Free chapter · Read without an account

BABI NA ƊAYA

by Fatima Eshak · FATHIYYA

Page__1.


*FATHIYYA*


Na

*BILLY S FARI*

Da

*UMM ASGHAR*


*YAN TAGWAYE.....*✍️

*PAID BOOK....*#400


GA MASU BUKATAR ƳAN BIYU DUKA GUDA BIYAR 1500

GUDA HUDU 1300

GUDA UKU 1000

GUDA BIYU 700

GUDA DAYA 400

_*RAFEEQ*_ (Hajja Ce & Asmy B Aliyu)

_*MUNƊO*_ (Ayusher Muh'd & Zee yabour) 

_*FATHIYYA*_ (Billy s fari & Umm Asghar)

_*.ZAMANINMU A YAU*_ (Nana Ɗiso & Jiddah Aliyu)

_*IYALINA (A'ilaty)*_ (Zainab Bawa & Sadiya Nasir Dan)

________________________________

   Tun tashin ta sallar asuba bata samu ta koma ba kasancewar daga ita har maigidan masu fitar sassafe ne, tana gama azkar ɗinta ta wuce kitchen don haɗa musu abinda zasu yi breakfast, duk da cewa tana da wadatattun ma'aikatan dasu ke taya ta aiki amma tafi son ta ciyar da maigidan ta daga abinda ta sarrafa da hannunta.


Yam fritters ta soya wato doya mai kwai sai tayi soup din kayan cikin rago, black tea ta dafa haɗe da kayan kamshi da ɗan flavour na strawberry da ta zuba a ciki. 


Sai da ta tabbatar komai ya kammala ta shirya a kan table kafin ta wuce zuwa bedroom don ta shirya, har wannan lokacin maigidan ta Farouq na naɗe a kan gado yana bacci.


Girgiza kai tayi ta wuce Bathroom tana murmushi "shi dai sweetheart baya gajiya da bacci" ta faɗi hakan cikin zuciyarta, fitowar ta daga banɗakin yayi daidai da tashin shi daga bacci.


"Good morning sweetheart, gara kayi ƙoƙari ka tashi ka shirya kada fa muyi latti" ta faɗa tana ƙarasawa gaban dressing mirror tana mai tsane jiƙaƙƙen gashin kanta da ta wanke da ɗan karamin towel.


"Mtss... Wallahi baccin nan bai isheni ba" ya ce yana ƙara ƙudundunewa cikin duvet.


Har ta gama shiryawa cikin atampar Julius Holland dinkin A shaped doguwar riga yana kwance bai motsa ba, kan gadon ta hawo haɗe da cewa, "Sweetheart ka tashi haka, ALLAH za muyi latti idan baka tashi ka shirya ba". Ta ƙare zancen tare da kai hannunta ta shafo fuskarshi, fuskarta ɗauke da murmushi, riƙe hannun yayi haɗe da kissing ɗin 'yan yatsunta kafin ya janyota gaba ɗaya cikin bargon ita ma ya rungume, kissing ɗinta ya shiga yi ta ko ina, kafin ta samu da kyar ya tashi ya shiga wankan ita kuma ta hau tattare ɗakin ta gyara. Bayan fitowar shi ma da taimakon ta ya shirya cikin Navy blue suit ɗin kamfanin dolce and gabana, shirt ɗin ciki kuma kalar sky blue.


Sosai yayi mata kyau a ido har ta kasa kau da kai daga kallon shi har sai da ya hura mata iska a fuska, kawar da kanta tayi tana murmushi cikin jin kunya don ba yau suka fara hakan ba dama. 


Duk da yadda mutane ke yawan faɗin kyawun ta, a karan kanta kuma ta san ita ɗin mai kyau ce amma har kullum ta kalli Farouq sai ta raina kyaun da take da shi domin kuwa shi ɗin kyakkyawa ne irin kyaun da idan yana yawa zata iya cewa har yayi mishi yawa, saboda tun daga saman shi har kasan shi Allah ya wadata shi da kyakkyawar ƙira, babu ta inda aka rage halittar shi komai na shi kamar shi ya zabawa kan shi.


Yana gaba tana biye da shi a baya hannunta ɗauke da hand bag ɗin ta da kuma jakar laptop ɗin shi sai mayafin da zata yafa da ta saƙala a kafaɗarta.


Saukowarsu kenan suka ji ƙarar door bell, a tare suka kai duban su ga bakin ƙofar suna tunanin wane baƙi suka yi haka yanzu da sassafe, ajiye kayan hannunta tayi akan kujera jin ana cigaba da danna ƙararrawar babu ƙaƙautawa, ta warware mayafin ta yafa tunda bata san wa zata tarar a bakin ƙofar ba ta tafi don ganin waye.


Gabanta ne yayi mummunar faɗuwa ganin wacce ke tsaye a bakin ƙofar, a sanyaye ta ce "Mami sannu da zuwa" tare da kaucewa ta bata wuri don ta wuce.


Wani irin wulaƙantaccen kallo ta watsa mata kafin ta shige ciki ba tare da ta amsa sannun da take yi mata ba, shi kanshi Farouq ɗin sai da yaji faɗuwar gaba da ganin Mamin a daidai wannan lokacin don yasan tunda ta doka musu irin wannan sammakon to ba zuwan daɗi ne tayi ba. "Sannu da zuwa Mami" ya ce tare da zama akan kujera yana gaisheta.


Fathiyya kuwa a sanyaye ta mayar da ƙofar ta rufe tare da janyo ƙafafunta da suka daɗe da mutuwa ta dawo cikin parlour don ganin nan da ta yiwa Mami ya sanyayyar mata da jiki kwarai da gaske, da akwai yadda zata yi ba zata koma ciki ba ficewarta zata yi ta bar gidan don tasan mawuyacin abu ne ba'a yi mata sanadin ɓacin rai ba a safiyar nan, zama tayi a ƙasa kan rug ɗin dake shimfiɗe a tsakar parlour kafin ta russuna tana gaishe da Mamin.


Da ƙyar kamar bata so ta amsa mata da lafiya kafin ta maida dubanta wajen Farouq suna cigaba da magana, tashi Fathiyya tayi ta nufi wajen dining ta ɗebo dukkan kayan breakfast ɗin da ta haɗa ta kawowa Mamin, sai dai tun kafin ta ajiye ta ce mata "kinga kwashe kayan tsiyarki ni ba abinci nazo ci ba, ko da kika ga nayi sakkon zuwa sani nayi idan ba hakan nayi ba ba lallai ne na samu ganin Farouq a kurkusa ba tunda shi ya mayar da kan shi bawan mace bai ajiye komai ba sai hidimarki, duk wani abu idan har bai shafeki ba to baya da wani muhimmanci a wurin shi".


A sanyaye ta juya don ta mayar da kayan kan table ɗin Mamin ta ce "idan kin kai sai ki dawo domin kiji dalilin zuwa na bana so kiji wai wai a gari kice an munafunce ki gara ayi komai a gabanki tunda dai ba tsoron ki ake ji ba".


Dawowa tayi ta zauna anan ƙasan rug ɗin bayan ta mayar da kayan, gabanta na wata irin faɗuwa don bata san yau kuma da wacce Mamin tazo ba, sai da ta kalleta kallon tsaf kafin ta maida dubanta ga Farouq ɗin tace "dama zuwa nayi na faɗa maka mun gama magana da Hajiya Halima ƙawata gidan Senator Bashir Dala kan cewa zaka je ku daidaita da Sameera don zaman nan naku ya ishe ni haka nan, aure shekara uku ana neman shiga ta huɗu amma har yau babu wani motsi, duk ga sa'annin aurenku nan har da masu yara biyu don Hajjajun Yaya Asabe ma da yake a jejjere take yin haihuwar ai cikin na uku ne da ita sai kai ka tsaya da mace ɗaya kamar rai alhalin ba wani abu take tsinana maka ba, yo me za'a yi da macen da ba zata iya samar maka da sanyin idaniya ba.


To gara ka buɗe kunnuwan ka da kyau ka saurareni aure a tsakanin ka da Sameera babu fashi, umurni ne nake baka ba shawara ba don gama nasan halinka yanzu ne zaka fara zille-zille har sai kasan yadda kayi ka kaucewa batun auren nan tunda ai ba yau muka fara yin hakan da kai ba, wallahi tallahi kaji rantsuwa irin ta ɗan musulmi baka isa ka kaucewa wannan auren ba don haka tun wuri gara ka fara shiri ka kuma san me zaka je ka faɗawa mahaifin ka don bazan lamunci ku haɗu ku ruguza batun auren ba kamar yadda kuka yi tayi a baya".


"Ke kuma" ta juya akalar maganar ga Fathiyya "ai dai kin ji dukkan abinda nace to gara ki san da sani ba zan yadda da zamanki ke ɗaya ba alhalin babu wata ƙaruwa da zamu samu daga gareki, tunda dai ke cikinki bana ɗaukar ƴaƴa bane to gara Farouq ya auro wacce zata haifa mishi zuri'a ko shima ya samu yaga ƙwan shi a duniya".


Tunda Mami ta fara magana Fathiyya ta sunkuyar da kai idanunta na zubar da hawayen da ta kasa haƙurin riƙesu har Mamin ta bar gidan, shi kan shi Farouq ɗin zancen na Mami ya doke shi duka mai tsanani domin kuwa bai tsammaci jin makamancin zance irin wannan daga bakin Mami a daidai wannan lokacin ba duba da cewa an ɗan kwana biyu da ta ɗauke hankalinta daga al'amuran gidanshi ta mayar kan batun auren ƙanwarshi Suhaila da za'a yi, ta kawo miji ba irin wanda Mamin keso ba don haka tace sai dai Suhailan ta kawo wani mijin ba wannan ba ko kuma ita ta haɗa ta da ɗaya daga cikin ƴaƴan ƙawayenta shi kuma mahaifin su yace bai san zance ba domin kuwa shi dai bai yadda da yiwa ƴaƴan shi auren dole ba, idan har ya duba mutum yana da nagartar da zai iya bashi aure to fa lallai zai bashi in har yarinya ta nuna shi take so, to akan case ɗin da ake kenan don haka ta ɗan tsahirta musu da batun ƙarin auren Farouq ɗin ashe dai ba mancewa tayi ba tana tune kwanton ɓauna kawai tayi musu sai da ta bari sun sakankance sun saki jikinsu sannan tazo zata wargaza musu kyakkyawan zaman su da suka faro cikin soyayya da ganin girman juna.


Miƙewa tayi tsaye tana gyara yafen mayafinta ta cewa Farouq "ka dai ji na faɗa maka ka samu lokaci kaje ku gana da Sameera don daga ni har Hajiya Halima baso muke yi auren yaja wani dogon lokaci ba".


Bin bayanta Farouq ɗin yayi don yi mata rakiya zuwa harabar gidan inda direba ke zaman jiranta, dama 'yan makaranta ta biyo ana ajiye su tace wa driver ya kawota gidan Farouq ɗin don tasan idan har ba sammako tayi musu ba ba lallai ne ta same su a gidan ba tunda dukkansu suna fita aiki.


Har ta shiga mota ya rufe mata ƙofar tana jaddada mishi lallai ne kada ya tsallake maganarta yaje ya samu Sameera su daidaita kansu.


*****.  ****.  *****.   

  Kwance yake saman wani irin katafaren gado na royal ya jingina jikinshi a jikin allon gadon tare da harɗe ƙafafuwan shi dake miƙe ɗaya kan ɗaya yana ƙarewa matar tashi dake tsaye a gaban madubi tana feshe jikinta da kalolin turaruka masu matuƙar ƙamshi da zasu kai kala bakwai dake jere a saman madubin kallo, ajiyar zuciya ya sauke a hankali jin wani abu na fisgarshi ganin yadda take motsa laɓɓanta data ɗauko lipstick tana ƙara shafawa bayan kwalliyar data gama cancare fuskarta da ita yanzu, ɗaurin ɗan kwalin dake kanta ta ƙara daidaitawa haɗe da gyara zaman yalolon mayafin dake jikinta ta ɗauki tsadaddar jakarta ta kamfanin Louis Vuitton dake gefe ta rataya sannan ta juyo ta zubawa mijin nata idanuwa da tuni ya shagala da kallonta ta cikin madubin, a hankali ta fara motsa baki tana yatsine fuska haɗe da kiran sunanshi kusan sau uku bai ji ba, sai a karo na huɗu da ta ce "Haba Mahmoud wai meye haka don ALLAH sai faman kiran ka nake yi kayi banza dani kana faman kallona sai kace baka taɓa gani na ba, gaskiya ni bana son irin haka". Ta ƙare zancen tare da juyawa tana sake kallon kanta ta cikin madubin haɗe da gyara zaman danƙareriyar sarƙar Gold dake wuyanta, yadda Mahmoud ke sauke ajiyar zuciya tare da lumshe idanuwanshi ya buɗe ta jikin madubin yana ci gaba da kallonta ya saka ta taɓe baki, a zuciyarta kuwa faɗi take yi "Ka ji da baƙar jarabarka can don ni bani da wannan lokacin yanzu".


Kamar yasan me take faɗa cikin sanyin murya ya ce "Zinnira! Wai yanzu kina nufin da gaske fita zaki yi ba tare da kin bani haƙƙina ba? Ko kin manta cewa ni ɗin mijinki ne kuma ALLAH ya halatta na neme ki a duk lokacin da nake da buƙatar hakan matuƙar kina cikin tsarki? Don me zan riƙa bibiyarki tun jiya ki bani bayan kin san ina da tsananin buƙatar hakan kina wulaƙantani? ba kya gudun mala'ikun ALLAH su tsine miki ne...". 


Tun kafin ya ƙarasa rufe baki ta juyo cikin ɓacin rai tana ɗaga mishi hannuwa fuskar nan tata a haɗe take cewa "Ahh..ahh dakata Mahmoud bana son haka! Ya zaka yi mini irin wannan fatan tunda ba hanaka haƙƙin naka nake yi ba kullum, in dai ba jaraba da son takura ni ba ai kasan da zancen fitar nan da zan yi tunda safe? me yasa baka nemi haƙƙin naka ba tun shekaran jiya sai jiya da yau, kaima kasan ba zan iya ba saboda cikin mutane zan shiga, kuma jikina ba zai iya ɓoye wahalar da zan sha ba".


"Amm..Nira mutane fa kika ce, sun fini ne?".


"Wait Mahmoud, kai kasan hakan da zaka yi zai iya haifar mun da gajiya da kasalar da zan kasa iya aikata abinda ya kai ni, saboda haka mu bar wannan zancen kawai ni gaskiya bana so, kuma kar ka sake yi mini irin wannan fatan na tsinuwar mala'ikun ALLAH, don wannan mugunta ne". Ta ƙare zancen cike da ɓacin tare da takowa gaban bedside drawer ta ɗauki key ɗin motarta ta fice daga ɗakin, runtse idanuwa Mahmoud yayi wani irin ɓacin rai na taso mishi haɗe da dafe goshin shi kafin can ya furzar da wata irin iska mai zafi daga bakin shi haɗe da miƙewa da sauri yabi bayanta, cikin sassarfa yake saukowa daga stairs ɗin da aka fidda tsarinsa tamkar shape ɗin S yana kiran sunanta ganin ta kusa sauka.


"Nira, Zinnira..magana fa nake yi miki". 


Tana jin shi ta yi banza da shi har sai data ƙarasa sauka ƙasa sannan ta juyo tana kallon yadda yake saukowa da sauri da sauri, lokaci ɗaya kuma tana ɗagawa masu aikin gidan hannu da ganinta ya sa su zubewa ƙasa suna gaisheta tare da basu umurnin ci gaba da aikace-aikacen da suke yi na goge-goge da share-share cikin palour.


Cikin ɓacin rai ya ƙaraso gabanta yana yi mata wani mugun kallo haɗe da cewa "Me kike nufi dani kenan?". Ya ƙare zancen yana watsawa masu aikin dake ƙoƙarin gaishe shi wani irin kallo daya sa duk suka bar wajen da sauri, zai sake magana ta ɗaga mishi hannu tare da folding hannayenta akan ƙirji tana kallon shi, tamkar wani sauna sai kuma ya kasa cigaba da cewa komai har sai da ta ce "faɗa mini yanzu ya kake so nayi Mahmoud?"


"Sarai kin san ko me nake so kiyi Zinnira, don haka ki juya ki koma daga ciki saboda sam bazan iya jurewa ba"


"Ya zama dole ka jure kuwa Mahmoud har zuwa lokacin da zan samu damar hakan, ko ka manta cewa mun tara mutane masu matuƙar muhimmanci a daidai wannan lokacin kuma ni kaɗai suke jira yanzu?"


"I don't care koma meye Zinnira, su mutanen da kuka tara sun fini muhimmanci ne ko sun..." Saurin katseshi ta yi ta hanyar ɗaga mishi hannu, kafin tayi tsaki tana bin shi da kallon ƙasa da sama tace "kaga Mahmoud bani hanya na wuce kana sake ɓata mini lokaci". 


Ta raɓa abinta ta gefen shi ta wuce cike da takaici tana ƙwalawa drivernta Idris kira don gaba ɗaya Mahmoud ya gama ɓata mata rai, bata tunanin ma zata iya driving da kanta.


Tamkar wani wawa ya bita da kallo sake da baki yana riƙe ƙugunshi cike da mamakin kalamanta, wani irin baƙin ciki da raɗaɗi yake ji a cikin zuciyarshi tare da tambayar kanshi yadda aka yi matar tashi ta canja mishi gaba ɗaya, sun koma tamkar ba auren soyayya suka yi da ita ba kullum cikin tashin hankali da matsaltsalu suke.


"Ya ALLAH" ya faɗa yana mai riƙe mararshi dake yi mishi wani irin ciwo tare da neman ɗaya daga cikin kujerun dake tsakar falon ya zauna yana jingina kanshi a jikin kujerar ya dafe kanshi haɗe da rufe idanuwanshi yana karanto addu'o'in daya sani a bakinshi don nemawa kanshi samun sassaucin abinda yake ji a zuciyarshi da kuma cikin jikinshi gaba ɗaya.


Mahmud dogo ne, shi ɗin ba fari ba ne ba kuma za'a ce mishi baƙi ba kalar fatar shi itace turawa suke kira da chocolate color, jikinshi irin lanky ɗin nan ne wato baya da jiki sam sai dai kuma yana da faffaɗan ƙirji da tsukakken ƙugu, yana da very coily hair irin na fulanin ƴan asalin garin Gombe don shi ɗin haifaffen can ne ya fito ne daga ƙaramar hukumar Nafaɗa, sannan yana da saje da ya haɗe da quarter million ɗinshi, yana da matuƙar tsare gida sosai da rashin ɗaukar raini, amma ga Zinnira duka tasirinsu dusashewa yake yi saboda yadda yake tsananin ƙaunarta, duk zafin ranshi da tsare gidanshi basa amfani akanta, shi yasa take yi mishi duk abinda taga dama ba tare daya iya ɗaukar kowane irin mataki a kanta ba.


Zinnira kuwa tana kai wa bakin ƙofar ficewa daga cikin falon drivern nata na ƙarasowa, cike da girmamawa ya gaishe ta ba tare da ko kallon shi tayi ba balle yasa ran zata amsa mishi gaisuwar ta cilla mishi makullan motar ta wuce abinta, da sauri ya juya ya nufi wajen motar bayan ya caɓe makullan tare da buɗe mata gidan baya ta shiga don dama tun kafin ya ida ƙarasowa ya danna remote motar ta buɗe, tana shiga ya rufe mata haɗe da zagayawa ta ɓangaren driver ya shiga sannan ya tayar da motar, tun daga nesa gate man ya wangale musu ƙatuwar gate ɗin yana russunar da kanshi ƙasa alamun gaisuwa a wurinta, bai ɗago ba sai da yaga sun wuce sannan ya sake maida ƙaton gate ɗin ya rufe yana tsinewa girman kai da wulaƙanci irin na matar gidan, wanda sam ko wanda ya ajiyeta a gidan baya yi musu haka.


Sai da suka hau kan titi sannan cikin girmamawa da ƙasƙantar da kai drivern nata ya juyo yana cewa "Hajiya ina muka nufa?" ta ɗauki kusan tsawon mintuna goma tana latsar wayar dake hannunta kafin tace "Madawaki Mansion zamu je" ta yi maganar ba tare data ɗago kai ta kalleshi ba, cike da karɓar umurninta ya ɗauke kan motar zuwa titin da zai sada shi da gidan mahaifin nata Alhaji Isma'il Madawaki dake unguwar Aso drive anan cikin garin na Abuja.


Babban mutum ne kuma shahararren ɗan kasuwa da ya yi suna a ciki da wajen ƙasar Nigeria, yana da matan aure biyu, Hajiya Maryam da ta kasance uwargida sai kuma Hajiya Fatima amarya.


Hajiya Maryam ita ce uwar gida ita ce kuma mahaifiyar Zinnira don ita ce ƴarshi ta farko, bayan haihuwarta da kusan shekaru biyar ya auro Hajiya Fatima, bai daɗe da aurota ba Hajiya Maryam ta sake samun juna biyu a lokacin itama Hajiya Fatima na ɗauke da nata, sai ya zamana kusan lokaci ɗaya suka haifi ƴaƴan su, Suhaila da kuma Suhaima, sati biyu ne tsakaninsu da haihuwa, daga nan Hajiya Maryam bata sake haihuwa ba ita kuma Hajiya Fatima taci gaba da haihuwarta inda ta sake haihuwar ƴaƴanta suma duka ƴan mata su huɗu Zainab, Asma'u, A'isha da kuma auta Hauwa'u wacce a yanzu haka take jami'a a mataki na ƙarshe tana karantar political science.


#Fathiyya

#Tagwaye

#Billy s fari

#Umm Asghar.


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol