Free chapter · Read without an account

Page:4

by Ramlat Abdulrahman Manga · SANIN GAIBU....

SANIN GAIBU...!!

   _Sai Allah_

ͲϴᏢ-ΝϴͲᏟᎻ 2023

    *Mai_Dambu*

    Page:04

Lekowa Inna Laminde tayi ta hangota d'are-d'are a gado, zaro idanu tayi cike da mamaki ta yafito ta da hannu. D'aga kafada tayi ita ba zata zo ba. "Kayya ni Laminde naga takaina. Tawo nan" ta kuma kiranta da hannu, juya baya tayi kamar ba da ita ake ba. "Sa'ade taso muje" tasan ba ji take ba da wannan kunnen, amma haka take sambatu da ta gaji da kanta, ta shiga cikin dakin ta dauko ta. Kuka ta saka tana niman kwanciya a kasa. Haushi da takaici ya cika Inna Laminde bata san lokacin da ta falla mata mari ba. Da sauri ta mike tana me kare fuskar jikinta yana rawa. Nuna mata hanya tayi babu shiri ta nufi hanyar tana kuka da ihu. Wanka ta mata har lokacin ihu take, "yau kuma sheganta kurma take ji?" Shiru Inna Laminde tayi bata kula shi ba. "Da Bara kika kaita sai kun samu tausayawar al'umma su bata sadaka." Banza tayi da shi ta cigaba da shirya yarta domin idan ta daka na Malam Aminu tabbas zata iya rasa turmin daka ta ta. Haka ta wuce dakin ta da Sa'ade ta shirya ta. Tsaf ta fito gwanin ban sha'awa hawaye ne ya zubo a Idanunta, mika mata kunu tayi ta sha. Amma tunda ta kawar da kai kamar taga kashi. Karshe fita tayi da jakar makarantar ta. Tana kuka har ta isa makarantar, tsayawa tayi a bayan ajin su zaune tana wasa da ƙara. Har aka fito tara tana wurin sai lokacin Halima da Nana yan ajin su suka zo wurin domin fitsari suka ganta zaune. Tana ganin su ta mike tana zare idanu, nufarta suka yi dama tana jin haushin an korota makaranta. Halima tana zuwa ta shure ta, bata kulata ba itama Nana ta maketa, tana mikewa ta kama kan Nana da hijab din ta shake ta, baki daya ta musu barin mahaukaciya, ta daki wannan ta daki wannan, sosai take jibgar su har sai da aka taru akan su, kafin aka wuce da su office din headmaster, duk suka durkusa. Ita dake bata da bakin magana shiru tayi, su da aka tambaye su, suka mata sharri, haka yasa aka zane ta domin sun fada bata zo makarantar ba, hakan ta fito daga office din tana kuka me mugun ciwo, kana jin kukan har cikin kanka. Aji ta wuce ta zauna tana shashekar kukan. Har aka tashi bata fasa kukan ba, koda ta dawo tun daga nesa ta hango Baffan dan dole ta share Idanunta tare da hàdiye kukanta, domin tasan ba karamin abu bane ya rufe ta da duka. Dake juma'a ce babu makaranta sai ranar monday. Suna zaune da abokan shi ana hira tazo ta wuce abin ta. Tana shiga cikin gidan ta samu an gama dafaduka, dakin su ta wuce ta cire kayanta, ta fito ta dibi ruwa ta wuce ban daki tayi wanka. Sannan ta koma daki ta saka kayan juma'ar da Innarta ta cire mata wata English me abc. Wanda Yayansu Ya'u ya musu sallah bara, sai farin hijab ɗinta yayi mata kyau, fitowa tayi dauke da abin sallah tana kallon Innar su. "masallaci zaki?" Dake ta juyo kunnen da take ji, gyada mata kai tayi. "Zauna kici abinci" motsa bakinta tayi tana girgiza kai. "Kin koshi ne?" Gyada kai tayi, dama tasan halin ta matukar tayi kuka bata iya cin abincin sai dai tayi ta fushi. Duk ranar juma'a yayan sun Iro yana turo me mashin ya kai su Binji suyi sallah da kwana biyu a can, kayanta kala biyu ta dauka suka fito domin yaron da iro ya turo ya iso. Ita kan burinta ba zata zauna a garin Binji ba, domin sokoto zata ta kai karan Innar su ta mare ta. Dama Inna Laminde tasha jinin jikinta tunda ta dake ta, yau zata tafi har Sokoto kai kara, tunda juma'a ce. Haka suka tafi Inna Laminde tana d'aga musu hannu. Dariya tayi tana faɗin, "Allah ya shirya min ke adawo lafiya daga kai kara da yaji." Lokacin da suka isa su Rabi da Harirah suka wuce gidan Yayarsu da sune ciki ɗaya. Ita kuma ta zuwa Ibrahim rigima, babu yadda ya iya dole ya bar shagon a hannun Yaran shi, suka tafi anan take son gaya mishi abin da Inna ta mata, sai misali take mishi bai gane ba. 

^°°•

Kallon Yarima Sadeeq yayi yana shirya mishi kayan sa, murmushi yayi ya tashi daga kwanciyar da yake yana daukar wayar hannu ya zuba idanu hoton wata kyakyawar budurwa ce akai tana da kyau me sanyi, gata kamar baturiya, danna kiran wayar yayi ya kanga a kunnen shi, har lokacin wayar a kashe take. Kiran Ummin shi yayi yana sallama. "Ubana kana lafiya?" "Ummina baki da lafiya ne?" "A'a kewarka nake" "Ummina" ya kirata a shagwab'e kamar zai tashi sama, murmushi tayi mishi sannan ta ce mishi. "Auta baka san ka girma ba ne?" "Ummina!" "Na'am Ubana" "har yau ni babynki ne" ya fada yana narkewa kamar yabi kasa ya kwanta , sake baki Sadeeq yayi yana kallon ikon Allah, abin shi mamaki ya ba shi. Dama haka Aliyu yake, "Ga Ummu Aymana" "Bata Ummina" wayyo Allah, anan Sadeeq ya gane me ake nufi da d'an Auta domin shi Auta ne amma babu irin wannan shakuwar da yayin shi mata da maza. "Didihhhh" ya kirata kamar ana tsikarar shi. "Na'am Autar Ummi" sake narkewa yayi yanar zai shiga wayar ya ce. "Didih, kin ji wai sun tura ni wani gari can me ma sunan garin Sadeeq?" "Maikulki" Sadeeq ya bashi amsa. "Kin ji wai Maikulki" "Allah sarki auyoo my Baby brother" yatsu ya dunkule ya saka a baki, "you pity for me?" "Mugun tausayi ma kuwa, kanina me nauyin chequer billion goma za a tura wani ƙauye" ta fada muryata yana rawa. Murmushi yayi, "ya isa haka ba sai kin yi kuka ba, ina kewar ku ne, don Allah ina Babyn baby?" "Hmm bata nan idan" "me yasa kuke boye min ita, me yasa idan na tambayi Ummina sai tace bata nan please meke faruwa ne? Na kira Dad yaki picking kirana." Ya fada kamar zai yi kuka. Amsar wayar Ummin su tayi tana faɗin. "ka kwantar da hankalin ka in sha Allah zata dawo" "but Ummina " "kana son nayi fushi ne?" Girgiza kai yayi kamar yana gabanta. "A'a " "Allah ya maka albarka " daga haka ta kashe wayar. Jikin shi ne yayi mugun sanyi, wannan shi ne karo na biyu da duk lokacin da ya bukaci magana da Ummu Mansurah ake hana shi magana da ita.

"Sannu nace sannu Aliyu" murmushi "yawwa Yarima Sadeeq " sai kuma suka fashe da dariya.

^°°•

International hospital Abuja Nigeria.

Cardiac department.

Zaune yake a gaban Babban likitan zuciya, yana wasa da wayar shi. "Mr Abdulhakim! Ka cigaba da shan maganin babu abin da ya samu aikin da aka yi a zuciyar sai ma nasarar da ake kara samu. Amma dole ka kiyayye damu sannan kana yawan motsa jiki domin bawa zuciyar damar aikin da ya da ce." Ya fada yana ajiye takardan da yake dubawa. Murmushi yayi yana shafa kasumbar shi. Sai da ya lumshe idanun shi , sannan ya bude idanun shi akan likitan ya ce. "Dr kana nufin an yi nasara kenan?" "In sha Allah anyi nasara yadda binciken ya nuna min " "Alhamdulillahi, duk da bana cire tsammanin daga rahamar Allah, amma nasan na kai matakin da dole na jira ikon Allah, na gode sosai." Rubuta mishi magani yayi , tare da mika mishi. Sake musabaha yayi sannan ya amshi takardan ya nufi inda motar shi ya ke, escort din shi ne suka taso suna bin bayan shi har inda motar su yake, suka bude mishi ya shiga yana sauke ajiyar zuciya. Duba wayar shi yayi wanda ya bari a cikin motar. "Seven miss call" ya furta a hankali, duba kiran yayi. Mother kurawa fuskar wayar yayi idanu, kafin ya dauke yana shin wani irin yanayi kafin ya kira layin."Abdul ina ka shiga ina kiran ka baka dauka ba?" "Kiyi hakuri na shiga meeting ne" ya furta a hankali, kamar ba zai magana ba. "Toh yayi maka kyau, kaga sakona a wurin sakataren ka?" Lumshe idanun shi yayi, yana jin wani irin nauyi a zuciyarsa. "Baka ji me nace ba ne?" Ta fada a fusace, domin tana da mugun zafi. "Ina jin ki Mami!" Ya furta a sanyayye. "Na ce kaga sakona a wurin Mubarak?" "Eh na gani, sai dai zan zo sokoton don Allah ki bani damar haka" yadda yayi maganar a hankali yasata saukowa domin tasan bai da wadataccen lafiya. Ita kanta ba don ranta take mishi haka ba, sai dai Abdul ya girman da yake bukatar iyali a tare da shi kodan lalluran shi. Dole ya ajiye mace a tare da shi."Allah ya baka lafiya, and likitan ka ya turo min sakamakon binciken lafiyar ka don haka ka dawo da wuri, domin a tsayar da magana ɗaya." " Toh Mami sai na zo" sai da ta kashe wayar ta, ya wurgi da na shi wayar. Baki daya an mai da shi kamar dan Babyn wasan Yara, bai da cikakken ikon kan shi sai yadda Mahaifiyar shi tayi da shi. Hatta matar da ake son ya aura muradun mahaifiyar sa ce ba muradun shi ba. Mahaifin shi ya xama kamar hoto sai yadda aka yi da shi, koda yake ai ba wani abu bane tunda haka ya taso ya gani. Duk da mahaifin su babban ma'aikancin gwamnati ne da ya rike manyan mukaman gwamnati har yayi retired aka kuma dawo da shi aiki. Cikekken sunan shi Abdul Hakim Sharif Hamidu, shi ne cikakken sunan shi a sanin shi dai tun farko auren iyayen su kamar babu soyayya da shakuwa. Sai dai biyayya ga iyaye domin yadda Mami take over acting yasa suka fahimci haka. Shi kuma irin wannan auren a gaban uban kowa mace tana iya nuna maka bata sonka. Domin a yadda ya samu labari mahaifin su yaron gida Alhaji Abdul Hakim bakasanmatsi ne me kamfanin gidan siminti na sokoto baki ɗaya. Tun kafin y aurawa Sharif Daulah ya nima mishi aikin gwamnati a babban mataki, yadda ba zata rena Sharif ba. Sai dai kash duk da wannan bai hana ta mugun rena shi ba. Domin Hajiya Daulah irin mata masu mugun izza ne da jin kai. Shi kuma irin mutane ne masu hakuri da sanyin hali. Wannan halin na shi da mahaifin Daulah ya gani ne yasa shi ba shi auren yar shi domin ko bayan ran shi zai yi wuya ya wulakantata. Sannan ya kuma fahimci Sharif bai da son zuciya domin yana da kokarin niman na kan shi, haka yasa shi nema mishi aikin gwamnati kafin Auren su. Duk da haka Sharif ba tsira a hannunta ba. Za a iya kiran auren su da suna rabo. Domin rabon Yara ne ya tara su zama inuwa ɗaya. Abdul Hakim shi ne babba suna kiran shi Abdul, sai Sadikkah take bin shi sai Afiyyah sai Taufiq, idan ka cire Abdul shi ne ya dauko halin mahaifin su. Sauran duk rashin Mutuncin Hajiya Daulah suka ɗauka. Lokacin da aka yi auren su ta tashi hankalin kowa har da shi mijin, ana ta samu cikin Abdul wanda tayi ta shan maganin zubda ciki. Amma Allah ya nuna mata ikon shi ta hanyar kare cikin har ta haife shi, sai dai kuma an haife shi da ciwon zuciya, sakamakon magungunan da tayi ta durawa da cikin shi. Har kasar waje Alhaji bakasanmatsi ya kai shi ya bude mishi file, duk bayan wata uku suna kai shi. Karshe da yaga zirga-zirgan yana yawa sai ya nima musu gida a can domin a lokacin babu me kudi irin shi, haka ya nimawa surukin shi damar ya karo ilimi itama kuma tayi karatun ta. Yaso tayi karanci bangaren jinya domin D'anta, amma fir taki sai kasuwanci ta karanta. A can ta haifi Sadikkah, rasuwar mahaifinta yasa suka dawo sokoto. Inda ta kafe zata tsaya akan kamfanin mahaifinta. Kasancewar ita ce yar shi daya tal.....

ASHRAF, SANIN GAIBU,TSINTUWA is not free, Pay N400 ONE, TWO N800, THREE 1K to 0008219237, Jaiz bank Azizat Hamza

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol