Free chapter · Read without an account
NUFIN ALLAH! Chapter 18
📱 *NUFIN ALLAH...!*🤲🏻 *Arewabooks@ayshadansabo*
*Paid book:500*
*Chapter 18*
_Free page_
Hira sosai suka sha a tsakanin junansu kafin Momy ta wuce kitchen,don fara shirya abinda zata tarbi Daddy dashi.Wanda a yau ɗin friday zai dawo weekend daga Abuja.
Najma Momy ta kira bayan Inna Mairo ta koma ɓangaren Gwaggo domin taya Tabawa ɗaura girki.A hankali Najma ke taya Momy ayyukan da ta bata,don ta fahimci tana da son koyan girkin da gaske.Bayan sun kammala Najman ce dai Momy ta saka ta dinga kwasan warmers ɗin zuwa ɓangaren Daddy tana shiryawa akan dining.Cikin tsari da nutsuwarta na halitta take gudanar da komi nata,abinda ke sake birge Momy kenan don tana son mace ta kasance nutsatstsiya ba mai rawar kai ba.
Hannah ɗaki ta shige tana chart da kuma karance-karancen novel da ta fara koya, don zaman kaɗaicin da take yi a port harcourt ɗin idan AD ya fita oficce, ya sanya ta fara koyan karatun novels da ake turawa a wani group da Anty Laurah ta sanya ta a ciki.Wani book ɗin Mamuhgee take karantawa mai suna IDON NERA,sosai ɗin book yake tafiya da zuciyarta take kuma jin daɗin karatun.Ta lunshe idanunta tana tunanin AD Dukku da son zuwansa a gobe ko yau ɗin, don da gaske kewar ganinsa take yi tsakanin jiya da yau da bata sanya shi a idanunta ko jin motsi ko muryarsa da ke kasheta ba. Momy ce ta kira wayarta time ɗin da ta idar da sallar zuhur da ta tashi ta gabatar da ƙyar, sabida kasalar da take ji.Ta ɗaga wayar tana sauraren Momy da ke bata umurnin fitowa tayi lunch tare dasu a dining.Ta aje wayar tana miƙewa ta canza rigar jikinta daga dogon shimi zuwa doguwar riga mai ƙaramin hannu.Rigar na wani haɗaɗɗan Indian material ne da yaji ɗinkin embroidery, wanda aka yisa tun daga wuyar rigar zuwa ƙasansa.Sosai tayi kyau da fresh irin na masu ciki, waɗanda hutu ya ratsa fatarsu babu wahala sam a tare dasu. Tare da Najma da Momy suka haɗu sukai lunch ɗin,bayan sun kammala Momy ta sanya Najma raka Hannah zuwa part ɗinsu da su Rabi suka kammala goge ko'ina.Sosai Najma ta yaba da tsaruwar part ɗin,wanda yafi na Gwaggon kaduna girma.Sannan tsarin ginin ma yafi haɗuwa, ga kuma rantsatstsun kayan ɗaki dana kitchen da aka yiwa Hannah irin na ƴaƴan gata,waɗanda iyayensu suka tada kai da naira.Don mahaifinta Alhaji Surajo ba ƙaramin mai kuɗi bane,don ma ya ɗan samu karayan arziƙin da har Daddy ya keresa,amma a baya ko Daddy ba zai nuna masa arziƙi ba.Ƴan asalin jihar kano ne su,aiki ne ya maida Alhaji Suraj ɗin Abuja da iyalinsa baki ɗaya.Sai dai yana da gida a kaduna da suke yawan hutu nan,daga nan su wuce kano a wasu lokutan.A hakane kuma ta hanyar yawan zuwa Kd da suke yi,suna ziyartan gidan Daddy da kuma yadda Adnan ɗin ke yawan ziyartan Alhaji Suraj ɗin idan ya shiga Abuja, Hannah ta ƙyalla ido ta gansa ta kuma maƙale masa.Babu kalar samarin da bata yi ba tsakanin Abuja da mahaifarta kano,amma ta watsar da kowa ta kama ɗan mutan Dukku.Wanda shi kuma zuciyarsa bata taɓa ƙaunarta ba, kawai auren nasu yazo a NUFIN ALLAH ne kawai.Wanda idan ya yi NUFIN abu ya kasance sai ya kasance ɗin,koda ace babu yarda da amincewar kowa ne.
Duk yadda Hannah ta so Najma ta jira yi dawowar Nasreen daga skull anan side ɗinta ƙi tayi, ta matsa zata wajen Innarta ne ta dawo ne.Hakanan Hannah ta ƙyaleta ta wuce,tana jinjina rashin saurin sakin jikin Najma da mutane sosai.Gashi kuma ita Allah ya ɗaura mata son Najma a ranta tun ganin farko, sabida yadda kyawunta da sanyinta ya tafi da zuciyarta.Sannan yawan murmushin da baya rabo da fuskar Najmar abin na sake birgeta, yana kuma ƙarawa Najmar kwarjini da kyawu matuƙa.
Najma na baro side ɗin Hannah ta wuce ɓangaren Gwaggo.A nan falo ta samesu suna hira,Gwaggo kuma na daga kishingiɗe tana amsa waya.Ta nema waje ta zauna tana sauraran yadda Gwaggo ke amsa wayar cike da ɗaga murya,wanda hakan ya zame mata jiki sam bata iya magana a hankali a waya ba.Bayan ta kammala wayar ne Najma tayi mata sannu da hutawa,ta amsa da fara'a tana faɗin, "Najmatu gobe fa sai garin giwa,tafiya babu fashi In Sha Allah! Don haka Nasreen na dawowa zaku je ku yo siyayyar tsaraban da za a wuce musu dashi.Duk dai na kammala tanadan abinda ya dace,amma su ƴan matan ƙawayen naki kece zaki san abinda zai fi birgesu." Najma godiya ta dinga wa Gwaggo bayan ta dasa aya a maganarta.Gwaggo ta nuna babu komi yiwa kaine, daga nan kuma sai ta sanya Najma zuwa kitchen ɗinta ta ɗakko mata kwanon nono da fura a fridge ɗinta.
Nasreen sai ƙarfe biyu da rabi ta shigo gidan a gajiye, direct ɗakinta ta wuce tayo wanka ta saka riga mara nauyi.Dining ta fito ta nemi abinci don da yunwa ta shigo gidan,sabida bata ci komi a skull ɗin ba yau ɗin.
Momy ce ta sanar da ita cewa Hannah na part ɗinta,hakan ya sanya Nasreen na kammala cin abincin suka nufi wajen Anty Hannah ita da Nabeela da tun rana ke ɗaki tana karatun books na skull don ita mayyar karatu ce. Daga can wajen Anty Hannah side ɗin Gwaggo Nasreen ta wuce wajen Najma.Ta samu Gwaggo da Inna Mairo tare da Tabawa a falo suna zantawa,ta tambayi Najma Inna Mairo ta ce tana ɗaki ta ɗan kwanta ta ce kanta na ciwo.Cikin hanzari Nasreen ta nufi ɗakin su Gwaggo bakinta ɗauke da sallama,ta hangi Najma kwance bisa bed da waya a hannunta.
"Beauty baby ya aka yi ne da kwanciya da ranarnan haka?" Nasreen ta furta hakan tana zama daga bakin bed ɗin.Najma da ƙamshin turaren Nasreen ɗin ya bugi hancinta kafin isar muryarta cikin kunnuwarta, sai tayi saurin tashi zaune da murmushi akan face ɗinta ta ce, "Sis kin dawo? Wallahi kaina ke ciwo amma na sha magani ya faɗa mini,yanzu karatu nake yi a waya." Nasreen ta jinjina kai tana duban fresh black beauty face ɗin Najma da ke glowing ta ce, "Ayyah! Sannu Sis, wato kin fara koyan karatun novel ko? Ni kinga ban iya ba,karatun skull kaɗai ya isheni." Najma ta jinjina kai tana faɗin, "Wallahi Sis na fara koya, kuma ina ƙaruwa sosai,kawai luv ɗin cikin books ɗin ne yake bani kunya da mamakin anya ko ni zan iya wata soyayya kuwa?" Najma tayi tambayar bilhakki idanunta akan Nasreen ɗin.Nasreen ta tuntsire da dariya tana faɗin, "I don't know now,but idan lokaci ya yi zaki iya fiye ma da wanda kike karantawa." Najma ta ɗan ɓata face cike da shagwaɓe murya ta ce, "Ni dai gaskiya bana ji zan iya kam, yanzu dai bani labarin me kika taho min dashi?" Nasreen ta saki smile ta ce, "Nothing beauty! Amma zamu fita yanzu ai sai mu biya musha COLD STONE muci pizza." Najma da sam bata damu da irin abubuwannan ba,sai ta ɗan yamutse face tana faɗin, "Ni dai ban iya shan kayan sanyinnan ba, shi ma pizza ɗin baki ga ban iya cinsa sosai ba." Nasreen ta miƙe tsaye tana duba time a gogon dake ɗakin ta ce, "Oya shirya Najma, lokaci na tafiya gara mu fita yanzu koma dawo kafin Daddy ya ƙariso." Najma ta sakko daga bed ɗin ta nufi closet ɗinsu ta ɗakko rigar da zata saka su fita ɗin.Nasreen na tsaye tana dubanta ta saka doguwar rigar boubou na wata pink ɗin atamfa,rigar ya yi mata kyau kalar kuma ya haska black skin ɗinta mai sheƙi da fresh.Ga kuma sassanyar ƙamshin turaren Miss Dior da ta fesa kaɗan na tashi a jikinta.Ɗankwalin kayan ta ɗaura tana ɗakko wani ƙaramin hijab irin na makkah da Momy ta bata ta saka.Hijab ɗin tsayinsa duka iya cinyarta ya tsaya,amma ya rufe dukkanin hannayenta bai dai ƙarisa sauka zuwa cinyarta bane.Kalarsa milk ne da ya shiga da kayan jikinta,wanda akai wa touch da milk colour a jiki,sai ta fito tayi wani irin mugun kyau.
Jere da juna suka fito zuwa falon Gwaggo, Nasreen nata yaba kyawun da Najma tayi.Daga Gwaggo har Inna Mairo idanunsu akan Najma suke,Gwaggo ta kasa shiru sai da ta furta, "Najma wannan kyawu da kike ta sake zabgawa haka." Najma ta saki murmushi ta ce, "Gwaggo a hakan?" Gwaggo ta jinjina kai ta ce, "Ƙwarai kuwa! Don baki ga yadda kyawunki ke sake fitowa bane shiyasa.Nasreen maza ɗakko min ƙaramar jaka akan gadona na sallameku." Nasreen ta wuce ta ɗakkowa Gwaggo jakan ta kawo mata.Ta amsa tana zuge zip ɗin ta ciro kuɗaɗe ta irga wanda zata basu tana miƙawa Najma tana faɗin, "Ungo Najma, ku siyowa ƙawayenki tsarabar da xaki kai musu gobe kin ji ko?" Najma ta amsa kuɗin tana godia Inna Mairo na taya ta ita ma.Sukai musu sai sun dawo suka fice don zuwa yiwa Momy sai sun dawo ɗin.Ita ma kuɗi ta ƙara musu ta ce Najma ta siya abinda take so,sannan ta sake ba Nasreen wasu kuɗin ta ce ta siya mata wasu abubuwan da zata wuce wa ƴan giwa dashi ita ma.
A gaban motar Nasreen Najma ta kame,hannunta riƙe da wayarta da ke sake shiga zuciyarta.Suna tafiya suna hiransu cike da nishaɗi, Nasreen na faman tsokanar Najma da cewa akwai wani guy da za ta haɗata dashi.Najma ta bankawa Nasreen harara tana faɗin, "Don Allah Nasreeny ki rufamin asiri, nifa wallahi da gaske nake ba zan iya wata soyayya ba." Nasreen tayi dariya sosai kafin ta furta, "Ba za ki yi aure ba kenan?" Najma ta jinjina kai ta ce, "Wannan kuma ai ana yinsa ko babu soyayyah, indai shi mijin zai soni ai shikenan ba dole sai nayi soyayya zan yi aure ba ai." Nasreen ta jinjina kai tana faɗin, "Gaskiya sai yau na yadda ke ɗin auta ce Najma." Najma cike da nuna halin ko inkula ta ce, "Hmmm! Ke wasa ki ke ganin komi Nasreen, ni kam da gaske nake furta dukkanin kalamaina."
Nasreen tayi saurin faɗin, "Kar dai ki cika baki, don ita soyayya bata ƙwanƙwasa ƙofa, shiga kawai take yi duk zuciyar da ta so ba tare da bada notice ba.So kada Yarinya ta zo ta cika baki watarana in ji ana kuka ana faɗin Nasreen ya zanyi da soyayyar wane." Nasreen ta ƙare maganar ta bushewa da dariya, hakan ya sanya Najma sake narke fuska kamar zata saki kuka ta ce, "Allah dai ya yafe miki Nasreeny! Amma kin gama dani yau wallahi."
Sosai suka ɗauki ɗauki lokaci a kasuwa suna siyayyar,Najma duk kuɗin da aka bata sai da ta ƙarar dashi wajen siyawa mutanenta su Lubah kayan gayu masu kyau.
Kafin su wuto gida sai da suka tsaya suka sayi COLD STONE ice cream da Shawarma,suka sake tsayawa a wani waje suka sayi Chicken Kebab sannan suka wuto gida. Suna shigowa Nasreen ta hango motar AD Dukku da ake ɗakkosa daga airport idan ya zo gari a fake a parking space, ƙirjinta ya yi wani irin bugawa da jin haushin zuwansa garin.Ta isa ta raɓa motarta da nesa kaɗan da nasa suka fito daga cikin tasu motar.Najma na kwasan wasu kayan dake back seat take faɗin, "Ina muka nufa?" Nasreen da gaba ɗaya mood ɗinta ya canza da ganin motar Yaya AD ɗin, sai ta ƙaƙaro murmushi tana faɗin, "Mu nufi side ɗin Momy kawai Najma, idan mun yi magriba sai mu je wajen Gwaggo taga siyayyar ko?" Najma ta jinjina kai cike da gamsuwa tana faɗin, "Okey to bari na kwashi waɗannan kayan." Najma ta ƙare maganar tana kwasan mafi yawan kayan da ke back seat ɗin ta nufi side ɗin Momy dasu.Nasreen ta rufe motar tana kwasan sauran kayan ta rufawa Najma baya, wacce har ta kusa isa ga ƙofar shigewa ciki.Kusan a tare suka isa bakin ƙofar shiga babban falon Momy, tun kuma kafin a amsa sallamarsu iska ya kwasowa Nasreen ƙamshin turarensa na CREED AVENTUS mai ƙarshen tsada ya buso hancinta.Muryar Momy da ta amsa sallamar da suka doka tare da basu izinin shiga, ya sanya suka kutsa kai cikin falon.Daddaɗan ƙamshinsa da ya haɗe dana ɗakin ya daki hancin Najma,hakan ya bata tabbacin akwai baƙo ko baƙuwar a cikin falon.Idanunta yakai kan wanda ke zaune ya baiwa ƙofar shigowa falon baya, kalar rigarsa da sassalkan baƙin gashin kansa irin na fulani kawai ake iya hangowa.Daga nesa dasu kaɗan Nasreen ta ce, "Mommy mun dawo bari mu wuce ɗaki." Momy ta jinjina kai tana musu sannu da zuwa, Nasreen kuma ta ɗanyi gaba kaɗan tana ɗaga murya yadda zai jiyota ta ce, "Yaya AD welcome!" Bai juyo ba sai hannu da ya ɗaga mata kawai.Hakan ya sanyata jan hannun Najma sukai ciki ba tare da Najmar ta ce komi ba ita.Momy tabi bayansu da kallo zuciyarta na sosuwa da yadda sam shi bai iya jan ƴan ƙanninsa a jiki yana nuna musu soyayya ba,tsakaninsa dasu gaisuwa ce sai idan ya ga dama ranar da ƴan kirkin ke kusa ya kwashesu zuwa shan ice cream ko cin abinci.Shi ma kuma zai yi wuya a dawo lafiya bai make wata ko ya yi musu faɗan da zasu shigo a tunzure ba,musamman Nabeelah da bakinta ba ya iya shiru.Shi kuma baya son yawan surutu da rawar kai.Anty Jiddah da ke bi masa,ita kaɗaice take ganin haƙoransa a waje har su zauna suyi hira suna kwasan dariya.Amma in ba ita ba ko Momy da wuya kaga ya zauna suna hira sosai cikin nishaɗi,sabida ita kullum cikin yi masa faɗa da nasiha take akan ya gyara halayensa ya kuma guje aikata saɓo a fili ne ko a ɓoye.Don dukkanin halayyarsa na shan ƙwayoyi da harka da matan banza ta sani, tana kuma yi masa addu'ar shiriya a koda yaushe. Ta dubesa fuska a haɗe bayan shigewar su Najma ta ce, "Adnan yanzu ko kallo Nasreen bata isheka ba bare ka buɗe baki ka amsa gaisuwarta, anya waɗannan halayen naka na banza zasu fissheka kuwa? Wasu ke dashi da ya kai ka, wanda zai jasu a jiki ya kula dasu ko bayan babu raina? Ina sha daga kai sai Jiddah garesu, kuma kai namiji kai ne jagora kuma uba a garesu.Idan baka basu fuska sunyi sabo da kai ta yadda zasu dinga iya tunkaranka da matsalolinsu ba wa kake so su tunkara? To wallahi ka shiga hankalinka tunda naga kai baka san kawaici da ya kamata ba.Saura kuma ka je ɓangaren Gwaggo ka kasa yiwa Inna Mairo gaisuwar mutunci kaga yadda zan saɓa maka." Ta ƙare maganar cikin nuna masa ɓacin ransa da take ji a zuciyarta.Ya ɗago manyan idanunsa da ke saye cikin baƙin eye glass ya dubi Momyn nasa mafi soyuwa a zuciyarsa,don yana mata wani irin soyayya da bai san iyakarsa ba.Sai dai duk da soyayyar da yake mata baya iya sakin jiki da ita yadda ya kamata,sabida bai shaƙu da ita kamar yadda ya shaƙu da Gwaggo da ta sangartashi ba.Ita Momy kullum cikin nuna masa kawaicin ɗan fari take yi, yanzu ne da take ganin tarbiyarsa ta ɓaci ita kuma Gwaggo ba wani cikakken kwaɓa masa take yi ba,sai hakan ya sanya ta fara sakin masa jiki tana nusar dashi hanyar da ya kamata ya bi wajen gyara ɗabi'unsa.Cikin sanyin muryarsa mai cike da aji da nutsuwa ya furta, "Ki yi haƙury Momy zan gyara,ni kinsan ban faye son raini bane shiyasa bana sake musu fuska,amma ai ina ƙaunarsu ina kuma ji dasu har cikin zuciyata." Momy ta taɓe baki ta ce, "In gani a zahiri ba a baki kaɗai ba,sannan ina fata ka ji maganata da kyau akan dawowar Hannatu nan da zama har zuwa lokacin da Allah zai sauketa lafiya ko?" Ya jinjija kai yana jin ciwo da takaicin samuwar cikin jikin Hannah na sake soya zuciyarsa, musamman da a yanzu ya tabbatar zancen fidda cikin ko maganar rashin ƙaunarsa da cikin sai dai ya zama tarihi.Don tunda magana ya zo kunnin su Momy,ya san sai Hannah ta haife cikin nan ko zai mutune da rashin ƙaunar hakan. Ya jinjina kai yana faɗin, "Naji Momy badamuwa!" Daga haka ya miƙe Momyn na binsa da kallo da yaba kyawunsa da cikar kamala da Ubangijin halitta ya yi masa.Don wani irin kyawu da fresh ya ƙaro na gaske, da alamu garin ya amshesa sosai.Ɗanyar gezner ce a jikinsa fara ƙal! Wanda akai wa ɗinki na musamman,ya yi kyau har ya gaji a cikin kayan.Fuskarsa dai kamar ko yaushe babu wani annuri,musamman a yanzu da ransa ya sake ɓaci da zancen cikin da kuma jin zafin Hannah da tun farko ta shigo da su Momy cikin maganar ba tare da ta biye masa an zubda cikin ba. Ya taka a hankali cikin tafiyarsa a nutse ya bar cikin falon bayan ya sanar da Momy cewa zai je ɓangaren Gwaggo. Yana tafe iskar alamun shigowar damina na ɗan kaɗa shi tare da baza ƙamshinsa a ko'ina,a haka ya isa ɓangaren Gwaggo bakinsa ɗauke da siririyar sallama.Gwaggo da suke zaune tare da Inna Mairo a falo suna zancen tafiyarsu garin giwa gobe, sai ta juyo muryar Adnan ɗin kamar daga sama.Tayi hanzarin amsa sallamar tana faɗin, "Shigo mana shalelen Gwaggo!" AD Dukku ya ɗage labulen tare da shigowa cikin falon baki ɗaya, yana mai sauke idanunsa akan Inna Mairo da ke facing ɗinsa.Ya cigaba da takowa zuwa cikin falon,ƙamshinsa na baje ko'ina tare da ratsa kafifon hancinansu Gwaggon.Inna Mairo ta ɗaga idanunta ta sauke akan kyakykyawar halittar da gaba ɗaya ya canza mata, don rabonta da ganinsa tun bai gama zama saurayi ba yana ɗan sakandiri.Ya sake yi mata kyawu a idanu tare da zama cikakken magidanci mai ji da aji da ƙuruciya,sannan a kallo ɗaya zaka fahimci ɗan gaye ne na gasken gasken,wanda hutu da kuɗi haɗi da jin daɗin rayuwa suka taɓashi matuƙa da gaske. Ta ɗauke kai daga dubansa lokacin da ya isa gaban Gwaggo ya zame ya zauna kusa da ita,yadda ya wani manne da jikin Gwaggon tamkar Yaron goye sai ya bai wa Inna Mairo mamaki.Gwaggo ta wani rungumo kansa ya haɗu da kafaɗunta tana faɗin, "Sannu da zuwa Adinanuna, barka da isowa shalelen Gwaggo.Ya hanya naga duk ranka a ɓace haka, ince dai lafiya lau ka iso ɗin ko?" AD Dukku ya sake narkewa a jikinta yana jinjina kai murya can ƙasa ya ce, "Lafiya lau Gwaggo, babu wata gajiyar hanya flight na biyo ai.Hope na sameku lafiya lau? Nima i really miss u sweetheart!" Gwaggo ta wani sake washe baki tana faɗin, "Ɗan nema kayi kewata shine baka fara isowa wajena ba, don tunda na ga ka shigo fuska a haɗe na gane wajen Zainab ka fara isa ta ɓato min ranka daga isowa ba za a bari ma ka huta ba." Adnan Dukku ya ɗan fidda ƙaramar murmushi yana ɗago idanunsa masu cike da kwarjinin da ke dukan zukatan ƴan mata ya ce,"Gwaggo ba wani faɗa tayi min bafa, ina fata kin aje min abu mai sanyi kamar fura ko zallar madarar shanu?" Tayi saurin gyaɗa kai tana faɗin, "Duka zaka samesu Adinanu,don jiya na saka aka kawo madara mai kyau don nasan kana tafe a satinnan.Ga Gwaggonka Mairo ku gaisa kafin a kawo maka furan yanzu." Sai time ɗin AD Dukku ya maida dubansa inda Inna Mairo ke zaune,duk mamakin yadda Gwaggo ke taɓara jikan nata da tun fil'azal kowa ya shaidi muguwar soyayyar da take masa.Ya yi ƙasa da murya tamkar wanda ake tilastawa yin magana,ya gaida Inna Mairon ba yabo ba fallasa.Ita ma ta amsa gaisuwar nata fuskar a sake tana sake yi masa barka da isowa, daga haka ta tashi ta bar musu falon zuwa ɗakinta.Yabi bayanta da kallo yana maida dubansa kan Gwaggo ya ce, "Gwaggo yanzu ita ce ƙanwar Daddy da ki ke bani labari? Tana matuƙar kama da Jiddah sosai." Gwaggo ta saki murmushi tana faɗin, "Jini kenan Adinanu, ai baka ga kama ba sai kaga yadda ƴarta Najma tayi kama da ita,kuma take kama da Jiddar sosai ita ma.Ina fata zaka girmamata ka kuma riƙe ƴar uwarka tamkar su Nasreen,domim nayi nadama iya nadama akan yadda na raba tsakaninta da mahaifanka a baya.Amma yanzu na gane kuskurena shiyasa na ce su dawo gareni domin in kyautata rayuwarsu ko Ubangiji zai yafe mini laifin dana aikata a baya.Sannan ina fata in tadda Kakanku Malam Muhammadu cikin salama a aljanna!" Gwaggo ta kai ƙarshen maganar cike da narke masa murya da nuna masa zallar nadamar da zuciyarta ke ciki.AD Dukku ya jinjina kai tare da ratsa hannuwansa a jikin Gwaggo ta yadda kansa ya samu kyakykyawan zama a kafaɗarta ya ce, "Sorry sweetheart! Komi ya wuce ai,zan yi ƙoƙarin hakan." Gwaggo ta saki ajiyan zuciya ta ce, "Yauwa Adinanuna,badon ba a shirya tafiyar da kai ba ai da mun je tare da ka gano garin giwa." Cikin sauri AD Dukku ya girgiza kai yana faɗin, "No Gwaggo! Bana son yawan tafiye-tagiye kema kin san hakan." Gwaggo ta taɓe baki tana ɗaga murya ta kira Tabawa, sai gata cikin hanzari ta iso cikin falon.Ganin AD Dukku manne a jikin Gwaggo ya sanyata sakin murmushi tana masa barka da zuwa.Ya ɗaga mata hannu cikin basarwa ya furta, "Tabawa sannu ko." Daga haka ya zame jikinsa daga na Gwaggo yana zama sosai kusa da ita.Gwaggo ta bai wa Tabawa umurnin kawo masa fura haɗe da soyayyiyar naman ragon da aka soya ɗazu,ta kuma ce ta haɗo masa da ruwa da lemu duka ta kawo.AD Dukku ya dubi Gwaggo cike da so ya ce, "Granny ina Hannah ne wai?" Gwaggo ta ɗan tsuke fuska tana hararansa ta ce, "Baka tambayi uwar taka ba sai ni ƴar kararen da aka so a ɓoye mini abinda ke faruwa, yanzu Adinanu sabida rashin tsoron mahalicci irin naka, ka ɗirkawa ƴar mutane ciki bayan duk ka gama nuna baka sonta akai auren,sannan yanzu kuma kace baka son cikin,don ƙaniyarka ba a haihuwa kai ka zo duniyar? To wallahi kar kaga ina wani lallaɓaka da shagwaɓaka, akan zancen cikin sai inyi maka tsirara a bainar nasi aji kanmu ni da kai.Kuma ba za ta koma garin ƙabilu ta haifo min jika ya yi kama dasu ba,anan zata zauna har ta haihu don tsakanina da kai akan cikinannan babu yarda babu amana.Tunda dai tun farko ka nuna baƙin cikinka akan samuwarsa, don haka ni babu ruwana da kai kama daina tambayata inda take ehe!"
AD Dukku da dariyar drama ɗin Gwaggo ke cinsa arai, sai ya maze tare da sake haɗe face ya ce, "Au yanzu Gwaggo haka zamuyi dake, daga zuwa Momy ta rufeni da faɗa,bata ma sanar min inda take ba yanzu kuma nazo inda zan ji sanyi kema zaki juyemin?" Gwaggo nan da nan sai ta sassauta murya tamkar mai son yin raɗa ta ce, "Kwantar da hankalinka, tana can ɓangarenku da ina zata ka ke zato? Kai ɗin ne ka bani haushi sosai akan zancen wai baka son haihuwa." AD Dukku da sam bai kawo Hannah na ɓangarensu ba, sai ya sauke numfashi yana duban Gwaggo kai tsaye ya ce, "Sorry sweety! Ai yanzu babu zancen cire ciki tunda kuna son abinku, ni dai babu ruwana ne don ban shirya zama uba ba a yanzu da nake ganiyar cin lokacina." Shigowar Tabawa ya hana Gwaggo cewa komi.Tabawan ta aje tray ɗin da ta ɗauro dukkanin abinda Gwaggo ta lissafa, ta aje a kusa dashi ta juya ta bar wajen.Hakan ya bai wa Gwaggo damar faɗin, "Eh mu muna son abin mu, don haka ko kana so ko baka so saika zama uban kana ƙaryan iyashegene Adinanu." Bai sake magana ba ya ɗauki cup ya zuba sassanyar furan da aka dama da asalin nono kindirmo,aka haɗa da kwakwa da madara duk aciki ya kai bakinsa.Ya kurɓi furan sanyi da garɗin furan na ratsashi, ya wani lumshe ido yana sake siffing furan har ya shanye wanda ya zuba tas! Ya dire cup ɗin yana kai hannu ya ɗakko yankan naman ragon ya kai bakinsa.Ya jima sosai tare da Gwaggo har sai da aka kira sallar magriba sannan ya miƙe don zuwa masallaci.Ya fito yana duban side ɗinsu tare da sakin ƙaramin tsaki, amma can ƙasan zuciyarsa na cike da ɗokin son kasancewa da gangar jikin Hannah da yake samun tarin nutsuwa a tattare da ita.......✍🏻
*Pay 500 in to this account number👇🏻*
*0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank*
*OR*
*PAY IN TO DIS ANOTHER ACCOUNT* 👇🏻
**** AISHA* *DANSABO IBRAHIM*
*ACCOUNT NAME:OPAY*
*Evidence of payment to this number:****
🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻*
*MTN*
*GLO*
*AIRTEL*
*9MOBILE*
*MONTHLY VADILITY 💃🏻*
*DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA *** DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻
#Lovestory#
#Najma#
#Aysha Ɗansabo Lemu🥰