Free chapter · Read without an account

Na sha biyu

by Maryam Abdul'aziz · ƘADDARATA CE A HAKA

*ƘADDARATA CE A HAKA*

 ©Maryam Abdulaziz_Maiƙosai(Matar Abdul)



P_12



Satin Nuriyya d’aya a asibiti a ka sallameta bayan matsawar da ta yi a kan lallai sai an sallametan.

 Tana zaune a d’aki ta yi tagumi da hannunta duka biyun. Munira ta shigo d’akin hannunta d’auke da d’an k’aramin kofi da ta had’owa Nuriyyan ruwan shayi.

 Ta k’arasa inda take zaune tana mai furta, “ Haba dan Allah wai Nuriyya me ya sa har yanzu ba za ki sanyawa zuciyarki salama ba ne ba, ki yi hak’uri in sha Allahu komai zai wuce tamkar bai tab’a faruwa ba.”

 Ta sauke hannayenta tana mai kallon Muniran da ta kafeta da idanuwa, kana ta ce, “ Na ji na yi hak’urin.”

Munira ta yi murmushi kafin ta furta, “ Yawwa ko kefa ‘yar albarka. Ungu maza ki shanye shi tas kin ji ki ba ni kofin.”

Ta ida fad’a tana mai mik’a mata kofin shayin. Ba ta mu sa mata ba , ta sanya hannu ta amsa tare da kaiwa bakinta.

 Sai da ta shanye tas kamar yadda Muniran ta ce da ita sannan ta dangware kofin kan ‘yar lokar dake jingi ne gefen gadon da ta ke kai.

 Munirata sake kallonta a karo na biyu kafin ta ce, “An yi zaman koto, kuma an sake d’aga k’aran, yanzu haka muna cuku-cukun samar da lauya kuma in sha Allahu za a dace, sai dai ina so ki shirya gobe muje wajen Baffa domin na san ya shiga damuwa jin abin da ke faruwa”

 Gyad’a matakai kawai ta yi, ba tare da ta bata amsa ba. Itama ba ta takura kanta a kan lallai sai ta ji amsa daga gareta ba.


Kamar yadda Munira ta ce, haka suka shirya washegari bayan sun yi sallama da su gwaggo suka nufi gidan gyaran halin dan ganawa da Baffan nata.

 Duk ya rame ya k’an jame sai ka ce ba Baffanta da ta sani ba, tuni zuciyarta ta sake karyewa.

  “ Kai ne haka Baffana? In sha Allahu duk wanda ya k’ulla wannan sharrin sai ya koma kansa, ka yi hak’uri Baffa” Ta ce da shi tana mai fashewa da kuka.

 Shi ma sai ya ji kawai ruwan hawaye na biyo kan kumatunsa, ya gaza dauriyar furta mata ko wacce iriyar kalma. Yana son jajanta mata a kana bin da ya samesu amma ya gaza, gaba d’aya kukanta ya raunata masa k’arfin zuciyarsa.

Suna haka, an rasa wanda zai rarrashi wani cikin kaf su ukun, a ka zo a ka mayar da Baffa domin lokacinsu ya cika.

Da kuka shab’e-shab’e majina na samun wajen shiga cikin bakinta suka kama hanyar gida.



  ****

Satin Nasir biyu da kwana uku suna zaune a falo gwaggo, Munira, Nuriyya, sai Inna. Ahmad ya yi musu sallama tare da shigowa falon bayan sun masa izini.

 Ya kalli yadda Nuriyya ta fad’a ta k’an jame dalilin damuwar da take cinta.

 “Dan Allah Inna ku dinga yi mata fad’a a kan ta rage damuwar nan, saboda babu abin da za ta haifar mata sai cuta, ji yadda ta rame ta k’anjame sai ka ce mai cutar k’anjamau ko k’yanda.”

 Gwaggwo ta yi murmushi kana ta ce, “ To ga ta nan dai kai ma ka fad’a sai ka yi mata fad’an naka ai ko ta ji naka.”

 Har ya bud’e baki da nufin yin wata maganar ta katse shi da fad’in, “ Ina ma ace yanzu muga su Nasir da Hamza sun shigo, wayyo dad’i ka she ni! “ Ta ida fad’a tana mai mik’ewa dan barin falon gami da kai hannayenta biyu saman ƙirjinta tamkar wata wacce ta rungume wani abun.


 Gaba d’aya suka bi ta da ido, tausayinta ya sake mamaye zuk’atansu.


Misalin wajen hud’u na yamma tana zaune kan sallaya tana mai addu’a tare da kai kukanta ga mahaliccinta Ummi da mahaifiyar Nusaiba suka shigo falon tare da yin sallama.


Ta shafa add’u’ar da take yi, ta nad’e sallayar ta isa gabansu tana mai mik’a gaisuwa.

 Duk da cewa d’akin da d’an duhu-duhu kasancewar duk an saki labulaye amma hakan bai hana bawa Ummi damar k’arewa Nuriyya kallo ba wanda ta ga duk ta motse kamar an cakumi burodi, duk ta yamushe kamar ya musasshen alayyahu.


 Sunaa had’a ido da Ummi ta kece da wani irin kuka, domin kallon fuskar Ummi sai taga tamkar fuskar Nasir take kalla.

Ummi ta shafo kan Nuriyya tare da furta, “ Kukan ne dai ‘yata, me ya sa kika kasa sakawa zuciyarki salama? Ki zama mai tawassali ki kasance mai kamun k’afa da sunayen ALLAH da shugaban Rahma Annabinmu Annabi Muhammad(S.A.W) sai ki ga Allah ya jib’anci al’amuranki ya tsaya miki ya kuma yi miki jagora a dukkan abin da kika saka a gaba. Su Hamza ai sun tafi kuma muna musu addu’ar samun nasara, a yanzu ita ce kawai ya kamace ki, sannan ki mayar da hankalinki a kan maganar Baffanki kin ji ko”

 Ba tare da ta ce da ita komai ba ta hau gyd’a mata kai alamar to. Haka Ummi ta shiga gaya mata kalamai masu kwantar da hankali, har su Gwaggo suka ratso falon suka zauna suna ma su gaisawa da juna.


***

“ Barista wallahil azeem ba gaskiya ba ne abin da ake tuhumar Baffana da shi, na rantse na san ko kad’an Baffa ba zai tab’a aikata abin da ake tuhumarsa da shi ba. Dan Allah ka taimaka mana ka amshi case d’in nan.” Cewar Nuriyya da take gurfa ne gaban wani lauya.

  “ Magana ta gaskiya babu wani abu da zan iya yi a kan case d’in nan, domin Magana ce a kan rai, kuma al’umma. An zaluncesu idan har na tsaya masa mene ne sunana? Mara imani da tausayi shi ne abin da mutane za su kalleni da shi su kuma rik’a jifana da kalmomin.” Cewar lauyan.

 Nuriyya ta share hawayenta da suke ta sirfa gudu kan kumatunta ta ce, “ Barista ka yarda da mu, sam ko kad’an ba shi da hannun a kan laifin nan , zarginsa kawai ake yi bai aikata ba sam wallahi.” 

 “ Na gama maganata tun farko, ba zan iya taimaka muku da komai ba.” Barista ya ce.


Munira dake tsaye ta sake furta nata rok’on da, “ Lauya ka dubi girman zatin Allah ka taimaka mana, kamar yadda Allah ya taimake ka har ka zama lauya.”

  “Ba zan iya yin komai ba” Ya sake fad’a.


Duk magiya da na ci da suke masa bai saka ya tausaya musu ba, haka ya ƙeƙashe k’asa ya bad’awa idonsa toka yaƙi amsar case d’in da suka kawo masa. Haka suka baro wajensa, tare da nufar wani wajen. Wunin ranar bi suka dinga yi kusufa-kusufa, lungu-lungu duk inda suka san za su sami lauya sai sun shiga sun kai musu tayinsu amma ba su sami wanda zai tsaya masu ba, haka suka dawo gida guiwa a salub’e, jiki babu wani cikakken kuzari.


Maiƙosai✍🏼

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol