Free chapter · Read without an account

2

by Nazeefah Nashe · TAKAICIN UBA

Takaicin Uba…..


Na


Nazeefah Sabo Nashe..



***.


❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️


2..






Zainab da tun shigowarsu bata ce komai ba, don tana da zafi idan ta ce zata biye ta Ayra fes zata mata mugun duka, sau tari Ayran ta fi shakkarta fiye da kowa a cikin y’an uwanta, don da wuya ta kulata amma duk ranar da ta bari ta kaita bango ranar Zainab d’in marinta take. Itace Yarsu ta biyu amma ta fi shakkarta fiye da Majeeda Babbar Yayarsu. Huci kawai take tana jin takaicin Ayra na sake katantawa da zuciyarta. Bak’in cikinta d’aya yarda za su fara aurar da d’iyoyin cikinsu Ayran na zaune a gida kuma ba wai rasa mazajen auren ta yi ba, tun bayan da ta fuskanci kyanta da jikinta ya na janyo hankalin maza gareta tun kafin ta gama Secondary school sai ta k’irk’irarwa kanta sanya dogon zumbula zumbulan hijabs kuma bak’ak’e wuluk da su. Ta bi kuma fuskarta da nik’ab ta k’unshe harta da hannunta sai ta sanya masa hand gloves da k’afafunta idan ka ganta sai ka zata d’aya daga cikin y’an k’ungiyar Shi’a ce. 


Ajiyar zuciyar da ta ja mai k’arfin gaske ya dawo da hankalinsu kanta. Ta d’ago fuskarta a had’e sosai kafin ta ce “Ammaty da laifinki kema, ya kamata ki nunawa Ayra ke kike iko da ita kuma kin isa ki zartar da hukuncin da ya wajaba ta bi shi da son ranta ko babu umarni ne Allah ya bata, kina da damar da zaki aurar da ita ga duk wanda kika so.” “A aurar da ita ba da amincewarta ba ta kashe kanta kenan ko?” Babbar yarsu Majeeda da ta fi su sanyin hali kusan duk ita ta d’auko halayen Amma ta fad’a idanunta cikin na zainab k’anwarta mai bi mata. 

Cikin takaici Zainab ta saki murmushi kafin ta ce “K’aryar banza ce ba zata kashe kanta ba wallahi kawai don ta saka mu k’i mata auren ne take wannan furucin, kuma raina mu ta yi don taga Amman bata da wani tsayayyen namiji da zai jajirce a kanta, ina ma Kawu Saddi zai dawo da naga uban da zai hana shi aura mata duk wanda ya yi niyya.” Amma kallon Zainab kawai take kafin ta girgiza kai “Tsaf zata aikata kisan kanta, kamar ba ki san kafiya da taurin zuciya irin na Ayra ba, da wannan tunanin fa ta tashi a zuciyarta, K’iyayyar maza a ranta take tun bayan da mahaifinku ya d’arsa mata hakan a ranta, ku cigaba da yi mata addu’a dai Allah ya kawar da wancan lamarin a zuciyarta ya sanya mata nutsuwa da tunanin cewa mazan ba duka suka taru suka zama d’aya ba, Allah ya mata jagora ya sa naga auran Ayra kafin kushewata.” 



Ayra kuwa tana shiga d’akin cikin b’acin rai ta tub’e suturun jikinta daga ita sai underwear ta shige toilet ta saba a yanayi irin wannan sai ta sakar wa kanta ruwa take samun sukuni. Gaba d’aya ta ware shower d’in a kanta tana burin zuciyarta ta sassauta daga yanayin b’acin ran da take ciki, amma ina kamar ana sake angizo mata b’acin ran, hotunan lamarin suna sake mama ye ganinta tamkar yanzu abubuwan suke faruwa ta runtse idanunta ta shiga dukan bango da dukkan k’arfinta kai kace zata ruguza duka tiles d’in toilet d’in ko zafin hannunta bata ji, hawaye kuwa zuba yake sosai a idonta. Ta tsaneshi ta tsani mahaifinta tsana mafi muni, bata jin har ya koma ga ubangiji zata yafe masa tarin laifukansa, bata ji ko mutuwa ya yi zata d’aga hannu ta rok’a masa gafarar Ubangiji. Tsawon lokaci tana cikin wannan yanayin kafin ta fito daga cikin tub d’in sanye da rigar wanka bata damu da tsiyayar ruwa da gashinta yake yi ba, ga wani irin kakkarwa da jikinta yake saboda ruwan sanyi ta sakarwa kanta duk da kuwa muku mukun sanyin da ake. Ba abinda ta yiwa jikinta illa towel da ta saka ta nad’e gashin kanta haka ta shige cikin blanket ta k’udundune kanta tana rawar d’ari sosai zazzafan zazzab’i ya rufeta ban da Amma ta hanata da tuni ta maka wancan Uban nasu a kotu.. tunanin da take kenan tana cizon leb’en bakinta da har suke fitar da jini Saboda datsesu da take yi. 


Kamar Amma ta san za’a yi haka ta biyo bayanta ita da Dijah da Majeedah. Suka ci sa’a k’ofar d’akin a bud’e take bata rufeta ba hakan yasa suka shiga kansu tsaye, da sauri Amma ta k’arasa gadon don daga inda suke suna juyo sautin had’uwar hak’oranta da suke bayyana alamar halin da take ciki. Amma na k’ok’arin yaye bargon Ayra na ja tana sake k’udundune jikinta murya a shak’e alamar kukanta ya tsananta take cewa “Barni na mutu Ammaty, tunda ba kwa son rayuwata, wallahi da na yi aure na zauna k’ark’ashin wani namijin gwara na mutu tun yanzu zuciyata suya take da zafi daga zancen auren ma ina ga an yi auren na tabbata idan ban kashe kaina ba zuciyata kuwa zata buga da kanta na mutu ku huta.” 


Cikin azama Amma ta jata jikinta ta rungume ta tausayi sosai take bata kuma laifinta ne da bata wayar mata da kai tun tana k’arama ba ta bari abin ya girmama a zuciyarta bata sanar mata Mazan ba halinsu d’aya ba kowa da halinsa, yanzu y’an uwanta ba gashi suna zaune da mazajensu lafiya ba cikin so da k’aunar juna, tun a lokaci bukukuwansu Ayran ta sha fad’ar ba zata tab’a aure ba, kuma ko mazajen nasu bata wa magana a zaton Amma duk wasa take bata san lamarin ya yi tasiri a zuciyar Ayra ba ta yarda ta dunk’ule maza waje d’aya ta lak’kaba musu halaye guda. “Kunna room heater Dija jikinta da zazzab’i sosai. Ki kuma kira min y’an uwanki na sake kafa musu sharad’in da duk wanda ya k’etare sai dai ya nemi wata uwar ba ni ba, ba zaku hallaka min yarinya ba tunda ba a kanku take zaune ba, ba kuma ta tab’a jawo min abin magana ba.” Amma ta fad’a cikin b’acin rai zuciyarta cike da tausayin Ayran. Da sauri ta ja Hand dryer tana busar mata da gashin kanta kafin ta shafa mata mai a sassan jikinta ta zura mata doguwar Riga mai nauyi sannan ta saka mata rigar sanyi shayi mai zafi ta saka Dija da suke tsaye jigum jigum ta had’o mata haka ta tilasta mata ta sha duk da tana turjewa sai da ta gama Amman ta hau murza mata k’afa sannan ta kalli sauran yaranta da suke tsaye musamman Zainab da ta fisu uzzira wa Ayran akan aure “Kada wanda ya sake mata maganar aure bana so, tunda ba a kanku take zaune ba, duk cikinku ba wanda ya fuskanci irin matsalolin mahaifinku fiye da ita a rayuwa ta taso da abin a ranta don haka tilastawarku ba zai sa ta mance da wancan k’addarar ba har ta yi aure ku barta haka nan idan Allah ya nufa zata yi aure zata yi idan bai nufa ba ku k’addara hakan Allah ya rubuta mata ba kuma wanda ya isa ya canja k’addarar bawa. Ba y’ay’a za ku aurar ba ko

Jikoki ku aurar shi Aure lokaci ne ko bayan raina kuma ban amince muku ku tialsta mata ba doka ce na saka musamman ke Zainab na fad’a na sake fad’a.” 

Tsit d’akin su kayi, ita kuwa Ayra farin ciki ne ya kamata duk

Wani nauyi da zuciyarta ta yi tuni ta yi k’asa a yau Kam ta tabbata Ammaty ta tace tana kuma gudun b’acin ranta. Ji ta yi kamar ta tashi ta taka rawa ta dinga kallon Zainab tana dariya k’asa-k’asa kafin ta ja bargo ta kwanta bayan ta sha maganin saukar da zazzab’i ta lumshe idonta barci mai dad’i yana d’aukarta. Amma ta tisa k’eyarsu a gaba suka fice. Ko a falo jajanta lamarin suka dinga yi Amma ta sake zabga uban tagumi tana duban yaran nata ‘daya a zuciyarta tana godewa Allah da ya raya mata har suka zama wani abu a duniya kamar ba su bane a lokutan baya ta dinga wahala da su, abubuwa da dama suka dinga rincab’e mata. Da sauri ta runtse idanunta ba ta son tuna wancan bak’ar rayuwar don muninta ya girgimama. Dijah ce ta fara kawar da tunanin ta hanyar cewa “Mu mata addu’a Amma, ina tunanin lamarin Ayra sai addu’a Khairan In sha Allah ubangiji zai kawo wani da duk k’iyayyarta da aure sai ta aureshi in dai mijinta ne.” 


Gaba ‘d’aya suka jinjina kai Amman ta fara korarsu ta hanyar cewa sai su tashi su tafi gidajensu tunda sun birkita mata y’a “Don sanda kuka sake zuwa kuma harzik’a min auta wallahi zaku sani.” Murmushi suke kawai suna mik’ewa ‘daya bayan ‘daya don dama yammaci ya kawo kai.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol