Free chapter 路 Read without an account

RAFEEQ Page 5

by Hajja ce 路 RAFEEQ

*RAFEEQ....*

*PAID BOOK...* #400


_*ASMY B ALIYU*_

Da

_*HAJJA CE馃憟*_



5......


Unguwar shara蓷a dake ja'in can ya nufa. Tun kafin ya gama yin parking ya kirata yace gashi a bakin gate. Sanye cikin doguwar riga ta atamfa orange da ratsin coffee brown a jiki, ta yafa 蓷an karamin vail wanda ya dace da shigar jikinta. A hankali ta isa inda yake tsaye jikin mota ya zuba hannayensa duka cikin aljihun gefe da gefe na rigar. "Shaheed Allah yasa dai lafiya dan gabaki 蓷aya hankali na ya tashi." Kallanta ya yi yana tsuke baki, gyara tsayuwar yai tare da shafa kyakkyawan gemunsa da yake ta faman she茩i. Sai da ya ja numfashi ya sauke kafin yace. "Ba gaisuwa?" Zee ta 蓷an janyo murmushi wanda iyakarsa zaman le蓳enta tace. "Sorry Shaheed ina yini..?" Amsa mata yai yana lasar lips 蓷inshi da ya fara bushewa yake fa蓷in. "Ko ke fa, daman tambayarki nake so nayi, dan Allah Zee ki gaya min gaskiya meke damun Rafeeq? Yace min 蓷azu kuka rabu but na ganshi cikin tsananin damuwa dan har asthma 蓷inshi sai da ta tashi." Wani irin zaro ido Zee tayi tana dafe kirjinta da taji ya buga da wani irin mugun karfi. Cike da tashin hankali take kallan Shaheed tana fa蓷in. "Shi me yace maka?" Shaheed yai mata wani kallo yana cewa. "Da ya yi min bayani bazan zo wajan ki na tambayeki ba, just tell me Zee meke damun 蓷an uwa na?" Ruwan hawaye ne ya fara taruwa cikin idanunta, sai dai bata bari sun sakko ba gashi bata san a gane halin da zuciyar ta ke ciki. "Kinyi shiru Zee ko ba zaki gaya min ba?" Ta wani rintsa ido tana jin zuciyarta na bugawa, bazata iya cewa Rafeeq baya santa ba. Haka kuma ba zata iya tona asirin zuciyar Rafeeq ba tunda shi be bayyana ba, ita kawai ya sanarwa cewa yana son Maimoon. "Bansan menene damuwarsa ba, nima naga baya cikin walwala da jin da蓷i lokacin da muna tare. Koda muka rabu ma yana cikin damuwa shi yasa na kirashi dan naji amma yaki 蓷agawa shine dalilin kiran da kaga nayi maka ina tambayarka ko yana gida? Kace bari kaje ka duba." Shaheed ya sake jan lallausan gemensa yana kuma tsuke baki kamar wanda yake shan alawa. "We have to figure out Zee, Ina tausayin Rafeeq abubuwa sun masa yawa, wallahi bana san kuma yazo ya dinga ganin ko dan iyayensa basa raye ne yasa duka wa蓷annan problem 蓷in sukai masa yawa. Yana da heart problem ga ulcer sannan uwa uba asthma 蓷in nan. Dan Allah Zee kiyi iya yinki wajan ganin kin cire masa tunani da kuma yawan shiga damuwa. Ya kamata ma ku fara maganar aure dashi, ko ke baki shirya ba?" Wani irin murmushi Zee ta saki wanda dashi gwara dukan kawo wu茩a dan yadda zuciyarta takeyi ka蓷ai azaba ce. Taya zata sanar da Shaheed cewar ba ita Rafeeq yake so ba? Ya zata sanar dashi cewar ba ita Rafeeq yake so ya aura ba? Taya zata gaya masa cewar Maimoon 茩anwarsa, jininsa ita Rafeeq ke so yake kuma san ya aure ta? Yarinyar da kwarjininta ka蓷ai ya hanashi bayyana mata sirrin dake ransa. "Idan kina yin shiru Zee zuciyata babu abinda bata rayawa. Ki fito ki gaya min menene abinda yake faruwa? Dan naga alamar kinsan wani abu game dashi." Kallanshi tayi da sauri kuma ta janye ganin idanunsa na neman sanya ta fallasa abinda ba huruminta ba. "Sai dai idan kana ganin babu damuwa ka tafi dani wajansa 茩ila ya iya gaya min." Wani irin bu蓷e idanu Shaheed yai yana fa蓷in. "Kai a'a Zee Daddy na nan, idan yaga kinje wajan Rafeeq har ya tabbatar da cewa ke budurwarsa ce zai iya fassaraki ko ya saki a wani matsayi marar da蓷i. Kawai dai zanyi 茩o茩arin ganin kunyi waya dashi a yau. Sai ki bugi cikinsa da irin salonku na masoya." Ran Zee ya fara 蓳aci da murya marar da蓷i tace. "Mubar wannan maganar please." Ya jinjina kai tare da cewa. "Shikenan ni zan wuce." Ta 蓷an matsa baya daga wajan motar tana cewa. "Agaida Maimoon." Yana murmushi jin an fa蓷i 拼ar uwarsa yace zataji, ya shiga motar ya bar gurin. Juyawa itama tayi jiki babu kwari ta shiga gida. Tana shiga parlor ta tarar da Ammie 蓷insu ta fito daga 蓷aki, harara ta zabga mata cikin 蓳acin rai take cewa. "Kin fita wajan Rafeeq 蓷in ne? Wai ni Zainab yaushe zaki yi hankali ne? Duk samarinki masu son auranki kin茩i basu fuska kin biyewa wancan yaron da ba shiryawa yayi ba ko? Toh bari kiji na gaya miki, tun wuri ki rabu dashi ki kama dahir, ga Salis nan babu irin nacin da baya yi akan ki bashi dama kin茩i. Last warning Zainab, kodai kice Rafeeq ya turo manyansa, ko kuma ki fita daga cikin rayuwarsa bana san sakarci." Tana kaiwa nan tabar wajan, Zee ta lumshe ido tana jin wani mugun tashin hankali. 茒aki ta shiga da gudu ta isa wajan madubi jikinta yana wani irin rawa, kallan fuskarta tayi hawayen da take 蓳oyewa suka shiga zirarowa saman fuskarta, kanta ta shiga ka蓷awa side by side a fili take fa蓷in. "Wane cikas gareni da ba zaka iya aure na ba Rafeeq? Me yasa dole zuciyar ka sai Maimoon wacce ba ta san ma kana yi mata soyayya ba? Ina sanka Rafeeq domin ka riga da ka zama zuciya ta (Albi), ka so ni please Rafeeq kar ka barni cikin tashin hankalin rayuwa." Kamar daga sama taji ana cewa. "San maso wani 茩oshin wahala, kina cikin gararin rayuwa Zeety." Da sauri ta waigo tana zare idanunta da suka yi jawur saboda kuka, ganin Sofia Yayar ta yasa ta juyawa ta fara ninke veil 蓷in da ta ciro a kafa蓷arta. Itama Yaya Sofia cikin rashin damuwa da 茩in kulawar da Zee ta bata yasa taci gaba da cewa. "Shi so dama haka yake idan bakai dace ba kamar dai yadda baki dace ba Zeety. Kina san Rafeeq amma shi bake ce a cikin tsarin sa ba, sai kiyi ha茩uri ki kuma yi addu'a Allah ya kawo miki nagari mai sanki." Zee ta juyo kallan Yaya Sofia tayi cikin zafin rai take fa蓷in. "Kina so kice shi ba alkairi na bane? Yaya Sofia idan ba zaki min addu'a Allah ya bani Rafeeq Habeeb Gwarzo ba kawai kiyi shiru kici gaba da zubamin ido." Sofia ta nufi wardrobe tana cewa. "Allah ya kyauta." Daga haka taci gaba da abinda ya shigo da ita 蓷akin, yayin da Zee ta koma kan gado tana ci gaba da hawaye. Sai wajan karfe takwas na dare sannan ya iya fitowa daga side 蓷insu. Sanye yake cikin jallabiya hannunsa ri茩e da wayarsa ya nufi cikin gidan. Dai-dai inda zaka shiga entrance 蓷in gidan cikin baranda yaji muryarta da alama waya take yi da Abdul-Wahaab, ji ya yi gabaki 蓷aya zuciyarsa ta wani hargitse saboda babu abinda ya tsana a duniyar nan irin yaga Maimoon tana waya da Abdul-Wahaab, gaba 蓷aya sai ya waniji duk ya ru蓷e. Tafiya yaci gaba da yi har ya isa wajan 茩ofar shiga, yana 茩o茩arin mur蓷a handle yaji tayi masa magana abinda bai zata ba. "Yaya Rafeeq." Cak ya tsaya kafin ya 茩arasa bu蓷ewa ya shige ciki dan idan ya tsaya tabbas zai iya yi mata abinda batayi tsammani ba. Maimoon ta rintsa ido Yaya Rafeeq akwai wulakanci ta rasa me yasa har ita wani lokacin baya saurarawa a cikin izzarsa. Kaitsaye kitchen ya shiga ya 蓷auki electric kettle, kayan dafa black tea ya zuba a ciki ya jona sannan ya janyo kwai guda biyu yasa cikin tukunya yana dafawa kafin ya koma parlor ya zauna. Yana canza Channel zuwa ta resetlling ta shigo parlorn murmushi 蓷auke a saman fuskarta. Wajan da yaje ta nufa, gabaki 蓷aya 茩amshin khumran jikinta ya kusa hargitse masa kai, yai saurin mi茩ewa ya nufi kitchen. Bayansa tabi cikin shagwa蓳e fuska tana masa magana. "Haba Yaya wai me nayi maka ne? Gabaki 蓷aya ka canza min Allah zan gayawa Daddy, Yaya kunake gani naji da蓷i a rayuwa ta amma kai sai wani shareni kakeyi kuma bansan menayi maka ba." Maimoon ta 茩arasa maganar cikin yanayi na son fashewa da kuka. Sai da ya kashe kettle 蓷in sannan ya dawo kusa da ita ya juya mata bayansa tare da dur茩usawa alamar ta hau. Zaro ido Maimoon tayi tana ja da baya cike da mamakinsa take fa蓷in. "Yaya me zanyi haka?" 茒an murmushi ya saki wanda iyakarshi saman le蓳ensa, ba tare da ya kalleta ba yace. "Goyaki zanyi yadda zaki gane cewa bana wulakantaki." Ya mi茩e tsaya tare da matsawa dab da ita har numfashinsu yana bugar musu fuskar juna, ta sake turo lips tana kuma ha蓷e rai. Kallanta yake yi da dukkan nutsuwarsa yana jin tamkar ya shigar da ita cikin kirjinsa sai dai basu saba irin wannan wasan ba. Yatsunsa biyu yasa tare da 蓷ago ha蓳arta sukai kallan cikin ido, ta sake turo baki cikin yanayin shagwa蓳a da ta gama zame mata jiki. Yadda tayi ba 茩aramin sake tayarwa da Rafeeq hankali tayi ba, cikin sauri ya janye hannusa yana komawa ya bu蓷e tukunyar da yake dafa kwan yana fa蓷in. "Ban san me kike so a waje na ba Moon." Cikin kitchen 蓷in ta sake binshi tana le茩a tukunyar da yake tsaye a wajan, yatsina fuska ta shiga yi tana ta蓳e baki take fa蓷in. "Yaya maimakon ka soya kawai sai ka wani dafa? Ni bana son dafaffan 茩wai, ko zanci sai dai gwaiduwa." Yana tsamewa yasa cikin 蓷an bowl mai 蓷auke da ruwan sanyi yake cewa. "Dama ni bake na dafawa ba." Maimoon ta ware idanu tana kallansa, a jikinsa yaji cewar shi take kallo dan haka ya 蓷ago a hankali ya zuba mata sexy idanunsa cikin na ta da suke farare kal. Ganinta kawai cikin kitchen tare dashi yasa shi jin tamkar a cikin gidan auran su suke tare. Da sauri ya juya, kofi ya 蓷a茩茩o yaje ya zuba tea 蓷in ya suba zuma a ciki, bowl 蓷in 茩wansa ya 蓷auka ya nufi hanyar fita daga kitchen yana cewa ta taho masa da gishiri. Yana gaba tana bayansa ganin zai fita dan ta 蓷auka a parlorn zai zauna tace. "Yaya Rafeeq." Maimakon ya amsa sai ya juya yana mika mata hannu alamar ta bashi robar gishirin. Bayanta ta mayar da hannunta tana sake kura masa ido. Tafiya yaci gaba da yi tana binsa har suka isa part 蓷in su, gab da zai shiga nashi yace da ita. "Bani kije ki kwanta dare ya yi." Da wata murya tace "Magana fa zamu yi Yaya." Kamar yace ba zai yi ba sai kuma ya shiga ciki, akan sofa ta zauna tana janyo bowl 蓷in kwan nashi ta fara 蓳are masa. "Yaya magana zamu yi daku kai da Yaya Shaheed but kaine kawai nake samu free Ya Shaheed tunda kuka dawo 茩asar nan Allah ya zuba masa yawo.." Wayar sa ce ta shiga ruri Maimoon dake kusa da wayar tasa hannu ta janyota. 'My Zee' Shine sunan da yake ma茩ale a wayar, haka kawai ta samu zuciyarta dajin babu da蓷i kawai ta zubawa sunan ido. Tashi ya yi yaje wajanta tare da kar蓳e wayarsa, ganin mai kiran yasa shi kallan Maimoon yana cewa. "Kije ki kwanta gobe sai muyi maganar idan Shaheed 蓷in ya dawo." Jikinta na wani irin tsuma irin na takaicin nan taci gaba da 蓳are masa, bata kalleshi ba tace. "Kayi wayarka ni ina ruwa na daku. Zan jira ka gama muyi maganar." Har wayar ta katse bai samu ya 蓷aga ba, sake kira akai yaje ya kar蓳i bowl 蓷in daga saman cinyarta yana cewa. "Kije kar Aunty taga bakya nan, idan na kammala uzuri na zanzo sai muyi maganar." Afusace ta mi茩e ganin yadda yake ta wani korarta daga 蓷akin. Zagaye shi tayi zata fice kawai taji ya ri茩o mata hannunta, ta sake tsuke fuska tana san 茩wace hannunta ya wani janyota zuwa right side 蓷inshi bayanta na jikin kirjinsa tana jin bugun numfashinsa a gefen wuyanta. Hakan yasa taji ta shiga cikin wani mugun yanayi, husky voice 蓷inshi ta 蓷aki cikin kunnanka yana cewa. "Sorry." Yana kaiwa nan yaja hannunta ya zaunar da ita cikin sofa shi kuma ya daga kiran. "Hello." Zee ta lumshe ido lokacin da muryarsa ta ziyarci cikin kunnuwanta. "Ina Maimoon?" Yaji ta jeho masa wannan tambayar, inda Maimoon 蓷in take ya kalla yaga tana ci gaba da 蓳are masa 茩wan yace. "Lafiya lau." Zee taji wani irin zafi a zuciyarta sai kace ba ita ta tambaya ba ya bata amsa. "Ance baka jin da蓷i duk soyayyar Maimoon din ce?" Hannu yasa yana shafa kyakkyawar fuskarsa tare dajan dogon hancinsa da ya 茩arawa fuskar tashi mugun kyau yace da ita. "Yeah." Ya fa蓷a mata iya gaskiyarsa. Wani irin kishi ya tasowa Zee ta daure duk da yadda zuciyarta ke zafi tana fa蓷in........




#ASMY B ALIYU

#HAJJA CE馃憟

#Rafeeq Gwarzo

#Maimoon Gwarzo

#Zee Leeman

#HANNU BIYU

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol