Free chapter · Read without an account

Page 9

by Ayusher Muhd · MUNƊO (Mai Hakuri)

*MUNƊO*

(MAI HAKURI)


Na

Ayusher Muhd🤸🏻‍♂️

Da Zee Yabour


*TEAM ƳAN TAGWAYE NOVEL*✍️


009


 Araab tunda yaga ta zauna ya tada mota ba tare da yace mata komai ba, ita kuma ganin haka yasa ta saki murmushin jin daɗi, ta sake gyara zama tare da maida kanta saitinsa tana kallanshi. Wata irin kaunarsa ce ke sake ratsa zuciyarta, kallan bakinsa tai yaushe zata samu damar sumbatar wannan bakin mai ɗauke da wani irin kyau? Ta maida idanunta kan kirjinsa idanu ta ɗan lumshe tana hangota kwance a kirjinsa yana shafa saman gashinta, bata san sanda murmushi ya bayyana a fuskarta ba cikin salo da rangwaɗa tace "Yayana dan Allah ka sakko daga hawan dakai ka zo muje mu sanar dasu Abba kaunar da mukewa junan mu, su kansu sunasan auran nan jiya tsautsayi ne yasasu yin magnar nan."

 Bai tankata ba sai ma lime ɗinsa da ya matsa a baki yana ƙoƙarin ajiyewa takai hannu da sauri, bai kalleta ba sai hannunsa daya maida kan sityarin motar ya cigaba da tuki, cike da shagwaɓa tace "Allah zanyi kuka."

Hannu yakai ya ɗan kara sautin radio ɗin dake cikin motar hakan yasata kallansa zuciyarta na sake tafasa ita kam ya zatai ko haushi ma bataji in yana wulakantata tsabar kaunar da takemai.

 Ta sake kwantar dakai tace "Yaya in an tashi maganar aure dan Allah kar kaja da nisa, na kusa gama school so nake daga na gama ayi, kaji?"

Yanzun ma bashi da niyyar tanka ta takuma sani, ajiyar zuciya tai ta dauki wayarta tace "Bari na kira Ummy......"

Waigowa yai ya kalleta ta cikin glasses ɗin dake fuskarsa, sannan ya mika mata hannu, tace "Mene?"

Kansa na titi ya sake mika mata hannun, ƙoƙarin ɗaura mai hannunta take yai saurin amsar wayarta yasa a kusa dashi sannan ya maida hannun kan sityari. Ƙasan lebenta ta ɗan ciza sai a lokacin idanunta suka kai kan titi tace "Yaya ya naga munyi hanyar gidan mu? Can zamu?"

Yanzun ma kamar bazai yi magana ba sai taji yace "I thought so kike mu je a matsayin Romeo da Juliet?"

Ido ta ɗan zaro kaɗan tace "Dagaske?" Nan ta ɗan yi tafi tace "Yes! Yaya please muje a matsayin in ba'a barmu tare ba bazamu iya rayuwa ba."

Bai ko kalli inda take ba itakam sai murmushin jin daɗi takeyi ai ko mai zai faru sai dai ya faru amma ita kam shi kaɗai zata iya aura dan akanshi ba abinda bazatai ba.

Bai tsaya a ko ina ba sai a kofar gidansu, cikin zumuɗi ta fito ta zagayo inda yake ta tsaya tana gyara mayafin kanta. Buɗe kofar yai ya zuro kafafunsa yace "Muje?"

Kai ta jinjina sannan ta buɗe baya ta ɗakko jakar da Ummy ta bata, iska ta furzar tana kallanshi tace "Yaya I just can't belong this."

Ga mamakinta gani tai ya zare glass ya ajiye a cikin mota sannan ya kule ya nuna mata gaba yace "Bismillah."

Cikin sauri tai gaba bakinta duk ya kasa rufuwa. Shi kuma a waje ya tsaya yana jiran ta sanar da zuwansa.

Tana shiga ta tarar da Mumy mahaifiyarta tana ƙoƙarin haɗa kayan breakfast akan babban tire, jin sallamarta yasa Mumy tsayawa ta zubawa ƙofar ido kafin tace "Meenal mantuwa kikai?"

Da sauri ta karaso ta rungumeta tace "Mumy tare muke da Ya Araab yazo ne ya sakewa Dad magana." Ajiye cup ɗin hannunta tai tace "Meenal kedai sam bansan ina ajinki yake ba akan yaran nan na tabbatar kece kika rokeshi yazo."

Ganin Mumy zata fara mita yasata saurin shiga falo Dadynta na zaune yana karanta jarida ta shiga, ya ɗago bayan ya amsa sallamarta yace "Uwata ba makaranta akace kin tafi ba?" 

Ta karaso tace "Yaa Araab ne ya dawo akan magana ta."

Nan danan fuskarsa ta ɗaure yace "Yaran da sam baya ganin mutuncin mu jiya ina mai magana yaran nan a cikin mutane ya disgani wai na rike 'ƴata shima bayaso? Sannan ya dawo yau yace min me?"

Nan danan ta shagwabe fuska ta ƙarasa ta zauna kusa da kafafunsa tace "Dady dan Allah kai hakuri kafi kowa sanin yanda nakesan Ya Araab, Allah in na rasashi bazan iya auran kowa ba."

Kallanta yai a fusace, hawaye ya gani a saman idanunta wanda ya hanashi iya yi mata faɗan da ya kwaso daga zuciyarsa, saman goshinsa ya shafa sannan ya mike ya rufe jaridar yace "Kice ya shigo."

Da gudu ta mike tai waje, Mumy ta ƙaraso ta ajiye kayan abincin tace "Abban Meenal bansan ya zamuyi da yarinyar nan ba."

 Ajiyar zuciya yai yace "Mu cigaba da mata addu'a ni kawai hankalina ne bai kwanta da yaran nan ba gashi ya raina mu baya wani darajamu."

Ta ɗan mike tace "Bari na baku guri....."

Sallama yai ya shigo ya zauna tare da lankwashe kafa ya gaishe da shi.

Fuskarsa babu wargi shima Dady fuskarsa babu wargin ya amsa, kallan Meenal yai dake zaune a gefe yace "Da gaske zuwa kai ka bada hakuri a cigaba da maganar auranku ko kuwa?"

Araab ya ɗan kalli Meenal sannan ya kalleshi yace "Kawu zuwa nai ku amshi laifinku sannan kuba Ummy hakuri akan abinda ya faru ku kuma janye kalamanku na kiranmu ƴaƴan mace. Dan ba kalmar da Ummy tafi tsana a duniya irin kalmar nan."

A fusace ya mike har wayarsa dake kan cinyarsa ta fad'i yace "What?"

Araab yana kallanshi hankali a kwance yace "Tunda take ta taɓa zuwa neman taimako gurinku? Ko kuwa ku kun taɓa tausayawa rayuwarta kun taimaka mana?"

Huci Dady ya shiga yi cikin matukar zafin rai ya nunashi da yatsa yace "Ni kake faɗawa haka? Nauyin ku akan mu yake? ko kuwa hakkinku ne akan mu? Munyi iya abinda zamu iya dukanmu hidimomin gidan mu sun ishemu."

Kai ya jinjina yace "Exactly! Babu nauyinmu akanku akan me kuke jin haushinta?"

Meenal kawai hawaye take ta matso kusa da Araab tace "Yaya please kayi shiru."

Mikewa yai yace "Kawu sannan wacce kuke da hakki akan kula da ita ka sanar da ita ta hakura da abinda ke ranta bazan iya haɗa jini da wanda basa kaunar mahaifiyata ba."

Yana kaiwa nan ya nufi ƙofa ya fita, Kawu huci kawai yake ya makawa Meenal kallo yace "Wallahi in kika sake min zancen yaran can sai kin fuskanci ɓacin ran da baki taɓa gani ba."


Araab Hassan kam mota ya shiga a fusace ya fizgeta ya bar unguwar, sai da yai tafiya mai nisa sannan yai parking ya ɗan kwantar da kansa saman sityarin motar yana sauke ajiyar zuciya, hawayen Ummy sanda take rokarsu Kawu akan su biya mai kuɗin makaranta sukace basuda kuɗi kawai ya tuno, sai gashi a ranar sun dawo gida aka sanar da Ummy wai birthday din Shattima Yayan Meenal akai. Yawun bakinsa ya haɗiya yasa hakori a kasan leb'ensa ya cije da karfi yanaji zuciyarsa na wani irin zafi.

******


 Salau kam sai daf da magriba ya iso garin Kano, kai tsaye unguwar su Jauro ya nufa yunwa duk ta bi ta addabeshi anan kan hanya ya sai brodi ya na tafe yana ci yana korawa da ruwa, ana kiran sallar magriba ya isa layin sai dai sam ya kasa gane gidan, sakamakon gyare-gyaren da akai a unguwar. Kusa da wasu samari dake tsaye suna magana ya nufa hannunsa ɗauke da burodinsa da ledar pure water, ya je gunsu yace "Bayin Allah dan Allah ko kunsan gidan Jauro? Jauro namu na Jiji?"

Kallansa sukai galala ɗaya yace "Ni gaba ɗaya ban gane hausar ba nadaiji kace Jauro."

Ya tsotse sauran ruwan ledar ya yar da ita yace "Jauro yanada yaro Balal ko Bakasan shi ba? Aradun Allah dai na manta sunan amma sunan matarsa Salame."

Dariya suka kwashe dashi sukace "Malam sai dai ka koma ruga ni duk abinda kake faɗa bangane ba." Kallan layin yai yace, 

"Jauro fa? Bafillatani dake zaune a unguwar nan."

Dariya kawai sukeyi wani ne ya fito daga cikin gidan da suke tsaye yace "Jauro kake nema?"

Da sauri Salau ya ƙarasa wajanshi yace "Jauro kuwa nake nufi." Saurayin yace "Ga gidan can na biyar daga ɓangaren hagu."

 "Biyar dai na yatsu ko?" Ya ƙarasa faɗa yana buɗe duka yatsun, wani ya kalleshi yace "Ɗan filo wannan dai wayan zagi ne danasan gidansu Bilal kake nema Allah da ba'a nuna ma ba."

Shi dai Salau yai gaba abinsa yana cewa ai yasan nan ne unguwar za'a tsaya raina masa hankali. Ƙofar gidan ya nufa yai shiru yana tunani yanda zaiyi ya shiga ciki, dan Salame har yanzu bai manta masifarta da rashin mutuncin taba, wanda hakan yasa ko yazo birni in Maccido ya aikoshi gun Jauro iya kacinsa waje baya shiga. Yana nan tsaye mota tazo tai parking, kurawa motar ido yai yana mamakin nawa ƴan birni suke kashewa gun siyan mota haka? Ya saki baki galala yana kallo yaga Raheena ta fito daga cikin motar sanye da wando da riga matsaysiya, ta yafa mayafi ɗan ƙarami, shikam kallanta kawai yake har sai data kusa shiga ciki sannan yace "Rahine?" Kallansa tai ganin saurayin bai tafi ba yasa taki kula Salau ta wuce ciki kamar bata ganshi ba.

Motar saurayin ne ta wuce nan kawai yasawa ransa gwara ya shiga ciki kar dare yai masa a wajan. Kamar daga sama yaji ance "Salau?"

Waigowa yai cikin hanzari ganin Jauro yasa ya buɗe hakoransa wanda rashin brush na kauye yasa duk suka koma yalaye. Daɗi ne duk ya rufesu nan Jauro yace su shiga daga cikin gidan. Sam Jauro baisan ma Raheena ta dawo ba Salame ta leko suka gaisa da Salau yace "Akwai ahinci ki kawo mai?" Baki ta tab'e tace "Bansan zaizo ba na raba abinci har an cinye." Jauro ya sani sarai wulakancin Salame ne sai dai baisan ya nuna cikin mutane.

Bayan sun sake gaisawa Jauro yace "Inasu Danejo?"

"Suna nan lafiya Maccido ne bayajin daɗi shiyasa ma na taso nazo wajanka." Idanu ya zaro cikin jimami yace, 

"Me ya sameshi?" Nan Salau ya kwashe abinda ya faru da sakon da aka bashi ya sanar masa. Yawun bakinsa ya had'iya yace, "Ni ne zanje? Sannan Danejo ce ta sanar maka da hakan?"

Yace "Eh yace mu taho tare da motar."

Nan danan zufa ya kwararowa Jauro shi kam bazai sake cin dukiyar da ba tashi ba, na gado ma har yanzu damunshi yake gashi Danejo ko tada zancen batayi sannan yanzu kuma ya sake cin wani? Balle ana zancen dukiyar Maccido wacce dukansu sun san kaso 70 na dukiyarsu nashi ne? Share gumi yai yace "Salau nikam bazan iya ba, sai dai in na ɗauko Maccido yazo da kanshi ya kula da dukiyarsa da ƴarsa....." Caraf sukaji ance. 

"Dukiya?"A tare suka juya suka kalli Salame wacce ta shigo har zaninta na neman hard'eta ta faɗi, duk jikinta amsawa yake saboda jin an ambaci dukiya tace "Dukiyar Maccido?"

Jauro ya haɗiyi yawun bakinsa yace "Salame magana da muke yi..." Ai bata ko kalleshi ba idanunta nakan Salau tace "Salau banda abinka ka riko burodi a hannu ba mahadi? Shi bread ai da abin haɗi ake cinsa, idan ba haka ba shaƙeƙa zai yi, kaga kafin ƴarka Raheena ta soya maka kwai sanar dani meke faruwa?" Ta karasa maganar tana kwallawar Raheena kira tana daga ciki ta amsa tace "Yi maza ki soyawa Salau kwai guda uku ki hado da shaye yunwa yakeji ya kwaso hanya." Cikin kukuni ta amsa da to.

Salau kam hankali a kwance ya sake yi mata bayanin komai, gaba ɗaya Salame ta rikice tace "Salau nikam dabobin Maccido sun kai nawa?" Ya kalli Jauro yace "Kawu kasan yawansu? Dan nikam aradun Allah ban taɓa kirgawa ba."

Salame ta sake gyara zama tace "Yanzu kana shan tea zaku tafi ko?"

"Da sai gobe naga yanzu dare yayi ko?"

Kai ta girgiza da sauri tace "Wani dare kuma ana zaune kalau? Sannan ya kuka tsara yanda zaku fito da dabobbin?" Salau yana kallanta yace "A bayan gari zamu jira sai dare yayi sai mu kwashe mu ɗauko su......" Jauro yai caraf yace, 

"Mu d'auko Maccido da ƴar tasa in suka zo nan sai amai magani."

Baki ta taɓe dan ta kula Jauro neman musu bakin ciki yake yi, ita kuwa wallahi ko saniya uku ce sai ta kwaso duk bakin cikinsa sai dai ya mutu. Da kanta ta mike ta shiga ciki tana zabgawa Raheena kira, a ɗaki ma ta taddata tana waya akan gado, ganinta yasa ta ɗan kashe tace "Au Umma ashe kince na soya kwai." Hannu ta mika mata tace. 

"Ɗan yi maza ki bani ɗari biyar." Baki ta turo ta jawo jakarta ta duba ba canji sai ƴan dubu ɗaya, kallanta Salame tai tace "Bani dubun mana."

"Allah Umma in na baki ba dawo min kike da canji ba." Hannu tasa ta kwata tace. 

"Kuma Allah ki ciro ragowar munada baki zamu siyo kayan abinci. Ki kuma taso yanzu ki soyo mai kwain." Tana kaiwa nan ta fito jikinta duk rawa yake. Falo ta shiga ta mikawa Jauro tace "Malam siyomai leman kwalba mai sanyi yasha duk ya gaji."

Baki Jauro ya saki matar da ko iyayenta ne sukazo bata siyo musu lemon kwalba shine yau dan tsira zata ce a siyowa Sallau? Amsa yai ya fita ai nan ta zauna tace "Rahi zata soyo kwan yanzu. Nace dabobbin bakasan ma yawansu ba tsabar yawa Sallau?"

Sallau yace "Eh amma dama can nashi guri daban ake kiwonsu." Ta ɗan haɗe hannaye tace 

"Amma a yanda nasan ku ta ina za'a kwashe dabobbi dayawa haka ba tare da kun sani ba? Bayan ku ba wani nauyin bacci gareku ba."

Shiru yai alamar tunanin kumafa haka ne.

"Me zai hana ai abin da safe? In an fito kiwo? Kaga dama sun bar turkensu mu kuma dama mu ajiye motar a inda za'a kaisu kiwon suna zuwa a sasu a ciki ko ya ka gani?" Dariya yai har da tafa hannu yace. 

"Aradun Allah wannan shine dai-dai."

Tana murmushi tace "To amma shi Maccidon naji ana amai magani anan me ya sameshi?" 

Sallau ya girgiza kai yace "Maciji ne ya cijeshi ko tafiya baya iya yi."

Nan da nan wani murmushi ya sake bayyana a fuskarta tace "Allah sarki gashi kuma daga kai sai Maccido ne kukasan inda muke a birni, dan Ardo ya hana kowa hulɗa damu tunda mun bar ruga." Sallau ya kalleta yace 

"Muma ba'asan muna zuwa ba ko Danejo sai yau tasan muna zuwa nan."

Ta jinjina kai tace "Allah sarki Munɗo itace wannan yarinyar ko?"

Kansa ya sadda ƙasa ya ɗaga kai alamar eh, tace "A matsayina na mahaifiyarta dole zan kula da ita zan adana mata dukiyarta har zuwa auranta, ka sanar da Danejo abinda nai a baya rashin sanin ciwon kai ne, amma yanzu dana girma a koda yaushe dana sani nake yi."

Kallanta yai yace "Ai Danejo har yanzu bata faɗawa kowa abinda ya faru ba, nima tsautsayi ne yasa na sani."

Raheena ce ta shigo da plate ta amsa ta ajiye mai a kusa da shi......



ƳAN TAGWAYE BIYAR 2023


ƘASAITATTUN LABARAI MASU DAƊI DA SANYA NISHAƊI, SABON SALO MAI ƊAUKE DA DARRUSA NA RAYUWA UWA UBA ƘASAITATTUN SOYAYYA MAI HUDA JIJIYA.

 

IYALINA (A'ILATY)🔥

RAFEEQ🔥

MUNƊO🔥

ZAMANIN MU AYAU🔥

FATHIYYA.🔥


DOMIN SIYAN GUDA BIYAR N1500.


DOMIN SIYAR ƊAYA N400.


Account Details 

2083371244

Zenith Bank

Aisha m salis


Ga MUTANEN MU NA NIGER 🇳🇪 

Tura ta Nita da sunan


Asma'u Buhari Aliyu

***


SAI KI/KA ISAR DA SHAIDAR BIYA TA ƊAYA DAGA CIKIN NUMBOBIN NAN.


***

***

***

***


#Munɗo Jiji

#Araab Hassan 

#Bilal BB

#Jauro Jiji

#Sallau Jiji

#One love 💕 




Zee Yabour

Da 

Ayusher Ce🤸🏻‍♂️

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol