri". Ta faษa lokacin data tashi tsaye tana binsa da kallo shima tashi yayi suka kalla juna murmushi ya sakar mata. Da sauri ta da'uke kanta tare da shooking d'in kanta da murmushi me sauti.
Jin sautin murmushinta yasa shima ya fad'ad'a nasa murmushi.
Taku tayi zuwa bakin window d'in shima cikin sauri yabi sahunta, yasa hannunsa biyu ya zagayeta dasu ya mannata a jikinsa, Runtse idannunsa yayi yana jin wani irin feelings d'inta, sam baisan ya rasa ta a rayuwarsa.
Bangaren Tanweer kuwa ajiyar zuciya ta sauke tare da runtse idannunta, tana matuk'ar tausaya ma d'an uwan nata da irin son da yake mata tun bata san soba yake nuna kulawarsa akanta , ta rasa mai yasa har yau bata jin sonshi cikin ranta baya ga na 'yan uwanta duk da tasan yana masifar sonta da rawar jiki a Duk abunda ya shafi lamarinta tare da rumgumarta amma ta kasa sakin jiki dashi gashi shi kusan bai da aiki saina nuna mata tsantsar so da kulawa a ko yaushe Amman hakan baya sata taji irin abunda take jin friends dinta na bata labari sai dai kawai ta biye masa, Sun jima a tsaye yana rungume da ita inda sabo ta saba da wannan hug din nasa wanda iya abunda yake iya samu kenan agunta bayan shi ba wani.
"Salamu Alai... !".
Momy tafad'a lokacin data turo kofar dakin yanayin data gansu yasa tayi saurin kokarin komawa tare da jan ko'far da sauri Tanweer ta zame jikinta daga rik'on da Ibrahim ya mata wanda shima tuni kunya ta gama rufe shi."Please Momy wait!". Ta fada lokacin data dan taka da sauri zuwa bakin ko'far tana kallon Momynta wacce ke kallonta cike ta tambayoyi ,ganin yadda take kamar tana Jin tsoron yin magana, sun dauki minis a tsaye a haka tana jujjuya ka'farta ta rasa meyasa take jin tsoron yin magana akansa duk da she don't know him.
"Tanweer I am waiting!". Momy ta fada lokacin data kalla Ibrahim wanda shima ya kasa kunne yake sauraran jin abunda ke zuciyar Masoyiyar tasa, wanda daga shi har Momy suna mamakin yadda take jimamin yin tambayar bayan she is not the type to.
"Ahm Momy!". Ta fada tana wasa da dan igiyar gaban shirt dinta.
"Oh Tan! Tunda baki da abun cewa I will have to leave inada abunyi". Momy ta fada lokacin data juya da sauri Tanweer ta riko hannunta cikin nata . "Please Mom!". Ta fada tana tabe lips d'inta cike da shagwaba kamar Wata 'yar karamar yarinya.
Yanayin yadda tayi har saida yaba Ibrahim dariya me sauti wanda bai tsamanin fitowarshi ba sai gashi ya fito, d'an kallonshi Tanweer tayi ta maida dubanta ga Momy wacce ke murmushi, ganin yadda Tanweer ta juyo a fusace yasa tayi saurin rufe bakinta da hannunta.
"Momy!". Ta Kuma kiran sunanta.
"Yes my angel!". Ta amsa itama cikin yanayin da Tanweer d'in ta kirata cikin zolaya ,d'an buga kafa Tanweer tayi a fusace ta raba ta gefen Momy ta wuce tana bubbuga ka'fafunta , Kallon juna Momy sukai da Ibrahim Momy tabi bayanta da sauri tana kiran sunanta shima jujjuyawa yayi yabi bayansu.
Tanweer na fita falon Dadynta ta nufa Kai tsaye . Ko sallama batai ba ta danna Kai, hango shi tayi zaune da system a gabansa da alama akwai abunda yake important a wannan lokacin musamman Jin ana niyyar kiran Sallar Magrib amma bai tafi masallaci ba.
"Dady! Dady!! Dady!!!". Cike da shagwaba take kiran sunan yana amsawa ba tare da ya waigo inda take ba tama kanta mazauni gefe, Ganin bai kalleta ba yasa ta fashe mishi da kuka.
Jin hakan ya k'ara d'aga masa hankali ya ajiye komai ya nufi inda take zaune. "Subhanallah me ya samu Babyna take kuka? Please tell me waya taba mun ke? Waya sa hawayenki me tsada tsiyaya ki fadamun Ko wayeshi a fad'in duniya!". Ya karasa maganar cike da zafi, dan inda akwai abunda ya tsana a duniya to bai wuce hawayen Tanweer ba.
Shigowar su Momyne ya katse mushi abunda yake fad'i nan take ya maida fad'an kansu, Tanweer har lokacin tana ji yana musu fad'a bata tanka ba sai da yayi me isarta tukunna ta d'ago. "Dady please I...inaso...". Sai Kuma tayi shiru tare da sunkui da kanta k'asa.
Da sauri Dady ya koma inda take zaune. "Me kike so? Ki fadamun komeye shi a kawo miki!". Ya fada yana hararar su Momy dake tsaye gefe guda.
Girgiza kai Tanweer tayi da kyar ta bude 'yan kananun lips d'inta. "Dama wanda na kad'e akace ban kad'e ba inason ganin shi domin nasan lafiyarsa". Ta fada cikin sanyin murya wanda ita kanta batasan tana da shiba, ta rasa me yasa tunda ta dawo hospital ta kasa samun nutsuwa akansa ta kasa cire kyawawan idannunsa daga zuciyarta.
"Tanweer yaron nan bashi ya kawo ki hospital ba, hasalima bai biyo suba ta Ina za'a nemosa Ko a samo wanda ya sansa?". Ya jero mata tambayoyi wanda yasa bugun zuciyarta k'ara gudu saboda tsoron ace bazata k'ara ganinsa ba.
"But I am worried". Ta furta hakan kamar zatai kuka.
"Please Baby karki damu kanki kan wani wanda baki sani ba talakan banza da wofi he does not deserve your worries especially your tears my Tan". Ibrahim ne ya jero mata wadan nan kalaman ganin duk tabi ta damu, tuna yadda ya shiga da'kinta ta jima bata sanda shigar shiba, ya tabbatar tausayi kawai ke damunta ba wani abuba, sai dai sam baiga abunda zaisa ta damu kanta akan wani talakan banza ba.
Nan suma mahaifinta sukaita lallashinta wannan daren da kyar ta iya cin abinci ta koma da'kinta Ko hira batai dasu ba, haka shima Ibrahim ganin mutuniyar tasa ba face tun wuri ya kama hanyarsa ya bar gidan, juyi kawai take akan makeken gadonta idan ta runtse idanunta babu abinda take gani sai kyakkyawar fuskarsa mai ษauke da kamala da natsuwa da alamun ya karantu yadda ya kamata saboda yasan mahimmancin dan adam, kafin ta gama fita haiyacinta taga yadda ya rude akanta Sai dai tayi mamakin da akace ba dashi aka kaita hospital ba, wani irin bugawa qirjinta yake da matsanancin karfi ,ta sake runtse idanunta gam bata son ganin komai sai shi mikewa tayi ta janyo system d'inta ta shiga yanar gizo.
*****
Misali karfe daya saura
Kwance minister yake akan makeken gadonsa kirar itly yana lumlumshe idanun alamun jin bacci yayinda matarsa hajiya zainab ke kwance a gefensa , dif yaga wuta ya ษauke yayinda duk wata na'ura dake aiki a d'akin ya tsaya cak ya daina aiki gidan ya ษauki shiru, shiru yayi yana mamakin d'aukewa wuta abinda bai taษa faruwa ba kenan tun kafin ya zamo minister har zuwa lokaci daya zamo minister gidansa bai taba rashin wuta ba ,yana cikin wannan mamakin
ya dinga jin motsin durowar mutane da yake dakinsa ta bangaren baya yake kuma daf da katangar gidan , ya yunkura ya mike zaune daga kwance da yake yana ฦoฦarin saukowa daga kan gadon hajiya Zainab tayi saurin riko hannunsa cikin nata, a she idanunta biyu jikinta na rawa tace "ina zaka ? "zan leka window ne ina jin kamar motsin mutane , "ba kamar kana jin motsin mutane bane, mutane ne da gaske Allah dai yasa ba yan fashi bane ?
"Yan fashi ya maimaita abinda tace cike da mamaki ?ta gyada masa kai kawai batare da ta sake cewa wani abu ba illa jikinta dake kyarma tsabar tsoro "okay Ki kwantar da hankalinki gidan nan akwai tsaro mai tsanani bana tunanin akwai damar da zai kawo yan fashi gidan nan , Ki tsaya anan ina zuwa ya karasa saukowa daga saman gadon qirjinsa na bugawa da matsanancin karfi ,da sauri ta sauko ta biyo bayansa ,a hankali ya qarasa bakin window dakinsa ya tsaya yana kallon haraban gidan inda idanunshi ya hango masa wasu mutane sanye da bakaken kaya fuskarsu rufe da face marks kowanensu rike da bindiga mutun ษaya daga cikinsu yana ฦoฦarin katse wutar data bawa haraban gidan zuwa gurin securitys da wasu bangaren , juyowa yayi da sauri hankalinsa a matukar tashe suka ci karo da hajiya zainab dake tsaye a bayansa ",wayyo Allah yarinyata ta furta haษe da yi hanyar fita, yayi saurin kamota jikinsa ya rungumeta tsam dan yasan halinta da mugun tsoro ",dan Allah ki natsu ya zaunar daita ya dauki wayarsa yana ฦoฦarin kiran number's din police bai Kai ga samunsu ba yaji an banko kofar dakinsa da karfin gaske wiki wiki sukayi da idanu ,kamil ya harske dakin da wata ฦatuwar fitila mai mugun haske zaka ษauka wutan lantarki ce jabir ya saita kan Alhaji Abubakar da bakin bindiga yayinda Anas ya saita kan hajiya zainab" move to the parlou'n ya furta yana tasa keyarsu , babu mutsu suka runtse idanunsu gam saboda tsabar tsoro a babban parlou'n gidan suka iske jaguwa zaune akan kujera mai zaman mutun ษaya ya daura ฦafarsa daya kan daya yana girgizawa hankalinsa a kwance tamkar shine mai gidan, tun kafin su karaso inda yake zaune Jibril yasa bakin bindiga zai dagi keyarsu jaguwa ya dakatar dashi da hannunsa durkushewa ministar da hajiya Zainab sukayi bisa gwiwowinsu tare da kife kansu a kasa suna rawar jiki sai dai gabadaya hankalinsu naga kofar dakin tanweer.
Securitys dake on duty suka taso ganin wutan gidan ya dauke gabadaya suna tafiya da tochligt a hannunsu suna mamaki yadda wutan gidan ya dauke gabadaya ,suna gama karasowa gurin mahadar wutan suka ji anyi kansu da bakin bindiga take suka d'aga hannuwansu sama "ku durkusa bama son ganin fuskokiku babu shiri suka yi sujjada ...
a hankali jaguwa dake zaune ya dubi Anas yana masa alama da hannunsa take ya fahimci abinda yake nufi dan haka ya soma motsa lip's d'insa " kayi kokarin kira police ko ?
da sauri hajiya zainab tayi sigil tace ",a'a..bamu kira police ba tayi maganar tana kallon mijinta " well wannan ba damuwarmu bane nasan kunsan abinda ya kawomu adaidai wannan lokacin, muna bukatar bayyanansu a gabanmu yanzu yanzu bama bukatar bata lokaci"minister ya da'n d'ago ya kalli jaguwa lura da yayi shine ogansu yace "wallahi babu kudi a gidan nan shiru jaguwa yayi yana kallonsa batare daya sake yin magana ba sai Anas ne yace "babu kudi kace ? minister ya gyada masa kai yana marairaicewa "seach everywhere ka fito min da duk abinda ke cikin gidan nan take Anas da wasu mutun biyu cikin yaran jaguwa suka shiga duduba dakunan dake parlou'n hakan yasa minister yayi saurin cewa ", kuyi hakuri karku taษa min lafiyar iyalina nasan kudi ne ya kawoku zan baku duk abinda kuke so muddin zaku barmu nida iyalinna ,gyaran murya jaguwa yayi take suka dawo inda yake jikin minister na rawa ya nufi dakin da yake ajiyar kudinsa Anas na biye dashi ghana most go uku suka fito dashi na kudi wani irin tsawa jaguwa ya bugawa minister" lallai ka cika mahainci wanda bai san darajar mahalincinsa ba ,kace babu pepa a gidan nan ? a rikice yace kayi hakuri wannan tsawar yasa tanwer dake kwance a d'akinta tana bacci ta farka a kidime ta zauna akan gadonta kafin daga baya ta sauko ta tsaya a bakin kofar dakin tana leke, hannuwanta duka tasa ta rufe idanunta jikinta na wani irin rawa saboda ganin bindigu dan parlou'n da haske sam bazakace ba wuta bane "anas .....
Jaguwa ya kira sunansa "Yesssss boss d'auko min wacan yarinyar dake lekenmu ya nuna kofar d'akin da hannunsa kai tsaye ya nufi d'akin , tana ganinsa ta saka wata razananniyar ฦara haษe da mannewa ajikin bangon d'akin Anas ya karawa tochligt din dake rike a hannunsa haske tare da tsura mata ido yana kallon kyakkyawar fuskarta mai tsananin kyau da ษaukar hankali kafin daga baya ya kai hannu zai damkota ta buge masa hannu tana kuka "don't don't ever touch me ta faษa tana sake mannewa da bango duk yadda anas yaso ya fito daita taki yarda sai buge masa hannu take, ya sake kai hannunsa a zuciye yaji an rike tsintsiyar hannunsa ya juyo a hankali idanunsa ya sauka akan jaguwa "boss gardama take ko na dauketa da wuta ? girgiza masa kai yayi "kasan bana son haka "angama boss ya mika masa hannu dan amsar tochligt din hannunsa babu mutsu ya mika masa, da hannu jaguwa ya nuna masa kofar fita kana ya haske mata fuska da tochligt...
Dam........... qirjinsa yayi wata irin bugawa da matsanancin karfi sakamakon ganin fuskarta ..
Duk ilahirin jikinta rawa yake , sai dai hakan bai hanata d'ago kyawawan Idanunta dan ganin mutumin dake tsaye agabanta ba wanda taji an kira da boss , take idanunsu ya tsarke cikin juna duk da face marks din dake fuskarsa hakan bai hanata ganin kwayar idanunsa mai zagaye da zara zaran gashi ido ba, runtse idanunta tayi tana nuna masa hanyar fita da hannunta murmushi ne ya bayyana akan labbansa cikin natsuwa ya kara taku biyu zuwa inda take makale da bango ......
DARLING'S