Free chapter · Read without an account
Chapter 14
*💮DUK KYAN NAMIJI💮*
............. ....👳.... ..............
0️⃣1️⃣4️⃣
Ba ƙaramin jin daɗin program ɗin Lubna ta yi ba. Ta ƙaru da abubuwa sosai. Tare su ka zauna da Hood wanda lokaci zuwa lokaci ta ke satan kallon shi. Lokacin da aka fara Q&A session da Hood ya tashi ya na gabatar da tambaya haka Lubna ta buɗe ido, baki da kunnuwa duk ta na kallon shi. She was amazed with how he speak with full confidence. Duk da dai turancin sa cike ta ke da intonation irin ta Malam Bahaushe amma kuma ba ƙaramin burgeta ya yi ba. Iya saninta da shi ta gane quality na confidence da courage a jininsa ya ke. Shi mutum ne da zai iya shiga ko ina ya representing kan sa. He can say anything anywhere without fear.
Da aka gama program ɗin aka tsaya aka yi hotuna wanda duk wani hoto da aka yi Lubna ba ta bar gefen Hood ba. In every picture da su ka yi ta na tsaye gefen sa smiling. Ƙarfe biyu aka gama taron. Sai da su ka fito daga Chartwell hotel inda aka yi taron Hood ya ce "Lulu ki hau keke ni zan wuce masallaci daga nan kuma zan je shago"
Ta riƙe hannun machine ɗin ta ce "kai ka kawo ni dan haka kai za ka mayar da ni"
"Lokaci ya ƙure Lulu"
" Lubna Hussain" muryan wani saurayi ya ankarar da su. Lubna ta juya ta ga saurayin nan da nan ta gane shi. "Nnnnnura, ya ka ke?"
Saurayin ya ƙaraso ya na faɗin " ai tun a ciki na ganki ina tunanin kaman ke kaman ba ke ba"
Ta yi murmushi ta ce "longest tttttime, Nura ka na ina haka?"
"ABU"
"Wow, Best of luck"
"Lulu hau mu tafi" Hood ya faɗa ya na kallon ta, ba za ta iya gane expression na fiskarsa ba amma kuma kamar akwai slight anger a tattare da shi.
Sai da su ka exchanging contacts sannan ta hau machine ɗin ...
Sai da su ka yi nisa da wajen sannan Hood ya ce " bayan na ce ki zo mu tafi shi ne har da tsayawa karɓan number, irin ga driver ɗin ki ko?"
"Classmate ɗi na ne, tun da mmmmmuka gama secondary school rabona ddda shi"
"And so? Idan ya na son ganin ki all this while, sai ya nemi gidan ku ai"
"I'm sorry" ta faɗi a hankali.
The only thing da ya banbantata da 'yan matan da ya taɓa mu'amala da su kenan "sorry". Babu randa za su haɗu da ba za ta faɗi kalmar nan ba. Yayinda wasu ke ganin kalmar da girma ita a wajen ta ba ta ɗauke shi komai ba. Ko lokacin da ya ke ma ta aikin project ma idan ta yi ba dai-dai ba ya fara faɗa da sauri za ta fara faɗin " i'm sorry" and that's the end of the argument.
Har su ka iso gida ba wanda ya sake magana. Da ta sauka ta ce ma sa" Thank you" za ta wuce ya ce " Lulu fishi ki ke dani?"
Ta girgiza kai.
" shi ne za ki tafi ba sallama"
"Ka gaida su Umma" ta faɗi a taƙaice.
"Zo ki ga wani abu" ya faɗi ya na lalubo wayar sa a aljihu.
Ta matso kusa da shi. Ya fara binciko hotuna a wayar. Sai da ya zo kan wani hoto ya nuna ma ta.
Ido ta zaro ganin hoton dan ba ta san an ɗauka ba. Ta kai lomar abinci aka ɗauki hoton.
"God! Hood, plz delete this pic"
"A kan me? Ni da waya ta"
"I look awkward fa"
"Ke ba ki san hoton da aka ɗauka bazata ya fi kyau ba ne"
"Ni kan ka goge" ta faɗi tana tura baki.
"Ai ba shi kaɗai ba ne yarinya. Sun kai goma na ɗauka"
Ta fara ƙoƙarin ƙwace wayan a hannun sa.
"Lulu wait.... wait..wait.... za ki sa na faɗi fa..."
Piit piit piit... horn ɗin mota ya katse su.
Hood ya ja machine ɗin sa yayinda Motar ta shige gidan bayan an buɗe gate ɗin.
Sai da motar ta shige sannan Hood ya ce " Lulu barinje Sallah lokaci ya ƙure"
"Ni kam sai ka goge hoton na gani"
"Kar ki damu zan goge amma sai na nunawa Umma, ta ga yadda 'yarta ke lomar shinkafa"
"Allah ni kam bbbbban yarda ba" ta faɗi kamar za ta yi kuka.
"Ok ok zan goge, but on one condition"
" what?"
"Duk lokacin da za ki fita, ki dinga rufe gashin ki da kyau"
Ta yi saurin gyara gyalen ta saboda ya ɗan ja baya kaɗan gashinta ya ɗan fito.
"Na gyara" ta faɗi ta na kallon sa.
"Thats good Lulu"
Yai murmushi sannan ya ja machine ɗin sa ya tafi.
Gaba ɗaya daskarewa ta yi a wajen ta na kallon sa har yai nisa ta ka sa motsawa. His smile was different. It was so real. Akwai farin ciki a tattare da shi. Murmushin sa ya tafi da ita completely.
Shi kanshi Hood yana tafe ne cikin nishaɗi. Tun da ya ke zuwa wajen Nafy bai taɓa samun kan sa cikin farin ciki haka ba but with Lubna everything is different...
.....................
Sai da ta dena ganin alamar sa sannan ta shige gida. Kai tsaye ɗakin su ta wuce ganin sallaya a shimfiɗe ta san Mama ta dawo. Ta cire gyalen ta da takalmi ta faɗa kan gado tana tuna abubuwan da ya faru. It's like duk maganganun Hood da ya gaya ma ta yau, ƙwaƙwalwarta saving ta ke exactly how he said it. Sai murmushi ta ke, ita kan ta ba ta san dalilin farin cikin ta ba. Ƙwanƙwasa ƙofa da aka fara yi ya fargar da ita.
"Yes come in" ta faɗi tareda tashi zaune. Abdallah ne ya shigo ɗakin fiskar sa ɗauke da ɓacin rai.
"Good afternoon Ya Abdallah" bai amsa ba ya ja kujera har gabanta ya zauna su na kallon juna.
"Kar ki munafurceni Lubna, tell me the truth"
Kallon mamaki ta ke ma sa. Yai ajiyar zuciya saboda haushin tambayar da zai yi ya ke, ya ce
"Lubna, soyayya ku ke da Hudu?"
"My God! Ya Abdallah i told you already. Hood is just my friend"
" just friend shi ne ki ke ƙoƙarin kama hannunsa ɗazu. I saw everything"
"It wasnt what you are thinking i was just trying to..."
"Trying to make him happy? Duk abinda ya ke faruwa Lubna ina sane. Hatta kayan da ki ka kai gidan su duk na sani. Idan mace ta fara nuna damuwa akan namiji alamomine na so...."
Ta ma rasa amsar da za ta bashi da zai yi ma ta dai-dai. Cikin faɗan da ya ke yi ne ya sake jefo ma ta tambaya "Lubna kin fara son Hudu ne?"
"Yes" ta faɗi da ɗan ƙarfi
"Yes kuma, Lubna dan Allah son shi ki ke?" Ya faɗi kamar zai yi kuka.
"Yes, i Like him. So what?"
"Lubna kin san mi ki ke faɗa kuwa?" Kafin ta bashi amsa Mama ta shigo ɗakin.
"Abdallah mi ya ke faruwa? Ya na ga dukkan ku kun yi zuru-zuru?"
Abdallah ya tashi ya fita ba tareda ya amsa ma ta ba.
Ta maida duban ta ga Lubna kawai ta ga hawaye a idon Lubnan.
"A'a Auta lafiya?" Ta ƙaraso tana jawota jikinta...
....................
Tunda ta tafi school ta maida hankalin ta ga karatu. Mama ta ba ta shawara akan ta dai na damuwa da maganar Abdallah ko Nafisa, rayuwan ta ne ta na da damar da za ta yi mu'amala da duk wanda ta ke so koda kuwa Hudu Carpenter ne. Ta tuna tambayar da Mama ta ma ta ranan *" to ke Lubna ki na son Hudun ne?"*
*"Nooo"* amsar da ta ba ta kenan.
Shi Hudun ma da aka bi aka dameta akan shi yana chan ya na sha'aninsa hankali kwance ko nemanta ba ya yi. Ta sake duba wayarta ko za ta ga kiranshi amma ba komai. Kwana biyar rabonta da shi kuma har yau bai kira ta ba. Umma ta kira ta ranan da su ka fara exams ta ma ta addu'ar sa'a amma shi ko text bai turo ba...
A gida chan murna da farin ciki a wajen Nafy kamar wanda aka ba ta license ɗin Aljannah. Suhail ne ya ce ta sanar a gida zai turo. Finally burinta ya kusa cika, wato auren mai kyau mai kuɗi kuma mai sunan gayu.
Hajiya ta gayawa ita kuma ta gayawa Alhaji. Alhaji ya ce zai kira Yayan sa su yi maganar. Washe gari Hajiya ta sake tuna ma sa saboda ta ga kamar baya haba-haba da maganar. A take ya kira Yayan sa ya ma sa maganar, shi kuma ya ce su zo wata sati. Zo ka ga yadda Nafy ta ke rawan shoki a tsakar gidan su...
Ganin maganar Nafy ya fara kankama ya sa Abdallah sa ke tuntuɓar Alhaji da maganar Lubna. Amsa ɗaya Alhajin ya bashi, idan Lubna ta ƙare exams ɗin ta ta dawo gida zai tambayeta ra'ayinta, idan ta amince da shi sai a haɗa bikin su da na Nafy. Hakan ya sa ya dage da kiran Lubna da aika ma ta text akan ta amince da shi. Sai dai ta ƙi, cewa ta ke " Hajiyar ka ba ta so, dan haka ka haƙura da ni"...
Saura kwana biyu 'yan uwan Suhail su zo Mama ta kira Nafy ɗakin ta. Tambayoyi ta fara ma ta akan Suhail ɗin sai dai irin amsoshin da Nafyn ke ba ta ya sa ta dakatar da tambayoyin ta.
"Nafisah kar ki ga kamar ina mi ki shishshigi a lamarinki. Yadda na ɗauki Lubna a matsayin 'yar da na haifa haka na ɗauke ki. Auren yanzu da ake yi saboda wasu ƙyale-ƙyale ba ɗaurewa ya ke yi ba. Ina so ki san waye Suhail ki yi ƙoƙarin fahimtar abubuwa dayawa a tareda shi kafin ki amince da zama matar sa. Idan saboda wani buri ko ƙudiri na son zuciya za ki aureshi ki gyara niyyar ki saboda zai iya zame mi ki matsala"
"Mama dan Allah mi ye aibin Suhail, kin sa ni a gaba tunɗazu kamar wani ɗan jagaliya na ce zan aura. An san asalin Suhail, ya yi karatu kuma aiki ma zai fara nan ba da jimawa ba. To mi kuma ake so?"
"Nafisa kenan, Allah ya shige ma na gaba amma ki dage da addu'a, ki yi istikhara akai saboda a irin wannan lokaci 'yan mata dayawa na tafka kuskure wanda daga baya za su zo su na da na sani"
"Addu'ar da na ke yi tuntuni shi ne Allah ya amsa min, ya kawomin irin mijin da na ke so. Mama ke dai ki dage da yiwa Lubna addu'a, ita tafi buƙatar addu'a a yanzu dan idan ba a dage ba Hudu Carpenter za ta kawo mi ki"
Maganar ta sa Mama murmushi ta ce " ai ba laifi ba ne idan ta kawo shin"
"Ku dai ku ka sani" Nafy ta faɗa tareda tashi ta bar wajen, yanzu jin kan ta ta ke a sama. Sai ma anzo bikin ta 'yan uwa da abokai da maƙota da 'yan gulma sun zo sun ga irin mijin da Allah ya bata abin kwatance ne...
'Yan uwan Suhail sun zo sun tambaya kuma an ba su inda su ka tafi da niyyar zuwa sati biyu ma su zuwa za su kawo sadaki. Yadda Hajiya da Nafy ke yiwa Mama habaici da ace tana sa abin a ranta da sai ta samu hawan jini. Tunda ta yiwa Alhaji maganar a binciki Suhail Hajiya Zainab ta sa ta a gaba. Nafy ma ba a barta a baya ba. Har da cewa wai Mama kishi ta ke dan Lubna ba ta da saurayi kamar Suhail. Yau da ta haifi ɗiya mace a gidan nan da yarinyar ta shiga uku. Ba ta haifa ba ma ansa 'yar rikon ta a gaba.
Duk da bincike sama-sama aka yi labari ya zo wa Alhaji akan kafin tafiyar Suhail Malaysia karatu ya na shaye-shaye. Sai dai da ya ke bai jima da dawowa ba ba za a tabbatar ko ya daina ko bai daina ba. Hakan ya sa Alhaji ya ce wa Nafy ta cewa Suhail ya na son ganin shi. Abinda ya ƙara tunzura Nafy da Hajiya kenan. Su ka sa Mama a gaba su na zaginta uwa na yi 'ya na tsaye ta na tinzirawa. Ko uffan Mama ba ta ce ba. Anty ne ma ta fito ta ke ta bada haƙuri. Daga ƙarshe Mama ta shige ɗaki ta bar su a wajen...
Irin cin mutuncin da aka yiwa Mama Ladidi ta kira Lubna ta gulmata ma ta wanda ran Lubnan ya ɓaci, sosai ta sake jin tsanar Hajiya a ran ta. Duk da gobe za ta ƙarasa jarabawar ta amma a hakan ta haƙura da karatu ta zo gida. Ko ba komai Mama na buƙatar ta a kusa.
Da yammacin ranan sai ga sallamar ta. Mama na aiki a kitchen ta shigo, da gudu ta zo ta rungume Mama ta baya ta ce"I miss you Mama nah"
"Lubna yanzu ke da gobe final exam na ki shi ne za ki zo gida"
"Na zo ki samin albarka ne" ta faɗi ta na murmushi.
Sai da su ka gama abinci su ka shiga ɗaki ta fara ba wa Mama hakuri akan abinda ya faru.
"Lah Lubna ai halin Hajiya Zainab ba sabo a ciki. Abu ne da shekara da shekaru tana yin sa kuma na saba da shi. Nafy 'yata ce dole ne kuma na ba ta shawara ko da kuwa ba za ta ɗauka ba"
"Mama kar ki damu a bikina ke za ki yi komai, you'll be the one to make all the decisions"
Mama ta yi dariya ta ce " bikin ki da Hudu Carpenter ko?"
"Ahhhhhhhh" Lubna ta sa ƙara yayinda Mama ta cigaba da dariya...
Duk yadda ta so ta kwana Mama ta hana, dole a daren ta koma bayan sallar Isha wanda Mama da kan ta ta maidata school ɗin...
Suhail da ya zo Alhaji ya ma sa tambayoyi na manya wanda daga ƙarshe tambayar duk ɗaya ce shin har yanzu ya na shaye-shaye? Suhail ya tabbatar ma sa ya riga ya watsar da ɗabi'an tun da daɗewa. Bayan ya tafi Alhaji ya kira Mama ya sanar da ita yadda su ka yi. Ta ce Allah ya kyauta dan yanzu ta yi alƙawarin tsuke bakin ta akan maganar Nafy.
Jin ba a fasa zancen kawo sadaki ba ya sa Nafy ta cigaba da farinciki ta na ƙiyasta sadakin da za a kawo a ranta...
Ranan graduation ɗin Lubna kusan du ka 'yan gidan sun je ma ta idan ka cire Hajiya da Nafy, har da Ladidi wadda ita ma ta ci kwalliya ta je aka yi ta hotuna da ita. Alhaji bai je ba saboda ɗaurin aure da ya je a Ningi.
Lubna na cikin hidiman graduation Hood ya kira ta. Hannun ta har rawa ya ke lokacin da za ta ɗau kiran.
"Congratulations Luluwa, ki na ina na zo na watsa mi ki ruwa?"
Fiskarta ɗauke da murmushi ta ce " ina cikin school"....
©AzizatHamza2020