Free chapter · Read without an account

BABI NA BIYU

by Fatima Eshak · FATHIYYA

Page__2.


*FATHIYYA*


Na

*BILLY S FARI*

Da

*UMM ASGHAR*


*YAN TAGWAYE.....*✍️

*PAID BOOK....*#400


GA MASU BUKATAR ƳAN BIYU DUKA GUDA BIYAR 1500

GUDA HUDU 1300

GUDA UKU 1000

GUDA BIYU 700

GUDA ƊAYA 400 

_*RAFEEQ*_ (Hajja Ce & Asmy B Aliyu)

_*MUNƊO*_ (Ayusher Muh'd & Zee yabour) 

_*FATHIYYA*_ (Billy s fari & Umm Asghar)

_*.ZAMANINMU A YAU*_ (Nana Ɗiso & Jiddah Aliyu)

_*IYALINA (A'ilaty)*_ (Zainab Bawa & Sadiya Nasir Dan)


________________________________

 Duk da tarin arziƙin da Alhaji Isma'il Madawaki keda shi, sai ya zamana dukkanin ƴaƴanshi mata ne ba yada ɗa namiji ko ɗaya in ba ɗan Amininshi da yake riƙo ba mai suna Mahmoud wato mijin ƴar shi Zinnira.


Mahmoud ɗa ne ga aminin Alhaji Isma'il da harkar kasuwanci ta haɗa su, da sannu kuma sai ya zamana shaƙuwa da zumunci ya ƙullu sosai a tsakaninsu ta yadda gaba ɗayansu suka koma tamkar ƴan uwan juna wato Alhaji Kabir Nafaɗa, ana haka wata rana tafiya ta kamasu zuwa Kano wajen harkar kasuwancin su inda zasu ajiye Haajar matar Alhaji Kabir wato mahaifiyar Mahmoud tare da Mahmoud ɗin da a lokacin bai wuce shekara biyar ba a garin Zaria zata je ganin gida, suna daf da shiga garin Kaduna suka samu accident.


Nan take ALLAH yayi wa Haajar rasuwa ita da drivern dake jan motar, Alhaji Isma'il da Mahmoud kuwa ko ƙwarzane basu yi ba, yayin da mahaifin Mahmoud kuma ke kwance cikin jini rai a hannun ALLAH bai ƙarasa mutuwa ba, ana ƙoƙarin ɗaukar shi zuwa asibiti ne ya riƙe hannun Alhaji Isma'il tare da janyo hannun Mahmoud dake faman girgizarshi yana kuka ya haɗe waje ɗaya, cikin jin jiki yake cewa "Abokina ga amanar ɗanka Mahmoud nan na baka ka kula dashi sosai, nasan nauyi ne mai girma na ɗora akan ka amma yaƙini da kuma yardar da nake da ita akan ka ya sanya ni yin hakan, kayi haƙuri ni nasan ba lallai ne na tashi ba amma ina da tabbacin cewa matuƙar yarona ya rayu a hannunka to zai samu ingantacciyar rayuwa...." kafin ya ƙarasa maganar ma ranshi ya ƙarasa fita. 


Sosai Alhaji Isma'il ya yi kuka ya shiga damuwa da tashin hankalin rashin aboki, amini kuma ɗan uwa a gareshi daga ƙarshe ya haƙura ya maida komai ga ALLAH don dukkanin mai rai mamaci ne, wannan dalilin ne yasa Mahmoud ya dawo zama a hannun shi lokacin Zinnira nada shekara ɗaya da haihuwa ya haɗa su duka ya ci gaba da basu kulawa, irin kulawar da idan ka gansu ba zaka taɓa iya banbance wa kace Zinnira ce ƴarshi shi Mahmoud ba ɗanshi bane saboda irin soyayyar da yake nuna mishi da yanda ya jashi a jiki, duk inda zai je kama daga kan Masallaci har zuwa harkar kasuwancin shi duka zaka samu Mahmoud a tare dashi, idan ba makaranta ba ko bacci babu abunda ke rabasu.


Hakan yasa ko daya gama haɗa degree ɗinshi na farko a fannin software engineering yana son fita waje ya haɗo masters Alhaji Isma'il ya hana shi saboda baya son ya yi nisa dashi musamman daya kasance shi ke kula da duka harkokin companies ɗin shi don shi bai yi karatun boko mai zurfi ba, iyakar shi Secondary School kaɗai ce yayi ya gama.


A lokacin kuma babbar ƴarshi Zinnira ta kammala karatunta na secondry school inda mahaifiyarta ta dage akan lalle ilalla sai dai a kaita waje taci gaba da karatunta a can saboda matsalolin da ake fama dasu na rashin cigaban karatu a fannin jami'o'i anan gida Najeriya, ko kaɗan Alhaji Isma'il baiso hakan ba har sai da Hajiya Maryam ta roƙi Mahmoud yasa baki cikin maganar sannan ya amince, a ɓangare ɗaya shima ko kaɗan bayan son zuwan Zinnira waje karatu saboda yanda yake matuƙar so da ƙaunarta, gashi yayi ta nuna mata hakan amma tayi kamar bata san yana yi ba don bashi bane a gabanta ganin cewa shi ba ɗan kowa bane face wanda mahaifinta ya tallafawa yake riƙe da cinshi da shan shi.


A ɓangaren Hajiya Maryam kuwa dama tuni ta tsani Mahmoud ta tsani zaman shi a wajen su, bata son shi bata ƙaunar ta buɗi ido ta ganshi ganin yadda shi ba ɗan gidan ba amma gaba ɗaya mahaifin nasu Zinnira ya ɗauki dukiyar shi gaba ɗaya ya damƙa ragamar kula da ita a hannun shi sannan duk wani abu da zai yi sai ya shawarce shi a ciki sai kace wani ɗanshi daya haifa alhalin ɗan ruƙo ne ɗan ruƙon ma ba na jini ba na dangin dangiro, a gefe ɗaya kuma tunanin idan Alhaji Isma'il ya faɗi yau ya mutu duka dukiyarshi da Mahmoud kaɗai ne yasan sirrinta ƴaƴan Hajiya Fatima ke da ita, saboda ita ke da ƴaƴa biyar acikin ƴaƴan nashi ita kuwa biyu kacal take dasu wato Zinnira da Suhaima duk kuwa da cewa ita ce uwar gida wanda hakan ke nuni da ba zata tashi da wani kaso mai tsoka ba. 


Wannan abun ya matuƙar addabar zuciyarta da ko isasshen bacci bata samu tayi saboda tsananin tunani, ana haka wani tunani ya zo mata a rai tuna yadda Mahmoud ke matuƙar son Zinnira. 


Nan fa ta tasata a gaba lokacin tana shekarar ƙarshe ta nuna mata cewa ta amince da soyayyar Mahmoud hakan zai sa mahaifin nasu ya iya bata wani ɓangare daga cikin kamfanonin nashi itama ta riƙe, daga nan sai suma su kwashi rabonsu saboda idan ya mutu tafi kowa sanin ba wani abu zasu samu ba daga cikin dukiyar, ita dai tumunin wanka kaɗai take dashi, su kuma bai wuce su samu kaso goma sha biyar ba cikin ɗari na daga cikin dukiyar mahaifin nasu ba, nan dai ta zauna ta tsattsara Zinnira tare da hure mata kunnuwa wanda tuni hakan yasa Zinnira tunzura tare da amincewa da maganganun mahaifiyar tata. 


Sannu a hankali ta fara kula Mahmoud haɗe da nuna mishi soyayya kamar ba gobe, shi kuwa dama abinda yake jira kenan daga wajenta don ya daɗe da mutuwa akan ƙaunarta, duk da kasancewar Mahmoud mutum mai zafi da kuma tsare gida indai a wajen Zinnira ne to duka zaka nemesu ka rasa, wasa wasa abu ya yi girma tsakaninsu don tuni Mahmoud ya sanar da mahaifin na Zinnira, cikin jin daɗi da farin ciki ya karɓi zancen hannu biyu ya kuma tsaida magana tsakaninsu kasancewar ya bincika itama Zinnira tace tana son shi, tana kammala karatunta da wata ɗaya aka ɗaura aurensu.


Wata irin soyayya, ƙauna, ladabi, biyayya da kuma kulawa take nunawa Mahmoud tamkar zata haɗiye shi wanda hakan yake ƙarawa Mahmoud ƙaunarta fiye da da, sannu a hankali kuma ta fara bijiro masa da zancen aiki, sam baya buƙatar hakan amma saboda ya faranta mata yasa ya amince tare da sharaɗin har sai idan yayi magana da mahaifinta shima ya amince da hakan, shi kuwa mahaifin nata sai yaga da ace taje wani wajen da sunan aiki gara itama ta tsaya anan kamfaninsa sai ta riƙe wani ɓangaren ganin tana da ilimi sosai kuma a waje tayi karatu fannin computer itama, kuma tana da experience akai yasa Mahmoud roƙon mahaifin nata da abata CEO ta duka companies ɗin guda biyu da wanda mahaifin nata ke kula dashi da kuma wanda shi Mahmoud ɗin ke kula dashi.


Da farko mahaifinta bai so hakan ba amma da yaga Mahmoud ya nace akan hakan sai ya amince bisa sharaɗin sai dai shi Mahmoud ya zauna a matsayin shi a babban kamfaninshi shi kuma ya sauka, in yaso ita Zinnira sai ta hau matsayin shi Mahmoud ɗin a ɗaya kamfanin, ganin ita fa ƴarshi ce kuma a waje tayi karatu tana da ƙwarewa da experience sosai a fannin da mahaifin nata keson ya zauna ya sa Mahmoud ya sake roƙon mahaifinta haɗe da lurar dashi idan ita ta karɓi matsayin irin cigaban da za a samu a wajen, nan ma mahaifin nata bai so ba amma sanin jajircewa da kuma hangen nesa irin na Mahmoud da zai kawo musu cigaba yasa ya amince mishi tare da cewa yayi duk yadda yake ganin ya kamata ba damuwa, shi kuma ya sauka kujerar ya koma gida ya zauna yana hutawa tunda ALLAH ya bashi waɗanda zasu iya ci gaba da kula da kamfanonin nashi.


Wannan dalilin ya sa Zinnira kasancewa kamar ita ce shugaban duka kamfanonin mahaifin nata yayin da shi kuma Mahmoud ke kula da wani ɓangare na kamfanin.


Yau ma wata kwangila ce suka samu daga National Assembly ta zuba sababbin na'urori a offices ɗin members na rep da sanatoci kasancewar anyi sabon zaɓe shine ta haɗa taro na musamman da manyan mutanen dake irin harkokinsu saboda akwai abubuwan da dole sai sun buƙacesu a wajensu kafin cimma nasara wajen aikata kwangilar yanda ya kamata sai gashi Mahmoud na nema ya takurata da zancen jarabarsa da kullum bata ci balle ƙarewa.


Tsaki ta saki a daidai lokacin da motar tayi Parking a katafaren gidan na mahaifinta dake da ɓangarori uku, ɓangare na farko shine na mahaifiyarta Hajiya Maryam, na tsakiya kuma na Alhaji Isma'il sai na can ƙarshe kuma shine na Hajiya Fatima wato amaryar Alhaji mace mai kirki, mutunci, sanin ya kamata da kuma rashin son tashin hankali ko ɗaya.


Da sauri Idris bayan ya gama daidaita parking ɗin motar ya fito ya buɗe mata ƙofa, ƙafarta ɗaya ta fara fitowa waje tana amsa waya tana yi tana ɗan bubbuga ƙafar a ƙasa, tafi mintuna bakwai a haka kafin ta gama wayar ta fito ta nufi sashen mahaifiyarta, zaune ta isketa saman dininig table an jere mata breakfast kala-kala ita da Suhaima dake sanye da rigar bacci ajikinta da alama bata daɗe da tashi ba.


"Morning Mommy" ta faɗa tare da wucewa ɗakin mahaifiyar tata kai tsaye wanda hakan ya sa Mamie kallon Suhaima ta ce "Auta eat your breakfast, bari naga Yayarki". 


Cikin rashin damuwa Suhaima ta kira wata mai aikinsu ta bata umurnin ta zuba mata breakfast tana latsar wayarta haɗe da soma cin abicinta hankali kwance. Mommy kuwa tabi bayan Zinnira jikinta har yana rawa don tasan abu ne mai muhimmanci sosai ya kawota tunda tasan yanzu lokacin fitar ta office ne, sun jima suna magana da ita sosai kafin ta miƙe tana faɗin "bari na tafi Mommy lokaci na tafiya, duk yadda meeting ɗin ya kaya zan kiraki a waya na faɗa miki".


"Ba damuwa Zinnira maza ki tafi, amma baza ki tsaya kiyi breakfast ba?"


"No Mommy na riga nayi latti gara na wuce kawai" ta faɗa daidai lokacin data ƙarasa saukowa daga stairs ɗin tana watsawa Suhaima wani kallo, ganin haka ya sa Suhaima ɗauke fuska don tasan ko me take nufi haɗe da cewa "Morning Aunty Zinney".


"Stupid girl kawai, zanyi lokacin kine tunda baki san girman manya ba a gidanku, idiot". Ta ƙare zancen tare da ficewarta, kuka Suhaima ta saka tare da jifa da sandwitch ɗin dake hannunta data ɗauko zata ci tana shura ƙafafuwa "kin gani ko Mommy? ALLAH shiyasa sam bana son shiga sabgar Aunty Zinney, ta fiye wulaƙanci sosai sai kace ni ba jininta bace, me take tunanin ta fini tunda dukiyar da take iko da ita bata mijinta bace ta mahaifina ce, ko gani take yi don tayi aure ni banyi ba shine zata riƙa wulaƙantani bayan shekaru biyar kacal ta bani? To wlh Mommy bazan ɗauka ba, duk ta sake kirana stupid ko idiot sai kin rabamu a gidannan".


Tana gama zancen ta ture plate ɗin dake gabanta cike da ɓacin rai ta haye sama abinta.


Zinnira kuwa tana fitowa a harabar gidan zata fita motar Hauwa'u autar Daddy gaba ɗaya na kawowa zata je school, don tuni Zainab, Asma'u da A'isha yayunta sunyi aure, ita kaɗai ta rage yanzu a ɗakinsu.


Duk da saurin da take yi haka ta tsaya tayi Parking motarta ta fito ta nufi wajen babbar yayar tasu Zinnira, lokacin tana ƙoƙarin shiga mota da Idris ya buɗe mata don yi tayi kamar bata gane taba.


"Ina kwana Aunty Zinniey?"

Da har baza ta tankata ba sai kuma ta juyo cike da ɓacin rai tana watsa mata wani kallo, hannunta ta ɗora a saman marfin motar kafin tace "look Hauwa'u sau nawa zan faɗa miki cewa ki fita sabgata? In ba gulma ba ke da kike cikin mota me ya tsayar dake bare har ki tako ƙafarki zuwa wajen nan?"


"Amma Aunty Zinniey meye laifi na don naga ƴar uwata na tsaya gaisheta.." tun kafin ta ƙare magana Zinnira ta katseta haɗe da cewa, "Kada ki faɗa mini magana Hauwa, ko kin manta kece ƴar ƙaramar ƙanwata a gidan nan, ki kama kanki kafin na shuka miki rashin mutuncin da sai uwarki tayi dana sanin kawo ki duniya" ta ƙare zancen tana nuna ta da ɗan yatsarta manuniya cikin ɓacin rai.


Zaro idanuwa ta yi haɗe da ja da baya ta ce "ALLAH ya baki haƙuri" sannan ta juya ta shige motarta ta bar harabar gidan.


Tana fita motar Zinnira na fita itama ta nufi Head office na companies ɗin nasu wato M&N GROUP OF COMPANIES don har lokaci na neman ƙure mata.


*****   *****   *****


A nan inda ya bar Fathiyya a zaune a nan ya dawo ya same ta har wannan lokacin bata bar zubar da hawayen ba, ita dai ta rasa dalilin da yasa Mami bata ƙaunarta da ɗanta, rashin haihuwa ma tararwa yayi domin kuwa tun farko dama ba ita taso Farouq ya aura ba shi kuma ya dage sai ita, haka nan dai ta haƙura ba don tana so ba sai don ganin itama iyayenta masu ƙumbar susa ne ko babu komai ba ƴar ƙananun mutane yaje ya jajiɓo mata ba.


Hannu yasa ya miƙar da ita tsaye kafin ya sanyata cikin jikin shi yayi mata kyakkyawar runguma yana ɗan shafa bayanta alamun lallashi, itan ma cusa fuskarta tayi cikin kirjinshi tare da sakin kukan dake cin zuciyarta gaba ɗaya har da shesheƙa.


Sun jima a haka tana kuka ba tare da ya hanata ba don shima da ace zai iya yin kukan tabbas da yayi ko ya samu yaji sauƙin abinda ya dunƙule ya tokare mishi a kirjin shi.


Sai da yaga kamar kukan na neman yayi yawa kafin ya fara lallashinta yana cewa "kukan ya isa haka nan, it's ok" yana ɗan bubbuga bayanta har ya samu ta rage ƙarfin kukan da take yi sai ajiyar zuciya da take ta faman saukewa.


Zama yayi akan kujera ya zaunar da ita a jikinshi tare da kwantar da kanta a kafaɗarshi yana cigaba da lallashinta duk kuwa da ba wata magana suke yi ba amma ta ɗan samu nutsuwa ganin yadda Farouq ɗin ya bata dukkan attention ɗin shi yana ƙoƙarin ganin ya rage mata damuwar dake cunkushe cikin ranta duk kuwa da cewa shima ba cikin daɗin rai yake ba tunda damuwar tasu duk iri ɗaya ce.


Sai masu aiki ne suka fitar da Breakfast ɗin da ta tashi tun asuba ta shirya musu domin dukkan su babu mai nutsuwar iya cin abinci don ita Fathiyya ma ko yunwar bata ji to haka shima Farouq ɗin halin da suke ciki yasa ya manta da batun wani abinci da basu ci ba.


A wannan ranar ko office basu iya zuwa ba, dama shi Farouq ba a ƙarƙashin kowa yake ba construction company ne da shi na ƙashin kanshi don haka rashin zuwan shi office ɗin ba matsala ba ne to ita ma Fathiyya ɗin dake aiki da COOPERATE AFFAIRS COMMISSION kasancewarta lawyer sai kiran office ɗin Farouq yayi ya bada excuse ɗin bata da lafiya don yasan a yadda take cikin rashin nutsuwar zuciya babu abinda zata iya tsinanawa ko taje aikin..


#Fathiyya

#Tagwaye

#Billy s Fari

#Umm Asghar.


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol