Free chapter · Read without an account
Na sha shida
*ƘADDARATA CE A HAKA*
©Maryam Abdulaziz_Maiƙosai(Matar Abdul)
P_16
Zaune suke Abban Ahmad, iyayen Hamza, Ummi, Gwaggwo, Munira, Inna da kuma Nuriyya.
Nasir ya ja wani numfashi kafin ya kai duban shi garesu ya furta, “Ummi ban taba tunani ko zatan zan sake rayuwa ba a nan gaba, sanda jirginmu ya kama da wuta ban san yadda aka yi na fice daga ciki ba, ni dai na ji tamkar an hantsila ni wani wajen daga nan kuma ban san me ya sake faruwa ba, hakazalika ba musan mene ne masomin kamawarsa da wutar ba, mun dai ji wani abu ya ce duum sai kuma jirgin ya kama da wuta. Tun da na bar jirgin ban san a ina nake ba, Kadawar iskar wajence ta farkar da ni da kyar na samu na yi salla sai kuma na sake bingirewa da bacci, kukan namun daji ne suka tashe ni domin kukansu na dinga ji tamkar a cikin baccina, ashe wani kasurgurmin daji na fado, ina bude idanuna na yi tozali da namun dajin nan sun kewayeni kiris ya rage su afka mini su yi yaga-yaga da naman jikina su taune ƙasusuwan. Addu’a na shiga yi ba ji babu gani, duk wacca ta zo mini bakina kuwa kawai furtata nake yi, cikin zafin nama na daka tsalle na bar tsakiyarsu na kwasa a guje, ban san adadin iya gudun da na yi ba, na iske wani kogo na shige cikinsa, sai da na shafe kwana biyu a cikinsa sai dai na fito na sha ruwa na koma, na dinga tunanin yaya za ayi na dawo gida gareku? Ta yaya zan zan sami abin sadarwa? Na fito na shiga tattakawa ban san inda na sake shigaba, domin yunwa ta sa bana gane komai tsananin galabaitar da ni da ta yi, tafiya kawai nake yi har Allah ya sa na bar dajin sai na iskeni bakin wata korama, na dinga watsawa kaina ruwa domin wahala da zafin ranar da na kwaso, babu abin da nake sakawa cikina sai ganye da ruwa duk kuwa da raunukan da suke jikina bana jin zafinsu kamar yanzu har kawo lokacin da Allah ya jefo mini su Hamza, abin mamaki da ya riske ni kuwa shi ne lokacin da nake ni daya sai Allah ya ara mini lafiya da dauriya amma lokacin da na yi tozali da su Hamza sai kawai na ji numfashina na neman sɓucewa daga jikina, na soma jansa da kyar inaa kokawa da shi. Babu abin da zance muku sai dai Allah ya saka mukun da gidan aljnna.”
Kowa na ya yi tsit tamkar an ci shirwa, kallonsa kawai suke yi cike da tausaya masa halin da ya tsinci kansa ciki, nan aka soma tofa albarkacin baki, Ummi da Nuriyya kuwa na sake godewa Allah da ya raya musu shi har ya sa aka gano inda yake.
***
Nasir ya soma samun sauki sosai, duk aikin da aka yi mishi kuwa an yi shi cikin nasara ya yi kyau matuka. Yanzu watan shi guda da sati biyu a asibitin ya soma murmurewa har kuzarinsa ya soma dawo wa.
Ranar Asabar ta dawo daga wajen Baffanta ta wuce izuwa asuibiti, domin kwana biyu ba ta leka wajen Baffan ba. Tana shiga wata abokiyar aikinsu Nasir din na yiwa Nuriyyan sallama gami da sake yi mata ya me jiki? Hira suke yi sosai da Nasir din nata Nusy ta kunno kai dakin, cikin hanzari ta yo kan Nasir tana wani lankwashe jiki tamkar tana cikin makale murya ta soma gaida shi gami da yi masa sannu da jiki.
“Sorry yaya Nasir ba na gari time din da abin ya faru, abin da ya sa na makara wajen zuwa dubaka kenan.”
“Babu komai Nusaiba hakan ma na gode.”
Ta dan turo baki gaba kafin ta kai ga cewa, “Ni fa yaya Nasir na jima da shaida maka ba suna na Nusaiba ba, Nusy shi ne suna nan.”
Ya yi dan guntun murmushi kafin ya kai ga cewa, “Ai Nusaiba shi ne asalin sunan kuma suna mai dadi da ma’ana, matar da ta yi yaki da gwagwarmaya kan addinin musulunci.”
Ta kawar da zancen ta hanyar furta, “Yaya Nasir me wannan take yi? Alhalin Ummi ta ce ka rabu da ita ko ka manta ne?”
Ta karashe maganar tana jefawa Nuriyya wani kaskantaccen kallo.
Nasir ya kalli fuskar Nuriyya ya ga ta haye ta kumbura kiris ya rage ta fashe ya saki siririn murmushi kafin ya kai ga dubansa ga Nusaiba kana ya ce, “Matata ce, an daura mana aure da ita, da kuma sahalewar ita Ummin.”
Maiƙosai✍🏼