Free chapter · Read without an account
Trapped
💠💠💠💠💠
©®AS-2023.
*♡DAUƊAR GORA¸.•💥*
(Cɪᴋɪ ᴋᴀ sʜᴀ ᴛᴀ)
Nᴀ
*HAWWA__B__KUMO.*
(Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
••••••••••
*It's all about:#Vesicovarginalfistula,#VVF,#Desined,#Stepmom,#Family-Saga,#Rural-Urban,#Nigerians,#Halfcast,#Arabian-Fulbe,#Arrogance,#Hated & #Romance..*
14
#Trapped
Rasa bakin magana Amado yayi,kuma ya san bai isa yayi musu ba,dole ya amsawa Baban da "tou! In sha Allah Baba" Baba Wada na gama yi masa ƴar nasihar da zai yi,yai masa sallama ya wuce ya bar gurin,tashi Amado yayi jikinsa a sanyaye,shi kansa tun ɗazu yake tunanin yanda zai yi da Aya,da can ma da take zuwa gidan tayi kwana biyu ake musguna mata saboda ba'a son mahaifiyarta itama abun ya shafeta,bare kuma yanzu da ake jin haushinta akan auren,kamar dai amincewarta akayi kou ita ta fito tace da su Iya tana sonshi,juyawa yayi ya shiga ɗakin da sallama,Aya dake kwance ta amsa ba tare da ta ɗago daga kwancen da take ba,har ya isa gurin da ya mayar makwancinsa ya zauna,sanda ya ɗauki wayarsa da ya ajiye ya shiga duba new texts ɗinsa,kamar bazai magana ba yace "ki shirya kayanki za mu yi tafiya gobe da safe in sha Allah.." Saurin kallonshi tayi gabanta na ɗan faɗuwa tace "tou!" Daga haka sukaiwa juna shiru,can bayan lokaci ta ɗago kamar za tayi kuka tace "amma ban yiwa Iyami da Ummiina sallama ba kuma?" Bai ɗago ba yace "tafiyar gaggawa ne" hawaye ne suka fara saukowa fuskarta,tana danne kukan dake son ƙwace mata tace "kuma idan na mutu fa a hanya? Ni dai bazan bika ba,gurin Iyami da Ummiina zan tafi" ɗago kansa yayi yana barin abunda yake ya zuba mata idanunsa,bilhaƙƙi ta shiga kuka kamar wanda ya zagi uwa da ubanta,kasa mata magana yayi haka nan yaji zuciyarsa ta shiga bashi umarnin yaje ya rarrasheta,tashi yayi ya koma kusa da ita ya zauna,yana kallonta da kyau yace "Aya please.. Stop crying ok? Let me explain this to u" da ƙyar ta bar kukan da take,yana kallonta ya shiga yi mata bayanin yanda suka yi da Babanshi not too long,cikin taushin lafazi yace "if kina son yin sallama da su bazan hana ki ba.. Yanzu ki tashi muje na rakaki ki masu sallama,amma tafiyar gobe da safe ne,kuma bazan iya ƙin bin umarnin mahaifina ba" saurin tashi tayi ta ɗauko sabon vail ɗinta cikin kayan da Ummiinta tayi mata,kamar ta san abubuwan nan za su faru,tayi mata ɗinkunan da kou lefen da ake a garin albarka,tunda akai maganar bikin suka ji shiru,har aka kaita babu kayan aurenta da sadaki babu dalilinsu suna hannun danginta,kuma kou bayan nan ma ba'a kai gida can gurin su Iyami ba,itama kuma ba'a kawo mata ba,da kallo ya bita har ta gama shirinta,ya tashi shima ya ɗauki wayarsa da key dake saman mirror suka fito,gurin ƙarfe 10pm ne lokacin duk garin yai shiru,da yake babu mutane a tsakar gidan,yana rufe ɗakin suka fito tare,kusan jerawa suka yi suna tafiya babu me magana da ɗan uwansa,har suka iso ƙofar gidan Iyami,a kulle suka tarar da gidan,dan tuni ƴan Yobe suka ɗauki hanyar komawa tun safe,yanzu daga Iyami sai Ummii kawai a gidan,ya kalleta yana tsayawa bayanta yace "think sun rufe gidan sun kwanta,kizo mu koma kawai bai kamata mu buga masu ƙofa yanzu ba dare ya yi" saurin juyowa tayi tana kallonsa ta cikin hasken farin wata da wutar NEPA,yana ganin yanda tayi fuskar kuka yace "pleaseee Dear.." Turo baki tayi tace "ni dai ka bari nai masu sallama,ai mun zo gidan kuma sai mu tafi ban gansu ba?" Ganin za tai masa rigima dole ya haƙura ya barta ta ƙwanƙwasa. Ummii da idonta biyu tana dai kwance ne kawai tunanin Aya fal ranta,jiyo kamar ana bugun ƙofa sai da gabanta ya faɗi sosai,ta daure cikin tsoro ta taɓa Iyami da gajiya yasa tuni bacci ya ɗauketa tana faɗin "Iyami kin ji kamar ana buga mana ƙofa" Iyami data tashi zaune tace "wane irin bugun ƙofa ni Halimatus'sadiya da tsohon daren nan?" Ƙaran bugun ƙofa ne yasa su sake saurarawa,kafin su taso a tare suka nufo zauren gidan cikin ɗan damuwa da tashin hankali suna maganar Allah yasa lafiya ba wani abu ne ya faru maƙota ba aka zo sanar masu,suna isowa zauren Iyami dake jikin ƙofar tana tunanin buɗewa tace "waye da daren nan haka?" Aya dake jikin ƙofar tsaye tana jiyo maganarta tace "Iyami nice.. Aya ce" gabansu ne ya kuma faɗuwa Iyami data shiga ruɗanin abunda ya fito da Aya yanzu ta furta "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Mene ne haka yake shirin faruwa da mu?" Ummii kam jikinta tsuma ya ɗauka tana tsaye bayan Iyami tana janyo duk addu'ar da yazo bakinta,Iyami tai saurin buɗe ƙofar tana ware idanunta tace "Shalele lafiya kika fito da wannan daren,kuma daga kaiki gidan miji kwana biyu?" Aya tace "lafiya lau Iyami,sallama muka zo yi maku" hannunta Iyami ta kamo tana sake shiga ruɗani tace "tou muje ciki" Aya ta juya ta kalli Amado dake tsaye har lokacin tace "Yaya ka shigo" gyaɗa mata kai yayi hannayensa a cikin aljihun wandonsa fuskarsa a ɗan sake yace "okay!" Sannan ya biyosu zuwa cikin gidan,a parlour suka zauna Amado ya gaishe da su Iyami cikin mutunci da ɗan jin kunyarsu,saboda yanzu ba da bane,ya saba zuwa ya shigo har cikin gidan,amma yau sai yaji nauyin abun,kou dan yanzu shi suruki ne a gidan oho. Aya na ta kallon Ummiinta da ta zauna hankalinta duka akanta,a hankali bayan sun gaisa da Iyami tace "Ummii ina yini?" Ummii tace "lafiya lau Aya,ya gidan?" Aya ta ɓata fuska kamar za tayi kuka tace "lafiya lau.. Bayan ma baki zo kin ganni ba" ajiyar zuciya Ummii tayi ba tare da ta ce komai ba,she's eager taji meke tafe da su,kamar Iyami ta san abunda ke ranta tana kallon Aya tace "Shalele sallamar me kuka zo yi mana?" Aya tana turo baki tace "Yaya ne yace za muyi tafiya gobe,shi ne nace zanzo nayi maku sallama" Iyami ta gyaɗa kanta zuciyarta na sakewa daga tsoron da ta shiga,idanunta akan Amado tace "Ahmadi! Wani gurin za ku tafi ne?" Gyara zamansa yayi sannan ya shiga sanar da Iyami duk yanda suka yi da Babanshi,Iyami da Ummii suna ta saurarenshi,yace "kou nima na yi tunanin hakan,saboda gurin aiki basu san na yi aure ba,duk yanda zanyi kuma su bani hutu they refuses to do so,shi yasa za mu tafi tare" Iyami na gyaɗa kanta cikin gamsuwa da maganarsa tace "tou Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi,amma da mun san za ku zauna can,ai da ba'ayi mata jere a nan ba,da sai a bar kuɗin idan kun isa a siya mata kayan" Amado yana ɗan lumshe idanunsa kansa a ƙasa yace "babu komai Iyami in sha Allah za'a siya,idan mun zo nan sai muyi amfani da wannan" Iyami tace "amma Ahmadi ai hidimar za tayi yawa,sai dai ku tafi da wani abun daga nan kou?" Ɗan murmushi ya saki yana shafa sumar kansa yace "Iyami ba sai mun yi haka ba,idan muka ce za mu ɗebi kaya daga nan zai zame mana wahala,gara dai idan mun tafi sai a siya a hankali" Iyami ta gyaɗa kanta tana cewa "tou shi kenan Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi,Allah kuma ya kaiku lafiya.." Ya amsa da "ameen.." Aya dake jikin Iyami tai kicin² ya kalla yace "Iyami za mu tafi,bamu gama shiri ba" Iyami tace "tou shi kenan Ahmadi,gara kam kuyi harama,sai dai nace kou za ka bamu adireshin inda za ku zauna,wata rana idan na shigo Kano kasuwa na biyo naga Shalele" Amado yayi murmushi yace "tou Iyami,amma bari na baki number ta sai ku kirani idan za kizo,zan zo na taho dake in sha Allah" Iyami tace "tou babu laifi hakan ma" tana kallon Aya da tai ɗai² a jikinta tace "Shalele tashi ki shiga ki kawo masa takarda da biro cikin jakarki ya rubuta ku tafi,dare yana sake yi" a hankali Aya ta miƙe ta wuce ɗakinsu,inda take ajiye jakarta ta nufa ta ɗauko assignment book ɗinta ta fallo paper ciki sannan ta fito,Iyami ta miƙawa takardan tana zama jikinta,daga shi har Iyami suka kalleta,Ummiinta dake zaune bata ce komai ba duk hiran da suke tace "Aya baza ki kai masa bane?" Kallon Ummii tayi tana turo ɗan bakinta,ta ɗauke kai ta matsa ta miƙa masa,yana kallonta ya amsa ya zana special digit ɗinsa da suna sannan ya miƙawa Iyami yana ɗan murmushi yace "Iyami za mu koma" Iyami dake karɓan takardan tace "tou Ahmadi mun gode ƙwarai Allah ya kaiku lafiya ya tsare hanya" ya amsa da "ameen.." Sannan yana kallon Ummii dake ɗan murmushi yace "sai da safe Aunty.." Ummii tace "tou Ahmadi Allah ya tsare hanya" ya amsa yana miƙewa ya fita,Aya kamar za tayi kuka take kallon Ummiinta tace "Ummii ni dai kice ya barni a nan please" wani kallo Ummii tayi mata tace "ki rufa min asiri Aya,ki tashi maza kibi mijinki,domin a yanzu daga ni har Iyami ya fimu iko dake,idan dai ba so kike a fara yawo da ni a garin nan ana cewa zan kashe maki aure ba.. Zagin da ake min ma ana cewa na ƙi aure na zauna yawon gantali ya isa haka.." Shiru tayi cikin rashin jin daɗin maganarta,daga Aya har Iyami jikinsu duk sai yayi sanyi,miƙewa Aya tayi tana mayar da hawayenta tace "Iyami mun tafi" Iyami ta tashi itama tana faɗin "tou Shalele,ki kula kin ji? Kinga dai babu wanda kika sani a can sai shi,dan Allah banda shashanci,ki riƙe Yayanki kuma mijinki a matsayin danginki,tsakaninki da shi yi na yi bari na bari kin ji? Allah ya baku zaman lafiya" share hawaye tayi tace "ameen.." Suka fito tare da Iyami tana sake yi mata nasiha,sai da ta rakota har ƙofar gida inda yake tsaye yana jiranta tazo su tafi,Iyami ta ɗan tsaya tana cewa "kuma ki dage da addu'ah da tsafta,in sha Allahu duk sanda muka shigo garin za mu zo mu ganki" Aya tace "tou Iyami.. Mun tafi,sai kun zo" Iyami na tsaye sukai mata sai da safe suka wuce,sai da sukai nisa sosai sannan ta juya ta koma tare da rufe ƙofar gidan tana ɗan sakin murmushi,ta wani ɓangaren tafiyarsu sosai yai mata daɗi,kuma ta san tabbas Baba Wada yana son ɗansa da ƴar ɗan uwansa ne,sai dai wani gefen tana jin damuwa da Aya za tayi nisa da su,yanzu baza su dunga ganinta lokacin da suka so ba. Aya kam kou da suka bar gidan,a hanya babu wanda yace da ɗan uwansa komai har suka isa gida,da taimakonsa sukai parking wasu cikin kayan da za su yi amfani da su idan sun isa can Kano a daren,suna gamawa tai shirin bacci ta miƙe a kan gadonta,shima Amado shirin kwanciya yayi a inda ya saba,da yake kusan dukansu a gajiye suke nan take bacci ya ɗauke su. Da asubah kou da suka tashi shi ya fara fita kamar kullum,sanda yaje yai alwala ya wuce masallaci,yau kam bai tsaya ba ana fitowa ya nufi gidan wani driver a garin yai masa magana,daga can ya wuto gida,lokacin Aya na shirin rufe ƙofa ta sake kwantawa dan bacci ne a idonta,ganin ya shigo ta fasa a tunaninta zai ɗauki abu ne ya fita,sai taga ya nemi guri ya zauna,yana ɗan kallonta bai jira gaisuwarta ba yake cewa "akwai mai cab da zai zo ya kaimu,so ban san ya za'ayi ba,na sanar masa za mu tafi da wuri" jikinta a sanyaye tace "Allah ya kaimu" ya amsa da "ameen" sai ta gaisheshi ya amsa,daga haka ɗakin yai shiru,shi yana azkar ɗin safiya da baiba,ita kuma tana can gurin tunanin tafiyar da za suyi. 7am saura ya gama shiryawa cikin white long sleeve shirt da black trouser jean,sosai yai kyau cikin shigar ya yi stocking rigar nashi kamar bature,while Aya kuma tana sanye da doguwar riga na material me kyau da ya amshi farar fatarta,kayan da za su tafi da shi ya dunga ɗauka yana kaiwa mota,a lokacin duka ƴan gida suna bacci babu wanda ya tashi sai su da basu koma ba,yana gamawa ya shigo yana kallonta yace "muje we are getting late.." Tashi tayi tana kallon ɗakin nata ta wuce suka fito,shi ya karɓi makullin ya rufe sukai gaba abunsu ba tare da sun yi sallama da kowa ba,a bakin layin gidan suka tarar da mai motar yana tsaye yana jiransu,Amado ya buɗe mata back seat ta shiga,sai da ya rufe sannan ya buɗe front ya shiga yana yin bismillah,Aya da jikinta yai sanyi ta gaisar da mutumin kafin ya tada motar suka fara tafiya a nutse,tana ta kallon hanya tana danne kukan dake son ƙwace mata har suka baro cikin garin,a hankali ta dunga sauke ajiyar zuciya tana jin wani gefe na zuciyarta ya yi free,kamar wanda aka saki daga jail,tunda suka taho motar yai shiru babu me magana,sai da me motar ya gaji ya kunna radio ɗin motar yana sauraran BBC Hausa,102Km suka share daga Kachako zuwa Kano,sanda suke shigowa cikin gari ta Zaria Road me cab ɗin ya ɗauke hanya,sun ɗan yi tafiya kafin su iso Sharaɗa industrial estate,daga nan Amado ya dunga bashi direction har suka iso arean da gidajen da suka kama haya suke,dai² get ɗin gidan yasa mutumin yayi parking,shi ya fara buɗewa ya sauka sannan ya buɗe mata,Aya kam tun bata fito ba take kallon arean ganin gidaje ne na alfarma a jere reras iri ɗaya masu bene,ba kamar a can garinsu ba data saba idan ta fito taga ginin laka,da yake duk apartments ɗin mutum biyu ne ciki sama da ƙasa,suka dunga sauke kayansu tare da me motar,sanda suka gama ya sallami driver ɗin ya tafi,yana kallonta yace "ki tsaya nan bari na shiga da kayan" a hankali ta gyaɗa masa kai tana ta kalle²,shi ya dunga shigar masu da kayansu,Aya duk a tsorace take saboda line da yai shiru babu motsin kowa sai kukan karnuka,yana fitowa ya ɗauki wasu kayan zai tafi,tayi saurin ɗaukan sauran kayan ta bishi,bai ce mata komai ba suka ƙarasa balcony ɗinsu ya buɗe entrance ya shiga ta sake biyoshi bumper to bumper,ɗakin da yake babu komai suka kai kayan,bayan sun fito ta tsaya tana kallon parlon gidan da babu komai cikinsa,shi kuma a ɗan hanzarce yana kallon wall clock dake nuna 8 saura na safe,yana juya idanunsa kanta yace "zaki iya zama?" Gyaɗa masa kai tayi ba tare da ta gane kan tambayar nasa kou ta tambayeshi ba,yace "okay! Ga bedroom nan ki shiga ki huta,zanje office sai anjima zan dawo,ki kula da kanki" rau² idanunta suka yi tace "ni kaɗai zan zauna a nan?" Yace "shi yasa na tambayeki ai kika ce eh" girgiza masa kai tayi a bit scared tace "ai babu kowa a gidan,ni bazan iya ba ka tafi dani" murmushi ne ya suɓuce masa yace "bazai yiwu na tafi dake ba,but follow me bari na kaiki inda za ki zauna,idan na dawo sai nazo,okay?" Gyaɗa masa kai tayi tana share hawayen da suka fara saukowa fuskarta,yace "let's go" yana juyawa ta biyoshi da sauri har tana tuntuɓe kamar wanda idan ya bari wani abu zai fito ya kama,suna fitowa sai da ya tsaya ya rufe gidan sannan ya nufi wani siririn hanya,suna kawowa bakin wani ƙaramin ƙofa ya buɗe sai ga staircases,ya haura itama haka,suka ɓillo another balcony a can saman dake da babban ƙofa me biyu kamar na parlonsu,knocking yayi tare da danna doorbell,daga ciki suka jiyo muryar mace tana cewa "yes! I'm coming" suna tsaye aka buɗe ƙofar,wata ƴar kyakkyawar matashiya ce ta buɗe wanda ta ɗan girmi Aya sosai,ganin Amado ta saki fuskarta tana faɗin "good morning Oga Ahmad" Amado ya amsa "morning Madam,ya gida?" Tace "lafiya lau alhmdllh.. Ashe baka fita ba" yace "yeah! Shigowata kenan garin tare da Madam" buɗe ido sosai tayi tana kallon Aya dake gefenshi tace "Wow! Dama kana da aure amma kake ta zaune kai kaɗai a nan?" Yayi ɗan murmushi idanunsa akan Aya,yace "no ba haka bane,2 weeks ago dai nayi auren" tana gyaɗa masa kai tace "ohh! Congratulations sir,Allah ya baku zaman lafiya" yace "ameen,thank u Madam.. Please kou zan iya barinta nan ta zauna kafin na dawo? Ina sauri zan wuce office and she's afraid" da sauri tana gyaɗa masa kai tace "laaaa! Babu komai kai tafiyarka kawai tazo mu zauna mana" yayi ɗan murmushi yace "na gode sosai Madam" tace "nice da godiya Oga,nima na samu abokiyar hira yau,kullum dama sai dai na zauna ni kaɗai a gidan,hakan kuma sounds too bored idan babu motsin mutum kusa,duk sai ka jika cikin kaɗaici" yana kallon agogon dake ɗaure wrist ɗinsa yace "thank u Madam sai na dawo" fatan alkhairi tayi masa,ya juya yana kallon Aya da kanta ke ƙasa yace "za ki iya zama nan idan na dawo zan zo,okay?" Ta gyaɗa masa kai tana ɗago idanunta ta kalleshi,murmushi yai mata sannan ya juya da ɗan sauri yabi stairs ya fara sauka,Aya data bishi da kallo fuskarta da ɗan murmushi da ƴar siririyar muryarta tace "Allah ya tsare ya bada sa'a" ya amsa mata yana ƙarasa sauka,matar tana kallonta tace "hey! Zo mu shiga ciki Mr's,ban tambayi sunan ki bama.. Ni suna na Tayyibah" Aya tai mata murmushi tana biyota a baya zuwa cikin parlonsu tace "ni kuma Ayshatou,amma ana kirana da Ayatullah" Tayyibah tace "Wow! Nice name kamar me shi" Aya tayi murmushi lokacin Tayyibah na janta suka zauna saman kujera,sai sannan suka gaisa da Tayyibah,a hankali ta dunga jan Aya da hira har tana bata labarinta,itama amarya ce matar wani abokin aikin Amado ce da tasu tazo ɗaya,sai dai da yake Amado ya fishi jimawa a aikin,duk abunda ya shige masa duhu kuma shi yake samu tunda ya fishi gogewa a aiki,shi ne yake ce masa Oga Ahmad,har itama Tayyibah ta ɗauki hakan,kasancewar bata jima sosai² da zuwa ba shi yasa babu wanda ta sani,ita kuma Aya duka sai ta kasa sakewa sosai sai dai tayi mata murmushi,har Tayyibah ta gane Aya ba me magana bace sosai kamarta,tashi tayi ta tafi kitchen ta kawo mata ruwa da drink sai snacks,a haka ma tana ta bawa Aya haƙuri wai bata san za su zo ba,Aya dai sai murmushi take saboda kirkin Tayyibah yai yawa. Tunda Amado ya tafi ya bar Aya hankalinsa kwance ya ƙarasa Company,while ita kuma Aya ganin Tayyibah ta shiga kitchen tana preferring lunch,ta ɗan kwanta nan bacci ya ɗauketa,sai da aka fara kiran sallah nan masallacin dake cikin estate ɗin sannan ta tashi,lokacin Tayyibah na shirya dining table,tai mata murmushi tace "kin tashi?" Aya tace "Mmmm! Zan yi sallah" Tayyibah tace "okay! Ga bedroom can ki shiga akwai toilet sai kiyi" Aya tace "tou!" Ta tashi ta nufi ƙofar da Tayyibah ta nuna mata a ɗan ɗarare,kallon ɗakin taita yi kafin ta wuce ƙofar da Tayyibah tace,komai na nan ya fita daban da irin yanda ta saba gani,dan ma dai ta san wasu abubuwan a gidan Iyami,tunda Ummiinta ta yi rayuwa Saudiyya duk ita ta wayar mata da kai,fitsari tayi ta ɗauro alwala sannan ta fito,lokacin Tayyibah ta shigo ɗakin ta buɗe press ta ɗauko mata hijab da sallaya ta shimfiɗa mata,Aya ta dunga kallon irin press ɗin tana mamaki a ranta domin ita dai bata taɓa ganin press a cikin gini ido da ido ba sai yau,sallah ta kabbarta Tayyibah kuma ta shiga toilet itama ta ɗauro alwala,sanda suka idar da sallah Tayyibah tace "muje muci abinci" Aya tace "tou!" Tare suka fito zuwa dining,Tayyibah ta zuba mata itama ta ɗiba,babu wanda ta sake magana cikinsu har suka gama,suka koma parlon suka zauna,Tayyibah tayi masu powering TV bayan taje ta ɗebo masu kayan gararta suna ci suna kallo,yinin ranar Aya na tare da Tayyibah. Sai guraren maghreeb sannan Amado ya dawo,sanda ya buɗe gidan ya shiga yai wanka ya ɗaura alwala ya fito zuwa masjeed,after yai sallah bai dawo ba ya tafi yai masu ɗan siyayyan abunda za su buƙata nan kusa da na abinci kafin ayi masu salery,lokacin da yake dawowa ana kiran sallar ishaa,bayan ya shigar da kayan ya sake fitowa yai sallah. Usman mijin Tayyibah da ya dawo ya tarar da Aya a gidan,bayan sun gaisa Tayyibah ta bishi ɗaki,ya juyo ya kalleta yana cewa "Baby baƙuwa muka yi ne?" Tayyibah tai murmushi tace "ehh tun safe take nan,matar Oga Ahmad ce ya kawota ta zauna nan kafin ya dawo" murmushi Usman yayi yace "Oga Ahmad yai aure amma babu sanarwa?" Tayyibah tace "auuu! Kuma bai sanar maku ba?" Usman yace "wallahi bai sanar mana ba,amma ban san dalilinsa ba" Tayyibah tai murmushi tace "nima da ya kawota yace min matarsa ce na yi mamaki,saboda ganin yarinya ce sosai,amma kuma kamar bai san da auren ba nake ga,duba da abunda yace min,2 weeks ago yana nan garin bai je ko ina ba" Usman ya tsaya yana kallonta jin maganar da take yace "haka ne.. Tou koma dai mene ne Allah ya basu zaman lafiya" Tayyibah tace "ameen.. Amma yarinyar ba ta da hayaniya,tunda ya kawota ta kame kanta,sai dai akwai fara'a,kuma ni sai nake ganin kamar ƙanwarsa ce dan suna ɗan yanayi da shi" dariya Usman yayi yace "kaii Baby daga zuwanta har kinga suna kama,Allah yasa baki dameta da surutu ba" ɓata fuska tayi tana kallonsa,yai mata murmushi yana jan towel ya ɗaura a jikinsa ya nufi bathroom,wanka yayi ya fito ya shirya sannan ya fita masjeed jin ana kiran sallar ishaa. Yana idar da sallah ya fito masallaci tare da nufo gida,sai lokacin sannan ya wuce ɓangaren su Tayyibah,yana haurowa saman ya danna bell,Usman da bai jima da dawowa daga masallaci ba,yana kallon Tayyibah da suke hira a gefe yace "think Oga Ahmad ne,bari na duba" ya tashi ya nufi ƙofar ya buɗe,Amado dake tsaye yaiwa Usman sallama sannan suka yi musabaha,cikin jin nauyinsu Amado yace "kuyi haƙuri na saku wahala kuma ban sanar maku aurena ba alhalin ana zaune lafiya,al'amarin ne yazo min nima babu shiri" nan ya ɗan bawa Usman ɗin haƙuri tare da labarin yanda auren ya kasance,Usman yace "haba Oga babu komai wallahi,ai nima na dawo Baby take sanar min,sai dai na yi mamaki" Amado yace "Allah sarki.. Na gode sosai Allah ya bar zumunci" Usman ɗin yana kallonshi yace "Allah ya sanya alkhairi Oga.." Amado yace "ameen.. Thank u" Usman yana juyawa jin Tayyibah na masa magana yace masa ya shigo,yace "bismillah Oga! Ka shigo daga ciki" girgiza kansa Amado yayi yace "a'a wallahi ba sai na shigo ba,kawai ta fito mu wuce gida dare ya yi" Usman yace "dan Allah Oga ka shigo,ka gansu can fa suna hira,baka ga yanda Baby ta yi murnar samun abokin hira ba,dama ita kaɗai take zama sai idan na dawo,yau kuma tunda ta samu ƙawa har labari take bani" Amado yace "Allah sarki.. Babu komai wani lokaci zan shiga,amma yanzu sauri nake akwai aikin da zanyi idan na koma" Usman yace "tou shi kenan Oga bari na sanar mata" daga haka ya koma yana kallon Tayyibah yace "Baby Oga Ahmad yana jiranta za su tafi" Aya na jin ya ambaci sunan Amado ta gyara zaman mayafinta tare da miƙewa tsaye,Tayyibah tana kallon mijinta tace "amma ai da ya shigo,idan suka yi dinner sai su wuce,ni har da su na saka girki" Usman yace "tou nima nayi masa magana amma he refuse to,ya ce yana da aiki ne" gyaɗa kai Tayyibah tayi tana kallon Aya tace "kai sister Aya har kin tashi kema daga jin ya dawo" cikin jin kunya Aya ta sauke kanta ƙasa ba tare da ta ce komai ba,Usman dake tsaye bayan kujera ya ɗan sunkuya yace "tou ki ɗebar masu abincin kawai idan sunje sai su ci" Tayyibah tace "ehh dama tunda yace a'a sai dai su tafi da shi ɗin" ta tashi ta wuce kitchen ta ɗebar masu a wani warmer me kyau ta fito,lokacin Aya da Usman har sun yi waje,ganin haka ta biyosu,ta samesu tsaye a balcony suna magana da juna,Amado sai godiya yake yiwa Usman,gaisheshi tayi ya amsa sannan ta isa ta miƙawa Aya warmer ɗin tana cewa "tunda tafiya za kuyi ga shi babu yawa dan Allah kada ku raina" Aya ta girgiza mata kai tace "a'a wallahi ai na ci ɗazu na ƙoshi" Tayyibah tace "taɓɓɓ ɗin ai kuwa wallahi sai kun tafi da shi,ni idan kun barni da shi nayi yaya? Har da ku dama nasa sanwa,dan Allah ki karɓa idan ba haka ba babu ni babu ke,Baby kai da Oga Ahmad ku zama shaida" kallonsa Aya tayi taga yana murmushi,tace "Yaya na karɓa?" Ya gyaɗa mata kai,Tayyibah ta buɗe idanuwanta tana dariya tace "ohh da baice ehh ba baza ki karɓa ba kenan?" Aya tayi dariya da ya ƙara mata kyau tana gyaɗa kanta tace "ehh!" Tayyibah tace "lallai ma ai kuwa da har bakin entrance ɗinku zanzo na ajiye" sun ɗan jima tsaye kafin suyi masu sallama,su Aya suna yiwa Tayyibah da Usman godiya suma suna yi masu,kusanma har ƙasa suka rakosu sai da suka ga shigarsu nasu gidan sannan suka juya,Tayyibah tana sake bashi labarin sanyin hali irin na Aya. Suna shiga gida Amado ya rufe masu ƙofarsu tare da wucewa bedroom,Aya ta biyoshi da warmer ɗin a hannunta,ta ƙarasa tare da ajiyewa gabansa ganin ya zauna gefen ƙaton semi orthopedic katifarsa,zaunawa tayi saman carfet dake shimfiɗe gaban katifar,kallon warmer ɗin yai kafin ya janyo ya buɗe,light food ne ciki jellop na spaghetti sai veg's da dry fish aka dafa da su yana ta ƙamshi,ya ɗago yana kallonta yace "je ki wanke hannunki a toilet kizo" girgiza masa kai tayi tace "ni na ci abinci ɗazu" kafeta yai da idanunsa yace "ai kin ji me kika ce ɗazu.. Yi sauri kije ki dawo kada yai sanyi" she has no choice than ta tashi ta tafi ta wanke hannun,kuzo kuga inda ake yinta tana zama ya turo mata warmer ɗin gabanta yana cewa "let's eat together.." Saurin kallonshi tayi gabanta na tsananta faɗuwa,bata taɓa zaton zai ce tare za su ci ba,shi kam kou a jikinsa kamar ma sun saba yin hakan,yana saukowa yasa hannunsa ya fara ci,daskarewa Aya tayi a zaune saboda kunyar data cikata,ita idan ba Ummii da Iyami ba,bata taɓa cin abinci da kowa ba musamman ma namiji,sai yanzu da take ganin hakan a gurin Yayanta,yana kula da yanda taƙi ci,ya ɗan dakata tare da kiran sunanta "Aya!" Kasa ɗagowa ta kalleshi tayi,yai murmushi yace "ci mana kou kina jin kunyata ne?" Gyaɗa masa kai tayi da sauri,cikin sigar tsokana kamar ba shi ba yace "ohh! Kou na baki a baki ne?" Saurin ɓoye fuskarta tayi tsakanin ƙafafuwanta,cikin tarin kunya tace "a'a!" Yace "okay! Idan ba kya so na baki ki ci ina kallonki" saurin gyaɗa masa kai tayi sannan ta gyara zamanta ta fara tsakura kaɗan² yana kallonta,bata ci da yawa ba ta tashi tace ta ƙoshi,ya nuna mata toilet yace "oyah! Go and wash ur hand,akwai brush da toothpaste" ta gyaɗa masa kai ta wuce,har ta kai ƙofar banɗakin ya sake cewa "ahah! Idan za kiyi wanka kizo ki duba towel a cikin press" amsa masa tayi da tou sannan ta shige,duk wannan abun da yake mata bata tabbatar da bai sa ta ji kunyarsa ba,sai da suka zo kwanciya bacci,taga ya miƙe saman katifar,ta tsaya can nesa sanye da riga da wandonta na bacci saman kuma ta saka hijab,tunda tai wanka ta fito tayi sallar shafa'i da wutr take sanye dashi kunya ya hana ta cire,sai da ya gaji da ganin haske a ɗakin sannan ya juyo ya kalleta yace "ain't u ready to sleep?" Kame² ta fara tace "Mmmm.. To.. Tou.. Ai ban san inda zan kwanta ba,baka nuna min ɗaki na ba" ya kalleta da kyau ganin da gaske take yace "nan ba ɗaki bane? Baza ki iya kwana a nan ba?" Yahun tsoro ta ɗan haɗiye kafin tace "a nan?" Yace "yes! Come ƙin matsowa tayi yace "zo mana" a hankali kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki ta dunga tahowa,yana kallonta har ta iso ta sake tsayawa ɗan nesa kaɗan,ya bita da wani kallo lokaci ɗaya ya miƙe,a tsorace ta koma baya da sauri tana shirin sakin kuka,taɓe bakinsa yayi ya wuceta,kamar bai ma damu da ita ba ya ƙarasa tare da kashe hasken ɗakin duhu ya mamaye ko ina,yana tsaye gurin yana kallon shade ɗinta da yake kayanta masu haske ne ya taho inda take,bata san yaushe yazo kusa da ita ba,sai da ya ɗagata ya nufi saman katifar,ihun tsoro ta saki tace "Yaya please.." Yace "ke ƴar rainin hankali baki san zan iya ɗaukanki bane?" Zazzare idanuwa ta fara tana yin kalar kuka,cikin sigar raɗa yace "tsoron me kike yi?" Kasa cewa komai tayi har ya sauketa kan katifar,ya kamo hijab ɗinta yai sama da shi ya cire yana cewa "ba'a kwanciya da kaya da yawa,baki san an fara zafi ba? Idan zafi yai yawa yanzu sai sanƙarau ya kamaki" can gefe ya ajiye hijab ɗin,ita kuma ta takure a gefe ɗaya,ta yi zaton zai mata wani abune daga nan,sai taji shiru bai sake magana ba yai kwanciyarsa gefenta yana addu'o'insa,addu'ar itama tayi kamar yanda Ummiinta take sata yi duk dare kafin bacci,tana gamawa ta juya masa baya tana zazzare idanuwa,a haka har bacci ya ɗaukesu duka. Da asubah kiran sallah ne ya tasheshi,bai buɗe ido ba amma yana jinta a jikinsa,ya ɗan ware idanunsa da mamakin sanda tazo kusa da shi,ya kalleta duk da ba ya ganinta da kyau,haka nan kusancin nasu yasa shi yaji jikinsa a wani irin mace,daurewa yayi ya kira sunanta "Aya!" Da yake ba ta da nauyin bacci tace "Mmmm!" Yace "wake up asubah ya yi" buɗe ido tayi a hankali tana sauke ajiyar zuciya,jinta a jikinsa yasa tai saurin tashi tana ja baya,yayi murmushi ya tashi ya kunna bulbs ɗin ɗakin sannan ya wuce toilet,ruwa ya fara watsawa jikinsa kafin ya ɗaura alwala,kou da ya fito bata iya kallonsa ba tai sauri ta wuce,ya bita da kallo yana sakin ɗan murmushi,a gida yai raka'atanil fajr sannan ya fita zuwa masallaci lokacin ana shirin tada iƙama,bayan an idar da sallah bai tsaya ba ya taho gida,a hanya suka haɗu da Usman ya miƙa mashi hannu suka gaisa,Usman ɗin yana tambayarsa Aya,yace "tana lafiya" har suka shigo get ɗinsu ya rufe sannan sukai sallama shi ya wuce apartment ɗinsu shima Amado ya ƙatasa balcony ɗinsu tare da buɗe ƙofa ya shiga,zaune ya tarar da ita saman sallaya tana azkar,har ta gama sannan tai masa barka da dawowa after then ta gaisheshi ya amsa yana zaunawa bakin katifa har ta idar sannan yace "zo ki kwanta idan zan tafi office zan tasheki" babu musu ta taso ta tafi can gefen data kwana ta kwanta tana sanye da hijab ɗinta. Bai koma bacci ba ranarma ya zauna yana duba wani plan na gidan Mai a Macbook ɗinsa,yana gyara abunda bai ba a ciki,7:30am ya tashi yana kallon Aya ta hasken da ya game gari,kamar zai tasheta kuma sai ya fasa ya hau shirinsa,yana gamawa ya fita gidan,balcony ya tsaya ya kira number Usman amma bai ɗauka ba,kamar ya koma kuma sai ya nufi apartment ɗinsu ya haura saman,nocking yayi kafin ya danna bell,Usman da bai fita ba yazo ya buɗe,ganin Oga Ahmad ne suka gaisa,Amado yace "i'm sorry na dameku.." Usman yace "babu komai Oga,ai an zama ɗaya" Amado yana ɗan murmushi yace "na kiraka baka amsa ba,shi yasa nazo na sanar da Madam,amma tunda kana nan dan Allah ka sanar mata na bar ƙanwarta a gida tana bacci,an jima ta shiga ta dubata please,ta nuna mata yanda za ta kula da gidan da sauran aikace².. Ba komai ta san yanda za tayi amfani da shi ba a nan,saboda yanayin nan da can gida akwai bambanci" Usman yace "okay! In sha Allah za taje ta dubata" Amado yayi masa godiya sosai sannan yai masa sallama yana cewa ya wuce office,Usman ɗin yana cewa "okay! Oga sai na iso in sha Allah" daga haka Amado ya sauka ya wuce gurin aikinsa. A ɓangaren Aya kuwa tunda ya fita ya barta take bacci,sai can lokacin da doorbell yai ring ta tashi tana murza idonta ta ɗauko hijab ɗinta da bata san ya akayi ya bar jikinta ba tasa ta fito,ta yi mamaki da bata ganshi ba,tana zuwa ta buɗe ƙofar,Tayyibah dake tsaye tai mata murmushi tace "good morning sister" Aya tai mata murmushi itama da ƴar siririyar muryarta tace "sannu da zuwa,shigo.." Tayyibah ta shigo ciki tana kallon parlon da babu komai ckinsa,tace "ba dai yanzu kika tashi ba?" Aya tace "ƙaran nan ne ya tasheni" Tayyibah tace "ohh! Sorry na tada ki" Aya na mata murmushi tace "babu komai.. Ina kwana?" Tayyibah ta amsa tana cewa "tun ɗazu Baby ya sanar min saƙon Oga Ahmad,ina aiki ne shi yasa ban samu na shigo ba sai yanzu" Aya tayi ɗan murmushi mai haɗe da ajiyar zuciya jin an ambaci sunansa,Tayyibah tace "mu fara gyaran gidan kafin kiyi wanka?" Aya tace "ehh! Bari nayi fitsari na fito" Tayyibah tace "okay!" Wucewa Aya tayi hanyar bedroom ɗinsu,Tayyibah ta bita da kallo ganin ƙanƙantar shekarun Aya take sosai,musamman da aka haɗata da Ahmad wanda ya ninka shekarunta har da ɗori,ta dunga gyaɗa kai cikin tarin mamaki,sai dai wai da Hausawa suka ce abunda babu ruwanka daɗin ji da kuma kallo gareshi,haka nan itama taja bakinta tai gum,Ayan tana fitowa suka hau share gidan Tayyibah tana tayata,wani abun da bata sani ba kuma tana nuna mata yanda za tayi,cikin ɗan lokaci suka gyara ko ina,wasu abubuwan duk na Tayyibah ɗin ne taje ta ɗauko suka yi amfani da shi,kafin 12pm sun gama gyara gidan sun shiga kitchen,Tayyibah ta nuna mata yanda komai yake da yake iri ɗaya ne da na gidanta,bambancin kawai nan ƙasa ne su suna sama,suna ganawa lokacin ana kiran zhuhur,suka je sukai sallah tare sannan suka ci abinci,ranar ma haka suka yini tare sai maghreeb da Amado ya dawo sannan Tayyibah taiwa Aya sallama ta tafi. Tun daga ranar idan Aya bata je gurin Tayyibah ba,ita za tazo kuma mafi yawanci ma Tayyibah ɗin ta fi zuwa gurinta,a haka har suka share sati da zuwa garin. Yau ya kama weekend,duk da babu aiki amma hakan bai hana shi fita ba,ya je duba wani aikin da aka ɗaurashi akai,tun safe bai dawo ba sai dare,lokacin da yake shigowa a mugun gajiye yake,suka gaisa da Tayyibah a tsaitsaye sannan ya wuce bedroom,taɓa Aya Tayyibah da ta gama karantar yanayin zamansu tayi,wasu abubuwan idan taga Aya ta yi ba dai² ba takan gyara mata,saboda sosai Allah ya haɗa jininsu,yanzu suna ɗan sakewa suyi hira har su bawa juna labarin abunda ya faru baya kou kuma haka nan dai hirar ta biyo takan wani abun su ɗan tattauna,even though Tayyibah ta fi Aya magana sosai,cikin sigar raɗa da tsokana tace "Sister ki tashi kije mana mijinki ya dawo kina zaune a nan,wannan ai duhun kai ne kike yi,ni baki ga yanda nake yiwa Baby ba wai?" A kunyace Aya ta tashi tabi bayansa,kou sallama basu yi ba Tayyibah ta silale ta gudu tana dariyar mugunta,so take ta zurmata saboda ta fahimci babu abunda ya taɓa shiga tsakaninsu...
#Me kuke tunanin zai faru tsakanin Aya da Yayanta a zaman nan nasu? 🤔😥 Kou ina mutanen gidansu? Ya suka yi da suka wayi gari babu Aya da Amado a gidan?
*MAZAN FAMA GLOBAL COMMUNICATION..*
```Muna farin cikin sanar da ƴan uwa tare da masoya cewa,wannan Company namu yana siyar da data akan farashi me sauƙi na networks da muke da su a Nigeria kamar haka:```
*MTN*
500MB—₦150
1G—₦300
2G—₦550
3G—₦850
5G—1,450
10G—₦2,750.
FOR DATA BALANCE
DIAL:*460*260# or *461*4#
*AIRTEL*
500MB—₦150
1G—₦300 2G—₦550
5G—₦1,4000
6G—1,650.
DATA BALANCE *140#
*GLO*
1.35G—₦550
2.9G—₦1,050
5.8G—₦1,500
7.7G—2,050.
DATA BALANCE *127*0#
*9MOBILE*
2G—₦1,200
3G—₦1,650
4G—1,950
6G—₦2,600
7G—₦2,900.
DATA BALANCE *228#
contacts:***
Account №:6074981401
Account name:Aliyu Muhammad Usman
Bank name:9 Payment Service Bank.
#Follow
#Vote
#Comment
#Share
#Asli Smasher.