Free chapter · Read without an account
Eight
TSINTUWA
Top-notch 2023
Ayshatuuu
Eight
*Ta_kwalam is a home for jewelry, your best jewelry plug and introducing my Bridal accessories rent! For me a wedding is a one day celebration, for you to buy lots of costly stuff and after the wedding sun tashi a aiki! A saukake na kawo muku inda zakiyi renting kayan amare kuyi kyau, a kudi kalilan ki kece raini kawata, sannan ki Gama ki dawo dashi. You don't need to buy much. I'm a DM away!*
Allah shi ne Allah, idan baka bautawa Allah ba wa zaka bautawa Hidaya? Ki kalli matsayi na yanzun sannan ki tuna rayuwa ta ta baya, ai kinsan ba mutum ke daukaka ba Allah ne, idan mutum ne ai ni dai da tuni Ina labari, ko ni ban taba tunanin hakan zata kasance ba Amma shi Ina ruwan Allah, ya daukaki Wanda baka taba tunani ba, ni dai na Zama misali sede nace subhannallah! Alhamdulillah!
A Haka dai roughly se da mukai watanni biyu, ko zancen makaranta ma ba nayi, buri na Naga Inna ta samu sauki Amma to kullum jiya iyau, tari take da gudawa, cikin watanni biyu ta kankance har abin na bani mamaki. Ranar na samu Baba laure nace Ina son Zan Kai Inna ta asibiti, tace min da wanne kudin? Nace Mata ai na Tara kudin wanki da nake yiwa Yan kusa damu, se washegari tace kada na fito to Mike asibiti idan da wani Abu na fada mata, da kyar na samu abun hawa Muka je asibiti, tana kwance se hawaye yake bin kuncin ta se ta rike hannu na ta matsa, ni Kuma nace
" Sannu Inna! Zaki tashi!"
A Haka muka je aka karbe mu, gwajin farko aka ce Mana tana dauke da kanjamau, nasan abin ki ne a wannan lokacin Amma bansan menene ita din ba, ta dubi likitan a hankali muryar ta Bata fita sosae tace
" Na sani ka gwada min Yata Amma nasan ni mutuwa zanyi!"
Yana ta Bata Baki kafin akai min gwaji ya nuna bani da matsalar komai, ta rungume ni sede gwajin tarin mu ya nuna dukka muna dauke da tari fuka wato TB shiyasa nake ta rama kenan, nake wani irin gumi cikin dare, a lokacin aka daura mu Kan magani Amma ita Inna seda aka kwantar da ita. Da daddare Ina gefen ta nace
" Inna menene kanjamau?"
Ta girgiza Kai alamar Bata sani ba Amma tasan a gurin Baba ta samu, ta Jima da Sanin Yana da ita, Ashe ta Kai shi asibiti lokacin da yayi wannan jinyar Kuma yaki karbar magani Wai Karya ake Masa, to Bai karba ba ta Ina ita zata karba? Ai ba zata Fara ba duk abin ta. Haka ta dawo gida kullum a tsorace take musamman tasan tunda yana da ita to tabbas tana da ita itama! Nayi ta kallon Inna Ina ayyana irin hakurin da tayi a duniya da Babu makamancin shi, ta kalle ni tayi murmurshi tace
" Kiyi hakuri da rayuwa Uwata! Kiyi hakuri ki karba rayuwa a yadda tazo Miki!"
Na gyada Kai na, a lokacin ba wani fahimtar abin da take fada nake ba, Haka dai washegari tayi da safe Sega Baba Laure tazo duba mu, bansan waye ya guntsa Mata ciwon da yake damun Inna ta ba ai se Taki shigowa, daga nesa Muka gaisa ta aje masar da ta kawo ta juya, nayi ta tunanin dalili Amma na dauka kawai na Kai Mata ta ci aka Bata magani se bacci! Na samu maaikaciyar na tambaye ta menene kanjamau
" Kanjamau cuta ce me karya garkuwar jiki wato HIV, acronym ne na human immunodeficiency syndrome, an same ta a wata shekara a jikin wata yarinya a jihar Lagos. Cuta ce da take Kama sojojin jiki ta kassara su, har yanzun masana na bincike Akan magunguna da Kuma yiwuwar samun waraka!"
Na ja numfashi nace
" Ya ake samun ta?"
Tace
" Ta hanyoyi guda uku kacal, sexual intercourse, sharing of sharps ko Karin jinin me dauke da ita, uwa ta bawa Dan ta wajen haihuwa, a ciki ko Kuma shayarwa! Amma bayan nan Babu wata hanya Kuma, zaku iya kiss, hugs, sharing spoons da soson wanka..."
Ta yimin comprehensive bayani Wanda yasa na fahimta, na tambaye ta me yasa mutane suke gudun masu ita, tace saboda Basu da ilimi akan ta suna ganin ko taba mutum su Kai zasu kamu, sannan mutane hanyar da Suka fi sani ta kamuwa da ita shi ne intercourse, to hakan ya kazanta wannan shi ne dalili. A takaice Inna kwana biyu ta kara and she kicked the bucket! Ya rabbu kadan ne ban haukace ba, nayi kuka kamar Zan fitar da Rai na, na matsa gadon ta inda aka lullube ta da fallen zanin jikin ta, naje ne kawai na siyo pap da zata Sha kawai se na taho, matar kusa da gadon da muke tace nayi sauri naje ana nemana, Haka naji zuciya ta tayi wani irin bugawa, kamar anzare min lakahaka naji, jiki a mace na nufi ward din, tunda na doso wajen ward din Naga kowa yayi tsuru Yana kallo na, gaba na ya sake faduwa I was so scared to go in, Haka na karaso kofar, dama location bed din daga entrance kana hango gadon, a nan na hango ta a lullube ta da wannan fallen zanin, wani Abu naji Yana bin kafafuna, se naji mutanen gurin na fadin fitsari take, a take pap din hannu na ya Fadi ledar ta fashe ya fantsalar ma mutanen gurin dani ma dake tsaye, naja wani numfashi, se amai, a take na fara kwara shi a wajen ta hanci ta Baki, tun daga wannan ranar shikenan in dai Ina cikin tashin hankali ta amai ake ganewa, suka rike ni Amma na fuzge na nufi gadon na yaye ta, ita din ce a kwance yadda ta sake kankancewa, na lumshe idanuna se kuka, na rike hannun ta da aka riga a kulle da tourniquet, kuka nake Ina goga Kai na a cikin ta, I was hoping tayi tari, I was hoping ta shigo tace min Bata mutu ba, I was hoping na samu cutar Nima na mutu! Ina zani? Wa nake dashi? Wa na sani?..."
Se na tsagaita na dubi Hidaya da take wani irin kuka hannun ta cikin nawa, ni bana kuka saboda na riga nayi kukan ya Isa haka, sede wanann naughty lump din Dake zuwa idan irin Haka ta faru, na dauki ruwa na Sha Dan na kora shi Amma Yana nan a tsaya. Na dube ta kuka take sosae na Ciro tissue daga cikin box na Mika Mata Ina Mata murmurshi me ciwo nace
" Haba Mana tun yanzun?"
Ta Kara rike hannu na tace
" You've went through a lot Adda, ko iya nan aka tsaya you're a good fighter!"
Nayi murmurshi kawai tare da yin shiru seda tayi shiru kafin nace
"Seda suka saka na nutsu kafin Suka fara tambayar inda Yan uwana suke Dan kowa yasan ni daya nake jinyar Inna ta, Dan wasu Yar albarka suke ce min, na fada musu Babu kowa Haka dai aka binne ta da wakilcin shugabannin asibiti hade da Kiran Yan sanda suka yadda, bayan an binne ta na dawo na kwashe kayan da Suka rage na fita Ina kallon hanya ba tare da Sanin inda zanje ba, ko na koma yamaltu deba na ayyana Amma ba Zan iya ba wannan tsaf zasu kashe ni, se na Yankee shawarar komawa can wajen Baba Laure, lokacin da na Isa kangon na samu dare har yayi, na Shiga ko digon tsoro bana ji a cikin zuciya ta Haka na shiga na kwanta na dinga kuka Ina hangen katakon da nake Mata shimfida Babu se ni daya, nayi kuka har cikin dare sannan na fara addua saboda Inna tunda ta Fara jinya take ce min na dinga addua na Kuma sani Allah na tare Dani a duk inda nake, wannan sun kasance words din ta, dukda ba ta da ilimi duba da wancan lokacin ba lallai ake maida hankali Akan girl child education both Western and religious knowledge Amma dai tana da ibada ina koya mata abubuwan da na koya Nima. Haka wannan Daren ya wuce, dare na farko da bacci Bai dauke ni ba, ki tuna shekaru na gaba daya ko Sha biyu Basu Kai ba. Washegari da wurwuri nayi sallah se lokacin naji Ina jin yunwa ku San kwana biyu ban ci abin kirki ba, na fito zuwa inda Baba Laure ke siya, na share gurin na gyara tsaf na zauna can gefe Ina jiran fitowa, Baki daya ciki na kugi yake na yunwa, na koma can tunanin Inna ta, Ina Yi hawaye Yana Kara sauka min a hankali, a Haka Baba Laure ta karaso, nayi saurin mikewa Dan karbar kayan hannun ta Amma ta tsaya tace
" Ke annoba Maza Maza bar gurinnan, kafin ma mutane suzo kowa yasan kanjamau kike da ita"
Na Fara kuka Dan shi kadai ne hope di na a wannan lokacin, na Fara kuka Ina rokon ta nace
" Baba Dan Allah bani da gurin zuwa"
Matar nan ta kore ni Amma se naje can na tsaya Ina kakarin amai, Babu komai a cikin, a Haka mutanen Suka Fara isowa nan suka Kore ni da Kara nayi ta gudu Dan tsira da Rai na, nayi kuka. A kalla nayi watagaririya na wajen kwana biyu, na Sha ruwa se guava ta bishiya, nayi mamakin energy da nake samu kafin kwana uku ya cika na fita kammani na, na kode, na rame na Kuma sake baki, idanuna sun Kara sake fitowa kamar na mujiya! Da daddare idan mutane Suka kwanta Haka Zan lallaba kangon na kwanta, asuba nayi na fita Amma ban samu me imanin da zai kula ni ba. A kwana na biyar na Kai karshen hakuri, a lokacin astagfurilla gani nake Allah ya manta dani hakan yasa na tafi titi na tsaya a tsakiya Dan kawai motar ta buge ni na mutu na huta, Ina ganin Babu wani afuwa a wannan rayuwar! Na runtse idanu na tare da rufe kunnuwa na da tafin hannu na Wai kar ma naji honk na tsorata, se ki nayi an dauke ni daga titin nayi gefe, na bude idanu na zuciya ta Banda wani mugun bugu Babu abinda take, mutane Naga a kaina suna fadin
" Tana motsi!"
Na bude idanu na, na samu an taru a kaina, na Mike da muguk karfi nayi titi aka sake rike ni, zaku ce da gaske Ina da aljanu, ana rirrike ni Ina ihu Ina fadin
" Ku bari na mutu, ku sake ni! Lemme die please!”
A lokacin gani nake bani da amfanin zama a duniya, gani nake mutuwa ce kadai Jin Dadi na. Wani mutumi da ko fuskar shi ban kalla ba ya tambayi abinda ya faru aka fada Masa duk abinda Suka sani sannan yace zai tafi Dani, aka saka ni cikin mota ya tafi dani, Bai min magana ba har Muka fita daga gari muka shigo wani babban gari, a lokacin ban ki ace yanke Kai na zaiyi ba, ko yayi amfani da ni for ritual ban damu ba as far as Zan samu solace to shikenan!
A Haka bacci me nauyin gaske ya dauke ni bansan doguwar tafiyar da mukai ba se tashi nayi Naga wani gida me kyau yayi parking! Naji faduwar gaba ya dube ni yace
" Meye sunan ki yarinya ta?"
Nace
" Nafisa!"
Yace
" Muje ciki!"
Na fito na bi bayan shi zuwa cikin gidan se kalle kalle nake, Muna shiga wani ubansun parlor na tarar da wata yarinya Bata wuce saa ta ba zaune Kan wheel chair, tana ta murmurshi tana fadin
" Abba oyoyo!"
Ya nufe ta ya rungume yace
" My Baby! Ina Mamaa?”
Ta dubi wata kofa a rufe tace Masa tana ciki, ya dube ni Ina tsaye a takure ya kwalla Kiran wata Christian girl yace ta Kai ni ta bani abinci nayi wanka sannan ta bani Kaya nasa, ta Kan wheelchair din tace
" Abba who's she?"
Ya dube ni lokacin da nake bin ta yace
" You wanted a sister right? I got you one!"
Wani ihu tayi ta Fara fadin
" Thank you Abba! Sister sannu da zuwa!"
Na Dan juya na sakar Mata murmurshi muka shige ciki Dan nayi wanka!