Free chapter · Read without an account

Seven

by A'isha kwalam Hassan · TSINTUWA



*Ta_kwalam is a home for jewelry, your best jewelry plug and introducing my Bridal accessories rent! For me a wedding is a one day celebration, for you to buy lots of costly stuff and after the wedding sun tashi a aiki! A saukake na kawo muku inda zakiyi renting kayan amare kuyi kyau, a kudi kalilan ki kece raini kawata, sannan ki Gama ki dawo dashi. You don't need to buy much. I'm a DM away!*



Ya kalle ni ya kalla Inna, ya dubi Aliya Dake taunar chewing gum ko inda yake Bata kalla ba, ya miko hannu ya Kama nawa yace cikin muryar lalalshi


" Waye ya dake ki?"


Ya San ba Inna bace ba, saboda tsoron shi da Kuma son da take min ba zai barta ta Dake ni ba ko da tana gigin hauka ne kuwa. Na kalla Inna da ta gyada min Kai Wai na fada masa aikuwa na nuna Aliya da index finger di na, Bai ko tambaye ta ko ni abinda ya faru ba Yana zuwa ya sakar Mata wani wawan mari Wanda ya dauke Jin ta da ganin ta na Dan lokaci, ko kafin ma ta dawo daidai tuni ya hankada ta ta Fadi ta buga Kan ta, wani irin Kara ta saki me firgitarwa, ko a jikin shi yayinda na tsorata na kanainaye Inna ta jiki na har rawa yake, yasa kafar shi ya Fara taka ta, tana ta ihu Amma Bai ko damu ba. Ganin ta dai na motsi shi Kuma Bai daina dukan ba yasa na saki Inna naje na rungume shi ta baya Ina fadin


" Dan Allah Baba karka kashe ta!"


Cak se ya tsaya ya juyo hade kallo na yace


" Ki dai na kuka na daina"


Muka shige daki muka bar shi nan tsaye da ita Yana kokarin kwara Mata ruwa, ya kwara Mata ta Mike a firgece kamar wata zararriya. In takaice Miki dai a ranar Baba a cell ya kwana, kinsan bariki ko? Kinsan abar banza ce se da yayi sati biyu sannan ya fito, gashi mu bamu San ka wanne cell bane ba balle mu je, mu ba wani muke kulawa a unguwa ba balle a taimake mu, a Haka suka sallamo shi ya dawo wanda kamar fitowar shi ake jira se ciwo, ya Fara wata irin jinya me ban al'ajabi a lokacin shekaru na Sha daya Ina js2 Hidaya. Innar dai ita ta zauna ta dinga kula dashi. Ko fitsari Bai iya zuwa yayi da Kan shi se de a kwance. Kullum idan na zauna se nace ma Inna mu je asibiti Amma se Baba ya hana, a Haka dai wata rana wajen watanni biyu se ya Fara samun sauki, jiki ya Fara sauki Muka Fara Jin Dadi. Dukda na Sha Jin Inna na adduar mutuwar Baba Amma da ya kwanta kullum addua take ya tashi. A Haka dai yayi sati ya Mike jiki nata sauki Ina ta zuwa makaranta Abu na. Wata ranar lahadi wadda Zan iya cewa wannan ita ce ranar da rayuwa ta ta canja Baki daya. Na tafi islamiyya da wurwuri, saboda ranar mune da shara ni da kawata Labiba, Muka share ajin mukai shimfida sannan na zauna can gefe Ina tilawar inda zaa karba. Wajen Sha biyu aka taso mu daga makaranta, Ina ta sauri naje gida saboda Inna tace min Dambu zata Yi, ni Kuma a rayuwa ta Ina son Dambu kamar yadda Baba yake son Dambu. Na karasa gidan na samu a bude na shiga da sallama Baki na, na samu Inna ta zaune gaban murhu da dukkan abubuwan yin Dambu, na gaishe da ita Amma Bata amsa ba tace min


" Uwata Baki ga baban ki a titi ba?"


Na girgiza Kai nace


" A'a! Ya fita kenan?"


Ta danyi tsaki tace


" Aikuwa dai ya fita fa tun dazun zai siyo min gyada da tuni na sauke abincin!"


Bance komai ba na wuce daki, Ina cikin cire Kaya naji ihun Inna daga tsakar gida, wani irin tsoro naji lokaci guda ya shige ni, wani ihu ta Kara saki Wanda yasa nayi saurin fitowa ko dankwalin kayan ba Kai ga daurawa ba a Kai na. A zube na gan ta, nayi Kan ta ba tare da na lura da mutanem Dake tsaye ba


" Inna me ya faru?"


Ta Kara sakin kuka tana fadin


"Baban ki ya rasu!"


A take Kai na yayi wani irin sarawa, ya rasu fa? Na ayyana, na karaso na kalla wani kwali da yake a aje na dubi Inna ta Dake tsugunne a gurin nace


" Kwalin menene?"


Tace


" Baban ki ne a ciki! Mota ta buge shi se kankaro shi akai a titi!"


Shi fa Mata da miji se de Allah, duk yadda take adduar Baba ya mutu saboda azabar da take karba hannun shi kalla Wai yau ita ke rusa wannan kukan, rayuwa kenan! Mun shiga tashin hankali Wanda ba Zan iya fada Miki makamancin shi ba, gwara ni dukda akwai wayo Amma still ni din yarinya ce, Inna ta ta Zama abin tausayi, idan ka kalle ta kamar zakai Mata kuka. Mutane da banyi tunani ba sun zo anyi jana'iza aka aika can Deba a fadawa 'yan uwan shi Suma sun zo Amma washegari suka Fara balain se an raba gado tunda bashi da da namiji Kuma iyayen shi ba da Rai. Ni nasan wannan gidan da muke ciki shi suke yiwa! Ana kokarin raba gadon bayan kwana uku da daddare nace


" Inna idan an kore mu Ina zamu je?"


Ta goge idon ta da gefen zanin ta tace


" Ban sani ba Uwata, bansan inda zamu je ba!"


Na saki hannun ta Ina karewa gidan kallo nace


" To Inna Baki da Inna ne? Ina ne gidan ku?"


Ta Kara sakin kuka seda ta Gama sannan tace


" Bari na Baki labari kinji, Ina da Inna Amma Ina kamar ki Inna ta ta rasu, ni kadai ta Haifa na taso a hannun matar uba, na Sha wahala sosae Uwata, mahaifi na ko a jikin shi, inaga a yaran shi mantawa yake da ya haife ni. A Haka shekarun aure yazo kowa Yana da saurayi ban da ni saboda a garin ma ba lallai mutane sun San da ni ba, kullum Ina cikin aiki kowanne aiki ni nake Yi. Bayan wannan na Sha Gori bani da saurayi karshe Ina shekara Sha biyar kamar mujiya Haka nake saboda duk garin mu Babu wadda ta taba kaiwa wannan shekarun ba tare da aure ba. A shekara ta Sha shida Baba na yace ya gaji da bani abinci Wai zai hada ni da wani alhaji, mutumin lokacin matan shi hudu zai aure ni ta hudu Wai ya saki daya, a wannan lokacin naki to mahaifin ki se yazo mun hadu naje kasuwa Yara na ta bi na suna tsokana ta nayi kwantai, ni mujiya ce me bakin jini. A nan mahaifin ki yace zai aure ni Amma mahaifi na yaki ya tsaya akan lallai se wannan mutumin wannan ne dalilin da yasa na gudu Wanda shi ne kuskure na farko da nayi a rayuwa ta uwata! Muka zo yamaltu deba Amma shi ma dangin shi se suka ki amincewa, karshe Muka zo nan akai Mana aure na tare, tun daga nan Babu Wanda ya Kara bi ta Kai na, se ni ce na taba zuwa gida, korar da Baba na yayi min ban Kara marmarin komawa ba Uwata! Yanzun was nake dashi daga ke se baban ki, dangin shi ma ba so nasuke ba balle su yadda su bamu gida"


A kankanuwar shekaru na nayi ta tunanin yadda zanyi, Ina zamu zauna Dan dangin Baba na kwace gidan zasuyi, washegari ita ce ranar da komai ya lalace! Kin tuna Aliya? Wannan karuwar Baban ko? To ita tazo wajen dangin shi da Yan unguwa ta fada musu ai Baba na dauke da ciwon kanjamau wato HIV cuta me karya garkuwar jiki! Kinsan a lokacin ba a waye ba, baa San ma ways of transmission ba kawai dai a Haka ake tafiya a jahilce. A ranar sukai Mana korar Kare daga gidan, ko hijabi Babu jiki na Haka muka fita, ko kafin mu fita sun riga da sun Fara kone gidan, a Haka muka samu ni da Inna ta muka fita, mukai ta baya wasu suka biyo mu, a lokacin Inna ba wata lafiya take da ita ba, ga rasuwar miji a Haka mukai ta gudu, can takalmi na ya cire na tsaya tare da tsugunnawa Ina wani irin numfashi nace


" Inna, innaaa takalma na"


Ta juyo tare da janyo ni tace


" Uwata bar takalman muje Zan siya Miki wani"


Ina tari sosae Haka Muka cigaba da gudu tana fada min mun kusa karasawa titi, anan na taka kusa, wani radadi ya ratsa Kai na, na sake sakin hannun ta nace


" Inna wayyo kafata"


Ta juyo ta tsugunna tare da rike kafar tawa tace


" Bari na cire Miki"


Bata jira abinda zance ba ta zare ta da karfin gaske, na saki wani gigitarciyar Kara da razana ta, jini ya Fara zuba alamar ta shiga deep. A Haka mukai ta gudu har zuwa wani lokacin, Ni na fara faduwa itama Dole ta tsaya, I was panting iska nake nema, saboda gudun da nayi, itama gefe ta zauna ga duhun maghrib ya Fara shigowa, se tari take. Munfi minti na talatin kafin dukkan mu Muka dawo daidai, na rarrafa na dafa ta saboda kuka take tun karfin ta, nace


" Inna ta sannu, kiyi shiru kinji?"


Ta kalle ni nasan tana tunanin yadda zata yi Dani take! A Haka dai tayi shiru se Kuma na fara kalle kalle ko zansan inda muke na tabbatar min bar garin mu saboda munyi gudu ba na Wasa ba, tabbas na yadda da reflex action saboda kowanne organ na jiki na seda ya amsa! A hankali Muka cigaba da tafiya har Muka Isa wani kango I'm sure lokacin Isha ta Jima da wucewa, na gaji Tiki's ga yunwa da kishi ruwa da nake ji, makogaro na ya bushe ruwa kawai nake bukata, Ina zuwa na hango famfo naje na Tara Baki na nasha na koshi sannan na samu wata jarka na durawa Inna a ciki na Kai Mata na samu tana ta tari, se da ya lafa sannan ta karba ta Sha na cire zanin jiki na dake akwai dogon wando a ciki na shimfida nace


" Inna kwanta ki huta!"


Saboda jikin ta wani irin rawa yake, Haka nan dai ta kwanta ni Kuma na koma can gefe Ina rarraba idanu. Ban taba ganin dare me tsawon wannan ba. Nayi bacci Amma sauro da Kuma tarin Inna na farkar dani, washegari na fita Dan samo Mata abinda zata ci, anan na fahimci nayi nisa sosae da garin mu. Can wajen me kosai naje na samu lokacin take fitowa, sede na karasa na tarar Ashe Masa ce, na tsugunna gefen pan din nata nace Mata


" Dan Allah na dinga Miki shara da aike ki bani Masa biyu na kaiwa mama ta?"


Ta dubeni da kyau dattijuwa ce, tace


" Daga Ina kike?"


Na fada Mata sunan garin, ta tambaye ni Inna ta na fada Mata se ta kulla min wainar tace na Kai Mata na dawo, har da kuka na saboda murna, naje na Kai Mata na samu zazzabi me zafi ya rufe ta, na zauna na Bata tana tambaya ta yadda na samu a takaice na fada Mata na koma gurin Baba laure, a hankali muka Saba da ita Ina Mata aiki Kuma tana bani Masa in return, ke Hidaya na Sha wahalar da bazan iya kwatanta Miki ba ko kadan


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol