Free chapter · Read without an account

Chapter 10

by Azizat Hamza · ASHRAF: beauty meets ugly

ASHRAF: Beauty meets Ugly

010

Top-Notch season 2

Duk abunda Ashraf yake so Ashraf zai samu. Irin rayuwar da Ashraf ya taso a ciki kenan. Sai dai wannan rayuwar bata yi tsawo ba.

Lokacin da aka haifi Ashraf ba ƙaramin farin ciki ne ya wanzu a familyn Alhaji Maikuɗi Abubakar ba. Shi da matarsa Sarah Aljabir suna rayuwa ne irin ta masu kuɗin 90's ɗin nan.

Babban gida, motoci, zuwa hutu ƙasashen waje a kowanni shekara.

Umura kuwa idan basu je dukkansu ba to dole ɗaya daga cikinsu zai je.

Su'ad ce ɗiyarsu ta fari. Babu abinda ta bari na kammanin mahaifiyarta. Shekara uku da haihuwan Su'ad Sarah ta haifi Zulfa. Ita kuma ta ɗau kamannin Babanta har baƙin shi. Shiyasa ma idan ka ga Su'ad da Zulfa tare ba zaka taɓa cewa 'yan gida ɗaya bane sai dai idan ka san cewa mahaifinsu Bahaushen Nigeria ne ita kuma mahaifiyarsu Balarabiyar Lebanon wacce zama da kuma aure ya maidata Bahaushiya.

Iyayen Sarah Aljabir sun zo Kano ne a farko farkon 1960's jim kaɗan bayan Nigeria ta samu 'yancin kai.

Mahaifinta Al-Jabir Khoury ya kafa kamfanin alawa. Kamfanin ya bunƙasa sosai dan a hankali ya dinga kawo 'yan'uwansa yana saka su cikin harkan.

Kwatsam watarana Allah ya masa rasuwa cikin baccinsa.

Sarah ita kaɗaice 'ya da zata ci gado dan yayarta mai suna Su'ad ta rasu tun tana ƙarama.

Ƙanin mahaifinta mai suna Mubarak Khoury ya hau kan gadonta ya cinye.

Ba a jima ba mahaifiyarta ta rasu.

Sarah ta wahala a hannun ƙanin mahaifinta kafin Allah yasa tayi aure ta rabu da shi.

Ba a jima da ta yi aure ba Uncle ɗinta ya rasu a hatsarin jirgi.

Iyalensa suka raba dukiyar aka manta da Sarah.

Kusan mijin Sarah shine ya zamo mata Uba da Uwa shiyasa take masa wani mahaukacin so.

Har yanzu akwai sauran tsirarun 'yanuwansu a Kano amma rashin zumunci ya sa kowa zamansa yake, idan ba wani biki ba ko wata hidima Sarah mantawa take da cewa tana da 'yan'uwa a Kano. Duk ƙoƙarin mijinta na ganin ya saisaita tsakaninsu abin ya ci tura. Igiyar zumuncin ya riga ya tsintsinke ne babu halin ɗaure shi.

Once in a long while tana zuwa ƙasar Lebanon. Amma kusan a ɓangaren Sarah za a iya cewa danginsu ya rushe, babu takamaimai inda zata kira kai tsaye da gida.

A ɓangaren Alhaji Maikuɗi shi ɗan dangi ne gaba da baya.

Sunansa Abubakar amma Maikuɗi ake kiransa kuma Maikuɗin ne aka san shi da shi har yau. Dan kuwa sunan Abubakar da yake amfani da shi a takarda ma sunan mahaifinsa ne saboda sunan mahaifinsa gare shi.

Mahaifinsa Alhaji Abubakar Wali babban ɗan kasuwa ne da yai ƙaurin suna a shekarun 40's har zuwa 70's. Ya rasu ya bar mata ɗaya da 'ya'ya takwas.

Maikuɗi shine babba sai Hadiza, Rabi'atu, Bashir, Halima, Yusuf, Sumayya da kuma Hindatu.

Mahaifiyarsu Hajiya Bilkisu da suke kira Hajja tana nan da ranta har yanzu. Alhaji Maikuɗi ya so ya kawota kusa da shi ta zauna amma sam ta ƙi, tace babu ita ba fita a gidan mijinta sai mutuwa.

A wajen biki Alhaji Maikuɗi ya haɗu da Sarah Aljabir. Kamar da wasa yace mata yana sonta ta kuma amince masa.

Wata bakwai da haɗuwarsu suka yi aure.

A ɓangaren Sarah Maikuɗi ya zo mata ne kaman knight in shining armour.

Tana cikin tsananin ƙunci da takurawa a wajen ƙanin mahaifinta.

Duk da banbancin asali da yare darajar mahaifin Alhaji Maikuɗi yasa ƙanin Mahaifin Sarah ya amince masa da aurenta.

Koma yanene dai auren nasu auren soyayya ne da aminci.

Ƙila a lokacin kyawun Sarah ne ya ɗau hankalin Alhaji Maikuɗi amma a zamantakewar aurensu nitsuwarta da haƙurinta ya ɗasa masa matsanancin sonta a zuciyarsa.

Shima ɗin kaman mahaifinsu bai da ra'ayin mata biyu dan haka koda abubuwa suka fara bunƙasa masa ko kaɗan bai bi shawaran abokai na ƙara aure ba.

Sai dai kuma maganar gaskiya idan ya fita ƙasar waje yin wani aiki yana ɗan taɓa neman mata wanda zasu rage masa kaɗaici.

Bai gane illar hakan ba sai da ya shaƙi ƙamshin mutuwa.

Yana bawa matarsa da 'ya'yansa kulawa na musamman. A lokacin da aka haifi Ashraf kullum yana maƙale da shi. Lokacin da yai wayo kuwa har office yana zuwa da shi.

Daga kan Ashraf Sarah bata sake haihuwa ba.

Da Saran da Maikuɗi duka ra'ayinsu ya zo ɗaya akan 'ya'ya uku sun ishesu.

Suna gwadawa Ashraf kulawa na fitan hankali. Ta inda abinda Ashraf ke so shi yake samu.

Kwatsam wata ranan Jummu'ah da safe Alhaji Maikuɗi da direbansa Malam Umar suka kama hanyar Kano saboda bikin ƙanwarsa Sumayya da za a yi.

A hanyar kuwa suka haɗu da mummunan hatsari.

Malam Umar a take ya rasu yayinda Alhaji Maikuɗi ya shiga coma na kusan kwana shaɗaya kafin ya farfaɗo.

Ya samu mummunan rauni a ƙashin bayansa. Tun daga Nigeria aka fara jinya kafin suka wuce Germany aka masa aiki, daga baya kuma aka mayar da shi Ingila a nan ya ƙarisa jinyarsa har Allah yasa ya warke, sai dai ƙafar tasa gaba ɗaya tayi condemn bata aiki.

Ga gurbin ƙafa nan amma basa iya tsinana masa komai.

Lokacin da aka yi masa aikin farko ma sai da yai kusan wata biyar yana kwance ko zama baya iya yi.

Jarrabawar rayuwa ke fito da ainihin halin mutum na haƙuri ko akasin haka.

Through all this matarsa Sarah ta zauna da shi. Duk wani jinya da ake ita ke ɗawainiya da jigila da shi.

Matar ƙwarai rufin asiri ce ga mutum. Akwai lokacin da 'yan'uwa suka gaza da kulawarsu amma ko sau ɗaya Sarah bata taɓa nuna gazawarta ba. Ita dai fatanta Allah ya bawa mijinta lafiya.

Lokacin da suke yawon jinya yaransu uku duka watsa su aka yi.

Su'ad ta zauna a wajen Kakarsu Hajja dama tana boarding school a Kano kuma ta saba da Hajjan sosai.

Zulfa ta zauna a hannun Alhaji Bashir a Kaduna.

Shi kuma Ashraf a hannun Hajiya Halima aka damƙa shi. Dama tana ji da shi ba kaɗan ba. Zamansa a hannun Hajiya Halima babu wani sauyi daga irin rayuwar daya taso ciki.

Yadda aka saba pamparing ɗinshi haka itama take mishi, kusan zaka iya cewa ma nata har yafi na Mom ɗinsa.

Akan haka ɗanta Salim da suke kusan sa'a ɗaya da Ashraf ya tsani Ashraf ɗin sosai. Har yau basa shiri.

Kamfanin Dad ya samu koma baya dayawa duk da ma dai ƙaninsa Bashir yana saka masa ido sosai. Amma mai abu shi yasan ya zai yi da abunsa.

Lokacin da Dad da Mom suka dawo Nigeria abubuwa suka fara sauyawa a hankali.

Zamansa a wheelchair bai hana shi komawa bakin aikinsa ba. Ya cigaba da jajircewa wajen ganin ya farfaɗo da kamfanin nasa da ke gab da rugujewa.

Da taimakon wani Bature da ya bawa riƙon ƙwaryar shugabancin kamfanin abubuwa suka fara dawowa daidai.

Ko sati biyu basu yi ba Dad yasa aka maido masa 'ya'yansa. Sannan yasa aka ɗauko masa yaran marigayi Direbansa ya ce zai ɗau nauyinsu har su girma.

Yadda yake ji da yaran Malam Umar ko 'ya'yan cikinsa albarka. Duk abinda zai yiwa 'ya'yan cikinsa to zai musu.

Ko kaɗan baya banbanta Ashraf da Umar duk da Umar ya bawa Ashraf shekara biyu.

Jinyar Dad ya ƙara kusanto zuciyarsa ga yawaita ibada.

Ko ma mi ya gani lokacin da suka yi hatsari to ya chanja masa tunaninsa har abada.

Ya karkatar da hankalinsa kan neman ilimin addini da kuma yawan ibada.

Da wannan matsayar ya sa baya yiwa 'ya'yansa da wasa, musamman Ashraf wanda dama an riga an sakalta shi.

Ranan daya fara dukan Ashraf shine rana na farko da alaƙar uba da ɗan ya fara sauyawa.

Ashraf ne suna buga game ɗin whot da Umar sai Umar ɗin ya winning ɗinsa.

Daga tashi sai Ashraf ya zage shi yace ya tashi ya bar masa waje ba zai sake wasa da ɗan driver ba. Ashe Dad ya turo kekensa wajen basu sani ba.

Yana jin abinda Ashraf ya faɗa ya daka masa tsawa.

Ya kira Ashraf gabansa yace ya Umar ya je ya kawo masa belt ɗinsa guda ɗaya.

Dukkansu basu yi tunanin cewa dukan Ashraf zai yi ba.

Da Umar ya kawo Dad ya riƙe hannun Ashraf ya juyar da bayansa ya fara shaɗa masa belt a baya yana faɗin "Umar ne ɗan driver? Umar ne ɗan driver? Ban ce maka Umar ɗana bane"

Ashraf ya dinga kuka yana kiran sunan Mom.

Sai da Dad ya masa bulala goma kafin ya bar shi.

Mom ta fito da gudu ta ɗauki ɗanta ta shiga da shi cikin gida. Ranan sai da suka yi faɗa da Dad akan dukan Ashraf da yayi.

Daga ranan kuma Dad ya koma duk laifin da Ashraf yayi sai ya dake shi.

Akwai lokacin da Ashraf ya gudu daga gida ya koma gidan Hajiya Halima saboda masifar Dad.

Dad da kansa ya je gidan yace a fito da Ashraf.

Abba ya fito masa da Ashraf sai kuka yake wai ba zai koma gidansu ba.

Da Hajiya Halima ta dawo ta ji abinda ya faru ta ɗau ƙafa taje ta samu yayanta akan ya bar mata Ashraf a wajenta.

Dad yace babu inda Ashraf zai je. Kai idan Ashraf ya gudu gidanta bata dawo masa da shi ba zai yi fushi da ita.

Daga lokacin duk wani sakalci da pampering ya ƙare ma Ashraf sai dai Mom tana yi a bayan idon Dad...



***

ASHRAF MAIKUƊI ABUBAKAR ya gani ɓaro-ɓaro a jikin takardar da ya karɓo yau da safe wanda ke bada shaidar zama supervisory manager na I T department ɗin kamfanin Dad.

Idan bai manta ba shine ya fara kawo cewa a ware ɓangaren Information Technology ya dawo ɓangarene mai zaman kansa saboda mahimmancin hakan a tafiyar da cigaban kamfani.

Wai sai gashi daga CEO an maida shi supervisory manager na iya gurin.

Ya tumurmusa takardar ya jefar da ita.

Ta tabbata Dad baya son shi.

How insulting a gabansa zai bawa Tahir CEO.

Tahir fa.

Shi da ace Umar ne ma abin sai ya zo masa da sanyi saboda koba komai Umar ya deserving matsayin saboda jajircewansa all this years. Amma Tahir. Tahir kura ne fa. So yake ya hanɗame komai shi kaɗai.

Saboda Tahir ne ma ya fasa komawa ƙasar waje.

Da farko ya gama made up mind ɗinsa akan ya gama yiwa Dad aiki. Zai koma America ya nemi band ɗinsu ya koma waƙa ko kuma ya nemi aiki a chan ya fara, afterall shi ɗin indigene ɗin England ne dan a nan aka haife shi.

But da Dad yace Tahir zai bawa CEO sai wani abu ya tsartu masa a zuciya.

Bai taɓa son Tahir ba. Kallo ɗaya ya masa ya gane cewa bashi da gaskiya.

Bai zo masa da mamaki ba lokacin daya je harkokinsa ya haɗu da Tahir da wata mace a hotel.

Ashe regular ne ma a hotel ɗin haɗuwarsa da Ashraf sai ya chanja wajen harkansa.

Nan ɗinma sai da Ashraf ya sake kama shi.

Dake gar ta san gar babu wanda ya buɗi baki yai wa ɗan'uwansa magana kowa ya kama gabansa.

Tun daga lokacin ko a wani hali suka haɗu babu wanda ya damu da ɗan'uwansa.

Ashraf ya so gayawa Zulfa abinda mijinta yake, amma idon Zulfa rufe yake da rashin son ganin laifin Tahir.

Da ya fara mata tambayoyi akan Tahir sai ta fara defending ɗinsa tana ɗaga jijiyar wuya wai ya dena sakawa mijinta ido.

Wani lokaci ya kan yi tunanin Zulfa ta san komai bata so a faɗa ne kawai.

Idan zai kira abinda Mom ke wa Dad da biyayyar aure to Zulfa kusan cewa zai yi bautawa Tahir take.

Ba zata iya ɗaga ƙafa ba tareda tayi hakan da neman yardar Tahir ba.

Shi akwai wanda ya taɓa ce masa ma wai Tahir yana da mata a garinsu amma bai maida hankali akan maganar ba dan shi a wajensa da ƙara aure da matan da Tahir ke nema a waje duk ɗaya ne.

A wajensa babu komai a cikin aure sai sex da kuma takura.

In dai zai samu a waje mi zai sa shi takura kansa da zama da mace ɗaya kuna zaune kuna takurawa juna babu farin ciki.

Shi kam babu macen da zai aura da zata hana shi jin daɗi a lokacin da yake so.

He's still young and wants to explore more about his sexual pleasure.


"Ashraf"

Muryan Mom ya katse masa tunani.

"Mom" ya kira sunanta ganinta tsaye a cikin ɗakinsa.

Bai san ya shagala haka ba, har ta shigo bai ji motsinta ba.

"How's work?"

"At least akwai 'yanmata dayawa a ƙarƙashina. Young fine corpers"

Yai maganar yana dariyan shaƙiyanci.

"Ashraf bana son iskanci"

"Mom it's an upgrade ai"

Zama tayi a bakin gado sannan ta nuna masa gefenta ya zauna.

Yana zama ta kama hannunsa ɗaya. "See, jiya Dad ɗinka ya faɗa mini plans ɗinsa. Ashraf ina gaya maka ne saboda ka san yadda zaka gyara halayenka. Wannan chanjin temporary ne fa, just for 6 months"

"Miye plan ɗinsa?"

Ganin ta samu hankalinsa yasa ta kamo hannunsa duka biyu.

"Habibi you know i love you right?"

yai murmushin gefen baki "Mom kenan"

"Ina so ka sani cewa your Dad loves you too. Duk abinda yake saboda kai ne"

"Haka kike faɗa duk lokacin da Dad ya dake ni. Mom ni na riga na haƙura da soyayyar Dad cause i'm not getting it any time soon"

"Look at me"

Ta shafa gefen fiskarsa. "Your Dad loves you"

"Mom ki faɗi abinda ya kawo ki kawai bana son motivational quotes. Ina son fita ne ma yanzu"

"Dad ɗinka yana so yai retire"

Ashraf ya waro ido yana jiran ƙarin bayani.

"Yace mini in dai ka gyara halayenka kuma ka yi aiki na wata shida ba tareda ƙorafi ba zai mai da kai matsayinka na da AND..."

Mom tayi shiru tana murmushi ganin hankalin Ashraf gaba ɗaya ya dawo kanta, wani nitsuwar da bata saba gani a tattare da shi ba yayi.

"And what?"

" Idan ka gyara kurakurenka kuma ka yi aure kafin shekaran da zamu shiga ya ƙare which i promise him you would. Yace zai bar maka komai"

"Komai?"

"Yes Habibi. WALI GROUP zai dawo hannunka. Ba CEO ba you will become the Chairman of the company komai zai dawo ƙarƙashin ikonka"

"Dad yana da cancer ne?"

"cancer kuma?"

"To idan ba ƙanshin mutuwa Dad ya ji ba taya zai barwa ASHRAF kamfaninsa. Ko dai akwai wani Ashraf ɗinne da ban sani ba"

" don't be silly Ashraf. Dad ɗinka bashi da cancer. Yana so yai retire ne daga aikin komai. Zamu koma Kano da zama, he wants to focus on charity work, tallafawa marayu and all that"

Ashraf yai shiru yana tunani.

"So my son. Kayi amfani da wannan damar ka yi abinda zai faranta wa Dad ɗinka rai. Kafin wata shidan nan ma su ƙare zaka iya ce masa zaka yi aure. Who knows kafin lokacin daya ƙayyade zai iya bar maka komai. Just be serious with your life Ashraf.

"Do it for me ka ji?"

Wani ƙyalli ne a idon Ashraf. Abubuwa yake hasasowa kansa wanda zai yi idan aka ce Dad ya bar masa komai ya koma Kano da zama gaba ɗaya.

It means gidan nan zai koma mallakinsa shi kaɗai. Babu mai saka masa ƙa'idar lokacin da zai fita daga gida da kuma lokacin da zai shigo.

It means maimakon kuɗi da yake kashewa a hotels da guest house zai iya kawo 'yanmatansa cikin gidan nan.

It means zai iya siyan motan da yake so ba tareda Dad ya mishi ƙorafin almabazzaranci ba.

Akwai abubuwa dayawa da zai yi idan Dad ya koma Kano ya dena saka masa ido a rayuwarsa.

"Habibi zaka kiyaye duka dokokin Dad ɗinka ko. Banda dawowan daren nan ka ji, and please ka dinga tashi da wuri kuna fita sallar Asuba tare"

Ita duk damuwarta bata so Ashraf ya rasa kamfanin Dad ɗinsa ne.

She was in constant fear na cewa idan aka cire Ashraf a CEO wani zai ƙwace masa kamfanin mahaifinsa.

Bata so abinda ya faru da nata dukiyar bayan rasuwan mahaifinta ya faru da Ashraf.

Shiyasa bata yarda da irin soyayyar da Dad ke nunawa Umar ba. Dan kada aje watarana ya bashi matsayin Ashraf.

Wancan Tahir ɗin kuma tun abinda ya faru shekarar da ta wuce data je gidansu ta cire rai da lamarinsa. Bashi da wata daraja a idanunta sama da cewa shi ɗin mijin Zulfa ne.

Dake tun lokacin da Dad ya fara jinya ta ajiye aikinta bata sake neman wani aiki ba.

She's a full time housewife tana nan kusa da mijinta.

Tana dai cikin board of trustees na Wali group amma ba wai fita take ta je aiki ba.

Da chan ta taɓa gwada kasuwanci amma abin bai ɗore ba. Manager data danƙawa kasuwancin ya kashe mata shago ya cinye kuɗi ya gudu.

Bata da zuciyar kasuwanci dama dai Hajiya Halima ce ta convincing ɗinta har ta buɗe wajen.

"Ashraf baka ce komai ba?"

Ashraf yai murmushi irin murmushin da ke bayyana ainihin kyansa.

Wani motivational quote ne ya zo masa rai FAKE IT TILL YOU MAKE IT.

Tabbas zai bi Dad a hankali har ya samu abinda yake so.

Infact daga yau idan ya je office ba zai dinga tashi da wuri ba zai tsaya yai aiki yadda ya kamata.

"Ashraf ba ka jina ne? Say something"

Miƙewa yai tsaye yana murmushi.

"Ashraf" Mom ta bishi da ido tana tunanin lafiyansa ƙalau kuwa.

Manna mata peck yayi a goshi yace "barin je na gaida Dad"

Ya fice daga ɗakin da sauri...

***

Zulfa ce kwance akan gado. Sanyi take ji duk da kuwa AC ɗin ɗakin a kashe yake.

Tsoro take ji kar hasashenta ya zamo gaskiya. Ta kasa zuwa ma ta siyo PT strip ta gwada ta gani.

Tahir yace baya son yara dayawa. Itama bata son haihuwan saboda shape ɗinta.

Throughout lokacin data ke ɗauke da cikin Tahir wani ƙiba ta haɗa tayi muni sosai. Fiskarta ba abinda bata shafa masa ba amma pimples ɗin da suka feso mata suka ƙi mutuwa. Sai sun lafa sai su dawo.

Maganin pimples data yi amfani da su alokacin idan zata tara su waje guda zasu iya cika babban bokitin roban fenti.

Lokacin da zata haihu CS aka mata, ita ta zaɓi hakan wai tana tsoron kar ta yage taji ana cewa ana iya yagewa a wajen haihuwa.

Bayan haihuwan Tahlil ta fara yin planning. Yaro ɗaya ya isheta tunda Tahir yace baya son yara sama da biyu.

Ta sake ƙudundunuwa cikin bargo tana ƙara lissafta kwana nawa kenan bata ga al'adarta ba.

Duk ta inda ta lissafta sai ta ga kwana shauku ne.

"Allah kasa ba ciki bane"

Tana cikin haka Tahir ya shigo ɗakin.

Kwana biyun nan yana sake mata fiska sosai saboda ya samu abinda yake so.

Wani lokaci idan yai dare ta tambaye shi sai yace mata bata san yanzu shine CEO ba. Meetings yake yi.

Dududu sati biyu kenan fa da aka bashi matsayin.

"Meya faru kike kwance?"

"Bana jin daɗi ne"

"To kije Asibiti mana"

Ta ɗan miƙe zaune tace " zan je"

"Yawwa ina so ki dafa abinci da yamman nan zan hosting baƙi. Official dinner ne dan haka ki dafa abubuwa masu daɗi"

Ba yau ta saba irin girkin ba ta san irin abinda yake nufi.

A yadda bata jin ƙarfin jikintan nan ba ƙaramin wahala zata sha ba.

Tahir baya son 'yar aiki shiyasa har yau ita take komai na gidan.

Da farko hakan yayi mata daɗi. Su biyu abinsu zata shiga kitchen ta masa girki kala-kala.

A hankali kuma sai ya zamo ba girkin bane matsalar lokacin da za a yi girkin ne matsalar.

Zata iya gama wahala ta dafa abinci idan yazo yace ba shi zai ci ba kaza zai ci. Kuma juyin duniyan nan idan tayi ba zai ci abinda ta girka ba sai dai ta girka masa abinda yake so.

Wani lokaci fa shi da kansa zai bugo yace ta dafa masa kaza idan ya dawo kuma yace ya fasa.

Haka kawai suna barci idan ya ji yunwa zai iya tashinta yace taje ta masa girki.

Wani lokaci idan tayi tuwo da dare ba zai ci ba sai da Asuba yace mata tuwo zai ci da safe.

Tahir baya cin ɗumame dan haka sabon tuwo za a masa da sassafe.

Sannan shi ba a girki a ajiye masa a cooler ya jima. Irin kiyi girkin dare tun da rana ɗin nan ki zuba a cooler.

At first it was fun. Tana yin komai cike da soyayya da alfahari. Har a ƙawayenta zaka ji tana faɗin 'ai Tahir baya cin ɗumame, Tahir baya cin abincin daya jima a cooler, Tahir baya son a zuba masa ruwan shayi a flask ya fi so daga kettle sai kofi'

Then ta haihu ta fara reno Tahir bai dena yin silly demands ɗinsa ba.

Abinda take yi da cike da farin ciki sai ya koma tana yi ne saboda gudun ɓacin ran Tahir.

On some days ma zai iya ce mata ba zai ci abinci ba kafin ya fita aiki sai ta shantake tayi girkin da zata ci ita da Tahlil sai ya dawo yace mata ina abincinsa.

Tun farko bata taɓa ƙorafi ba wannan yasa abinda yake ya bi mata jiki. Courage ɗin da zata yi amfani da shi ta furta masa magana tace masa bata son abinda yake shi take ɗauka ta shiga kitchen ta masa abinda yake so a lokacin da yake so dan ta faranta masa rai.

"Ya na ga kina wani ɓata rai"

"Tahir dan Allah kayi haƙuri na yi order abinci wallahi hajijiya nake ji"

"Na taɓa cewa ki min order abinci a gidan nan?"

"Amma Tahir ..."

Ɗaga mata hannu yayi.

"Kar ki fara yau. Baƙina zasu zo around 8pm ki tabbatar kin shirya komai"

Har ya kai ƙofa ya juyo yace " don't disappoint me Zulfa. Kin san halina"



***


A nan muka kawo ƙarshen free pages.




©AzizatHamza2023













Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.