Free chapter · Read without an account
Two
*Ta_kwalam is a home for jewelry, your best jewelry plug and introducing my Bridal accessories rent! For me a wedding is a one day celebration, for you to buy lots of costly stuff and after the wedding sun tashi a aiki! A saukake na kawo muku inda zakiyi renting kayan amare kuyi kyau, a kudi kalilan ki kece raini kawata, sannan ki Gama ki dawo dashi. You don't need to buy much. I'm a DM away!*
Batuul na wajen window yayinda seat di na ke gefen nata, she's super excited akan zuwan ta Nigeria, tun dare da mukaje airport take ce min she can't wait ta iya Hausa, ta koya yaren Ammin ta sannan taji irin abincin da naci na girma, Haka Kuma above all taga Anty Hidaya dasu Amal! Hannun ta cikin nawa har ta Fara kokarin bacci, ta kwanto jiki na, na rungume ta cikin jiki na tare da kunna karatun Quran na saka a kunne na, a hankali bacci me nauyin gaske ya dauke ni, abin mamaki har Muka tsaya trans in a Ethiopia dake Ethiopian airlines ne Ina bacci, abun mamaki nayi dogon bacci Haka Wanda na Jima banyi ba. A airport muka zauna saboda hours ne away da tafiyar ta mu, na zauna Ina jin surutan Batuul, sede nayi murmurshi ko na Bata gajeriyar amsa, I was nervous, I was scared, I was anxious, I was trembling in fear, I was sad, I'm hurting bansan me Zan tarar ba, uwa uba ka kwashe shekara da shekaru a wata uwa duniya tun baka ma San kanka ba har ka Zama mutum Amma Kuma ba Wanda zai tare ka ba! Idanuna Suka Dan cicciko Amma nayi saurin wanke fuskata saboda kuka shi ne Abu na karshe da nake son nayi a yanzun, idan har na cigaba da Zama vulnerable to ya zanyi nayi raising Batuul, ya kamata na Zama strong and devoted uwa, tana da kalubale da zata fuskan ta me yawan gaske, Dole ne na dauki damarar Goya Mata baya a dukkan halin da ta tsinci Kan ta.
Wajen misalin karfe takwas na dare Muka Isa babban filin jirgi na Malam Aminu Kano airport Dake birnin kano ta dabo ci gari, ko da mai kazo an fika, Amma ni dai a tarin illimin da na kwankwado akan cancer bana tunanin akwai Wanda ya fini. Lokacin da na zama certified medical oncologist, Babu irin zarya da baai min ba daga embassy din Nigeria akan gwagwabar offer da suka bani Dan sun fahimci ni din Yar can ce, sede me zasu ce min, kasa ta Bata iya Kare ni ba lokacin da aka saida ni, lokacin da na yanke kowanne tsamanni daga afuwar rayuwa, se yanzun da na zama wata sannan zasu neme ni? Bashi da amfani. Idan har kasa ta ba zata iya Kare citizen din ta kwaya daya ba to bana tunanin zata iya Kare sauran! Amma dai ni din Yar Nigeria ce
Dukda ban zauna a Kano ba Amma dai kowacce jiha a Nigeria, Nigeria ce. Ina sakkowa a jirgi idanuna sanye da wani farin glasses me kyau, mutane da dama sunce glasses na yimin kyau, se na tuna ranar da nake hawa jirgi a Lagos, ranar da ita ce Rana ta karshe Dana bar gida zuwa wata kasar a matsayin daliba Ashe ni zamba cikin aminci akai min, gani na dawo a Karo na farko tun bayan wancan tafiyar, na tafi yar Ina karamar yarinya wadda duniya ta guje ta, gani na dawo a matsayin babbar mace wadda duniya take nema ruwa a jallo. Tabbas kayi karatu, karatu kariya ne babba, duk Wanda ya ganni a yanzun zaiyi tunanin can ni wata sharariyya ce Amma Ina ba Haka bane ni Yar malam shehu ce!
Duniya abar tsoro ce, bahaushe yayi gaskiya da yace Wai duniya budurwar Wawa, tabbas Wawa ke daura abota da duniya, saboda yanzunnan zata dauke ka ta aza bisa koluluwa, kowa ya sanka, ka Zama Wanda kowa ke fada yayinda ta zo aje ka se tayi wurgi da Kai yadda ba zaa tuna da Kai ba, Haka duniya take, duk sabon ka da ita zata juya ma baya kamar Baku Saba ba, idan ta daukake ka zakai tunanin ba zata musguna maka ba, zaka ji tamkar Kai dinnan Kai kadai ne nata, idan ta musguna maka se kaji kamar Kai kadai ta tsana duniya kenan! Kunga fame, wealth and Abu uku ne masu tsoratawar ku kiyaye su, na Kara fada muku ku kiyaye su!!!
Tun a arrivals na Gama yin komai da ya kamata, tun anan nasan na dawo Nigeria, gidan Babu kwaba Babu hantara, yadda mutane ke take doka yadda suke so, bakon Abu ne a guri na, kasancewar ba ruwa na da abinda Bai shafe ni ba na dauke Kai na, muna karbar luggage Muka fito, na Shiga cilla idanu ta inda Zan hango Hidaya, abun mamaki Batuul ce ta gane ta, aikiuwa nayi saurin karasawa inda take na rungume ta, ta juyo tare da rungume ni itama tana wani irin dariya me nuna tsananin farin ciki
" Allah nagode maka yau gani ga Adda!"
" Sannu Adda! Sannu. Batuul welcome home!"
Ta fada tana saki na Tate da riko hannun Batuul, Ina Jin Dadi na amsa se kallon ta nake, mace ce Fara tas me kiba wadda ta buskude bayan haihuwa, Dan Sanin da nayi Mata kafin auren ta ba tada kiba ko kadan, tana da nata irin kyan sede ba me yawa bane ba dukda in person wannan ne karon farko da muka hadu ni da ita, Amma sabon da mukai over the years zakai tunanin tare Muka tashi saboda yadda muke da ita! Hammar da na fara bugawa yasa tace
" Adda muje ku huta!"
Na bude idanu na nace
" Wallahi, 13h journey is not a joke!"
Wata TSINTUWAr alheri ce, yayin da wata musiba ce, na Kama hannun Batuul Muka cigaba da tafiya, Ina ta kallon yadda gurin yake, it feels odd been here after so many decades gaskiya, Amma Kuma se naji ko ba komai wannan shi ne ainahin gida duk inda zanje, komai Zan Zama I'm still a Nigerian!
" Naf Naf! Kece?"
Yadda aka fada sunan, kaf duniya nayi muku ta mahaukaci mutum daya ke Kira na da wannan sunan, shi kadai yake fada Kuma bayan Barin shi rayuwa ta Babu Wanda ya Kara Kira na da Naf Naf! Wani irin Abu naji ya dirar min a kirjina, naji tamkar idan na juya Naga shi dinne na harbe shi ya mutu, ko Kuma na hankade shi ya fasa Kai, kwakwalwar shi ta tabu and he should run mad, duk dai wannan din are just thought about how much I want him to be ruined, Yana cikin mutane uku Wanda ba Zan taba yafe musu ba Kuma Ina musu fatan dukkan musiba ta sauka a Kan su. Na juya Dan na tabbatar shi dinne, shi dinne kuwa mamaki sosae a fuskar shi na gani na, kilan yayi tunanin bazan taba dawowa ba, kilan a tunanin shi Saba alkawarim dawo Dani Nigeria da yayi zai Hana na dawo! He's wrong and mistaken, ai shi komai muqqadari ne!
" Ashe da gaske kece Naf Naf!"
Na kasa ce Masa komai, saboda ban ga wahala a tattare dashi ba, se wannan gayun Yana nan dukda shekaru sun dan tafi Amma ana masking din su da gayu!
" Nafisa yaushe Kika dawo? Kinyi aure?"
Wannan kalmar ta karshe ta sani bude Baki a hankali nace
" All thanks to you...!"
Bai ma jira me zance ba ya katse nu da fadin
" Nafii nasan na Miki laifi, Naf Naf ki yafe min!"
Na zuba Masa idanu Ina mamakin kalmar yafiya daga bakin shi, alhamdulillah da yayi realizing yayi kuskure, Amma kafin nayi magana se Hidaya dake tsaye tace
" Adda waye wannan? Kin San shi ne"
Nayi murmurshi Ina bin shi da wani disgusting look, har cikin zuciya ta nake Jin tsantsanin shi, gaba daya kallon da nake Masa yasa ya Sha jinin jikin shi, dukda dare ne yalwatuwar hasken gurin zai bashi damar ganin yadda nake kallon shi, itama wata da banma Lura da ita ba tace
" Honey wacece wannan!"
Kafin ya Bata amsa na dubi Hidaya nace
" Wannan! Azzalumi kenan Kuma macuci sannan mayaudari, maha'inci kuam munafiki!"
Matar da nake tunanin matar shi ce tace
" Keee! Who are you to call my husband all these?"
I'm still calm, ma'ana a nutse nake ba zaka fahimci yanayin fuskata ba saboda yadda nayi kokarin composing Kai na, wannan TSINTUWAr alamu Allah ya ara min Rana na amayar da abinda yake dankare a kirji na shekara da shekaru!
" Ban saka Baki dake ba, so stay out of it!"
Na kalle shi idanun shi sunyi ja, I can see how humiliated and embarrassed he was, ban taba kawowa shi me dagawa zai tsinci Kan shi a Haka ba, cikin kwantar da murya, da lallashi yace
" Nafii let bygone be bygone Dan Allah ki yafe min!"
Nayi murmurshi Wanda ke Kara saka Masa anxiety, a ran shi Yana tunanin yaushe na Zama strong Haka? Tun yaushe na dai na kuka, ya manta shekaru sun tafi
" Amma dai LL you're complete bunch of idiot and stupid! Na yafe maka? Ashe Zan yafewa mutanen gombe, idan na yafe maka tabbas Zan manta abinda Yan Jos sukai min! LL ba Zan taba yafe maka ba, se mun tsaya gaban Allah yayi Mana hisabi ni da Kai, have you ever thought how I was? What I went through? Kayi tunanin how heartbroken I was ranar da na san you were lying from the start? Wallahi LL ba Zan yafe maka ba, Kuma ba Zan dau na Kai karar ka wajen Allah ba.."
" Nafii please..Nafisa nasan..."
Na girgiza Kai kawai nace
" Ai Kai makaryaci ne, ai bakin ka karya kawai ya iya.."
" Haba Nafi how could you hold on to this? Shekaru nawa sun shude Amma Baki manta ba"
Bance Masa komai ba Dan Ina ga LL Bai san gravity of the situation ba, Bai San how much disaster yayi causing ba, magana dashi ba tada amfani, naja hannun Batuul Muka wice Hidaya tayi shiru Dan ni bana yawan magana, Bata Kuma taba tunanin I hold grudges har Haka ba. Ta Yaya ma Zan manta da LL, shi kadai da ya kawo min hope ya Kuma shattering wannan hope din!
Allah ya taimaka da driver tazo ba me gidan ta ba, da gaisuwar zata Zama wata iri, Kuma ba Zan so hakan ba saboda Hidaya da family din ta were a stepping stone a cikin rayuwa ta. Tafiyar was silent har muka Isa gidan ta, Batuul tuni tayi bacci, tunda na rike hannun ta naji ta damke nawa nasan so take ta tambaye ni me yake faruwa da wancan mutumin wato LL! Muna zuwa gidan na tarar da wani irin grand welcome, mijin ta Nasir da yaran su Amal, Abba se karamar su me sunana Little, seda hawaye ya zubo min, wasu irin mutane ne wannan, they accepted me dukda ni din bani da kowa. I was so happy Haka Batuul, Muka ci abinci mukai hira har na manta da wancan asshole din LL! Se da nazo Zan kwanta se abun ya dawo min daga farko, na shiga toilet kamar yadda nake da nayi kuka sosae idanu na sukai ja sannan na dawo na kwanta Kan gadon Hidaya Wanda dakin ta bamu ni da Batuul! Se wajen karfe hudu bacci ya lallabo ya sace ni har naso makara asuba, se Batuul ce ta tashe ni, Ina Yi na koma saboda yadda nake Jin zazzabi Yana neman rufe ni. Abu kamar Wasa wajen goma na safe Hidaya ta shigo, tana shihowa ta same ni numfashi daya daya, da mamaki ta karaso Kai na tace
" Adda Baki da lafiya!"
Na dago idanuna sunyi jawur kamar gauta, ta taba jiki ma zafi rum, ga Batuul gefe na tana kuka, ta dube ta tace
" Se ki Kira ni ai Amma nayi tunanin baccin gajiya kuke"
Karshe dai asibiti Muka tafi AKTH, I called a friend da mukai karatu a India tare, yazo a take aka bani taimakon gaggawa, kusan yini nayi a asibiti kafin Muka dawo gida! A Daren nace ni fa gida na Zan koma Hidaya tace ai se na huta ta sanni idan naje aiki zanyi ba Zan huta ba!